Author : Hafsat C Sodangi Category : KDP NOVELS
ba za a bari ba, ki kiyaye ni fa! Me
take zuwa ku ke yi? Gulma ko ba ki
munanan shawarwari da koya miki
dabi'un banza? To ya ishe ni haka."
Karo na farko da al'amarin Ishak ya
gundure ni na zuba mishi ido ina kallonshi.
Yana dandanna wasu lambobi ne a
waya, alamar zai yi kira. Kamar na ba shi
amsar maganganunshi sai naga ba zan iya
ba.
Yayi mun kwarjini da yawa sai kai na
wuce shi na shiga bandaki nayi wankana
na fito.
105
Lokacin nan kuwahar ya gama
shirinshi. Jamfa ce a jikinshi dogųwa ta
yadin shadda geitzner ja. Tayi mishi wani
irin kyau.
Ban taba ganin ya saka babbar riga ga
wata kila don baya ra'ayinta. Yana rike da
hularshi yana kokarin karyata haka kawai
na ga kalanta bai yi mun ba.
Na mika hannu na dauko watamai
ruwan ja da brown da wani ratsin nace ko
za ka ajiye wannan ne ka saka wannan
zuba mun ido ya yi yana kallona.
A hankali na ce mishi na gane kamar
tafi shiga da kayan. Ya mika hannu ya
karba bayan ya ajiye ta hannun nashi.
Ya karyata ya saka a kannan shi sannan
ya feshe jikinshi da turare. Yayi mun kyau
a idona. Ina matukar son yin mu'amalla
mai kyau da Ishak irin wacce nake ji ana
bada labari,
106
Don na san rayuwa ce da take faruwa a
zahiri. Ya juyo da kallonshi gare ni, nima
shi nake kallo.
"Zan tafi hawan Idi, ana saukowa zan
dawo, don zan yi baki daga office dinmu.
Ayi mun shiri na abubuwan ci sosai don
suna da yawa."
Na ce,To Allah ya bada sa'a." Ya
kuma amsa mana lbadunmu. " Ya ce,
"Amin.Ya fita.
Zama nayi na yi kwalliya ta burgewa ba
kadan ba, na dauko yadin material wanda
Ishak ya karbo mun daga gun Tela na saka
ya kuma karbi jikina ba kadan ba.
Gashi kuma na fara yin kibar ciki ga
fatata da ta yi haske tayi laushi zan iya
cewa ban taba yin kyau irin hakan ba.
Hindu ta shigo ita ma tayi kwaliya sosai
ta shadda da ta sha ado. Ta ce, "Kai Aunty
Hauwa, kin gan ki kuwa? Kin ga irin kyan
da ki ka yi?
107
Nayi murmushi na ce, Haba Hindu,
har na kai ki? Ta ce, "Haba wane ni, keta
dubi kalari kin san yadda ado yake yi wa
farin mutum kyau kuwa?"
Na ce,"Ke kuma ga ki doguwa kin san
kyau yana ga dogon mutum. 99 Gaba daya
muka yi dariya. Na ce mataTo barka da
sallah, Allah ya maimaita mana."
Ta ce,"Amin." Ta kwashe manyan food
flask guda biyu da na cika da abincin
gidanmu, daya dai miya ce da taji nama
don kuwa raba miyar nayi biyu na juye
rabi.
Dayan food flask din kuwa soyayyen
naman kaji ne da cincin da kek. Na saka
mata a nan ne don kaninta ne zai rike
gudun bari.
Ban zuba shinkafa ba don nasan Umma
zata dafa. Na shiga shiryawa Ishak abincin
bakinshi komai na tanadan mishi.
Karfe goma daidai ya shigo gidan. Nayi
mishi barka da sallah ina kallon shi ga
108
zatona zai yaba kwalliyata tunda ko da ba
dabi'arshi ba ce yin hakan.
Ai kuma yau sallah. Bai ce mun komai
ba har na gama shirya mishi abincin shi.
Ya ce "Da kin bari sai sun zo muci tare."
