Author : Binta Umar Abbale Category : Romantic Hausa Novels
Asp sosai
amma dole tabi umarnin mijinta tunda ya gane kuransa yanzu ta tabbatar da cewar tana da
muhimmanci a rayuwarsa.
Allah ya taimaka Asp din a gidan Zeey yake, taji dadin hakan sosai, amma kuma boy yaronta
yana gurin Nabila dan tunda suka zo gidan take dawainiya dashi nono ne kawai yake kawoshi
gurinta.
Wata shawara ta yanke a zuciyarta, hijab dinta tasa ta fito falon babu kowa duk suna daki da
sauri ta kama hanyar fita shawarar data yanke kenan daga baya an kawo mata yaron.
Kai tsaye Side dinsu ta nufa, da yake bracck din akwai haske bata samu matsala ba, sai dai
haushin karnuka da suka cika mata kunne.........Kai tsaye sashenta ta nufa zuciyarta cike da
tunane-tunane masu kyau da marasa kyau.
*Kada ki karanta min littafi idan baki biya, kada ki siya ki fita dashi, 'Yar uwa kada ki ganshi a
group kiyi shearing domin hakkina ne, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500
ne.....0542382124...Binta umar gtbank. idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da
wannan number* *07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/21, 7:53 PM] Matar 'Dan Aljannah: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na
hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176
domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai
domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*132*
Asp yasha mamaki lokacin da Madam ke sheda masa cewa Zinat bata gidan, koda ya kira
wayarta domin ta bashi tabbacin inda take, sai ta hau inda-inda, da yake mutumin yana kusa
da ita shi ya k'arbi wayar yayi gyaran murya Asp yaji muryarsa ta doki kunnunsa, shuru yayi
yana mamakin al'amarin. Yace." Gata nan a kusa dani wahala ta ta k'are ai na fad'a maka dama ba'a shiga tsakanin
masoya."
Maganar ta bashi dariya yayi kadan kafin yace." Dama ni na isa na shiga tsakaninku? kawai dai
nayi hakan ne domin na nuna maka kuskuranka amma banyi da wata manufa."
Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." To daka kai har ita abinda ku kayi min sai Allah ya saka min."
Cike da mamaki yace." Yanzu dai Kana so mu nemi gafararka kenan?
Yace." Kwarai kuwa shine samun nutsuwarku domin Allah ne kadai yasa da sauran kwana na a
gaba da tuni sai dai labari na."
Asp ya fashe da dariya da fadin." Ai na kara tabbatar da cewar duk wata burga da kake da
fuffuka k'arya ce wannan yarinya itace rayuwarka gabadaya kwana biyu kacal duk ka susuce
kamar ba jarumin namiji ba."
Ya shafa gemunsa yana mata wani sihirtaccan kallo hannunta ya sake rintsiwa a cikin nasa
yace." Asp sanin abinda ke zuciyar mutum sai Allah sai kuma shi wanda zuciyar take jikinsa
amma kana hasaso gaskiyar abinda ke cikin zuciyata wannan shine gaskiyar magana.''
Ajiyar zuciya ya sauke da fadin." Alhamdulillhi abokina nayi farin cikin hakan, kuma ina rokon
Allah yasa wannan abunda ya faru a tsakaninku ya zama karshen matsalarku, Allah ya kore
fitina a tsakaninku."
Cikin farin ciki da jin dadi ya amsa da "Ameen suma ameen mutumin kirki na gode kwarai da
kokarinka a kaina da kuma iyalina, ina rokon Allah ya bani ikon kyautata maka."
Ya amsa da ameen ya rabbi kafin suyi sallama cikin karamci da mutunta juna.
*****
To alhamdulillhi bayan faruwar wannan matsala wani abu mara kyau ko tashin hankali bai sake
faruwa ba a tsakaninsu, duk wasu tunane-tunane da yake marasa kyau a da ya ajiye ya daina,
yana kokarin kyautatawa iyalinsa shi kansa sai yanzu ya gane cewa zaman lafiyar da suke
shine kwanciyar hankalinsa.
****
Kowa ya san dai abinda commissioner ya aikata ya sa'bawa dokar 'kasa wannan dalilin yasa
bayan ya warware aka gurfanan dashi a gaban mai sharia, ba tare da jayayya ba ya amsa
laifinsa, wannan dalilin yasa mai sharia ya sasauta masa, amma tabbas hukuncin kisa ne a
sauka a kanshi, saukakawa sharia da yayi baiyi jayayya ba yasa mai sharia ya yanke hukuncin
cewa a kai shi can gidan kaso (prison) na tsayin shekaru biyar kafin a kashe shi.
