Author : Binta Umar Abbale Category : Romantic Hausa Novels
tunda kasha fada min cewa kana da burin auran mata hudu to amma me yasa ka boye mana ai
wannan munafurci ne."
Yaji haushin kiranshi da tayi munafiki, amma sai ya danne yace." Ki dinga tausasa harshenki
gurin yi min magana ban ji dadin wannan kalmar da kika kira ni da ita ba."
Tayi saurin cire jikinta daga nashi, tana masa wani irin kallo kafin tace." To wane suna ka dace
dashi? shin idan ka sheda mana cewa za kayi aure zamu hana kane."?
Ya daga mata hannu da fadin." Ya isa kada ki zage ni."!
Ya zuba masa rikitattun idanuwanta dake cike da fitina!
Ya duba agogon dake daure a hannunsa, lokaci ya kure babu damar ya tsaya yi mata dogon
bayani, kawai ya kama hanyar fita ba tare da yace mata komai ba.
Da sauri ta tare masa hanya duk ta firgice kamar yau ne ranar da aka farayi mata kishiya.
"Wacece wacce zaka aura."?
Wannan tambayar tayi masa.
Sai kawai yaga babu amfanin jayayya a tsakaninsu, tunda ta bukaci sanin ko wacece bari kawai
ya sheda mata ya wuce gurin.
" Kayi shuru kana kallona ga alama baka da gaskiya."
Ta sake narka masa wata bakar maganar.
'Bacin ransa ya danne kafin ya daidaita kansa yace." Nabila ce."
Wani irin murda cikinta yayi jin sunan wacce ya kira, a take gabadaya jikinta ya kama rawa!!
"Nabil.....Nabila wacece haka."?
Ta tambayeshi idonta a tsaye a kansa.
Kauda kansa yayi kafin yace." Yarinyar abokina Asp nasan yanzu kin gan......Kafin ya karasa
maganar ta daddage ta kurma ihu! tana rike kanta!
"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! ya kira kafin yay gaggawar rike ta yasa a jikinsa, cikin dakin suka
koma tana ta tuttureshi yana sake riketa, wasu mugwayen hawaye ne suke ambaliya a fuskarta.
Yaji zuciyarsa tana nema ta karye koda yayi yunkuri tashi ya tafi aiki sai ya kasa, bayaso ya
fita ya barta cikin wani hali.
Ta dinga kuka tana kallonshi! bakinta sai rawa yake tsabar tashin hankali da mamaki ya hana ta
magana.
Shima nasa idon yana kanta gabadaya jikinsa yayi sanyi ya rasa da kalmomin da zai
rarrasheta.
Sai kawai ya cire kakin jikinsa ya nemi guri ya kwanta baya tsammanin zuwa gurin aiki a cikin
wannan yanayi.
Murya a dashe tace." Dama can kai kake neman auranta shine saboda munafurci ka boye min
har da cewa da kai aka kar'bi kudin auranta."
Ya tashi zaune yana kokarin tarairaiyota jikinsa ta janye ta matsa can gefe har yanzu kukan take
tana masa wani irin kallo na ba kayi min adalci ba.
Murya a raunane yace." Bani bane daga baya Allah ya juya al'amarin kaina Zinatu ki nutsu nayi
miki bayani abinda ya faru."
Hanci taja ba tace komai ba kawai ta zuba masa ido tana sauraransa.
Ya sake raunana murya tunda ya gane hakan da yake yana saurin kassarata shiyasa ya mayar
da hankali.........Cikakkenan bayani yayi mata yanda zata fahimta sosai ya kuma shigo da
maganar bazawarsa wacce da yake neman auranta a boye ya dora da fadin." Dalilin faruwar
wannan al'amari na janye auranta ba don bana sonta ba, sai dai domin na rufawa abokina asiri,
kuma ni a ganina auran Nabila ba matsala bane a tattare damu bakid'aya! a matsayinki na
uwargida nake neman alfarma a gurinki cewa ki kwantar da hankalinki kada kiyiwa al'amarin
mummun zato! kisa a ranki cewa babu yanda Allah baya juya alamarinsa! inaso kuma ki sani
cewa har yanzu matsayinki na nan a cikin zuciyata, babu wata mace da zan aura da zata fiki
matsayi a gurina, samun zaman lafiyar gidana yana tattare dake, gabadaya kece zaki wanzar
da samuwarsa idan kinyi min haka kin gama min komai wallahi.
