Author : Binta Umar Abbale Category : Romantic Hausa Novels
har ta fita daga falon, girgiza kai tayi tana mamakin al'amarin,
tabbas an san kishi halak ne amma a ganinta irin nasu aunty Zeey din ya sa'bawa sharia
domin kuwa zuciya za ta sanya su aikata abinda ba shikkenan ba.
Ita dai zata cigaba da hakurin zama da Hamra'u tunda dai Allah yasa yarinyar ta gane gaskiya
to sai suyi hakurin zama da juna.
*BAYAN WATA UKU*
Zaman lafiya da daidaito yake wanzuwa a gidan tun bayan dawowar Hamra'u babu wata
matsala data sake faruwa, kowacce na kokarin kyautatawa 'yar uwarta hakan yayi wa Uwale
dadi, sai dai kuma shi daga b'angaran uban gayyar babu wanda ya san abinda yake cikin
zuciyarsa sai Allah sai kuma shi, amma yana bala'in jin haushin had'e masa kai da sukayi, idan
Zinatu tayi magana a gidan to ta zauna, duk yanda yaso ya ruguza alakarsu ya kasa, a yanzu
Hamra'u tafi jin maganar Zinatu a kan tashi maganar, babban takaicinsa kenan, zai bada
umarni ayi abu amma idan ya dawo gidan sai ya tarar ba'ayi ba.
Hamra'u cikinta wata bakwai ta gaza komai ta lanjare abinka da mara jiki, cikin har rinjayarta
yake saboda girmansa, anyi scanning an tabbatar da cewa twins 'yan biyu ne duk mata,
wannan dalilin yasa likita ya kafa mata dokoki, wannan bai dameta ba tunda akwai kyakykyawar
fahimta a tsakaninsu, gabadaya ta tattara mijin ta barshi a gurin Zinatu......Hakan yayi masa
dadi mutuka, amma bai nuna ba, sai ma ya fara wasu irin zantuka domin neman magana da
tada zaune tsaye.
Cike da mamaki ta kalleshi bayan ya gama maganganunsa.
"Ta nan ka bullo kuma."?
Ta fada tana masa kallo na rashin fahimta.
Yace." Eh kwarai kuwa ai gaskiya ce, gabadaya kin tattara komai kina zalintar 'yar mutane duk
abinda ki kace shi za'ayi idan kina tursasa Hamra'u to ni baki isa ba."!
Cike da karsashi da kwarin gwiwa yake maganar.
Ta danne bacin ranta dalili ba taso suyi hayaniya hakan babu amfani, amma ta lura kwana biyu
neman masifa yake da ita.
"Kai yanzu dan Allah ba kaji kunyar fadin wannan maganar ba."?
Shuru yay mata yana duba wayarsa.
Ta girgiza kai cikin 'kunar zuciya tace." Ka tashi ka tafi dakin nata ai ba rike maka kafafu nayi ba,
domin bani na gayyatoka ba."
"Ba za'a tashi ba." ya fada yana watsa mata harara!
Ta daga masa hannu da fadin." To tunda abun ya kasance haka kaje can ku yanke shawara da
matarka, amma kada ka kara shigo min daki ranar girkinta."
"Kin riga kin lalata min ita yaushe zanyi magana taji ta saurara."
Ta dinga kallonsa da mamakin furucinsa ta rasa wane irin hali ne dashi kwana biyu ya d'ora
mata karan tsana masifar yau daban ta gobe daban.
Tashi tayi ta fita daga dakin ta barshi, shi kad'ai ya gama duk wasu uzurinsa ya fito cikin milk
din jallabiya, tana zaune a falo tare da Marakisiyya suna kallo yazo ya fita yana baza 'kamshin
turare, bayanshi tabi da kallo tana ayyana wasu abubuwa a kanshi gabadaya ya sauya halaye
sai tsiro musu da abubuwa yake marasa dadi.