Na ce, Ai ba ka da tabbacin lokacin
zuwan nasu tunda yanzu ne ma aka sauko
daga Idi, kaci ko babu yawa zai rage maka
yunwa." Sai dai na daure ne kawai nayi
mishi wadannan bayanan.
Don tuni zuciyata ta fara hankoron
fushi. Na shiga daki na zauna a bakin gado
naga abin bai yi mun ba.
Na gaji da abubuwan ko in kula da
Ishak yake yi mun ko ma meye zai faru
kawai ya faru a yau dinnan.
B Ban san lokacin da na ganni zaune kan
kujerar da ke gabanshi ba.
Na kare mishi kallo yana cin abincin shi
cikin nutsuwa kana kallon shi ka san ba shi
da matsala.
109
Ya dago ya kalle ni Yaya lafiya?
kullum salon tambayarshi kenan. Ban ce
mishi komai ba ban kuma daina kallon
nashi ba.
Kina da matsala ne? ko wani abu yana
miki ciwo. Wani tunani yazo mun cikin
raina da kuma yasa na fasa yi mishi
magana na mike da nufin komawa daki.
Hauwa'u na juyo tare da amsawa. A tun
farkon zamana da Ishak zan iya kirga
adadin lokutan da ya kira sunana.
Zo ki kwashe wadannan kwanukan na
gama." Na zo ina kwashewa., Dan
sassaucin da na samu na mu'amalla ni
kaina nasan don juna biyun da nake dauke
da shi ne wani lokaci ya kan tambaye ni
akwai matsala ne ko kuma wani abu yana
yi miki ciwo?
Haka nan ya rage yawan dadewa a waje
karkari ya kai karfe goma shi kenan.
Na gama kwashewa da karin gyaran
wurin na dawo dakina na kwanta don
110
dan samu na huta ayyukan da na kwana
biyu ina yi.
Ya shigo dakin sanye da farar singilet
da wandon kayan da ya cire ya miko mun
kudi bandir din Naira dari sababbi fil da
su.
Na mika hannu na karba ina jira yayi
mun bayanin abinda za a yi. Ya ce, "Ki
ajiye barka da sallanki ne. in tsaya cewa
kudin nan sun yi mun dadi ma bata baki ne.
Sai dai kan nayi mishi godiya aka fara
buga sallama. Ya juya ya shiga dakinshi
don dauko rigar shi da ya tu6e.
Ni kuma na jawo gyalena mahadin
material din jikina na yafa na fito har ya
ba su izinin shigowa. Lallai kam bakin
Ishak da yawa.
A can gefe na zauna müka gaisa da su.
Ban tsaya kallonsu ba amma nasan sun
kusa goma. Ban iya komawa ba lokacin daa
111
na shiga kicin tunanin yadda zan yi na kat
musu sa'a shima ya fito ya zo kicin din.
Bani abincin kawai ba sai kin shiga ba
tunda kun gaisa.Ya fara kwasa yana
shigarwa sannan na hada Plate-Plate da
kofuna na sake mika mishi ya shiga.
An dai kai kamar mintina talatin na
motsin plate da cokula kawai nake jiwowa,
yayin da nake zaune a single dakin dake
tsakar gidan.
Kafin daga baya hira ta barke. Ina
sauraronsu kowa da abinda yake fada
game da abincin yayin da ake sakawa
wasu waigi.
Hira sosai şuka shiga yi daga baya da ta
kunshi wajen aiki da kuma wasu al'amura.
Koda nake kwance a kan gadon dakinnan
na kasa barci duk kuwa da irin gajiyar da
nayi saboda muryar Ishak da nake jiyowa,
Da yadda yake dariya da wasu
abubuwa. Mamaki ya kama ni, dama yana
112
hira da mutane da ni ne.bai yi ko kuwa ya ya?
Ba su tashi tafiya ba sai wajen azahar
suka fita gaba daya don yin sallah, bayan
sun nemi nazo muyi sallama ya ce musu
nayi barci.
Na dawo dakin na sake gyara shi tsaf
kamar ba a yi komai a ciki ba, sannan nayi
sallah na hau gadona na sake kwanciya.
