Author : Hafsat C Sodangi Category : KDP NOVELS
MAI DAKI...
NA
HAJ. HAFSAT C. SODANGI
(Mrs. Yunus Abdullahi Dabai)
1
MAI DAKI... (1)
auwa'u Idris." Nayi maza na
Lmike tsaye tare da amsawa
saboda tun kafin ya kira sunana dama na
riga na harhada littattafaina, na zuba su a
cikin Jakata.
Ya waiwayo ya zub. mun ido sannan ya
ci gaba da kallon dogon littafin da ke ajiye
a kan teburin gaban nashi, wanda yake
littafin sunayen dalibai ne wadanda suka
biya kudin Makaranta, da kuma wadanda
ake bi bashi.
Ya ci gaba da kiran sunayen daliban
daya-bayan-daya duk wacce ya kira kuma
to zata tashi.
Sai da ya gama kiran sunayen ne sannan
ya waiwayo ya kalle mu ya ce, "To
tsayuwar me kuma ku ke yi a nan?
Cikin sauri kowacce ta fara nufar inda
yake, tana fada mishi uzurinta, wata ta ce
"Malam Babana yayi tafiya ya ce na bada
hakuri kafin ya dawo, sati mai zuwa.
7
Wata ta ce "Malam ni Babana ya ce ayi
hakuri kasuwa ce tayi gardama, zuwa wata
mai kamawa. Cikir sa'a kuma duk wacce
ta kawo uzurinta yana sauraronta tare da
ba wata dama.
Sai dai ni kam ban ma doshi inda yake
ba, don kuwa a wannan karon ban san me
zan cewa Malam Ali ba.
Ya waiwayo a karo na biyu ya sake
kallona "To ke tsayuwar me ki ke yi a
nan? Ko kuwa kina da wani abin da ki ke
son fada ne?
Na ce, "A'a a hankali ya ce ai ke ko ma
me za ki ce mun a wannan karon babu
abinda zai sa na saurare ki.
Ni na dade ko ma na ce tunda nake a
cikin Malamtaka ban taba haduwa da
dalibar da ke cin garabasar karatu irin naki
ba. Haba! Wane irin abu ne wannan?"
Na rataya Jakata na juya tare da kokarin
fita a cikin ajin, cikin sanyin jiki lokacin
8
da naji an kira sunana cikin sauri, na amsa
tare da juyawa.
Sadiya Tanimu ce dalibar da ke zaune a
kujerar da ke bayana.
"Ba ni littafina da ki ka karba dazu."
Na dora Jakata a kan bencin da ke
gabana na fara kokarin binciko mata
littafinta na darasin English (Turanci) da
na ara a safiyar yau don kwafar rubutun da
aka yi a lokacin da bana nan.
Malam ya ce, "Uhum, ba ka ji abin ba,
zat tafi miki da littafi. Allah dai ya
sauwake irin wannan abu to wai idan uba
bai tsaya yaga ya ilmantar da ya yanshi a
wannan zamani ba me zai yi mishi ne na
gata kuma?
Da irin wannan wahalar banzan da ki ke
yi na kullum kina cikin wadanda ba su
biya kudin Makaranta ba dama aure aka yi
miki ki ka huta don ban san yadda za a yi
kici jarrabawar gama Makaranta ba a irin
wannan tambelen da karatunki yake yi.
9
Ni halina da Hausawanmu kenan wai ba
za su tsaya suga sun biyawa ya'yansu
kudi sun yi karatu ba, amma idan an tashi
aurensu sai kaga mata ta sunkuya
karkashin gado tana zaro 'yan marofiya da
masu hannun katako."
Yan aji suka kwashe da dariya,
yayinda na mikawa Sadiya littafinta na
kama hanyar barin ajin.
"Ki hutar da kanki kada ki dawo, don
kuwa sai dai idan ban gan ki ba ko a ina ne
kuwa za a kore ki gida.
In tsaya cewa maganar Malam Ali bata
6ata mun rai ba ma to zance ne, kuma ku
san kullum haka yake yi mun, idan yazo
ajinmu koran kudin Makaranta ba zai bar
ni da takaicin koran kawai ba, sai ya bini
da bakaken maganganu.
