MAI DAKI BOOK 1 HAUSA NOVELS BY SODANGI.docx

Author :  Hafsat C Sodangi Category :  KDP NOVELS

Chapter   5 / 7

12K to 15K   out of 19.3K words

karewa ba ne,

kuma na lura idan na ce zan zauna ina

85

kwana ido biyu saboda bacin ran da yake

sa ni to zan wahala ba kadan ba.

Kwana da kwanaki muna cikin wannan

hali ya mayar da wancani dakin na shi

nima kuina ga nawa.

Tsakanina da shi gaisuwa ce ta sate ta

dare kuwa bana ma sanin sanda yake

dawowa. Nayi iyakacin addu'o'in da zan

yi a kan hakan ban ga canji ba.

Gyaran daki nake yi lokacin da na sake

cin karo da littattafan Momi. Na bude

daya na fara karantawa. Wunin ranar bata

kare ba sai da na gama shi tas na dauko na

biyun shima haka.

Cikin kankanin lokaci sai na koma

wurin Momi neman kari. Kullum da safe

idan na gama aikina na gida sai na zauna

nayi ta karatuna bana tashi sai sallah ko

cin abinci.

Sai ya zamana na koyi abubuwa in-iri

wadanda wani bai taba zaunar da ni ya

koya mun ba.

86

Abubuwa da suka danganci zama da

miji, zama da mutane, girki, kuia da kai.

gyaran jiki, kai abubuwa daban-daban.

Idan nazo wani wajen naji takaici, wani

wajen nayi dariya, wani wajen naji tausay1,

wani wajen kuwa naji kamar labarina ake

bayarwa da' Ishaf.

Don haka ga abinda zan yi. Damuwata

tayi matukar raguwa, na kuma y1 niyyar

yin amfani da shawarwarin da Marubuta

suke bayarwa da suka danganci zama na

aure na kuma Zubar da na banza.

Tsawon sati biyun da muka yi a hakaa

muka yi ta da Ishak gaisuwar safe, dn uwa

da daddare kan ya dawo nayi barci.

Amma na kuduri aniyar gyaran aurena

don na fahimci ba haka ake auren ba.

Aure yana yin nasara ne idan har akwai

kyakkyawar alaka ta addini da

zamantakewa a tsakanin ma'aurata, uwa

uba: kuma soyayya ta gaskiya da take

haifar da yafiya a kowanne lokaci.

87

Sannan Annabi (S.A.W) ba haka yayi

Zama da nashi 1yalin ba, don kuwa babu

wani mutum da zai nunawa matarshi

kwatankwacin irin soyayyar da ya nuna ga

iyalinshi.

Babu kyamata, babu hantara bare

tsangwama a cikin al'amarin aure. Miji da

mata (ma'aurata) duka su baiwa junansu

lokaci na hira, kulawa, da tausayawa

wacce suke haifar da karin soyayya da

fahimta a tsakani.

Na jawo akwatin kananan kayana na

bude ina dubawa tare da tunanin wacce

zan yi amfani da ita.

Duk da ina jin kunyar yin hakan amma

idan har zai kawo mun gyara ga aurena to

ko meye zan yi idan ba sabon Ubangiji ba

ne.

Rigar bata wuce mun iya gwiwa ba,

haka nan shara-shara ce don kuwa kusan

koma: nawa a bayyane yake.

88

Na gyara gashin kaina wanda na wanke

shi da man wanke gashi na (Trichup)na

kuma shafe shi da kayan gyara iri-iri.

Duk da ba wani tsawo ne da gashin

nawa ba ya yi kyau ba kadan ba. Ga jikina

da yayi luwai-luwai saboda jin dadi.

Maganar gaskiya ita ce Ishak ya wadata

ni da abubuwan jin dadi da suka danganci

abinci da na gyara.

Sai dai a yanzu na fahimci ba su ba ne

masu muhimmanci wanda bai bani ba shi

ne komai, wato soyayyarsa da lokacinsa.

Na kuma kuduri aniyar nema ta hanyar

da ta dace.