Gabadaya jikinta ne ya mutu, maganganunsa sun kassarata mata jiki! ya fita gaskiya! ta ko'ina,
kuma bata da wata hujjar da zata ha nashi auran yarinyar, idan ta cika 'yar halak to yana da
kyau ta marawa mijinta baya, ma'ana ta bashi goyon bayan auran Nabila dalilin mutunci da
karamci da dattakon Asp yafi karfin komai a gurinsu, wannan dalilin yasa zuciyarta tayi sanyi ta
amince da auran, babban farin cikinta, yarinyar tana da tarbiya kuma tana ganin mutuncinta,
amma dole ta sake jadadda masa cewa ya ja mata kunne tun kafin ta shigo gidansu a tsare
yake basa bukatar wani tsari nata kawai tazo bi shine kwanciyar hankalinta.
Da yake neman kwanciyar hankali yake a gidan nasa yace." Insha Allah ta kwantar da
hankalinta babu wata matsala da zasu samu da yarinyar, amma dai duk da haka zai sake
jadadda mata cewa dole ta basu girmansu.
Sai daf da sha biyu ya tafi gurin aiki. Asp ya sameshi a ofis yana duba wasu takardu suka gaisa
a tsanake kafin ya sheda masa cewa Yarinya fa ta amince sai dai fatan zaman lafiya da juna.
Yayi farin cikin jin haka daga gareshi godiya ya shiga yi masa bakinsa kamar gonar audiga, shi
kuwa Asp din da yake akwai barkwanci sai ya shiga tsokanarsa yana kiransa da ANGO! sai
washe baki yake suna tsokanar junansu kamar ba surukan juna ba.
****
A daran itama Hamra'u ya sheda mata abinda ke da akwai, aikuwa basu rintsa ba, dan kwana
tayi tana kuka da rokonsa ya janye auran! kada ya kawo musu wacce zata lalata musu
zamantakewa.
Duk yanda yaso ya fahimtar da ita abun yaci tura sai kawai ya rabu da ita ya shirya ya fita gurin
aiki.........Da kyar Uwale da Zinat suka fahimtar da ita, sai daga baya itama ta gane cewa Asp ya
wuce haka a gurinsu.
A cikin kwanaki biyun da suka rage soyayya ce mai karfi ta kullu a tsakaninsu, A waya yake
kasheta da kalamai tun tana jin kunya da nauyi har ta sake itama ta fara mayar masa da
martani. gabadaya idonsa ya rufe ya manta shaf da cewa ita din fa yarinyar abokinsa ce, koda
yake ai NAMIJI ba abun kunya ne a gurinsa.
A na gobe daurin aure yaje har gidan Asp din da sunan zance a cewarsa yana so su tattauna
da amaryarsa.
Asp kunya ta kamashi kawai sai ya girgiza kai domin al'amarin abokin nasa a yanzu mamaki
yake bashi.
Dabararsa ta zuwa shine ya jadadda mata manufarsa cikin wayo da dubara yake nuna mata
zamantakewar gidanshi cewa tayi hakuri da matanshi ta kuma dauke kai akan duk abunda zai
faru, duk abunda ta tarar a gidan tabi mutukar bai sa'bawa sharia ba, insha Allah shi kuma yayi
alkawarin kwatanta adalci a tsakaninsu.
Taji dadin bayaninsa domin munafikin namiji sam beyi ba a rayuwa, da alama shi wannan
daban yake a cikin maza.
Nan ta tabbatar masa da cewa insha Allah tayi alkawari daga 'bagaranta wata matsala ba zata
faru ba.......!
*Wannan shine karshen labarin GOJE! ina rokon Allah ya yafe min kuskurena.....Allah kuma
yasa a amfana da abunda na rubuta! Allah yasa damu da alkairi masoya NAGODE sai mun
sake haduwa daku cikin wani littafin nawa mai zuwa da yardar ALLAH*
*Kada ki karanta min littafi idan baki biya, kada ki siya ki fita dashi, 'Yar uwa kada ki ganshi a
group kiyi shearing domin hakkina ne, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500
ne.....0542382124...Binta umar gtbank. idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da
wannan number* *07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/21, 7:53 PM] Matar 'Dan Aljannah: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na
hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176
domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai
domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*133*
Shuru fadar ta d'auka bayan k'are jawabin da ya hargitsa tunanin duk wanda yake zaune a
gurin.
Bahaushe yayi gaskiya da yake fadin da d'an gari akan ci gari, ashe dama da sanya hannun
Maijidda gurin faruwar al'amarin da ya tashi hankalin masarauta da duk wanda ke cikinta,
tunaninsa bai taba kawo masa cewa Maijidda za taci amanarsa ba, ashe duk abunda take akan
iyalinsa na ganin idone dama Aysha ta jima tana jadadda masa cewa ba mutuniyar arziki bace
amma baya yarda da maganarta, cikin ikon Allah sai gashi yau ya tabbatar da maganarta.
Ya kalli Sadiq dake gurfane a gabansa yana zabga wani irin gumi! ya zubar da hawayen har ya
gaji fargaba da tashin hankali duk sun dabaibaiye shi.
Ga mamakin duk wanda ke zaune a gurin sai kawai sukaji yace ." Ka tashi kaje Allah ya
shiryeka tare da masu irin halinka."
