GOJE par 5 End writing by Binta Umar Abbale -1.pdf

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 8

1 to 3K   out of 21.2K words

[5/21, 7:52 PM] Matar 'Dan Aljannah: _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na
hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176
domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai
domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._





*123*
Asp ya hangi abinda yake shirin faruwa! cikin 'karaji! yace." Umaru kada ka harbi kan domin
hakan ba hujjah bane."

'Dakin yayi tsit! tsananin tashin hankali ya hana su aikata komai!

Asp yaja jiki da rarrafe ya iske gurin da yake tsaye har yanzu bindigar na wuyansa.

Ya rike kafafunsa jikinsa na wani irin karkawa yace." Na fada maka kada ka harbi kanka Umaru
zaka mutu kafuri domin abunda ka aikata a yanzu ba haram bane jahadi kayi kuma kayi dai-dai
domin karshensa kenan a kashe shi kamar yanda ka kasheshi saboda haka ka cire bindigar
nan daga wuyanka."
Dr Salihu dake tsaye jiki a sanyaye yace." Wannan magana haka take ranka ya dade kada ka
aikata aikin daka sani kayi hakuri mu jin dadin abinda kayi a yanzu kuma muna alfahari da
hakan."

Gabad'aya hayaniyarsu ta cika dakin kowa yana fadin albarkacin bakinsa.

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke ya juya yana kallon gawar a kwance tayi muni! fuskar ta kara
'baki babu alamun rahama a tare da gawar!

Dr Salihu ya iso gurin a hankali ya cire bindigar daga hannunsa, ajiyar zuciya ya sauke da sauri
ya matsa daga gurin, fita yayi yaje adana bindigar ya dawo dakin.

Lokocin likitocin sun rufu kan Asp suna bashi taimakon gaggawa!

Umar din ya tsugune gaban Gawar! yana dubata.

Dr Salihu ya tsuguna da kayan aiki a tare dashi.

Binkicen gawar yayi sosai nan ya tabbatar da cewa ya mutu mintina ashirin da suka wuce.

Ya kalleshi da fadin." Abin mamaki da al'ajabi ko ya akayi wannan takadirin ya samu nasarar
shigowa asibitin nan."?

Murmushin takaici yayi kafin yace." Idan nace Najeria babu tsaro sai a musanta! handama!
babakere! cin hanci! zamba! cikin aminci cin amanar 'kasa! zalinci! duk ya tattara a wannan
'kasa shuwagabbani kuma suna kallo. Dr Salihu ko shakka ba nayi wannan d'an ta'addan dake
gabanmu yana da d,caurin gindin shuwagabbani."

Dr ya sauke zazzafar ajiyar zuciya da fadin." Yau dai karya ta kare wai bori ya kar boka
gashinan a kwance ka alkadarinsa wannan babbar nasara ce a gareka amma a ina zamu
samu cikakken bayani.

Shuru yayi na minti biyu kafin yace." Akwai sanya hannun Dr Shu'aib ina zarginsa."

Dr Salihu ya jima yana kallonsa kafin a sanyaye yace." Amma ban ta'ba tunanin cewa Dr
Sha'aib zai ci amanar aikinsa ba tsayin shekaru goma yana aiki ba'a ta'ba kamashi da wani laifi
mai muni ba sai a wannan lokacin yana da kyau dai ayi binkice sosai.


Yaja dogon tsaki da fadin." Idan babu sanya hannunsa babu yanda za'ayi wannan dan iskan ya
san in da nake, bari na sheda maka cewa kai tsaye da nufin kisa ya shigo dakin sai kuma yayi
rashin sa'a! ni na kasheshi babban burina kenan naga gawarsa a kwance a gabana."
Cikin karsashi da kwarin gwiwa yayi maganar!

Dr Salihu dai gabadaya jikinsa yayi la'asar tausayin Abokinsa ya cika masa zuciya, wannan shi
ake kira da mugun ji! ko mugun gani! ba shakka azal! ce ta ritsa da abokinsa amma kaf tarihin
rayuwarsa bashi da wani tabo Dr Shu'aib mutumin kirki ne kowa ya sheda hakan.


Washe garin ranar da al'amarin ya faru gari ya d'auka Asibitin ya cika da mutune da kuma 'yan
jarida babban burinsu a bar su su shiga domin su dauki hoton gawar sannan kuma su samu
zantawa da Jarumin da ya kawo karshen d'an fashin daya Addabi kasa.