To ya za'ayi, bahaushe yace." Son zuciya 'bacin ta, zuciya mugun nama idan kabi ra'ayinta ta
kai ka ta baro, Allah kasa mufi karfin zuciyoyinmu.
A ranar da aka tasa 'keyar Commissioner of Police gidan kaso (prison) a ranar aka mayar da
Asp kujerarsa wato shugaban 'yan sanda abokinsa Umaru GOJE ya maye tashi kujerar mai
taken kakakin rundunar 'yan sandar jahar KATSINA. haka abokan suka wanzu cikin hidimtawa
al'umma da kare 'kasa tare da abinda ke cikinta.
****
"Aunty Maijidda miliyan biyar nakeso ki bani aro."
Kai tsaye ya fadi maganar idonsa 'kuri a kanta.
Ta kalleshi ta sake kallo takaicinsa duk ya cika mata zuciya tace." Sadiq ashe baka hankali don
ubanka me za kayi da miliyan biyar."?
Ya 'bata rai da fadin ." Kinga aunty Maijidda babu ruwanki da abinda zanyi da ita kawai ki bani
bana bukatar surutu."
Tace." Bani dashi ka tashi kuma ka fice min daga gida mara mutumci''
Cikin fusata ya buga hannun kujera ya mike tsaye yana huci! da numfarfashi yace." Ni kike kira
mara hankali "?
Tace." Eh kai ne mara hankali Sadiq ko zaka dake ni ne."?
Ya zabura! kamar zai kai mata mari! tayi saurin gocewa gabanta na faduwa take kallonsa.
Ya cize baki yana hura hanci da fadin " Zaki gane baki da wayo sai na tona miki asiri."
A gaggauce ya kama hanyar fita.
Da karfi ta kira sunansa "Sadiq." ko juyowa bai yi ba ya bude kofa ya fita kai tsaye fadar sarki
ya nufa da yake safiya ce fadar sarkin cike take da jama'a 'yan uwa da abokanan arziki da kuma
masu zuwa sulhu da sasanci.
Cikin rashin kintsi ya shiga fadar,
gabadaya ido yayi caa! a kansa.
Guri ya samu ya zauna ya tsirawa sarkin ido tamkar wanda yake binsa bashi.
Sarkin jikinsa yayi sanyi haka kawai yake tausayawa yaron, rayuwarsa ta gurbata gurin
shaye-shaye da rashin kintsi da kamun kai. wannan dalilin yasa duk abinda yaron ya bukata
daga gurinsa yake tallafa masa.
Gyaran murya yayi a nutse ya kira sunansa.
Ya amsa yana me sunkuyar da kansa kasa
Yace." Kana bukatar wani abu daga gurina.
Yayi shuru yana dawurwura! har yanzu idon jama'ar dake gurin na kansa.
Sarkin ya kalli shamaki dake kusa dashi yace.'' Wannan yaron ga dukkan alamu akwai abinda
ke tafe dashi a kawo min shi kusa dani domin naji daga gareshi.''
Shamaki ya kamo hannunsa ya tsuganar dashi gaban Sarkin kafin yace." Yaro kada kaji tsoro
ka fadi abinda ke tafe da kai, ni ina magana ne da yawun sarkin dake gabanka a halin yanzu.
Sadiq wani irin gumi ya fara yanko masa.
Wai shin ma ya akayi ya kawo kanshi gurin nan?
Idan ya tonawa 'yar uwarsa asiri ai tare suka had'u suka shirya sharrin tilas shima ya fuskanci
hukunci .
Cikinsa ya duri ruwa ya dinga wani irin k'ugi kai Allah ya tsinewa (kamru uwar laifi) sai yanzu ta
sake shi ya gane wautar da yake kokarin tafkawa.
Alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare dashi sai gumi yake sharcewa ya kasa cewa uffan sai
magana ake masa.
Sarki a jikinsa yake ji akwai matsala dan rashin gaskiyar dake tare da yaron yafi komai daga
masa hankali, addua yake akan Allah yasa ba zuwa yayi ya kashe rai ba.
Ba zato ba tsammani! Sadiq yaji saukar tsabga a bayansa.
Ya gantsare tare da kurma uban ihu! idonsa akan dogarin dake tsaye a kansa da murtukekiyar
bulala a hannunsa sai zare masa ido yake.
Cikin hargagi! yace." Hattara 'yan samari nan ba gurin harigido bane ba gurin gardama da
jayayya bane yi kokari ka fadi abinda ya kawo ka Sarki yana sauraranka."
Bulalar ya daga da niyyar sake zabga masa Sarkin ya dakatar dashi.
Ya sauke hannunsa da fadin." Gyara kintsi! Allah ya 'karawa sarki lafiya."