Ishak bai dawo ba sai wajen hudu da
rabi. Na mike na bishi dakinshi baya ciki
alamar yana wanka na zauna a bakin
gadon ina jiran fitowar shi.
Tunda ya fito nake bin shi da kallo har
ya sanya short da jallabiya fara sol, sannan
ya sake kallona.
Ga wannan suka ce na baki goron
sallah. Yana miko mun kudi na kalli
kudin a hannunshi da yake miko min,
sannan na kalle shi shima ni yake kallo.
113
"Ya ya dai akwai matsala ne?" Na ce,
"Eh akwai, wannan ma da ka bani da safe
gasu nan na dawo maka da su bana so."
Ba karamun kada shi maganata tayi ba,
don tsawon zamana da Ishak ban taba
amsa mishi magana ba ballantana nayi
jayayya da shi.
Kuka na fara yi a daidai lokacin da na
fara magana. "Ni ba zan iya irin wannan
rayuwar ba. Dama abinda yasa nake ta
hakuri na dauka haka ka ke, haka
dabi'arka da halayyarka suke. To ashe ni
kadai ka ke yi ma.
Ya ce, "Wacce irin banzar magana ce
wannan, ke lafiyarki kuwa?" Na ce,
"Lafiya kalau, na dai gaji ne. Ban taba
saka kaya a gidan nan ka ce yayi kyau ba.
Ban taba yin girki kaci ka ce yayi dadi
ko bai yi ba, ban taba yin wani abu da
nufin na burge ka ka yaba mun abinda nayi
ba.
114
Ni a kullum a wajen ka a kushe nake.
Bana gwaninta a wajenka sai kuskure. Ni
kulluma wajen ka mai laifi ce ni.
Ba ka ganin nawa da mutunci saboda
ni, babu wani mutum da zai shigo cikin
gidan nan da sunan wurina yazo ba tare da
ka wulakantashi ni kuma ka bata min
ba..."
"Ke dakata! cikin tsawa ya dakatar da
ni. "Ita ce ta turo ki ki zo ki titsiye ni?
Kina nufin kin isa ki sa ni nayi abinda ban
yi niyya ba?
Wannan abin da ki ka zo ki ke yi ba zai
sa na canza daga dokata ta kada wani ya
shigo mun gida ba ko wanene ba tare da
yardata ba.
Kuma tunda yanzu na kara gane aibun
hakan nasan abinda zan yi kenan har kin
fara bin shawarwarinsu ne kina titsiye ni
akan abin da bana so. To babu laifi."
"Ba titsiyeka nayi ba, kuma ni babu
wani wanda yasan abinda muke yi
115
ballantana har ya bani shawara a kan
abinda zan yi.
Amma wacce irin rayuwa ce wannan?
Za ka iya zama da abokai kuyi hira kuyi
dariya tare amma ni matarka ta aure ba ka
da lokacina?
Idan gari ya waye ka fita ba zan sake
saka ka a idona ba sai wani wayewar
garin? Amma ni kana saka mun takunkumi
na yin mu'amalla har da 'yan uwana, to...
kafin na karasa tuni ya dauke ni da
marin da na kife a kasa.
"Ki rinka fahimtar lokacin da mutum yá
gundura da abu." Ya watsar mun da kudin
a wajen ya dauki mukullin motarshi yayi
waje.
A hankali na mike na goge hancina da
naji alamar ruwa-ruwa yana biyowa, jini
ne. Ban ci gaba da kukan da nake yi ba sai
dai duk da gargadin da zuciyata take yi
mun kan abinda nayi nufin yin ban fasa ba.
116
Wannan karon shi ne karo na uku da
Ishak yake dukana, Jakata na dauko har na
fito na nufe ko'ina sai na tuna ko kudin
mota ba ni da shi.
Dawowa nayi na bude dakin Ishak har
yanzu kudin suna watse a kasa na sunkuya
na dauki gudan dubu guda uku a kudin da
bakin shi suka ce ya bani na sake shig
dakina na dauko kaya set daya na sake fita
a gidan bayan na rurrufe ko ina na tafi
gida.