Labari har fadar shugaban k'asa cewa a daran jiya *GOJE! ya samu nasarar kashe UBAN
DABA!* wanda ya addabi 'kasa da ta'addanci sai dai kafin ya samu nasara a kansa sai da
sukayi dauki ba dad'i! anan ya samu nasarar galabaitar da kakakin rundunar 'yan sanda Jahar

katsina wato Asp Musa Baharu yanzu haka dai yana kwance ana bashi taimakon gaggawa."


Mai girma shugaban kasa yayi farin cikin faruwan hakan, ba kuma tare da bata lokaci ba ya tura
wakilansa domin zuwa su tabbatar da al'amarin kana kuma suyi jinjina tare da mik'a gaisuwa da
godiya da yawunsa.


Comissinoner ya kasa zaune ya kasa tsaye! jikinsa sai rawa yake bakinsa ya bushe tsabar
fargaba da tashin hankali sun ha nashi sakat! sa'i da lokaci gabansa sai ya yanke ya fad'i!
watakila ya tattara kayansa ya gudu shine kawai kwanciyar hankalinsa.


Umaru shi da kansa ya bada Umarnin d'aure Dr Sha'aib a cewarsa a gurinsa za'a samu duk
wasu bayanan da ake bukata.


Da farko dai gardama ya fara, sai suka cire imani da tausayi suka fara laftarsa! babban
mutum da girma da iyali sukayi masa tik! suna masa tujara! duka ko ta inaa!.......Yana kuka da
hawaye da majina ya daga hannuwasa da fadin" Ku saurara zanyi bayani."
Suka saurara da dukan da suke masa. wasu zafafan hawaye masu zafi suka fara tsare a
saman fuskarsa.


A daddaure! aka shiga dashi dakin.

Sun kai su ashirin a tsaye a kansa!

Asp dake kwance a hankali ya tashi yana kallonsa sosai yake mamakinsa! fuskar salihai
gareshi ba za kayi tsammanin zai aikata wani mugun aiki ba.


Umaru kuwa yana tsaye ya goya hannuwansa a baya. shima mamakin Dr Shu'aib din yake, wai
dashi aka hada baki domin ganin bayansa.


'Yan jarida biyu maza da mace daya suka shigo dakin da kayan aiki a tare dasu.


Ganin shigowarsu yasa kai tsaye ya nufi gurin da Dr Shu'aib din yake gurfane! gumi yayi masa
dabaibaiyi.
*(Allah mugun ji da mugun gani Allah ka karemu)*

Ya tsuguna gabansa a nutse ya kira sunanshi.

Cikin tararrabi da damuwa ya kalleshi bakinsa ya bushe tsabar wahala!

Zuciyar musulci gabadaya sai tausayinsa ya rufeshi, amma bai nuna a zahiri ba, ya sha kunu
da fadin." Dr kayi mana cikakken bayani gamu gabad:aya ga kuma manema labarai shin ya
akayi *Uban daba!* ya samu damar shigowa asibitin nan da mummunan kudiri, ya shigo dakin
da nake kwance jikinsa sanye da kayan aikinka yanayin hallita ya sanya da yawa mutane basu
sheda waye ba saboda basaja! shin ya akayi hakan ya faru."?


Ya jima kansa ya sunkuye yana dawurwura! kafin da kyar yace." Umaru kaddara ce ba halina
bane wallahi azal ce ta afka min."


Yace." Duk na yarda da maganarka amma kasan cewa idan da kaddara tabbas akwai son
zuciya a ciki akwai sanya hannun shugabbani a tunani sunyi maka alkawarin makudan kudi shin
ko ba haka bane."?


Maganar a kan hanya take, wannan ne dalilin da ya sanya ya kasa furta kalma guda. tabbas
hakane.


Yace." Shurun ka na nufin maganata a kan hanya take."

Ya kalleshi idonshi jawur! ya tara 'kwallah! yace." Umaru babu ruwan shuwagabbani a cikin
wannan al'amarin. abunda na sani shine mai girma Commissioner naku shi yayi tattaki ya
sameni har cikin gidana da mummunan kudirinsa.

Cin amana ba halina bane. ba a shedar kai amma tunda nake ban ta'ba yunkurin cin amanar
aikina ba sai a wannan lokacin. nayi mamaki mutuka lokaci guda na amince da manufarsa. a
take yayi min alkawarin miliyan goma bayanshi wani babban dan kasuwa Alhaji Mutari mai
zinare yayi min alkawarin miliyan ashirin mutukar na amince da manufarsu.
Nan na tambayesu dalilin da yasa suke bukatar ganin bayanka.

Dukkaninsu suka tabbatar min da manufarsu....Commissioner yana adawa da yanda Allah yayi
maka d'aukaka! yayi maka baiwa! ya daga darajarka! duniya ta sanka manyan mutane suke
alfahari da kai! a cewarsa yana ji a jikinsa watarana zaka iya gadar kujerarsa ko kuma ka iya
mulkar kasar baki daya. to wannan dalilin yasa yake jin haushinka yake bukatar ganin bayanka
a doron duniya.