Na dawo falo na zauna na ci gaba da

yan karance-karancena, don kada barei ya

dauke ni.

Yau sha daya saura kwata ya dawo. A

lokaci na dawowar Ishak kuwa to ya dawo

da wuri. Ya shige dakinshi ban ce mishi

komai ba kamar yadda bai kalle ni ba.

89

Gabana sai faduwa yake yi, kodai na

kyale shi ne kawai? Kai a'a, na dauki

abincin da na ajiye mishi wanda ni kaina

rabon da nayi girkin gidan da shi har na

manta saboda ba ya ci.

Nayi sallama a daidai. kofar dakin na

shiga ba tare da na jira amsawar shi ba.

Wanka yake yi, don haka na zaunaa

bakin gadon ina jiran shi. Ya fito yana

goge kanshi da karamin tawul nayi mishi

sannu na kuma gabatar mishi da abinci.

Bai ce mun komai ba sai da ya zo zai

kwanta.

Ya ce, "Ni fa kwanciya zan yi ko za ki

je dakinki ne?" Wani abu ne ya tokare ni a

wuya, na mike na dawo dakina na kwanta.

Don takaici sai kawai na fashe da kuka.

Me ke faruwa ne'? Shin fita hanyar Ishak

zan yi ko ya ya? Abu daya ne ya sani na ji

sanyi da naje debe kwanukan abincin da

na kai mishi naga ya dan ci.

90

Yau ma shiri sosai nayi mishi ban damu

da korata da yayi ba jiya, don kuwa gyara

nake so.

Kuma na kuduri aniyar yi ta kowacce

hanya in dai ba fin karfina abin ya yi ba.

Ganin da nayi ya dan ci abincin yasa ni

yin niyyar yi mishi wani abincin da nufin

neman burge shi.

Sai dai kash! Ban ma san abincin da

yake so ba. To amma na cire wannan

tunanin a raina kawai nayi abincina mai

kyau kuma na burgewa na dan hada mishi

da kunun zaki.

Yau ma irin kwalliyar jiya nayi. Ban

kuma yi barci ba har ya dawo. Dakin shi

na bishi yana kokarin daure igiyar rigar

barcinshi na ajiye tiren da ke dauke da

food flask da sauran plate da cokula na

Juya na je na dauko Jug din da na ajiye na

kunun zaki na dawo.

Ina shigowa ya ce, "Ki kwashe

kwanukan nan ki fita da su ba zan ci abinci

91

a wannan daren ba." Raina bai baci ba, na

ce "To ga kunun zaki mai sanyi ne sosai."

Na kalli yanayin shi yana daga kwance

hakan ne yasa na jawo kofi na tsiyaya

mishi kunun na mika mishi.

Kamar dai ba zai karba ba sai ya mike

ya zauna ya karba ya kara miko mun kofin

na kara, mishi na tashi da niyyar fitar da

kwanukan abincin da ya ce ba zai ci ba.

Har na juya ya kira ni "Zo ki zuba mun

kadan." Na ce "To." Kadan din na zuba

mishi na kara mishi kunun zakin sannan

na jira ya gama na kwashe kwanukan na

fitar.

Ban koma dakin ba nawa na shiga nayi

kwanciyata. Da sassafe ban koma barci ba

sammako nayi na yi mishi abin karyawa

cikin sauri na kawo mishi.

Har ya gama shiri lokacin da na shiga.

Kwalliya sosai nayi ya kalle ni ya kalli

tiren kayan karyawan. Na ce "Ko za ka

karya ne kafin ka fita?"

92

Bai musa ba zama ya yi na zuba mishi

ya karya har ya mike sai ya kalle ni

"Unguwa za ki je? Na ce, "A'a." Ya ce,

"Au to na dauka ko kin fara fita ne ba ki

tambaye ni ba."

Na ce, "A'a ba za a yi hakan ba." Yau

wuni nayi cikin jin dadi a raina. wajen

karfe uku da rabi yaron da ya saba aikowa

da cefane yayi sallama.