Ni kuma ba abin in yi zuciya na ce na
daina zuwa ba tunda idan na ce haka ba
zan yi karatun ba kenan, don kuwa ba biya
mun din za a yi ba.
10
Duk wadannan takaicin da nake sha
lada ne akan a ce an fara jarrabawa, ranar
da duk wani dalibi yake. dokin zuwanta
saboda lokaci ne na nuna bajinta da kuma
gwaji kan abin da aka koyar da kai da
kuma gane irin fahimtar da ka yi. ab
Sai dai ni takan zo mun ne cikin
tsananin fargaba, don kuwa rana ce ta babu
sani babu sabo, idan har ana binka ko da
kwandala ce daya to babu ko shakka za a
kore ka gida.
Na rinka bin Malamai kenan ina kamun
kafa wadanda za su tabuka mun wani abu
ma wadanda babu wani taimako da za
su yi mun ba.
Wani lokaci ma kaga an bar wasu sun
shiga ajin jarrabawar wata kila saboda su
din kudin zango daya ake bin su, ko kuma
wasu sauran canji da ba su gama biya ba
N1 kuma a hana ni ko wani Malami ya
tausaya yasa baki sai ka ji Malam Ali yana
11
cewa ai ko an barta ta shiga da alkawarin
biya ba biya zata yi ba.
Ana binta bashin da ya kai na shekaru
uku, don haka barta nan kawai ta karaci
zamanta ta tafi.
Idan har akwai wani abu da nake burin
yin shi a rayuwata, to kuwa karatu ne, sai
dai ina ji ina gani abin yana nema yafi
karfina.
Babana ba shi da karfi, ba zai iya biya
mun kudin Makaranta ba, haka nan bai
ciyar da gida ba. Har a yanzu da muke mu
bakwai 'ya'yan Mamanmu, shi din
albashinshi a wurin da yake aiki bai fi
Naira dubu goma sha biyar ba a wata.
To da me ya ciyar damu, da me ya biya
mana kudin Makaranta da kuma sauran
hidindimu na rayuwa? Ta kai ma shi
kanshi ya hakura da karatun kannena maza
ya saka su a sauran wurare irin su, koyon
dinki da kuma kanikanci don ganin ya
12
maida hankalinshi kan nawa karatun ni
kadai amma abin ya gagara.
Don kuwa da albashin nashi kafin wani
watan ya zagayo an lamushe shi a bashi.
Dan sauki-saukin da muke samu to na
sana'ar dinkin da Ummanmu take yi ne
inda wani lokaci takan samu tayi cikon
cefane har ta adana mana dan abinda muke
hidima da shi na sallah.
ldan shekara ta zagayo babban abu guda
daya kuma mai muhimmanci a wurinmu
gaba daya shi ne muna da kwanciyar
hankali da nutsuwa tare da addini mnai
yawa a cikin gidan namu.
Don haka zama muke yi cikin
kwanciyar hankali da nutsuwa.
Na kamo. hanya don komawa gida
zuciyata cike da kunci, don kuwa wani irin
nisa ne a tsakanin gidanmu da Makarantar
wanda kuma a kullum da kafa nake zuwa
nake kuma dawowa.
13
Sannan a mafi akasarin lokuta na kan
tafi ne ba tare da nayi karin kumallo ba,
don kuwa na kan kasa hakurin jira don
kada nayi latti.
Tafiya zan kuma tafi ne ba tare da ko
sisi ba har sai na dawo ne zan ci abincin da
na samu an yi.
Ina karyo kwanar unguwarmu na hango
Abdussamad zaune kan dakalin shagon
askin dake makwabtaka da gidan su.
Wani irin faduwar gaba na samu, nan
take na juya na koma ta daya hanyar duk
kuwa da cewar ita din tafi nisa zan iya
cewa kusan kullum aka koro ni kudin
Makaranta, to sai na ganshi matukar ba
komawa tashi Makarantar yayi ba.