Alhaji Muktari mai zinare ya tabbatar min da cewa. kai ne kayi sanadiyar tattalin arzikinsa,
wannan dalilin yasa ya sanya ido akanka har ya samu nasarar samun labarin asibitin da kake
kwance.
A take suka had'u shi da Commissioner suka sauya min ra'ayi! suka rinjaye ni na amincewa
bukatarsu.
Wannan shine abunda ya faru." Cikin rauni da rashin confidence ya 'karasa maganar.

Asp ya kalleshi da fadin." Dr Shu'aib kaci amanar aikinka! bayan haka kuma kaci amanar k'asa!
kwanakin da suka wuce na dauka tare da kai muke jajanta yanda al'amura suke faruwa. rashin
tsaro ha'inci da cin hanci! ashe ta ciki na ciki zuciyarka babu alkairi! akan miliyan talatin ka
yarda kaci amanar Allah har ka bada goyon baya kashe rai! shin ka dauka kai cewa zaka
zauna a duniya ba zaka mutu ba? haba Malam yanzu kana maganar kaddara! akwai ta amma
kuma son zuciya yafi yawa a ciki saboda haka dole ka fuskanci hukunci daga hukuma!

A raunane! yace." Asp na amince da kowane irin hukuncin da za'a yanke a kaina! kamar yanda
na sheda muku da farko wallahi ba halina bane tsautsayi da kadd.........Umaru ya katseshi ta
hanyar buga masa tsawa. "Ya isa haka."! shuru yayi yana kallonsa.
Ya kalli jami'an tsaron dake tsaye a kansa umarni ya basu cewa a fita dashi.
Suka mikar dashi tsaye. damar da 'yan jaridar suka samu kenan suka dinga daukar hotonsa
suna masa vedio sai sunkuyar da kansa yake abin duniya ya dameshi! basu fasa d'aukar
hotonsa ba har sai dai aka shige dashi mota tukkuna.

Kaf ya tattara bayanai da hujjoji da suka cancanta! da kansa ya kira kakakin rundunar 'yan
sandan jahar! domin su sake tattaunawa, dama kuma shine ya bashi wu'ka da nama domin yin
binkice akan al'amarin. bai jirayi komai ba ya had'a komai kai tsaye kotu aka shiga dashi.

Mummunan labarin da ya faru a garin Katsina shine Commissioner yayi mummunan accident a
hanyarsa ta tserewa! yanzu haka dai yana kwance a asibiti rai a hannun Allah. amma kuma
cikin ikon Allah an samu nasarar kama Alhaji Mutari mai zinare yana hannu ana gudanar da
binkice a kansa.
*Allah kayi mana tsari kasa mufi karfin zuciyarmu!*


To sai da 'kura ta lafa tukkuna! iyalinsu suka samu damar zuwa dubasu.

Lokacin Asp ya warware sai abinda ba za'a rasa ba, amma fuskarsa duk ta fitar da tabo in da
Allah ya taimaka ma idonsa bai nakasa ba!


Kowa ya ke'be da iyalinsa domin jajantawa juna. babban farin cikinsu ganin mazajen nasu sun
samu sauki tare da samun nasara akan aikinsu. hakan ya faranta musu rai mutuka.

Ita da Hamra'u suka zauna a gefe da gefensa ma'ana suka sanya shi a tsakiyarsu.
Ita kam Uwale tana gefe zaune kan wata kujera.

Hankalinsa kaf yana kanta tausayinta duk ya dameshi gabadaya kammaninta sun sauya
sakamakon tsufan da cikin jikinta yayi.

Ya kamo hannunta ya rike cikin nashi. a tausashe! yace." Kiyi hakuri kinji ko."

Murmushi tayi kafin tace." Me akayi."?

Ya sauke sanyayyar ajiyar zuciya da fadin." A halin da kike ciki a yanzu ya kamata ace ina kusa
dake amma hakan bai samu ba, sai rashin kwanciyar hankalin da ya faru! amma insha Allah
komai zai wuce da ikon Allah."

Murmushin dai tayi don ta kwantar masa da hankali tace......




