Author : Binta Umar Abbale Category : Romantic Hausa Novels
masu kyau! ga duk mai bukata sai
yayi magana....07084653262_
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/21, 7:53 PM] Matar 'Dan Aljannah: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na
hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176
domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai
domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
_Team d'in Zinatu naga comment's dinku í ½í¸ƒ kuna yin kishi saboda Zinatu ta taimaki Hamra'u
da maganin mata! bahaushe fa yace ciwon ya mace na ya mace neí ½í¹ˆKishiya kuma 'yar uwa ce
mutukar zama yayi dadi_
*126*
To da sauki-sauki za'a ce bai sha wahala ba a lokacin da yayi tarayya da Hamra'un, sosai yayi
mamakin al'amarin ya kuma sanya a ransa cewa matarsa na daga cikin jerin salihan mata
nagari! yasan cewa abinda tayi ba kowace mace zata iya ba, yaji dadi sosai kuma ta kara
matsayi da girma a idonsa.
Haka ya dimanci Hamra'u babu dare babu rana. mutukar yana gida to tana cikin fargaba!
kalankasa ce sam bata da juria shi kuma abun haushi yake bashi adduarsa kullum shine Allah
ya sauki matarsa lafiya.
Rabo idan ya rantse babu yanda za'ayi Hamra'u ta dauki ciki sati guda kowa ya fahimta domin
mai bala'in laulayi ne.
Ta lanjare! ta gaza tabuka komai kullum tana kwance tana juyi ga zubda yawu da amai duk ta
figale!
Gabadaya ta fice masa daga rai! ya daina sha'awarta saboda yawun da take tarawa a bakinta
ga rashin wanka da tsabtar jiki, saboda cikin da suddabaru yazo mata sam bata san zubawa
jikinta ruwa.
A lokacin kuma shi sai Allah ya jarabce shi da fitina da rashin hakuri! ga matayen nasa duk
babu cikakkiyar lafiya.
A wani dare ya zunguro mata nakuda!
Domin gurfana yayi a gabanta yana rawar murya kan ta barshi yayi ko sau daya ne.
Tausayi ya bata ganin abinda yake kamar wani zautacce!
Ashe jira yake ta bashi dama yana samu ya fara sukuwa a kanta shaf ya manta da lalurar dake
tare da ita.
Ta galabaita sosai! tana rokonsa ya bari haka.
A lokacin yake jin wani karfi ji yake kamar ranar suka fara had'uwa! wasu hawaye suka dinga
sulmiyowa daga idonsa ya gaza tsayar dasu shi ya san ko na meye.
Ya samu satisfied amma a maimakon ya sauka kokari yake ya cigaba dan joystick din taki
rusina tana nan a tsaye alamun dai bata gaji ba.
A galabaice tace." Idan ba kasheni kakeso kayi ba dan zatin Allah ka bari haka wallahi dab nake
na haihu domin ni ka dai nasan abinda nakeji."
Jikinsa yay sanyi jin abinda tace.
Ya kama fuskarta ya dinga sumbata yana shan bakinta kamar ba zai bari ba.
Da kyar ya bawa kansa hakuri ya kuma yi kokarin kwantar da zulamarsa ya sauka daga kanta
ba dan ransa yaso ba.
Toilet ya nufa yana jin wani irin farin ciki a tare dashi.
Da kyar ta iya wanka tazo fitowa daga toilet din kafa ta rike ta gagara takuwa!
Ta rintse ido tana kiran sunan Allah!
Duk ya rasa yanda zaiyi ya riketa yana tambayar abinda ke damunta.
Can kasan makoshi tace." Haihuwa zanyi ciwon yafi na kullum.
Hannu na rawa ya fito da waya ya fara neman Asp domin ya turo masa Madam su shirya zuwa
asibiti.
To kafin ma Madam din ta shigo faya ta fashe.
Jin abu na dannowa yasa ta zube a gurin tana wani irin nufarfashi!
Ya riketa sosai a jikinsa yana mata sannu gabadaya tausayinta ya rufeshi.
Madam ta shigo taga halin da ake ciki. kallo daya tayi mata ta gane cewa akan ga'ba take.
Tayi-tayi dashi ya fita amma fir yaki yace lallai a hannunsa zata haihu.
Hakan nan ta kyaleshi ta gyara gurin ta shimfida wata leda sannan ta umarceshi daya kwantar
da ita akai.
