GOJE par 5 End writing by Binta Umar Abbale -1.pdf

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 8

9K to 12K   out of 21.2K words

buga mata sai kace wata
'yar cikinsa


Ta dauki wayar tare da daidaita yanayin maganarta.

"Barka da yamma." shine ya gaisheta.

Ta amsa da fadin."Barkanmu dai ya aiki."?

Yace." Alhamdullhi fatan kun sauka lafiya."

A takaice tace."Lafiya lau."

Yace." Ina yaro na."? jim tayi kafin tace." Tun bayan zuwanmu Kawu Ado ya turo aka daukeshi
yana dai can gidansa.

Yace." Naji dadin hakan.".

Shuru ya ratsa na second biyu, ta daure tace "Baka tambayi mai jiki ba."

Yace." Ai nayi ta kiran wayar Hamra'un bata dauka ba."

Murmushin takaici tayi kafin tace." To ta yaya zata daga wayarka bayan kana tsangwamarta
ranar lahira za'a tuhumeka kada ka kira sunana dan wallahi ni ba zaka had'a baki dani ka cuci
matarka ba."


"Allahu akbar malama sai ki fada min cutar da nayi mata, wai shin mai yasa kike kokarin dora
min laifi ne."?

Shuru tayi masa takaicinsa duk ya isheta.

Yace." Bani Uwale mu gaisa domin ina da Uzuri."

Tace." Yawwa dama akwai maganar da zan fada maka."

Yace." Wace magana ce."?

Ta jima tana tunanin hanyar da zata bi gurin sheda masa halin da ake ciki, da kyar dai tayi
shahada ta fara fada masa mawuyacin halin da suka iske mahaifiyar matar tasa a ciki da irin
taimakon da tayi mata.


Ya gama saurara tsaf har ta kammala, ya ja dogon tsaki da fadin." Wanene ya saki aikata
hakan."?

Tace." Babu kowa tausayi ta bani wallahi har sai dana zubar mata da hawaye.


Yace." Zakiyi wani kukan domin wannan da ki kayi shafar mai ne, abinda nakeso dake yanzu
shine maza ku dauko matar nan daga asibiti domin lalurar dake damunta bana asibiti bane.


Shuru tai masa domin bata tsammanin aikata abinda ya umarce ta.


Yace." Ko ba kiji abinda nace ba."?

Jiki a sanyaye tace." Naji.''

Ya kashe wayarsa ransa duk a 'bace! ya tsani kankanba! a lokacin da take shaida masa abinda
ta aikata yaji a jikinsa cewa akwai abinda zai faru, aikuwa a daran jikin Dayyiba ya rikice wasu
manya manya kuraje suka feso a jikinta! sunyi jawur! sun d'uri ruwa sai kaikaiyi suke mata tana
zumduma ihu!

Su kam likitocin babu wata damuwa a tare dasu suke gudanar da aikinsu, suka dinga zurkud'a
mata karfe suna fashe k'urajen suna matse wani irin ruwa mai wari da kauri da jini babu kyawun
gani.


Al'amarin ya tsananta sosai gabadaya jikin Dayyiba ya baibaiye da Kuraje babu masaka tsinke,
dan koda suka isa asibitin suka iske halin da ake ciki sai da hankalinsu ya tashi.


Gaje na goge guntun hawayen fuskarta tace." Hajiya Zinatu kinga yanda abu ya dawo ko
shiyasa nace wannan lalurar bana zuwa asibiti bane.

Jiki a masifar sanyaye tace." Nima naga alamar hakan saboda haka bari na samu likita muyi
magana idan da yuwuwa a bamu sallama muje gida.


To shima likitan dai bai yi jayayya ba, domin ansha kawo masa marasa lafiya irin wannan,
sukan yi iya bakin kokarinsu akai idan ya gagaresu kawai sallamar mutum suke tare da fadin
aje a gwada na hausa.


Amma bai basu sallama a ranar ba yace. sai zuwa gobe tukkuna.

Aikuwa a daran rai yayi halinsa, Dayyiba ta amsa kiran ubangiji, INNALILLAHI WA'INA ILAIHI
RAJI'UN!


Mutuwar tayi masifar girgizata ba kadan ba, ta dinga kiran sunan Allah a zucci a bayyane.

Gari ya kacame! da surutu! kace nace! kowa da abinda yake fada cewa kishiyar Hamra'u ce
sanadiyar mutuwar Dayyiba.
Da yawa wasu sun yarda da hakan, amma wa'inda basu yarda ba sun fi rinyaje.

Ita dai uwar dakin Uwale ta shiga ta kwanta tana kuka, dama sai da mijinta ya gargad'e ta
amma taki jin maganarsa.