Na zauna ina duba cefanen yadda ya

saba kawowa ne bambanci kawai shi ne

kafar Saniyan da na gani a ciki. Na dauko

wayata duk da ban taba yin hakan ba, ban

kuma san ya ya zai dauki hakan ba.

Tana yin kara ya dauka, "Lafiya?

Tambayar tayi mun wani iri, amma sai na

daure na ce "Dama zan tambaye ka ne,

kafar Saniyar da na gani za ka ci abincin

dare a gida ne?"

"Da can sauran cefanen da ake kawowa

tambaya ki ke yi?" Na ce, "Aa." Ban

saurari jin karashen maganar ba na kashe

93

wayar saboda abinda naji a cikin zuciyata

na tamkar ina kokarin cusa kaina da yawa

a wajen Ishak.

Na hada kayan kawai na sanya

kowanne a mazauninshi na kuma wanke

kafar da niyyar yin miyar ganda da ita.

Sai da na hada komai sannan na dora

tuwon shinkafa. Na gyara kicin din na

kammala komai a mazauninshi. Na dawo

daki nan ma na kara kikkintsa abubuwan

da suke bukatar kintsi.

Sai da na gama ayyukan abinci sannan

na shiryawa Ishak nashi abincin a inda na

saba, tare da sauran kunun zakin jiya

wanda ya kara jika.

Yayi dadi ba kadan ba. Na shiga wanka

na hado da alwala nayi sallar Magriba

sannan na zauna domin nayi shafa.

Yau ana idar da sallar Isha'i kawai sai

ga Ishak shi kanshi ya gane nayi mamakin

hakan, sai da ya gama shirinshi kafin ya

fito ya zauna a falon.

94

"Kawo mun abincin nan wurin". Na

shiga dakinshi inda na ajiye abincin nashi

na fito dashi na zuba. Ba karamin abinci

yaci ba, don kuwa miyar tayi dadi ba

kadan ba.

Na gama kwashe kwanukan sannan na

dawo ina kallon tashar da ya kamo ta

Aljazeera yana sauraron labarai.

Sai wajen karfe goma sannan na mikKe

don kwanciya. A raina nasan 1dan na ce

zan jira Ishak ban san lokacin da zai

kwanta ba.

Haka nan kwanakin da nayi ina zaman

jiran dawowarshi sun sa barci ya kama ni

da yawa. Na gama shirina na zauna a

bakin gado ina addu'o'ina da na saba yi na

kullum kafin kwanciya, sai ya shigo.

"Zo mana." Na mike na bishi.ba zai

yiwu na ce Ishak yana neman mata ba don

kuwa ban gani da ido ba bani kuma da

wanda zai fada mun.

95

Amma idan abin shi ya motsa mishi na

fushi ko halin da ya saba yana jimawa ba

tare da ya neme ni ba sat da tun da na

samu na fara shawo kanshi ta wannan

hanyar al'amuran gidana sun dan fara yi

mun sauki.

Na farko dai ya daina zaman karfe sha

daya ko sha biyu a waje, idan yayi dare to

karfe goma, duk kokarin da nayi kuma na

ganin na gane ko na fahimci abin da yake

yi a wajen na gagara.

Tun da na lura da shi na gane ina janye

hankalinshi da irin shigar da nake yi mishi,

kullum da irin wacce nake canzawa.

nKo da ba ya cewa komai kuma ina gani

a aikace. Sai dai abubuwa kullum da irin

wacce take zuwa.

Shirin da nayi musamman don naje gida

yau amma sam 1shak ya ki yarda, duk

kuwa da na gaya mishi cewa Umma zanje

gayarwa saboda rashin lafiyar da take yi.

96

Har Hindu da Móminta sun je sun

dubota amma sam shiya ki barina ya

kuma ki żuwa shi ya dubota.

Kullum sai dai na kirata a waya. Na

záuna na buga tagumi duk wani abu da

nake Rokarin ya rage mun Bacin rai ya ki.

Da ya dawo kuwa ban fasa yi mishi

abinda na saba ba. Amma gari na wayewa

da na kara rokonshi ya ki, ban ce mishi

komai ba.