Na kane da niyyar na share shi nayi
kamar ban ganshi ba, don haka na
sunkuyar da kaina na ci gaba da tafiyata
har na dan gota su.
14
Sai naji ya ce "Barka da dawowa, ranki
shi dade. Cikin wayancewa na ce "Af, ai
ban ganka ba ne. 9 Tare da dan murmushi.
Ya mike ya nufo ni tare da kakkabe
wandonshi yayinda yake karasowa inda
nake. Ya dan tabe baki tare da cewa.
"Da dai kamar ban sanki ba ne ki ka
fada mun haka, to dana yarda.
Na fara gaishe shi bayan mun faraa
tafiya yana amsawa. Na ceAshe baka
koma ba har yanzu?
Ya ce, "A'a na koma jiya dai na sake
dawowa da yamma saboda wani yajin
aikin da Jami'o'i suka fara satin can da ya wuce.
Na ce, "Cabdijam! Abin dai babu dadi
Ya ce, "Eh to, kusan hakan, kin san
yanzu babu ranar komawa dai kenan
halin yajin aikin kasar nan, idan ba
matukar sa'a muka ci ba sai mukai
watanni biyar nan gaba zaune Gwamnati
15
bata dauki wani kwakkwaran mataki a kai ba.
Tunda su babu ruwansu, don talaka ne a
matsala tunda mu ne muka cika
cikin Jami'o' i kasar, su nasu suna can Turai
suna karatun cikin kwanciyar hankali, mu
kuma muna nan muna gwagwagwa.
Karatun da zai dauke ka shekaru hudu
idan ba matukar sa'a kayi ba sai ya kai ka
shekaru shida kana yi ba ka gama ba.
Shi yasa ai tun yanzu muke muku
addu'a komai ya gyaru kafin zuwan naku
lokacin, sai dai banga alamar ke za ki yi
nisa ba, nafi zaton aure za ki yi da alama.
Na kalle shi na ce, "Uhum! Sai anjima.
Na shiga gida saboda karasowar da muka
yi kofar gidan mu.
Akwai mutunc1 mai yawan gaske a
tsakanina da Abdussamad, don kuwa duk
shariyata da mutane suke magana akai, shi
kam muna gaisawa har ma mu dan yi hira
saboda shi ko na wuce shi to zai yi mun
16
magana har ta kai ma ba na ma iya wuce shin.
Makwabcinmu ne sosai, haka nan
Babana da Babanshi suna mutunci sosai a
tsakaninsu.
Nayi sallama na shiga gida, yan
kananan kannena ne suke wasa a tsakar
gida da alama Umma ta hana su fita zuwa
kofar gida ne.
Tasi'u da Sabi'u, a guje suka taho suna
rige-rigen karbar Jakar Makarantana. Na
mikawa Tasi'u saboda nasan Sabi'u ba iya
dauka zai yi ba, na kuma yi mishi dabara
ta hanyar daukanshi na cilla shi sama na
cabke.
Don kada ya saka mun rikici muka
karasa shiga dakı, suna yi mun hirar su ta
shirme Umma tana zaune a kan tabarma a
tsakar dakinta, yanka take yi na atamfa.
Na tsugunna nayi mata sannu da gida,
ta amsa ba tare da ta tambaye ni dalilin
17
dawowana ba, don ta riga tasan abinda ke
dawo da ni a irin wannan lokacin.
"Shiga ki tube kayan Makarantarki ki
saka na gida, ga dumame nan sai ki diba
kici. Na ce, "To.
Sai dana gama cinye dumamena daa
muka ci tare da su Tasi'u sannan na sake
hada kwanukan da sukalalacena wanke na
sake gyara gidan, na wanke bayan gida
sannan na sake dawowa wurin Ummana
ce, "Umma za a dora wani abu nea
wuta?
Ta ce, "Dan saurara dai tukuna muga
dawowar Auwalu ko?" Na ce, "To." Na
mikena shiga dakina dake tsakar gida na
dauko littattafaina na Makaranta don na
dan yi bita.
Har karfe daya na rana shiru Auwal bai
dawo ba, hakan ne ya sani sake tashi na
shiga cikin kicin dinmu na dauko dan
sauran garin kwakin da ke ajiye don na
jika musu.