Babu kunya a daran ya lallabo da bukatarsa, aikuwa ta furje tace." Tunda yana zarginta da
zalinci to yaje can gurin matar tasa ya biya bukatarsa itama ta daina yarda tunda abun arziki
yana zama sharri
Yayi-yayi da ita ta'ki, sai ya shiga kwantar da kai yana yi mata dadin baki tai masa banza ta
cigaba da gyarawa yaronta shimfida.
Kallonta yake yana lumshe idonsa lokacin tana sanye da karamar riga iya gwiwa mai santsi duk
ta kwanta a jikinta komai yana gani a idonshi, hallitarsa ta sanja wata irin jaraba ce take cinsa.
ya dinga wani micincina ido yana shafa gemunsa.
Ta gama komai ta nemi guri ta kwanta duk yana kallonta.
Kallonsa tayi da fadin." Idan zaka fita ka kashe min fitila.
Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace ." Kina tunanin kinfi karfina ko."?
Da sauri tace." Me za kayi min to ko ka danne ni kayi ta karfi babu abunda zaka samu."
"Haka ki kace."?
Shareshi tayi, ta gyara kwanciyarta tare da rufe jikinta da bargo.
Ya tashi yaje ya kashe fitila ya dawo gaba gadi gadon ya nufa.
Da sauri ta tashi zaune tana kallonshi yana kokarin cire rigar jikinsa.
Kamar ya san abinda take shirin aikatawa yayi gaggawar rike hannunta rikon tsauri yayi mata
ya fara gudanar da abinda yake ganin shine mafita a rayuwarsa.
To da yake sun riga sun zama daya ya gama gane lagonta duk turjiyar da take masa abu daya
yayi mata ta bada kai bori ya hau, dan har sai da ta fishi ficewa daga hayyaci! ita dashi a
wannan fagen ba'a cewa komaií ¾í´
*****
To har yanzu dai Commissioner yana kwance a asibiti tare da kyakykywar kulawa daga manya
likitoci hakan ba yana nufin komai ya wuce ba, Aa ana so ya warware ma'ana ya samu sauki a
yanke masa hukuncin da ya dace da abinda ya aikata a matsayinsa na wanda yayi rantsuwa da
Allah cewa ya dauki amanar kula da k'asa da kuma al'ummar dake cikinta, iyalinsa na cikin
tsantsar tashin hankali duk da cewa basu rasa komai ba na rayuwa amma tabbas suna da
tabbacin cewa hukuncin da za'a yanke masa mai tsauri ne, dalilin gagarimin laifin da ya aikata
na cin amanar k'asa.
******
Haihuwar Hamra'u tazo da tangard'a, wannan dalilin yasa babu shiri aka shiga da ita dakin fid'a
domin ceto ranta da abinda ke kwance a cikin nata.
Anyi cikin nasara an ciro tagwayen mata kyawawa farare tas masu kama da ita lafiyarsu lau,
itama kuma alhamdulillhi, ta tashi da hankalinta an kuma kira sunanta ta amsa.
Wannan ya sanya hankalinsu duk ya kwanta ganin yanda Allah ya takaita wahala komai anyi
cikin nasara da amincewar ubangiji.
Allah kenan kana taka yana tasa, a daran Hassanar ta mutu ta bar Husainar, likita ya tsananta
binkice gurin gano dalilin mutuwar yarinyar bai ga komai ba dan Ubangiji bai so ya gani ba,
kawai dai ya kar'bi abarsa ne bayan ta nuna kamanni.
Ban ta'ba ganin kukan Umaru ba sai a ranar ya dinga share hawaye yana kallon Usainar yaso
Allah ya hada duka ya bar masa domin da haihuwar yaran Allah ya jarabceshi da masifar son
su.
Hakanan sukayi hakuri suka barwa Allah ikonsa.