Galadima ya kalleshi da fadin." Allah ya baka nasara iyakar hukuncin kenan."?
Murmushin takaici yayi kafin yace." Galadima wannan shine hukuncin da nake ganin zan iya
dauka akan zuriar Malam Buba, sun ci albarkacinsa abinda suka niyyata ya faru Allah ya
takaita, ita yarinyar yanzu haka tana dakinta zaune kalau wannan shine babbar nasarar da
muka samu."
Gabadaya fadar ta cika da kabbara "Allahu akbar"! an gaishe da adalin sarkin mai aiki da ilimi
da sanin ya kamata, adalin sarki ne wanda za kayi masa laifi shi ya saka maka da alkairi
UMARUL-FARUK kenan, haka duk masu irin sunan suke akwai tausayi da kyauta kulawa da
sadaukarwa hakuri juriya cikin ko wane hali.
Gabjejan dogarin dake tsaye a bakin kofa ya bugawa Sadiq din tsawa tare da nuna masa
hanyar fita." Ganin yanda jikin dogarin ke rawa yasa ya tsorata da sauri ya mike takalmi a
hannu ya kama hanyar fita daga masarautar yana godewa Allah da ya takaita masa wahala.
Ya jima yana tunanin ta yanda zai tunkari Gimbiyar tashi da maganar saboda sanin halinta
amma ya zama dole ya sanar da ita domin tana da hakki akan hakan.
Ya gama yi mata bayanin komai tana sauraransa amma ba taji irin hukuncin da ya yankewa
Maijidan ba.
Tace." Yanzu ita Maijiddar wane hukunci ka yanke a kanta kasan dai wannan abunda ta aikata
dole a dauki mataki saboda gaba."
Shuru yayi yana nazari.
Tace." Nasan dama wannan matar ai ta gama da kai babu wani mataki da zaka dauka a kanta,
shikkenan ni zan dauki mataki idan kai ba zaka dauka ba."
Ya kalleta da fadin." Wane irin mataki zaki dauka wannan maganar fa na fada miki ne saboda a
fita hakkinki amma daukar mataki ba'a hannunki yake ba.
Ta fusata! da fadin." Idan ban dauki mataki akan Maijidda ba kace ni ba 'yar halak bace."!
Ya zuba mata ido yana kallo da bacin ran maganarta a tare dashi.
Safah ta shigo ta same su suna kallon juna sai kace zakaru! kowanne ransa a 'bace!
Guri ta nema ta zauna a nutse tace." Allah ya kori shaidan din da yake kokarin ratsa tsakaninku.
Ta kalleta da bacin rai a tattare da ita ta shiga sheda mata abunda ke faruwa.
Itama rai a bace tace." 'Yar uwa bake kadai zaki dauki mataki ba nima zan dauki mataki akan
Maijidda domin wannan abunda ta aikata bai kamata a zuba mata ido ba."
Ganin sun hada kai yasa ya sassauta yana so su saurareshi.
Fafur! suka ki sauraransa ko wacce na kawo masa hujjojinta.
Yace." To yanzu ya kuke so nayi? Aysha ke kin san irin taimakon da Malam Buba mahaifinta
yayi min ya kuma yi miki a lokacin da yake raye to mai zai sanya bayan ransa na wukalanta
bayansa
Tace." Malam Buba daban Maijidda daban ai ganin hakan yasa take duk abinda takeso to
wannan karon ba zata kai labari ba.
Safah tace." Nifa zama da ita na gama ranka ya dade Safara'u ko Maijidda wannan shine
hukuncin dana yankewa kaina.
Yace." Abinda kuka shirya kenan."?
Itama Ayshan tace." Kwarai kuwa ko ka saki Maijidda ko kuma mu tattara mu barka da ita.''
Yanda suke jadadda maganar yasa jikinsa duk yayi sanyi, shi yanzu ina zai iya rayuwa idan
babu su.
Itama Maijiddan ya mahaifinta ne ya bashi kyauta kafin ya rasu shiyasa yake mutunta ta amma
tilas yayi wani abu akan al'amarin.
Yace." Idan na saki Maijidda bawai daku biyu kawai zan dawwama ba ina da damar karo biyu
akai saboda haka kuyi hakuri ku cigaba da cud'awa da ita, kuna mata adduar shiriya."
Safah tafi d'aukar zafi duk hakurinta a ranar rufe ido tayi ta dinga zazzaga masa bala'i kamar
wani sa'anta! Dashi da Ayshan mamakinta kawai suke.
"Ranka ya dade baka da hujja! domin duk wanda yaji wannan al'amarin ya san kaine baka da
gaskiya! Maijidda tayi garkuwa da 'yar cikinka domin cikar burinta Allah ya kare, to ina mai
tabbatar maka da cewa watarana dani ko 'yar uwata za tayi garkuwa tunda zuciyarta babu
alkairi saboda haka ni kam ba zan zauna ba, tunda ka zabi zama da Maijidda Allah yasa haka
shi yafi alkairi."