Fadar tayi shuru na 'yan mintina, kafin a nutse Sarki ya kalleshi da fadin." Abubakar Sadiq ni
abinda nake hasashe shine kaje ka dauko magana a cikin gari kazo ka gurfana a gabana
domin na zame maka garkuwa to ka sani cewa ni UMARU ba zan lamunci zalinci ba duk irin
hukuncin da ya cancanta da abunda ka aikata shi za'a yanke maka."
Ai kawai sai ya fashe da kuka! ya rike kafafunsa da fadin." Ranka ya dade ka gafarce ni wallahi
ba laifi na bane duk abunda ya faru Aunty Maijidda ce ta bamu umarni."
Jin ya ambaci sunan amaryarsa yasa ya tsira masa ido da mamaki a tare dashi.
Daga farko har karshe ya warware yanda akayi suka shirya sharrin amma beyi tasiri ba, tunda
wacce sukayi niyyar sabautawa rayuwa addua iyaye na tasiri a kanta, tana dakin mijinta a halin
yanzu har da zuria a tsakani.
*Kada ki karanta min littafi idan baki biya, kada ki siya ki fita dashi, 'Yar uwa kada ki ganshi a
group kiyi shearing domin hakkina ne, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500
ne.....0542382124...Binta umar gtbank. idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da
wannan number* *07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/21, 7:53 PM] Matar 'Dan Aljannah: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na
hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176
domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai
domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
_*Mafi akasari masu bibiyar littatafan BINTA mutane ne masu mutunci da karamci da kuma
dogon tsinkaye! babu yanda za'ayi suci zarafi na ko su gaya min mara dadi koda kuwa kuskure
nayi cikin hikima zasu tunasar dani domin na gyara, amma abin mamaki wasu cima zaune da
ban san da zamansu ba, sune suke cin zarafi na bayan sun karanta littafina har suna kirana da
wasu kalmomin da basu cancanta ba, NAGODE bahaushe yace anayi da kai gwara ba'ayi da
kai matakin NASARA ne, da yawa masu tsinkaye sun fahimci inda na nufa a cikin wannan
littafin nawa mai suna GOJE! Alhamdulillhi naji dadi masoya da kuka bani goyon baya har Allah
yasa na kammala isar da sakon dana dauko. Kunyi da aljihunku kana kuma kunyi da
muryoyinku, Littafin GOJE! yazo da sabon salo kowa ya sheda hakan, ina rokon Allah ya bani
rai da lafiyar da zan cigaba da nishad'antar daku tare da wa'azantarwa. daga karshe nake baku
hakuri sakamakon tsaikon da littafin ya dinga samu bayan ya dauko gangara! kuyi hakuri insha
Allah hakan ba zata sake faruwa baí ½í¹í ¼í¿»*_
*GOJE*
*(SADAUKI OMAR RETURN*)
*ENDí ½í´š*
*ALHAMDULILLHI*
*134*
Ya kalleshi cikin jadadda aniyarsa yace." Da gaske nake magana ba wai da wasa ba inaso ka
bani auran yarinyar nan domin hakan shine maslaha a gare mu bakidaya." Shuru yayi na minti
biyu kafin ya cigaba da cewa.'' Kasancewar mun riga mun sanar da jama'a ranar daurin aure a
yanzu abune mai wahala gami da jin nauyi mu sake sanarwa mutane cewa lamarin auran ya
lalace duk da cewar ba daga bangaranmu aka samu matsala ba amma da kunya, wannan
dalilin yasa naji sha'awar auran yarinyar a cikin raina nasan daga 'bangaran ka ba zan samu
matsala ba sai dai daga ita yarinyar idan da hali ka sheda mata al'amarin idan ta amince
Alhamdulillhi."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Ban yi mamakin faruwar wannan al'amarin ba Umaru,
nasan komai yana tafiya ne cikin kudirar ubangiji, wani baya auran matar wani haka zalika
wani baya haihuwar dan wani, tabbas daga 'bangarena baka da matsala, zanfi kowa farin cikin
kasancewar hakan, sai dai akwai gagarimar matsalar da nake hangowa mutukar al'amarin nan
ya tabbata."
Murmushi yayi a nutse yace." Ka kyautata zaton alkairi abokina wannan al'amari da zai faru
insha Allah alkairi ne, matsalar dai bai wuce ace rashin amincewa daga 'bangaran iyalina ba,
kada ka damu da wannan, a yanzu akwai kyakykyawar fahimta a tsakaninmu, insha Allah zan
zaunar dasu na fahimtar dasu yanda al'amarin ya kasance, burina shine ita yarinyar ta amince
shikkenan sai komai yazo cikin sauki."