Kwananta goma sha hudu sati biyu kenan aka sallamesu suka koma gida lokacin ta warware
sosai tana iya komai da kanta sai dai wasu abubuwan Zinat din ke mata ko kuma ta sanya daya
daga cikin hadimanta suyi mata.
Kwana arba'in da biyu da haihuwar jini ya 'balle mata, hankali a masifar tashe suka nufi asibiti
aka fara bata taimakon gaggawa!
Sai da kwana ta biyar a kwance a asibiti sannan ta samu sassauci, likita ya kafa sharudai da
dokoki kafin ya sallameta suka koma gida.
Ba batun bin ba'asi ya shigo dakinta ya rufe ta da masifa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita
ba, a ganinsa Ita take cutar yarinyar har hawan jini yake so ya kamata.
Wannan al'amarin yayi bala'in 'bata mata rai! da yake shad'ain yana kusa! abinda yake so
kenan! sai ya kara rura wutar rikicin suka dinga masifa yana fada tana fada karshe dai 'bacin
rai yasa yace ta fitar masa daga gida, ita kuma tayi rantsuwa ita din 'yar halak ce sai ta fitar
masa daga gida kamar yanda ya bukata. amma kafin hakan dole ta in da aka hau ta nan ake
sauka.
Wayar Asp ta kira domin sheda masa halin da ake ciki...
[5/21, 7:53 PM] Matar 'Dan Aljannah: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na
hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176
domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai
domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*131*
Cikin girma da dattako aka saukeshi, yanda ake karramashi da mutuntashi ya sanyayar masa
da jiki, anya kuwa zancan zucci yake shida zuciyarsa.
Gama cin abincinsa ke da wuya magajin sarki ya shigo, cikin sakin fuska da wasa da dariya
suka sake gaisawa kafin ya isar da sakon da yake tafe dashi cewa maimartaba na bukatar
ganinshi.
Duk kwarin kansa da jarumtarsa sai da gabansa ya fadi jin cewa maimartaba na bukatar su
tattauna, ko babu wannan dalilin haka kawai mutumin yake masa kwarjini!
Yayi kokarin danne fargabarsa ya mike tare da aro jarumta yabi bayan magajin sarkin dan amsa
kiran da ake masa.
Yaji dadin ganin sarkin shi kadai, ya cire takalmansa a nutse ya shiga fadar da sallama a
bakinsa.
Shima ya amsa fuskarsa a sake hakan zai nuna maka cewar yana farin ciki da zuwan Umar
din.
Ya zauna kusa dashi daga kasan kafafunsa irin zaman rakuma yayi kai a kasa yake mika
gaisuwarsa.
Cike da annushuwa ya amsa yana tambayarsa hanya tare da iyali.''
Ya amsa da "Kowa lafiya lou ranka ya dade duk suna gaisheku"
Yace."Muna amsawa da kyau Umaru naji dadin zuwanka ina fatan dai babu wata matsala dake
faruwa tsakaninka da iyalinka, domin ni babban burina a duniya ace yara na suna zaune a
dakin mazajensu da dadi babu dadi ayi hakuri da juna domin shi aure ibadah ne, kuma jin
dadinsa kadan ne don haka ayi hakuri da juna ana kai zuciya nesa."
Yayi kwatakes da jin nasihar da sarkin yake masa, wannan ya tabbatar masa da cewa yarinyar
bata gidan, dan haka da sauri yace." Insha Allahu zamu kiyaye za kuma muyi iyakacin bakin
kokarinmu gurin kwatanta adalci sai dai dan adam tara yake bai cika goma ba, ranka ya dade
ina neman afuwa dangane da abubuwa na rashin dadi da suka dinga faruwa a can baya sharrin
shadain ne, yanzu alhamdulillhi muna zaman lafiya da juna babu wata matsala da ikon Allah.