Ba karamin mamakın ganina suka yi ba,
don kuwa ban gaya musu zuwana ba.
Babana muma yake yi daga ganinshi
kuma na san ya dan samu canji, don kuwa
yayi fes da shi. Umma atamfar da nayi
mata ce a jikintą, haka nan su Taşi'u.
Umma ta zubo mun abinci ta ce "Ga shi
nan duk da dai daga gidanki yake." Na dan
yi murmushi na ce "Umma ba ni, naki
mana na ci,"
117
Ta ce, "Fuwo ne miyar taushe." Na ce,
Eh bani kawai. Cin abincin nayı sosai
sannan na sha kunun zaki. Ta ce, "Amma
ai ba yau muka yi da ke za ki zo ba ko?
Lafiya dai ko?"
Na dan yi shiru ban ce wa Umma koai
ba. "Idan akwai wani abu kiyi magana
mana, naga kamar ranki a bace yake."
Na rasa ta inda zan fara yin maganar
nan take kuma na kama kuka, sosai da
sosai. Sai dai na kasa cewa Umma ga
matsalata.
Ta ce, "To ko nayi, iki magana da
Babanku ne? Na girgiza kai na ce, "A'a."
Ta ce "To ki share hawayenki kiyi hakuri
kowacce mata da ki ka gani, da irin
matsalarta.
Shi aure haka yake, kina hango na wani
ne wani kuma yana hango naki. Ki daure
ki zamo mai sirTi a tsakaninki da mijinki.
Babu mai ganinki ya ce kina da matsala
kwata-kwata, tunda mijinki ba gaza miki
118
ba, bai kuma yi tsari ba a ce tun yanzun
kin koyi kai kararshi ba ki iya warware wa
kanki matsalarki ba tare da wani ko wata
ya fahimta ba.
Ki tashi ki koma kada ki dade kuma ya
zama matsala, tunda dai da'alama ma ba ki
sanar da shi zuwan ki ba."
Sai da Umma tayi wannan maganar ne
naji gabana ya yi matukar faduwa. Na
koma gida idan Ishak ya dawo kuma muyi
ya ya kenan?
Ban bari Umma ta fahimci halin da
nake ciki ba, dauko kudin dake Jakata nayi
na bata biyu na baiwa su Tasi'u canjin
kudin mota ta dari takwas na rage kudin
da za su mayar da ni gida.
Fitowar da zan yi kenan na hango motar
Ishak ta karyo kwanar unguwarmu, cikin
sauri na koma gida.
Umma ta ce "Lafiya?" Na ce, "Gashi
nan zuwa shima.". Ta ce, "To, to Allah
119
yasa kalau. Umma ce da kanta tayi mishi
shimfida suka gaisa.
Sannan aka kira Babana da ke tare da
wasu daga cikin makwabtanshi suna
tattaunawa. Gaisuwa sosai suka yi sannan
ya kawo goron sallah ya baiwa su Tasi'u.
An dan jima kafin ya nemi na fito mu tafi.
Bai ce mun komai ba har muka iso gida,
daidai an fara kiran sallar Magriba. Bayaan
gida na wuce nayi alwala na fito don bada
farali.
Shima a dakin shi yayi sallah. Ban fito
ba don kuwa na riga na kudurawa rainaa
zan zauna ne da lshak irin zaman da yake
so muyi da shi, tunda dai haka ya zaba.
Lekowa yayi dakina ya kira ni na shiga
yana tsaye. "Kwashe mun kudin nan. Na
sunkuya na kwashe su gaba daya..
Ya ce, "To zauna." Na nemi wuri a kasa
na zauna. Tashi ki zauna a bakin gado.
Nayi kamar yadda ya ce shima yazo bakin
gadon kusa da ni ya zauna.
120
"Na dauka kina da tarbiyya hakan ne
yasa ban taba yin zaton za ki yi abin da ki
ke yi a yau ba. Sake gaya mun abubuwan
da ki ka ce ba kya so wadanda nake yi
miki sai na kula nan gaba na daina.