A kan cinyarsa ya kwantar da ita ya zauna sosai saman ledar kamar shi zai haihu.
Nishin da kansa yake zuwa ta dinga tana kiran sunan Allah Madam din na taimaka mata. shi
kuma sai karkawa jikinsa yake gumi duk yay masa dabaibaiyi wannan tashin hankali har ina!
ashe haka mahaifiyarsa tasha gumurzu! kafin ta haifeshi! yaji wasu zafafan hawaye suna
kokarin kwace masa.
Yana can yana zulumi da rawar jiki ta haihu! kukan baby ya dawo dashi hayyacinsa!
Ya rintse idonsa yana kiran sunan Allah.
"Alhamdulillahi-Alhamdulillhi-Alhamdullahi."
Sai da ya fadi haka sau uku sannan ya bud'e idonsa.
Lokacin Madam ta daga yaron tana d'aure masa cibiya bayan ta yanke.
Duk da ya fahimci abinda ya samu sai da ya tambayeta.
Tace." Eh namiji ne gashinan tubarkalla kamar kayi kaki ka tofar."
Murmushi yayi yana sake godewa Allah a cikin ransa.
Sai da maijego da babyn sukayi tsaf sannan su Uwale suka ji labari.
Irin wannan haihuwar tana da dad'i! Uwale bakinta kamar gonar audiga godiya kawai take ga
Allah.
Hamra'u kadaran kadahan! amma a zahiri ta nuna farin cikinta, sai dai kuma babu wanda ya
san zuciyar mutum sai Allah.
Ganin yanda yake ta murna da kai kawo ya sanya itama take adduar Allah ya sauketa lafiya
domin taga irin farin cikin da zai yi.
Kwana uku da haihuwar yayi wa yaron huduba da sunan abokinsa Asp *MUSA* kenan.
Uwale tace ya cancanta hakan kuma yayi dai-dai.
Asp ya gaza boye farin cikinsa yayi ta godiya akwati uku ya ciko da kaya masu tsada na
maijego da takwaransa.
Wannan haihuwa ta janyo alkairai masu yawa! domin wani irin kyautuka ya dinga samu daga
manya manyan mutane! maijego ita kanta ta samu alkairai masu yawa daga gurin abokan
aikinsa da sauran masoyansa.
A kayi shagalin suna mai kayatarwa.
'Yan jarida masu neman labarai suka abin yayatawa a gari.
Hamra'u dai daki ta shiga taci kukanta ta koshi! gani take kamar ma yanzu babu mai kaunarta.
Mutanan *Kafur!* din ma da suke nuna mata kauna daso yanzu gabadaya sun manta da ita.
alherin da Zinat din take musu yasa sun mayar da hankalinsu gurinta, suyi tayi mata fadanci da
kirari! ita kuma tana musu kyautuka na bajinta. duk yawansu da suka zo bikin sunan sai da
suka samu alkairi daga gurinta suka tafi cike walwala da farin ciki tare da alkairai masu yawan
gaske.
'Dayyiba ta sake bazama! neman asiri wannan karan babu sassauci! ta kudiri mummunar
aniya!
Ta taki nasara samo zazzafar asiri sai dai kuma yana da had'ari tace taji ta gani zata iya.
Sai dai cikin ikon Allah kafin ta isa gida Allah ya mantar da ita sharud'an daka a gindaya mata.
Ta firgita sosai! sai ta juya domin komawa gurin bokan.
Kafin ma ta isa bukkar taji ana katantanwa! da ita ba'a ajiyeta a ko'ina ba sai a kofar gidanta!
Baki a murgude kafa da hannaye a shanye! anan gurin kudaje sukayi mata dabaibaiye yawu na
dulala a bakinta.
Cikin tashin hankali aka shiga da ita gida ana mamakin al'amarin.
Labari ya samu Hamra'u ta dinga kuka ta rikice musu lallai sai taje ta duba mahaifiyarta.
Dama yana jin haushinsu yace babu in da za taje.
Ya riga ya yanke hukunci duk wanda ya sa baki sai ransa ya 'baci!
Zinat ganin abinda yake bai dace ba, ta bullo masa ta bayan gida.
Suka dinga sa'insa! a tsakaninsu shi yana nuna mata ikonsa ita kuma tana nuna masa rashin
dacewar abinda yake, iyaye sun wuce wasa.
Ya fusata! yace." Idan ke kike da iko sai ki bata izini taje."
Ya buge rigarsa ya fita daga gidan.