Yana fita sai na shirya na dauki gyalena

burina bai wuce naga halin da Umma take

ciki ba, tunda ni dai zamana da ita ban

taba jin tayi wata rashin lafiya ba.

Don haka hankalina a tashe yake ba

kadan ba.

Jikin nata babu dadi sosai, amma duk

da haka ban zauna ba don kuwa kwata

kwata ban fi awa daya ba na dawo.

Na dawo duk da dai ban ji dadin ganin

da na yi wa Umma ba, na samu saukin

97

damuwar rashin Zuwa dubata da.ban yi ba

kwana da kwanaki.

Ban dade da shigowa ba sai ga Ishak ya

shigo ina yi mishi sannu bai tsaya amsawa

ba sannan yanayinshi gaba daya ya canza.

Ina ki ka je? Shi ne tambayar da ya

fara yi mun. Nan da nan na kama inda-

inda kan in san abinda zan ce tuni ya

dauke ni da mari kauu!

Duka Ishak ya yi mun mai shiga jiki,

sannan yayi ficewarshi ya komawurin aiki.

Tun daga lokacin wani irin zazzabi yaa

rufe ni wanda yafi kama da na bacin rai da

bakin ciki.

Bai dawo ba sai can cikin dare. Ina

zaune a tsakiyar gadona har a lokacin

kukana bai kare ba.

Washegari, kuwa ga zazzabi, ga karin

tsamin jiki, Don haka ko, tashi nayi abin

karyawa ban yi ba. Sai da naji yunwa tana

neman nakasa ni ne na tashi na lallaba na

hada tea na sha.

98

Har dare yau ma ban samu nayi abinci

ba, don kuwa ko sallah da kyar nake iya

mikewa nayi.

Haka nan yau ma da ya dawo sha dayan

dare bai leko ni ba, dakinshi ya shige da

gari ya waye ya yi sammako kamar dai

dabi'arshi ta da.

Nayi kukan takaici har na gaji nayi

shiru, Ishak wane irin mutum ne wanda ko

kadan bai san hakkin zaman aure ba?

Amma kuma shi yana so ya sanyawa

mutum dokar rashin adalci kuma yabi.

Lallabawa nayi na shiga gidan su Hindu

duk da sanin da nayi me hakan yake nufi

idan har ya gane.

Momi tana ganina ta fara salati. "Ba ki

da lafiya ne Hauwa'u? Na ce, "Eh Momi.

Hindu nake nema." Ta ce, "To je ki gida

gata nan."

Hindu ce ta gyara mun gida ko ina,

sannan na sa ta tayi mun faten tsaki don

abinda zan iya ci kenan.

99

Na kuma yi matukar sa'a na samu na

sha sosai nayi wanka na dan samu karfi a

jikina.

Ita ce kuma ta taya ni nayi girki sosai,

tuwon semovita miyar kubewa danya da

taji tantakwashi da naman rago na' hada

komai na ajiye wa Ishak a wurin cin

abincinshi na shige daki na kwanta.

Duk da dan (Paracetamol) din da na

samu na sha jikina bai yi sauki ba, sai

dada tsananta yake yi.

Da sassafe na lallabo na shiga dakin

Ishak yana zaune yana duba wasu takardu

rabon da na saka shi a idona kwana hudu

kenan yau.

Yanayin da ya ganni a ciki bai hana shi

yamutsa fuska ba. Wane irin abu ne haka

ke wai wacce irin yarinya ce? Kin ga

yadda ki ka yi wujiga-wujiga kuwa?

Don Allah can wuce ki gyara jikinki

kafin ki zo mun nan muryata tana rawa ta

ce, "Ba ni da lafiya ne.

100

To idan ba ki da lafiya sai ki zo mun

haka? Mits! Fita don Allah kije kiyi wanka

wawiyar yarinya kawai."

Dawowa daki nayi na zauna sai da

nasha kukana ya ishe ni sannan na mike na

lallaba nayi wanka na saka doguwar riga

mai gyale na zauna na hada tea din da zan

sha.

Ruwan lipton ko birebi ban iya ci ba, na

koma na sake kwanciya don ko

Paracetamol din da zan sha ba ni da shi ya

kare.