Amma abinda ba zan lamunta ba shi ne,
ki kara zuwa mun cikin fusata irin na yau
ki ce za ki gaggaya mun bakaken
maganganu kin gane ko? Ba ke ce za ki
koya mun yadda zan rinka mu'amallata da
wasu ba.
Ina so ki san ke din ba za ki taba zama
mai sa ni ko mai hana ni ba, koyi samuna
cikin nutsuwa kina yi mun magana ta
yadda zan gane har kullum cewa ni ne
mijinki ba ke ce mijina ba kin gane ko?
Dokata ba za ta sauka ba na cewar ban
son shigowar waccan yarinyar cikin
gidana ba don a zahiri ga abinda ki ka yi
mun a yau wanda a da ba ki taba yi mun
ba, gabanin fara mu'amallarki da ita.
121
Na dago ido ina kallonshi "Zan kuma
dauki mataki da kaina ba sai kin shiga
matsala tunanin fuskantarta ba. Ba zan
lamunci masu son shiga lamarin aurena ba.
Na kuma yafe miki fita da ki ka yi ki ka
je gida a yau ba tare da kin nemi izinina ba
sai dai ina so ki san kin fitan ne a madadin
wunin da za.ki je na gaisuwar sallah."
Na mike da nufin fita a dakin. Ya ce
"Dawo ki zauna. Na dawo na hau gadon
na kwanta sai dai kuka na kama yi saboda
tukukin da zuciyata take yi mun.
Washegari da safe kamnar ba zan yi
kwalliyar ba, sai kuma naga kaina kawai
nake yi wa, don haka sai na yi kwalliyata
na sanya atamfa super exclusive holland
wacce ya yi mun a sallar.
Kadan ya rage na ce tafi yi min kyau a
jikina a kan material din da na saka jiya,
ita ma kalarta mai kyau ne kwarai, ruwan
kwai da jajja da kore kadan.
122
Adon atamfa tana matukar sanya
mutum kwarjini ba kadan ba. Na kammala
shirina na fita kicin ko bi ta kan Ishak ban
yi ba.
Sai da na gama ayyukana na kicin
sannan na shiga dakinshi don na kwaso
abubuwan da ya yi amfanida su da kuma
gyaran bandakin shi.
ldon shi biyu na same shi, sabanin dazu
da yake barci. Na shiga bayan gidan na
gama gyarawa sannan na zo don komawa
duba girkina.
"Zo mana." Na juyo na ce "Ga ni. "
Magana yake son yi sai dai ya rasa ta inda
zai yi ta, abinda na fahimta kenan.
Ya dai zuba mun ido sai da na gaji na
ce "Ka kira ni. Ya ce, "Eh na gane baki
nuna mun kwalliyar taki ba ballantana na
ce tayi kyau, ko ba haka ki ka ce na ringa
yi miki ba?"
Na juya nayi tafiyata ba tare da na ce
komai ba, ina gab da gama abinci ne naji
123
ana ta6a kofa. Na leka ta wurin da ake
ganin mutum.
Gabana ne yayi mummunan faduwa a
madadin farin ciki, Sadiya Tanimu ce. Na
dawo kamar na kyaleta ta gaji ta tafi, sai
kuma naga bai dace ba.
Dakin Ishak na shiga har yanzu yana
kwance na rasa yadda zan yi nayi mishi
bayanin don nasan yadda yake daukan
baki.
Sai shi ne ya yi mun tambayar tashi ta
fama Ya ya dai?" Na ce, Nayi bakuwa ne
kawata ta Makaranta ce tazo."
Bai sake kallona ba ya ce, "To menene
ki bude mata mana." Na juya na koma
muka rungume juna cikin tsananin farin
ciki.
Ta rike baki daidai ta shigo falo ta ce
"Kai Hauwa'u, kin gan ki kuwa? Kin yi
wani irin kyau abin ma ba a ko magana."
Na dan yi murmushi na ce "Sadiya
kenan. Ta