Hanyar fita ta nufa fuskarta babu annuri ko kadan.
Sunanta ya kira tare da bata dawowa ta zauna.
Taje ta zauna tana dauke kai.
Ya jima yana mamakinta, tunda suke bata ta'ba yi masa figala irin wannan ba, Safah tafi masa
Maijidda sau miliyan.
Yace." Shikkenan tunda dai kun hade kanku bakwa kaunar Maijidda a gidan nan zan duba
maganarku da safe kowa zai ji matsayinsa.
Safah ta bude baki za tayi magana, Aysha ta dakatar da ita.
"Ki bari tunda yace sai da safe kowa zai ji matsayinsa shikkenan kada ki sake cewa komai."
Aikuwa sai taja bakinta tayi shuru.
Al'amarin da yayi masifar bashi mamaki! har yanzu ya gaza gane cewa Aysha ce ke auran
Safah ko kuma shi, tsayin shekaru masu yawa haka al'amarin yake tafiya a tsakaninsu.
Ya kallesu babu walwala a tare dashi yace." Ku tashi ku bani guri."
Suka tashi a tare suka kama hanyar fita babu nadama a tare dasu.
Kallo ya bisu dashi yana mamakin yanda suke gudanar da al'amarinsu, yana ganin ko ya rabu
da Maijidda ya kawo wata cikinsu wahala zasu bata gwara ya hakura ya zauna dasu da halinsu.
Wannan shine karshen turka-turkar!
Saki daya kacal ya rubutawa Maijidda ba tare da cikkenan bayani ba.
Ayshan ce ta karbi takardar da kanta ta shiga har sashen Maijiddan ta bata takardar tare da
gogar zana dan bata fayyace mata komai ba.
Maijidda dai ta duba abinda ke takardar cikinta ne ya rud'e sai da ta shiga bandaki ta fito hankali
a masifar tashe ta tura jakada can fadar sarkin cewa tana da magana dashi.
Jakada ya sheda mata cewa Sarkin yace sai daddare ta sameshi gurin hutawarsa.
Ta zauna tasa takardar a gabanta ta dinga rusa kuka wiwi!
********
Aunty Zeey dai ta shiga ta fita ta rusa auran da Asp yake nema.
Yana zaune a ofis yarinyar ta kira shi a waya take sheda masa cewa ta fasa auransa domin taji
cikakken labari cewa shi din mijin tace ne a gidansa, saboda haka ba zata aureshi ba tayi
zaman takaici.
Asp ransa ya baci mutuka yaso ya fahimtar da ita amma fafur! taki sauraransa domin ta tsorata
da yanda ta samu labarin abinda yake gudana a gidansa wannan dalilin yasa ta yanke
shawarar rabuwa dashi domin ita babban burinta tayi aure a inda zata samu nutsuwa da
kwanciyar hankali.
Umar ne ya shiga ofis din ya sameshi ransa a bace nan yake tambayarsa, ya shiga sheda
masa abinda ke faruwa.
Yaja tsaki da fadin." To meye abin damuwa da daga hankali? tunda kaga Allah yayi haka to
babu alkairi a tsakaninka da yarinyar, saboda haka kada ka wani damu ka kwantar da
hankalinka a nutse sai ka duba wacce ta dace tunda gasu nan budurwa bazawara duk wacce
kakeso, wallahi ni kaina auran nakeso na kara da wata bazawara yarinyar ta kwanta min a rai
sosai ina nan ina binkice a kanta."
Asp yaji sassauci sakamakon shawarwari daga abokinsa, nan ya manta da maganar suka
shiga wata wacce ta shafi aikinsu.
***
*BAYAN SHEKARA DAYA*
Junior wato mai sunan Asp yayi wayo har ana shirin yi masa k'ani Zinat haihuwa ko yau ko
gobe itama Hamra'un laulayi take, lokacin cikin wata biyu da sati biyu, duka suka zame masa
hoto kowacce da yaje gurinta da matsalarsa zata lanjare ta fara wayyo-wayyo abinda ya tsana
kenan a rayuwarsa, kawai sai ya kyalesu ya mayar da hankalinsa gurin neman auran da ya
sanya a gaba domin Allah ya hallata masa yana kuma da iko to babu abinda zai sanya ya tauye
rayuwarsa.
Sai dai mutum yana tashi Allah na tasa, a zahirin gaskiya yaso ya auri bazawararsa amma
sakamakon abinda Allah ya kaddarata yasa ya rufawa abokinsa asiri......Abinda ya faru shine.
An gama shirye-shiryen komai na bikin Nabila an sanya ranar