Yace." Alhamdulillhi Umaru babu wani bawa da zai kasance a duniya ba tare da kuskure ba,
saboda haka kada ka damu dangane abunda kake tafe dashi, na amince da kai dari bisa dari,
shine dalilin da yasa na dauki 'yata na baka aure, saboda haka magana tuntuni ta wuce a
gurina, Allah ya kiyaye gaba."
Cike da kwarin gwiwa ya amsa da "Ameen.'' yana jin sanyi a zuciyarsa yanzu ya kashe matsalar
yana da tabbacin cewa ko zuwa tayi ta kawo k'ararsa mahaifin nata ba zai saurareta ba.
Ya wani risinar da kai cikin sigar girmamawa yake ta godiya da irin alkairin da akayi masa
Wannan abunda yake ya kara kankaro masa daraja da mutunci a idon sarkin.
Tun a mota ya kira wayar Asp yake sheda masa abinda ke faruwa.
Asp din yace." Ikon Allah ni kuma kaga yanzu muka gama waya da ita ta bani tabbacin cewa
tana KANO din gidan Hassana 'yar uwarta.
Dogon tsaki yaja ya girgiza kansa dake bala'in sara masa yace." Kaga ni yanzu na wucr bichi na
kusa isowa gida amma tilas na juya baya tunda ka tabbatar min da gaskiya.
Sam bai bashi tausayi ba, yace." Eh hakan shine maslaha amma ka fara sheda mata zuwanka
ta waya bayan haka kuma ka tanadi kalaman da zasu tausasa mata zuciya."
Ya hadiye wani kuttun takaicin da ya tokare masa a wuya, wai shin da Asp yake wannan
maganar shi yafishi sanin abinda zaiyi, gabadaya ma haushin Asp din ya kamashi ya kashe
wayar ba tare da yayi masa sallama ba.
A kalar motar ya juya da tunanin abinda zai faru idan suka hadu
[5/14, 6:44 PM] Matar 'Dan Aljannah: Sai bayan isha'i ya shiga unguwar tarauni a cikin unguwar
gidan Hassanan yake, gidan bai bace masa ba duk kuwa da cewa zuwanshi daya.
Parking dinsa keda wuya mijin Hassanar ya fito daga gidan da cazbaha a hannunsa da alama
massalaci zai shiga.
Ya karasa bakin motar yana mamakin maganinsa.
Akwai sabo a tsakaninsu duk da ba'a gari daya suke ba amma sa'i da lokaci suna gaisawa a
waya.
Ya mika masa hannu suka gaisa cikin girmama juna.
Alhaji Sa'ido yace." Allah dai yasa lafiya Umaru na ganka cikin dare wallahi ba kaji yanda jikina
yay sanyi ba.
Jin abinda yace ya sanya shima jikinsa mutuwar yace." Alhaji Zinatu ba ta gidanka kenan."?
Ya gyada kansa da fadin." Eh ai ni rabon da in sanya Zinatu a idona har na manta sai dai wani
sa'in muna gaisawa a waya a duk lokacin da suke waya da 'yar uwata na kan bukaci ta bani ita
mu gaisa."
Wani zazzafan gumi ya karyo masa, gabadaya ya rasa yawu a bakinsa kafafunsa ne ma suke
rawa gabadaya ya rasa yanda zai bullowa al'amarin, kawai sai ya shiga kici-kicin bude mota ya
shiga.
Alhaji Sa'ido yace." Umaru akwai matsalar da take faruwa tsakaninka da iyalinka ka nutsu ka
tsaya mu tattauna sha'anin mata sai hakuri."
Ya shiga motar ya zauna yana kokarin tayar da ita yace." Alhaji afuwa kayi min hakuri tabbas
hasashenka gaskiya ne sai dai a halin yanzu bani da nutsuwar da zan tsaya nayi wata doguwar
magana saboda wani dalili don Allah idan ka shiga gidan ka mika min gaisuwata."
Jiki a sanyaye yace." To shikkenan Allah yayi mana magani, Allah ya kiyaye hanya."