Sai kawai ta yanke shawarar shedawa Asp halin da ake ciki.
Shima ransa ya 'baci sosai.
Yace." Suyi hakuri zai magana dashi.
To da kyar ya shawo kansa har ya amince.
Ya dinga jin haushi koda ya dawo gidan sabgar gabansa yake bai saurari kowa ba itama bata
kulashi saboda ta san duk rintsi ba zai kwanta ba sai ya duba yaronsa.
Aikuwa wajen sha daya na dare ya shiga dakin.
Cikin alamun bacci ta tashi zaune tana kallonsa.
Yace." Kin fara bacci ne."?
A dakile ta amsa.
Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Ya jikin abokina ina fatan zazzabin ya sauka."
Tace." Eh yanzu dai babu baccinsa yake tun dazu.
Ya kunna wayarsa yana dubashi.
Yaron yayi wayo sosai watanshi hudu yanzu kamar dan wata bakwai.
Yace." Gobe zaku shirya zuwa *Kafur!* amma a ranar zaku dawo dukkanku."
Tace." Har ita Hamra'un."?
Yace." Eh har ita domin zamanta a garin sam bai da amfani."
Cike da mamaki take kallonsa kafin tace." Ya asalin bashi da amfani bayan iyayenta da duk 'yan
uwanta suna garin.'
Yace." Mahafiyarta bata da kirki mutuniyar banza ce."
Ta dinga kallonsa da mamakin maganarsa.
Tace." Wai dan Allah me tayi maka ne ka tsaneta haka."?
Tsaki yaja da fadin." Ba lallai sai kinji ba amma bari na baki sako idan kun isa garin ki sheda
mata cewa duk wanda ya shafeni yafi 'karfinta kuma duk abinda ta k'ulla yana dawowa
kunnena."
Tace." Kai waye ya fada maka? dan Allah kada ya yarda da jita-jita na mutane.
Yace." Mutumin da ya tabbatar min da gaskiyar al'amarin mutumin arziki ne idan kina bukatar
magana dashi sai na had'aku."
Tace." Ni ina ruwana dashi kuma! sai dai kai daka yarda da maganarsa.
Ya buga mata tsawa! jikinsa na kyarma yace." Ki kiyaye bakinki. domin wannan bawan Allahn
ya tsaya miki bayan sahalewar Ubangiji shima yana taka muhimmiyar rayuwa a rayuwarki da
tuni kina kwance babu lafiya.
Ta dinga kallonsa tana mamakin maganganunsa. Wato aljanunsa ne suke sheda masa duk
abinda yake faruwa.
To ita kam a duniya me tayi wanda mahaifiyar Hamra'u zata cutar da ita.
_Ba kiyi mata komai ba tsabar rashin tsoron Allah ne_
*Wanda suke bukatar ayi musu typing da Azimi su d'aga Hannuí ¾í´ª*
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/21, 7:53 PM] Matar 'Dan Aljannah: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na
hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176
domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai
domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*BARKANMU DA SALLAH í ½í¸Š*
_*RAHMA IDRIS GA GORON SALLAH NANí ½í¹í ¼í¿»í ½í¸€*_
*127*
Da taimakon Zenat shirye-shiryen tafiya k'auyen *K'afur* ya kammala, sunyi tsaraba daidai
gwargwado sai dai shi uban gayyar yace babu in da zashi a cewarsa yana da aiki a gabansa,
Hamra'u kamar ta fashe da kuka saboda bacin rai! ta lura dashi ya dauki karan tsana ya dorawa
mahaifiyarta ta rasa meye dalili, a fakaice ta dinga share hawaye, tausayinta ya rufe Zinat din,
yana shirin fita ta sameshi a dakinsa domin ta nuna masa cewa abinda yake wa yarinyar bai
dace ba, iyaye sunfi karfin wulakanci duk d:a nagari ba zai so yaga ana wulakanta iyayensa ba.
Tana ta magana yayi shuru bai ce komai shirya jikinsa kawai yake, ya zauna gefan gado yana
daure igiyar takalminsa, tace." Magana nake da kai ka share ni abinda kake sam bai dace ba,
kuma rik'o bashi da amfani ka dai daure kaje ka duba jikin matar nan yanzu idan kuma rai yayi
halinsa mai za kace."?
Ya kalleta babu sukuni a fuskarsa yace." Da zata mutu da yafi alkairi."
Gabanta na faduwa ta dinga kallonsa tana mamakin furuncinsa.