*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/21, 7:53 PM] Matar 'Dan Aljannah: _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na
hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176
domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai
domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._




*124*
"A halin da ake ciki yanzu bana tare da damuwa ko wata fargaba! dalili kuwa nasan cewa duk

wanda ya dogara ga Allah tabbas zai tsaya masa, ma'kiya sunyi nufin ganin bayanka Allah bai
nufa ba, gaka nan a raye kana cigaba da samun nasara a kansu hakika Allah yana tare da kai
da duk wani mai gaskiya da zuciyar imani! ina cikin farin ciki sakamakon ganinka da rai da
lafiyarka, kuma zan cigaba da yi maka addu'a Allah ya tsareka a duk in da zaka shiga Allah
kuma ya d'aukaka darajarka duk wanda ke san ganin bayanka Allah yayi maganinsu."

Tun sanda ta fara maganar yake kallonta gabad'aya farin ciki mara misaltuwa ya Dabaibayeshi
yau ya tabbatar da cewar yarinyar na 'kaunarsa tunda ga zahiri nan, duk mutumin da zai damu
da kai ya kula da kai a lokacin da wata masifa ta sameka lallai babu shakka baka da masoyi
sama dashi.
kawai ya cigaba da murza hannunta dake cikin nashi, tsabar farin ciki ya ha nashi cewa komai
ya kawai tsura mata rikirkitattun idanuwansa wanda suke kassara mata gabban jiki.

Kunyar abinda yake takeji gefe guda kuma tausayin Hamra'u duk ya dabaibaye ta.

Ta kalleshi tana nuna masa ita da ido.

Tana zaune tsuru duk ta muzanta. ta rasa ina zata jefa rayuwarta.

A hankali ya juya ya kalleta. shima kunyar ya d'an ji amma da yake namiji ne sai ya waske ya
janyota jikinsa harda rungumeta.

Hakan ya faranta mata rai mutuk'a!

Itama Zinat din taji dadin abinda yayi.

A sanyaye tace." Yayana ya jikin? Allah ya tsare ya kiyaye gaba.

Cikin kulawa ya amsa da "Ameen ya Allah na gode sosai Allah yayi muku albarka."

Gabadaya suka amsa da "Ameen.

Uwale dake can gefe a zaune tana kallonsu tace " Wato Umaru idonka ya rufe baka tunani na
ko."?

Murmushin yayi da fadin." Uwale ke gaisuwarmu dake ta daban ce, kece uwargida fa da
tsohuwar zuma ake magani.

Tace." Ban yarda ba Umaru ni kam ina kishi da hakan.''

Dariya yayi da fadin." Ashe baki yarda da maganata ba, Uwale kafin na samu kowa ke na samu
saboda haka kada kiyi kishi ki kwantar da hankalinki."

Ta'be bakinta tayi ta mike tana kallonsu tace." Ku tashi muje duba abokin mijin naku idan kun
gama soyayyar."

Hamra'u ta rufe baki da fadin." Uwale soyayya kuma."?

Tace." Kwarai kuwa ai duk naga abinda kuke kunsa shi a tsakiya kowacce tana kwarkwasa."

Zinat maganar ta bata dariya da mamaki! wai soyayya! mutumin da bai da ishashshiyar lafiya.
koda yake shi din ma da zai samu faraga abinda zai aikata sai yafi haka.


To a takaice dai sai bayan la'asar suka fara shirin tafiya gida.

Mutumin ya wani lanjare wai shi lallai ba zasu tafi gabadaya ba dole wata ta zauna a cikinsu.

Uwale tace." Nasan wacce kake hari a cikinsu ka duba da kyau bata da lafiya cikinta ya tsufa ko
ta zauna babu abunda za tayi maka.

Shuru yayi yana nazarin maganar.

Zinat din tace." Babu komai ke Hamra'u ki zauna tare dashi Aunty Zeey ma tana tare da Asp sai
ku zauna a tare."


Hamra'u farin ciki ya cika mata zuciya, amma ta barshi a ranta bata fito dashi ba fili ba.

Uwale tace ." Hakan shine maslaha." Bai iya cewa komai ba tunda a zuciyarsa ba haka yaso
ba.

Yaso ya samu sararin da zai rage zafi da ita amma hakan bai samu ba, tsabar idon Uwale da
Hamra'u yasa ya hakura ya danne zulamarsa da turtsetsan cikin ma sha'awa take bashi.


Bayan tafiyarsu Asp ya dinga tsokanarsa da cewa lallai kada yayi wasa tunda ya samu dama
kawai yaci amarcinsa a asibiti yanda ransa yake so.


A zuciyarsa sam! bai sa abun a ransa ba, wacce yake kulafuci daban da wacce take gabansa,
itama macace amma gabadaya hankalinsa baya kanta.

Tare da Aunt Zeey suka shiga kasuwar garin sukayi saye-sayen da za su bukata na yau da
gobe.

Kowacce tana kula da mijinta dai-dai gwargwado amma dai babu wata shakuwar kirki a
tsakaninsu gaisuwa ce

1 / 8