Ya amsa da "Ameen ya rabbi Alhaji na gode kwarai."
Alhaji Sa'ido bai gusa da gurin ba har sai da ya ga b'acewar motar daga layin gidan nasa
sannan yayi addua a zuciyarsa ya kama hanyar massalaci kamar yanda ya dauki niyya.
Sai da ya hau titi sosai sannan ya lalubi wayarsa dan ya gaza hakuri yana tokin motar ya kira
wayarta.
Ta daga da sallama , a bakinta.
Muryarsa ya raunata da fadin." Kina so zuciyata ta bindiga ko."?
Tai masa shuru ba tace komai ba.
"Kin mayar dani shakatafi kina min yawo da hankali so kike na kwana a kan kwalta ina
galantoyin neman in da kike."
Zumbura baki tai da fadin." Na maka fa ina gidan Aunty Hassanata''
Ya fesar da wani zazzafar huci! cikin kunar zuciya yace." Daga can nake kuma Alhaji Sa'idu ya
tabbatar min da cewa bakya nan okey tunda kina so na shiga tsakiyar motoci su bugeni
shikkenan bukatarki sai ta biya." Da sauri ya kara karfin motar ya figeta da mugun gudu! yana
sane yayi hakan.
Aikuwa hankalinta ya tashi jin k'ugin motoci da iska a kunnanta.
Kashe wayarsa yayi ya Ajiye ya saisaita tafiyar da motar.
Gaza hakuri tayi ta fito daga daki hankalinta duk a tashe take shedawa Asp abinda yake shirin
faruwa.
Yace." Rabu dashi duk barazana ce kada ki kuskura ki sheda masa kina gidana."
Maganar sam bata gamsheta ba, gabadaya ma hankalinta ya karkata kansa.
Ta dauki waya ta kira shi sai da ta kusa katsewa ya daga, bai saurari maganarta ba yace." Sha
biyu dai-dai na dare za'a kawo muku gawata."
Gabanta yana faduwa tace." Wace irin magana ce wannan ka daina don Allah."
Yace." Allah idan baki fada min inda kike ba to ba zan dawo gidan da lafiya ba, gani ma zaune a
mota cikin wani daji."
A sanyaye tace." Amma dai kasan abinda kayi baka kyauta ba ko."
"Na sani kuma na baki hakuri ai kowane dan adam yana laifi mai zai sanya ba zaki yafe min
ba."
Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace." Na yafe maka amma don Allah kada ka kara
zargina da wani abu bana jin dadin hakan Hamra'u da 'ya'yanta bani da nufin cutar dasu.
Ya sake jin wani sabon so da kaunarta na ruruwa a zuciyarsa......."Zinatu baki da matsala dani
na amince dake dari bisa dari na kuma tabbatar da cewa ke alkairi ce a tare dani abinda ya faru
tsakaninmu sharrin shadain ne amma da izinin Allah hakan ba zai sake faruwa ba.
Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Ameen ya Allah yanzu kana ina."?
Ya gyara zamansa kan kujerar motar da fadin." Ina hanya insha Allah nan da lokaci kankani zan
iso ina fatan nazo na sameki a gidana."
Tace." Insha Allahu dama banyi nisa ba, ina gidan abokinka."
Cike da mamaki yace." Wa kenan."?
Jim tayi kafin tace." Wa kake dashi bayan Asp ina gidanshi."
Murmushin takaici yayi yace." Dama sai da na zargi hakan a zuciya wato hada baki kukayi
domin ku wahalshe ni ko ."?
Murmushi tayi ba ta iya cewa komai ba.
Yace." Zan kashe waya amma ki tabbatar da cewa na sameki a gida."
Tace." Kada ka damu kai dai kayi draving a nutse."
Yace." Insha Allah."
Kashe wayar tayi tare da tunanin yanda za'ayi ta iya fita daga gidan, tana jin kunyar