Tsaye ya mi'ke da wayoyinsa a hannunsa.
"Ni zan fita." ya fada babu wata damuwa a tare dashi.
Ta mike da fadin." Gaskiya ka sauya halinka dan wallahi abinda kakewa yarinyar nan ba daidai
bane.''
Ya fusata! ya nunata da tsaya da fadin." Wai shin ke kike auranta ne ko kuwa? kada fa kiyi min
rashin kunya dan zan 'bata miki rai nace ban zanje ba duk abinda za'ayi aje ayi."
Ganin yanda yake magana a hasale! yasa ba ta sake cewa komai ba ta fice daga d'akin ranta a
masifar 'bace.
***
Yanayin halin da suka samu 'Dayyiba ya firgitasu, gabad'aya kammaninta sun jirkice ta rame
tayi ba'ki'kirin ba ta san ma wanda yake kanta ba. Hamra'u dai fashewa tayi da kuka tana kiran
innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! wane irin ciwo ne wannan.
Gaje 'yar uwa ce ga Dayyiba itace kuma take jinyarta, nan take sheda musu cewa an kaita
asibiti amma har yanzu an kasa gano abinda ke damunta ganin haka yasa suka dawo gida suke
na hausa.
Ta jima tana jajanta al'amarin kafin ta sauke zazzafar ajiyar zuciya, tasa hannu ta goge hawaye
daya sakko a saman fuskarta, ido ta tsira mata, tana kwance kamar jikakken tsumma! sai
gwalantu take yawu da majina na dulala, k'udaje na bin jikinta 'Yar uwarta na kore mata da
mafici.
A sanyaye tace." Allah ya sawwa'ke amma wane irin asibiti ku ka kaita."?
Tace." Na gwamnati ne."
Ta girgiza kai da fadin." Ba wai na raina na gwamanatin ba, idan babu damuwa yanzu a shirya
ta sai mu kaita na kudi idan kun amince insha Allah zanyi komai."
Gaje ta share hawaye da fadin." Wallahi da har mun hakura domin munfi gazgata cewa wannan
ciwon ba na asibiti bane amma ba za muqi ba, bari Mijinta ya shigo sai a sheda masa.
Tace." To shikkenan babu damuwa.
Uwale da tunda suke maganar ba tace komai ba sai yanzu tace." To Allah dai ya sawwake ya
bata lafiya.
Gabadaya suka amsa da ameen."
Ta juya ta kalli Hamra'u dake share hawaye tace." kiyi hakuri addua zaki mata ki daina kuka da
sanya damuwa a ranki insha Allah zan tsaya muku daga abinda ya sawwaka daga gareni.
Ta rike hannunta da fadin "Na gode sosai Allah ya saka miki da alkairi, abinda nai miki ki yafe
min."
Ta rungumeta da fadin." Baki min komai ba Hamra'u zaman tare ne, idan ma kinyi min na yafe
miki Allah ya yafe mana baki daya."
Uwale da Gaje suka amsa da "Ameen cikin yanayi na alhini da damuwa.
To koda Malam Shafi'i yaji maganar bai yi jayayya ba, lokaci guda ya amince domin
gabadayansu hankalinsu ya tashi da al'amarin.
Babban asibiti suka nufa da ita, duk irin shige da ficen da ya kamata ayi a kanta anyi a take a
lokacin ta kar'bi account din asibitin ta turawa Magajin Sarki dan uwanta domin ya tura musu
zunzurutun kudin da suka bukata kimanin dubu dari takwas da hamsin.
Shi kansa Magajin sarkin sai da ya jajanta al'amarin kuma ya tausayawa matar, saboda haka ba
tare da bata lokaci ba, ya tura kudin, aikuwa manya likitoci suka tsaya a kanta domin bata
taimakon gaggawa.
Sai da komai ya kammala sannan ita da Uwale sukayi musu sallama direba ya daukesu suka
nufi masaukinsu, Uwale ta shiga hidimar dora abinci, ita kuwa wanka tayi ta kwanta tana
hutawa, amma fa har yanzu akwai fargaba da damuwa a tattare da ita, tana da tsananin
tausayi shiyasa duk lokacin da ta tuna halin da mahaifiyar Hamra'u ke ciki sai hankalinta ya
tashi.
Kiran wayarsa ne ya tayar da ita, da lalube ta janyo wayar tana dubawa.
kamar ta ajiye wayar domin har yanzu tana jin haushin tsawar da ya