Yace." Hakane Allah ya tabbatar da alkairi maganar Nabila kuma zan zauna da ita a yau da ikon
Allah komai zai zo da sauki za kuma mu tattauna da mahaifiyarta."
Cikin farin ciki ya mika masa hannu sukayi musabaha da juna kafin yayi masa sallama ya kama
hanyar fita. Asp din ya bishi da kallon mamaki! hakane kowane mutum da akwai ranarsa, dama
fargabarsa jin kunyar jama'ar daya gayyata ace kamarshi commissioner 'yan sanda ya gaza
gano wanda yazo gidansa da niyyar auran 'yarsa, wannan shine babban takaicinsa, amma cikin
ikon Allah abokinsa ya rufa masa asiri a lokacin da yake cikin tararrabi, tabbas zuciyarsa tayi
na'am da abokin nasa, baya fargabar bashi auran 'yarsa, domin shi yafi kowa sanin halinsa.
Tana cikin k'unci da damuwa sakamakon yaudarar da Sulaiman yayi mata, sai gashi Ubangiji
yayi mata tagomashi da samun nagartaccan namiji, koda mahaifin nata ya sheda mata niyyar
abokinsa a kanta, babu jayayya ta amince, domin dama can tun fil-azal mutumin yana burgeta
da kyawawan dabi'unsa, gashi d'an gayu kyakykyawa kuma jajurtaccan namiji, babu ruwanta da
matansa, tunda shi ya bukaci auranta ta amince Allah ya sanya alkairi, to itama Madam tayi
farin cikin faruwar hakan, domin dama tana cikin halin damuwa da takaici sai gashi Allah ya
share musu hawaye ya maye musu gurbi da namijin da yake da wahalar samu a wannan
zamanin, tayi addua sosai tare da fatan zaman lafiya madawwamiya.
To da yake a gidan Zeey yake bayan sun gama tattauna maganar sai yayi musu sallama ya tafi,
koda yaje can din ma kasa shuru yayi dole itama tana da hakki ta san abunda yake faruwa a
matsayinta na matarsa, nan ya sheda mata duk abunda yake faruwa.
Ko a jikinta dan bata nuna wata damuwa ba ko farin ciki ba, sai dai a can kasan zuciyarta taji
dadin kasancewar hakan, yanzu ai dole ita Zinat din ta san wacece Madam da makircinta.
Washe gari Asp din yana fita ta dauki waya domin kiran Zinat din.
Lokacin suna tare da maigidan yana shirin fita gurin aiki.
Ta daga wayar suka gaisa kamar gaske, can kuma sai Aunty Zeey din ta fashe da wata
mahaukaciyar dariya kamar sabuwar kamu.
Shi kansa Umar din dake can gefe a zaune sai da yaji taratsin dariyar.
Tace." Aunty Zeey me yake faruwa ne nifa matsala ta dake kenan."
Ta tsagaita dariyar da fadin." Murna na kira nayi miki"
Tace." Wace irin murna kuma."?
"Au zaki nake ni kenan." cikin zaurance tayi maganar.
Tace." Bangane hausarki ba don Allah kiyi magana ta fahimta mu gama na sallami mijina zai fita
gurin aiki."
Cike da mamaki tace." Sannu da kokari gaskiya na jinjina bajintarki amma ina zargin munafikin
mijin naki bai sheda miki cin amanar da suka kulla miki ba."
Gabanta ya yanke fadi, da sauri ta kalli gefan da yake, yayi saurin dauke kansa yana sake
tamke fuskarsa, cigaba yayi da daura blet dinshi.
A sanyaye tace." Don Allah kiyi min bayani.
Tace." Oh!oh! wa'ka a bakin mai ita tafi dadi nasan dai komai nisan jifa kasa zai fado amma dai
ki zauna cikin shiri nan da kwana uku zakiji bud'a! "Ayyiriririri!!!!." kawai sai ta kashe wayar tana
kyalkyala dariya.
Kafafunta sukayi sanyi kalau da kyar take jansu ga ciki tirtsitsi a gaba ta iske inda yake tsaye da
turare a hannunsa.
Wani irin yanayi ya shiga ganinta cikin muguwar damuwa! ya riga yaji komai matar abokinsa ta
fasa k'wan wanda dama yana shirin fasa shi a ranar.
Hannuwansa ya bude tana zuwa ya rungumeta yana shafa gadon bayanta cikin nutsuwa yasa
bakinsa a kunnanta ya sanyayyar da murya a hankali yace." Ta fada miki zanyi aure ko."?
Kanta ta dago tana kallonshi kafin tace." Tayi min jirwaye dai! nasan dama akwai wannan ranar