Ishak bai fito ba sai wajen sha daya

kasancewarta Asabar. Sanye yake da Jeans

blue a shirt long sleeve wuce muje.

Hijabi na dauko muka fita zuwa asibiti.

Muna zaune a gaban Likita bayan ya

tabbatar mana ciki ne da ni karami, ya

kuma rubuta mana prescription na

magunguna wadanda muka karba a

chemist din asibiti muka kamo hanyar

komawa gida.

101

Tsananin zazzabin da ke damuna vasa

ban ma lura na gane hanyar da Ishak yab

ba sai da ya ce mun fita ki shiga ina

jiranki.

Na duba naga a kofar gidanmu muke,

cikin sauri na bude kofar motar na shiga.

A kicin na samu Umma taji sauki sosai, na

durkusa a gefen kicin din tana kallona.

"Hala kema ba ki da lafiyar ne ko naga

kin zama haka?" ban bata amsa ba sai

kuka da na fara yi mata.

"To menene kuma na kuka ai hakuri za

ki yi ba a yiwa ciwo kuka Hauwa'u, ki

zama jaruma. Ban daina kukan da nake yi

ba har ta gaji ta.ce "Ko dai kina da wata

matsala ne?"

Ban san me zan cewa Umma ba, ta gaji

da tambayata ta ce "Uhm, hakuri fa ake yi

da komai ma da ki ka gani na duniyar nan,

ballantana zaman aure.

Kada ki sa wa kanki wata damuwa

game da lamarin mijinki tunda dai bai

102

gaza miki da komai ba. Bai zama lallai sai

ka samu yadda ka ke so a kowanne lokaci

ba, kin gane.?"

Na tashi na yi wa Umma sallama na fito

muka dawo gida da Ishak. Wanda tsawon

watanni goma sha daya da nayi da shi a

matsayin matarshi ta aure bai sa shi ya yi

tunanin rana daya yaje ya gaisa da iyayena

da suka ba shi aurena ba.

Har kuma da rashin lafiyar da Ummana tayi.

Ciwo sosai nayi na wajen wata kusan

guda ina kwance ko aikin gida bana iyawa,

sai Hindu ta shigo tayi mun.

Ban samu saukin laulayin da naketyi ba

sai ana gab da sallah, ba ta fi sati biyu ba.

A cikin akwatina na dauki atamfa daya

da shadda mai laushi na bayar aka kaiwa

Umma don ta dinka atamfar ta bayar da

shaddar don a dinka wa su Tasi'u, tunda

bani da kudin da zan saya musu.

103

Ni kam Ishak yayi mun har kala biyu

masu kyau sosai, ban ma san da su ba sai

da ya karbo su daga wurin Tela.

Daga ni har shi din shirin sallar muke yi

ba kadan ba. Ta bangare na dai wannan ita

ce sallar da zan yi ta farko a dakin aurena.

Shi kuma yayi sayayya na abinci ba

kadan ba. Nayi cincin, cake, sannan nayi

miya mai dadin gaske da taji naman

Saniya.

Sannan na soya naman kajina gaba

daya. Ga kunun zakin da nayi wanda ya ji

kayan yaji sosai da busasshen dankali.

Hindu ce ta shigo da sassafe tun kafin a

tafi sallar Idi ta rinka mika mun abincin

gidajen makwabta saboda sammakon da

nayi na gamawa.

Tayi sallama a bakin kofä saboda sahin

da tayi Ishak na nan, na amsa mata na fito

ina tambayarta akwai,sauran gidan da ba a

baiwa ba ne?

104

Ta ce, "A'a." Na ce, "To don Allah idan

kin yi wanka sai ki kai mun na gidanmu

Ta ce, "To."

Na shiga daki da shiri na shiga wanka.

Ke zo nan. Ishak ne ya kira ni.

Kwanakin baya ba na hana yarinyar

nan shigowa gidan nan ba? Ba na ce bana

so ba? Gidannan wai shin ba gidana ba ne?

Idan na ce bana son abu menene dalilin

da yasa

5 / 7