Hawaye take sharewa tare da adduar Allah ya fitar da ita.

Har akayi jana'izar Dayyiba tana kwance a daki domin fargaba take taje gidan mutuwar saboda
tana gudun abinda zai biyo bayan zuwan nata.


Koda ya samu labarin mutuwar matar bai damu ba, a ganinsa mutuwar itace tafi mata alkairi,
koda taji sauki ta dawo gida wahala zata sha ayi ta fama da ita dan ba zasu ta'ba fahimtar me
ya janyo faruwar hakan ba sakamako dai ya bayyana a yanzu alamu sun nuna cewa ta shiga
hurumin babban aljanin da baya son wargi.

A daran ranar wani mugun zazzabi mai zafin gaske ya rufe ta, ta rufe jikinta a gado tana ta
makyarkyata da faduwar gaba, ba komai ne ya janyo mata wannan zazzabin ba sai fargaba da
tashin hankalin faruwar al'amarin da take ganin kamar itace silar faruwarsa.

*Kada ki karanta min littafi idan baki biya, kada ki siya ki fita dashi, 'Yar uwa kada ki ganshi a
group kiyi shearing domin hakkina ne, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500
ne.....0542382124...Binta umar gtbank. idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da
wannan number* *07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/21, 7:53 PM] Matar 'Dan Aljannah: _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na
hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176
domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai
domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._



*128*

*(Rahma Idris) daughter (Zainab Khabir Ishak) da sauran magoya bayan wannan littafi na
GOJE ina mai baku hakuri, hakikanin gaskiya na san dole ranku ya 'baci, na rashin samun
Update kullum kamar yanda nayi alkawari, Kuyi hakuri nima ba sa'an raina ba, haka Allah ya
tsara min ina cikin jarabawarsa😭 a halin yanzu bani da nutsuwar typing, abubuwa da yawa sun
dameni, wannan shine cikar mumuni, dole rayuwa ta tafi da jarabawa, muna rokon Allah ya
jarabce mu da irin wacce za mu iya daukaí ½í¹í ¼í¿»*

*KUYI HAKURI KU SANYA NI CIKIN ADDUARKUí ½í¸­í ½í¹í ¼í¿»*


Da zazzabi ta kwana ta tashi, jiki ram! duk ta fyade tayi wata irin rama ido yayi zuru-zuru!
Uwale hankalinta ya tashi, ita ta dinga dawainiya da ita kafin Umar din ya sauka a garin.
Ganin halin da take ciki ya sanya jikinsa sanyi, ya umarce da ta shirya maza suje asibiti likita ya
dubata, kafin ya dawo daga gidan mutuwar, domin yana so su kama hanyar gida a ranar.

Uwale tace." Daka bari ayi sadakar uku mana."

Kansa kawai ya girgiza ya sanya takalmansa ya fita da sauri.

Kai tsaye gidan mutuwar ya nufa.

Duk da yana jin haushin mai mutuwar sai da ya tausayawa iyalinta. ya shiga har cikin gidan
yayi musu gaisuwa, jama'a sukayi caa! a kansa, sai ya dinga jin kunya da nauyi abinda ya faru
yasan da yawa daga ciki akwai abinda suke tunani a kansa da matarsa.

Sai da ya fita daga gidan kana ya samu yaro ya umarceshi daya kira masa Hamra'un sosai
yarinyar ta bashi tausayi .


Ta fito ta sameshi yana waya.

tsayuwa tayi jikin bango( garu) tana kallonsa itama duk ta rame abinka da mai k'aramin ciki
fargaba da laulayi sun sanyata a gaba.


Cikin kulawa ya kalleta da fadin." Ya karin hakuri."?

Wasu hawaye masu zafi suka kwace mata.

Ya girgiza kansa da fadin." Kiyi shuru ki daina kuka addua zaki cigaba dayi mata.

Ta share hawayen fuskarta tana sauke ajiyar zuciya.

Yace." Jikin naki da sauki ko."?

Kanta kawai ta iya dagawa.

Minti biyu yana kallonta kafin yace." 'Yar uwarki ma babu lafiya sakamakon abinda ya faru ina
fata dai kinyi mata kyakykyawar fahimta akan lamarin.

Taja hanci kanta a sunkuye tace." Wallahi bana zargin aunty Zinat domin da kyakykyawar niyya
a zuciyarta, kawai dai lokacinta ne yayi, suma mutanan dake zarginta dan basu san wacece ita
bane.

Ya jima yana kallonta kafin yace." Naji dadin hakan sannan ina fatan suma sauran mutanan
dake zarginta su gane gaskiya.