18
Na kawo sugar na saka na mika musu
cokala sannan na dauki buta don yin
alwalar sallar Azahar.
Haka rayuwarmu take a gidanmu, kusan
kullum muna kwanciya ne da daddare ba
tare da mun san abinda zamu ci idan gari
ya waye ba.
Haka nan idan safiyar tayi muka samuu
muka karya kumallo, to ba ma sanin abin
da zamu ci idan rana tayi.
Saukin abin ma shi ne, yanzu Auwalu
ya kawo karfi yana kuma matukar
taimakawa.
Auwalu shi ne wana da nake bi, shi ne
kuma da na fari a wajen Iyayenmu baki
daya.
A yanzu haka makanike ne a cikin
babbar kasuwa, sai dai har yanzu ba
kwarewa yayi ba, amma yana matukar
samun' alheri ba kadan ba.
19
Saboda sa'ar da yayi na haduwa da
shugaba na kwarai, illa ko yau ma shi ne
ya shigo da cefane a hannunshi
Don haka na shafa fatiha cikin sauri na
fito na karbe shi.
"Akwai itace ne? Na ce, "Bari na
duba. Na leka kicin din na ce, Akwai,
amma dai babu yawa.
Ya juya ya fita, yayinda ni kuma na fara
kacaniyar dora girkin, ya sake shigowa da
itace kai biyu a hannunshi ya zuba tare da
miko mun Naira ashirin.
Ki bai wa Tasi'u ya sayo miki maggi,
ni na manta ban siya ba. Na ce, "To." Ya
juya da niyyar komawa wajen aikinshi.
Tuwon masara nayi tare da miyar
kubewa danya, saboda ita na gani a cikin
cefanen, ta kuma yi dadi da yawa na tuka
don mu samu na dumamen safe.
Na kwashe na adana na kowa tare da
rufewa na janye itacen na dora ruwan
20
wankana a kan garwashin sannan na
kawowa Umma nata.
Sai da nayi wanka na yiwo alwalar
sallar La'asar, don kuwa zan iya cewaa
yanzu dabi'ata ce hakan saboda kusan
kullum abincin yamma muke yi.
Na idar da sallar La'asar na jawo
kwalbar maina da Auwalu yake kawo mun
mai kamshi.
Duk da ba wani mai tsada ba ne, shafa
shi yana sani naji ni'ima saboda kamshin
shi.
Na murza hoda da dan kwalli na jawo
atamfata na daura sannan na fito nazo 1in
da Umma take na zauna don naci nawa
abincin.
Muka dan fara hira wacce yawancinta
akan Makarantata ce. Tace "Sai ki
yawaita addu'a, Allah ya zabar miki mafi
alheri a ciki, ko karatun idan zai yiwu.
21
ldan kuwa ba mai yiwuwa ba ne to sai
kiyi aure a kai ki dakinki kema ki nutsu ki
zauna a wuri daya.
Babban burin Iyayena bai wuce na
ganin nayi karatu ba, ko da kuwa wacce
irin wahala za su yi don ganin hakan.
Hakan ne yasa da Umma tayi mun
wannan maganar gabana yayi matukar
faduwa, ta soma hakura kenan ko ya ya?
Na ce, "Umma aure fa ki ka ce?
Ta ce, "Eh shi na ce idan karatun ba zai
yiwu ba menene amfanin zaman gidan
tunda kin riga kin isa auren.
Shi ma Babanku ai ya nga ya fara
hakura tunda naga an kwan biyu ba tare da
yayi maganar Makarantarki ba.
Jikina yayi matukar yin sanyi, dafin
maganar Umma sai dai ban ce mata komai
ba, don ba maganata ba ce tunda ba zan
iya tuna ranardas wata magana
makamancinyar wannan da ta danganci
aure ta hada ni da ita ba.
22
Aunty Hauwa'u kizo in ji Yayan su
Lubabatu. Na waiwayo na zuba ma
Tasi'u ido, na ce "In zo fa ka ce?