Shuru tayi ba tace komai ba.

Hannu yasa cikin aljihu ya dauko kudi da yawa ya bata da fadin ." Ayi sadaka insha Allah ranar
adduar bakwai zan dawo sai mu tafi tare.

Tace." Zaku tafi ne yau."?

Kai ya daga yana duba agogon dake daure a hannunsa.

Jikinta duk ya mutu jin cewar zasu tafi.

Ya kalleta tare da d'an girgiza kansa hakurin dai ya sake bata kafin yayi mata sallama ya fice
daga soran gidan.


A tsaitsaye ya gaisa da Kawunansa kafin ya isa gidan ta shirya tsaf tana zaune gefan gado
tare da kokon fura da nono a hannunta, tunda tayi wanka da ruwan dumi taji sassauci.

Uwale dai cewa tayi sai ranar adduar bakwai idan yazo sai su tafi domin yanzu tana iya tafiya
surutu ya biyo baya, abinka da kauye.

Sai da sukaje asibiti aka dubata kafin su dauki hanyar gida, ita dashi babu mai magana, sai
yaronsu dake wasa da gwalantu a kwance a bayan mota.


Sai wajan biyar da rabi suka isa gidan.

Da kanshi ya bude mata motar ta fito jikinta duk yayi tsami! kafafuwanta ma rawa suke da kyar
take tafiya, ya bita da kallo kafin ya girgiza kai ya sunkuya ya dauko d'ansa yasa a kafada ya bi
bayanta dashi.


Zaune a gefan gado ya sameta ta hada ta gumi hawaye na zuba saman fuskarta.

Ya dora mata yaron a jikinta dan kuka yake alamar yana bukatar nono.

Nonon ta fito dashi tasa masa a baki ya kama yana tsotsa.

Kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya ita dashi.

Yace." Naga kin sanya damuwa a ranki har da ciwo hakan da kike zai janyo miki wata damuwar.
domin ita wannan matar lokacinta ne yayi, nasan kuma kin san da cewa mutuwa dole ce, baki
da laifi tunda ke taimako ki kayi, Allah kuma da zuciya yake hisabi.


Taja hanci tana girgiza kanta tace." Wallahi nayi dana sanin zuwa garin nan, domin da nasan
abinda zai faru da ban daga hankalina ba, ashe tsautsayi ne yake kira na."

Yace." Babu wani tsautsayi ko kinje ko baki je ba lokacinta ne yayi zata mutu saboda haka ki
cire wata fargaba daga ranki.

Shuru tayi ba tace komai ba,

Ganin haka yasa ya nufi toilet domin wanke jikinsa shi kansa da fargaba da damuwa ya wuni ga
wata irin yunwa da take damunsa.


Washe garin ranar da ta dawo Aunty Zeey tazo, sosai taji dadin zuwanta, suka dinga hira, har ta
gaza boye mata abinda ke damunta ta sheda mata, ita kanta aunty Zeey din sai da jikinta yayi
sanyi kuma ta tausayawa Hamra'un.

Suna tsaka da hira Madam da Nabila sukayi sallama.


Cikin sakin fuska ta amsa ta mike domin girmamawa. gurun zama take nuna mata, ita kuwa
aunty Zeey din kamar wacce aka aikowa da mutuwar iyayenta, muraran ta fito da bacin ranta da
kishinta.


Madam wayayyar macace mai ilimi da sanin ya kamata, ta kalleta da fadin." Zainab kina nan
kenan."?

Ta dauke kai da fadin." Aikuwa."

Murmushi tayi kafin ta juya tana amsa gaisuwar da Zinat ke mata, a mutunce suka gaisa
Madam tayi mata gaisuwa daman abinda ya kawota gidan kenan.


Aunty baki a tabe ta kalli Nabila da fadin." Ke kuma kin isa kenan babu wanda yake da
mutuncin samun gaisuwarki a cikinmu.

Tace." Haba dai Aunty Wallahi ina ta gaisheki ba kiji ba sai nace bari ku gama gaishe-gaishe sai
mu gaisa a nutse.

K'aramin tsaki taja ta kawar da kanta.

Itama Nabilan taji takaicin abinda tayi mata amma sai ta daure ta sake gaisheta, ta amsa kamar
bata so.

Ta juya ta gaishe da Zinat din tare dayi mata gaisuwa. ta amsa a sake da nunawa kulawa.

Ba su wani zauna ba suka suka tashi da niyyar tafiya, har bakin kofa ta rakasu tana godiya.

Tana juyowa suka hada ido da Zeey sai harararta take, taja tsaki mai karfi kafin tace." Wannan
matar kike wa ladabi matsiyaciya sumu-sumu macijin sari ka noke.

Ta zauna kujerar dake fuskantarta tace." Aunty zeey me yasa kike zagin Madam ne? wallahi ni
duk laifinta da kike fadi ba tayi min komai ba.


Tace." Dama yaushe za tayi miki tunda baku hada miji ba, matsiyaciya ai gashinan tana zaune
da god'amemiyar 'yarta taki auruwa, babu mashinshini."


Cike da mamaki tace." Aa kamar an sa ranar auranta.

Tsaki taja da fadin." A bakin wa ki kaji babu wani mai so bakin jinine da ita.

Yar dariya tayi kafin tace." A bakin maigidana naji cewar dashi aka karbi kudin auranta an sanya
shekara guda.

Aunty Zeey jikinta yayi sanyi ta zuba mata ido da mamaki a tare da ita.

Tace." Wallahi kuwa kin san abinda yayi Asp shi yayi mijina shiyasa na samu labari.

Tace." Aikin banza to meye abin rufa-rufa dan ya fito ya fada min wani abune mtwwws! ni na
rasa me yake damun Asp wallahi matar nan gabad'aya ta shanye shi sai abinda tace masa.....


*Kada ki karanta min littafi idan baki biya, kada ki siya ki fita dashi, 'Yar uwa kada ki ganshi a
group kiyi shearing domin hakkina ne, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500
ne.....0542382124...Binta umar gtbank. idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da
wannan number* *07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/21, 7:53 PM] Matar 'Dan Aljannah: _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na
hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176
domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai
domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya

muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._





_*(Uwace ita a gurina kuma 'Yar uwa ce, ina jin ita din kamar 'yar uwa ta ta jini, ta damu da
damuwata😭 ta kasance kullum mai min addua da fatan alkairi, na rasa a wane matsayi zan
ajiyata a zuciyata, tana kira na da Mamana, ni kuma ina kiranta da Daughter, dalilin rubutuna
muka hadu, tsayin shekaru hudu muna tare abin farin cikin kuma muna gari d'aya, Daughter
ZAINAB KHABIR ISHAK koda nisan in da kike ya kai birnin sin sai nayi fatan Ubangiji Allah ya
sadamu da juna, to ballanatana muna cikin gari daya, wannan zumuncin zai cigaba da
wanzuwa da ikon ALLAH. na jinjina miki k'warai Allah ya saka da alkairií ½í¹í ¼í¿»)*_



*129*
Cikin nazari take kallonta tana auna maganganunta, ba tun yau ba ta lura da cewar tana da
masifar kishi irin wanda ba a so, to idan ba hakaba meye laifin Madam mace mai mutunci da
sanin ya kamata, a ganinta idan haka duk kishiyoyi suke to babu shakka za'a samu maslaha a
zamantakewa, amma Zeey ta tsawwala da yawa, tunda suke da Madam bata ta'ba zagin Zeey
ko ta fadi wata mummunar kalma a kanta ba, amma ita a koda yaushe cikin zagin matar take.

Ajiyar zuciya ta sauke tace." Zeey ki sanyawa zuciyarki salama don Allah kiyi tsaftataccen kishi,
ba wai ina goyan bayan Madam bane amma a ganina kamar bata da matsala da zakiyi hakuri to
babu shakka zaku zauna lafiya."

Tsaki taja da fadin." Na lura dai tsakaninmu babu amana fuska biyu gareki Zinat idan ba haka
ba mai zai sanya a gabana kina goyan bayan mutsiyaciyar matar nan da kowa ya san da cewa
mutuniyar banza ce wacce babu abinda tasa a gaba sai bin bokaye da zinace-zinace duk
domin biyan bukatarta." cikin masifa da kumfar baki take maganar.
Ita dai tsabar mamaki kasa cewa komai tayi, kawai ta dinga kallonta tana jimanta al'amarin.

Tana cigaba da zagin Madam din ta lalubi mayafinta ta yafa, ta mike da fadin." Ni nayi nan ai
yau na fahimci inda kika nufa kuma."

Ta mike da fadin." wallahi Zeey baki da fahimta itafa rayuwa gabadaya hakuri ake da ita, amma
duk kin bi kin tayar da hankalinki sai zage-zage kike akan kishiya wacce bata damu dake ba, ta
mayar dake shashasha wallahi kiyi gaggawar gyarawa."

Ta watsa mata kallo mai muni kafin taja wani dogon tsaki fuuuuu! ta kama hanyar fita tana
surutai marasa ma'ana.

Baki a bud'e ta bita da kallo

4 / 8