Ya ce, "Eh shi ne ya aiko ni gashi nan
ma a zaure. Umma ta ce "To ki ka sani ko
wani abu zai tambaye ki?
Na ce, To bari naji naga bai taba
aikowa gidanmu a kira ni ba." Hijabina na
sako na fita kofar gida inda yake tsaye.
Wata gaisuwar muka sake yi yana
kallona "Ya na ganki fuskarki wata iri?
Na dan yi murmushi na ce, "Ai da ka
kirani ne baka ji yadda zuciyata tayi ba, sai
da gabana ya fadi.
Ya ce, "To da alama dai ba ki da
gaskiya kenan." Na ce, "A'a rashin
gaskiyar me? Na dai dauka wani abu ne ya
faru kuma ka san ban saba hakan ba. 99 Ya
ce, "Eh to, ai komai dama farashi ake yi
ko?
Ua juya inda su Tasi'u da Sabi'u suke
harkokinsu ya mika musu Naira ashirin ya
23
ce a siyo biskit suka karba tare da fallawa
da gudu don sayowan.
Ba wai don yazo wurina ko kuma kofar
gidanmu ba ne yasa shi yin hakan, dama
can dabi'arshi ce inda duk ya gan su to zai
saya musu ko biskit ko cakulet.
Ya waiwayo inda nake "To ya ya
yanmata ya karatu? Na ce, To mun
gode Allah, ni yanzu kina aji nawa ne?"
Na ce, "SS1." Ya ce, "Dama nayi zaton
kina tafiya ne tare da su Luba, sai dai a
hanya za ki tsaya tunda ban ga alamar kina
mayar da hankali tare da bada himmar yin
karatun ba."
Na ce, "Me yasa ka fadi haka? Ya ce,
A'a na gane kamar aure ki ke so.
Wayancewa nayi tamfar maganar bata bata
mun rai ba.
Kuma kafin na samu amsar ba shi sai na
hango Babanmu yana tahowa daga wurin
aiki kuma yake na ce "Ni zan shiga gida
ga Baba nan ya dawo.
24
Har kasa Abdussamad ya tsugunna ya
gaida Babana, sannan ya wuce ni kuma na
shigo gida ina yi mishi barka da zuwa.
Ban wuce dakina ba abincin Babanmu
na dauko na kai mishi dakin Umma tare da
ruwa. Yana sanye da kayan gida da alamar
har ya cire na aikin shi sannan na sake
mishi sannu da zuwa na wuce dakina.
Washegari da sassafe kamar kullum sai
da na hada mana abin karyawa, kunu da
dumamen tuwo sannan na saka uniform
dina na dauko hanyar Makaranta.
Kamar daga sama ina shiga ajinmu
kafin na zauna sai ga Malam Ali ya shigo,
ya ce "Maras zuciya, ai dama nasan yau
ma sai kin dawo shi yasa na bugo
sammakon zuwa ajin naku don na gani.
Ba kuma zan bar ki ko darasi daya ki
samu ba. Juya kawai ki tafi." Na juyo na
kamo hanyar dawowa gida, yau kam ta
lungun unguwarmu na biyo don kaucewa
idon Abdussamad.
25
Ban tsaya yin komai ba kan yar
yamushashshiyar katifata na hau na
kwanta ba zan iya cewa ga iyakacin abinda
Zuciyata take gaya mun ba, illa iyaka dai
kawai nasan babu mamaki, ni din ba zan
samu cikar burina ba ne a rayuwata shi ne
na ni din na zama Nos, wato Malamar
jinya.
Nayi kuka har na gaji ban san sanda
barci ya dauke ni ba, na dai farka ne naji
ana kiran sallar azahar.
Na mike tare da yin salati da na tuna ko
abincin rana ban dora ba, tunda idan ina
gida ni ce mai yi. Na fito cikin sauri na
samu har Umma ta riga ta sauke tana rabo.
Shinkafa da wake ne, da mai da yaji.
Nayi mata sannu sannan na shiga bandaki
don kama ruwan in alwala.
Har na gama hidimomina na gida yau
ko waiwayon littafan Makarantana ban yi
ba, don