Mummunan Zato 1 Complete Hausa Novel

Author :  Halima K Mashi Category :  Complete Novels

Chapter   9 / 10

24K to 27K   out of 29.6K words

bata haihu ba,don haka zatayi ta zuga mijinku kan cewa kada ya kusance ki,ke yarinya ce in kin ji tana haka ki mata shiru, amma da lokacin ƙwanciya ya yi ki tafi gurin mijinki kin ji? Sai Hajiya Jummai ta turo ƙofa tare da sallama, sai Karima ta ja baya alamun bata son Jummai ta ji, amma yanda A'isha taga sanda suka haɗa ido suka yi wata alama da gira sai jikinta ya bata cewa ƙila sun shirya wani abu ne.

Yinin ranar ta amsa wayar Uncle kusan sau taƙwas, duk dai dan yaji halin da take ciki. Ta kira Umma da Abba da kuma Yaya Abdulrahman, shida saura ya shiga ɗakinta amma daga gani ya fara zuwa ɗakinshi, domin ya canza kayan shi daga suit zuwa jallabiya fara kar. Ta ce sannu da dawowa,an dawo lafiya? Ya ce lafiya lau Beby,ba dai wata damuwa ko? Ta ce eh,ya ce to bari muyi sallah, ta ce to. Wanka tayi tasa riga da siket na atamfa,bata damu da yin wata ƙwalliya ba, domin shafa wannan shafa wancan ba damuwar ta bane. Ta yi sallah tare da nafila raka'a biyu,ta zauna tana yin azkar ɗin yamma. Ayatul kursiyu ake fara karantawa, sannan falaƙi da Nasi da ƙulhuwallahu, sannan ta ce "am saina wa amsalmulkulilahi Rabbana as aluka khairan mafiy hazihil lailati wa khaira ma ba a daha,wa'a uzubika min sharri mafi hazihillailati wa sharri ma ba a daha, sannan ta ce:-

Allahumma bika amsaina wa bika asbahna,wabika nahya wa bika na mutu,wa ilaikal masir.

Allahumma anta rabbii laa ilahaaha illa anta kalaƙatani,wa'ana abduka wa anna ala ahdika wawa'aduka mastaɗa'atu a'uzubika min sharri ma sana'atu abu'u laka bi ni'imatika alayya wa abuu'ubi zanbi fagfirlii fa innahu la yagfiruz zunuba illa anta.

Haka ta yi ta kawo addu'o'i har zuwa isha'i ta yi sallah tare da yin shafa'i da wuturi,tana zaune tana tasbihi, Uncle ya shigo da sallama. Ta amsa, sannan ta yi mishi sannu da shigowa, ya amsa ya ce in kin gama zo muje,dama ta gama ta yi addu'o'inta ta shafa shima ya shafa tare da cewa Allah ya karɓa ta yi ɗan murmushi sannan ta ce Amin. Ya ce me kika roƙar mana? Ta dube shi, sannan ta sunkuyar da kai ta ce alkhairi, ya ce kin sani a ciki? Ta dube shi, "na manta" ya ce "to daga yau in kin yi sallah ki dinga saka ni cikin addu'arki, Allah yana saurin amsar addu'ar mace a kan mijinta, haka nan ta mijin akan matarsa. Ta ce to, ya juya zo muje, ta bishi suka ratsa falon shiga cikin wani labule, sai ga gurin cin abinci,dinning ne na glass mai kujeru shida,can gefe ga wani mai kujeru taƙwas,gurin ya tsaru gwanin sha'awa.

Hajiya Jummai ta shigo ta wata ƙofa bata hanyar da suka biyo ba, ashe kitchen ne, da fara'a ta shigo,ta dafa A'isha wadda tunda ta shigo ta soma jin wata muguwar faɗuwar gaba,ta rasa dalili duk lokacin da Hajiya Jummai ta zo inda take sai gabanta ya dinga wata muguwar faɗuwa.

Hajiya Jummai ta ce, ƴar ƙanwata kin fito? Cikin in-ina A'isha ta ce, in in ina yini? Jummai ta zauna tana cewa, lafiya lau, Alhaji Saddiƙ ya yi murmushi sannan ya ce,gata nan sai kunya da tsoro,dubi yanda duk ta rikice daga shigowar ki.

Jummai ta ce, daina tsorona ko kunyata,ni ƴar'uwarki ce kin ji ko? Ta jawo plate ta soma zuba ma Alhaji shinkafa fara da miyar ganda,ta tura mishi, ita ko cous-cous ta zuba sannan ta ce me zaki ci ne ƙanwata? Shiru A'isha ta yi Uncle ya ce zuba mata shinkafa itama. A'isha dai tana jin su ba ta ce komai ba, domin ita ƙamshin abincin ma bai mata ba,tana ɗan tsakura tana korawa da ruwa kaɗan kaɗan,ya dube ta Beby ba ki cin abinci fa, ta ce ni dama bana cin abinci sosai. Jummai ta ce ki ci fa nan gidanki ne.

Bayan sun gama, ya dubi Jummai ya ce, to Jummai ga dai ƙanwa nan sai kiyi ta haƙuri da ita saboda yarinya ce, duk da na san A'isha tana da hankali da biyayya, duk in tayi ba dai-dai ba ki gyara mata, sannan ki nuna ta ga ma'aikatan gidan nan, ta ce insha Allah.

Ya dubi A'isha, Beby kin ga ƴar'uwarki nan kiyi mata biyayya sannan da akwai masu aiki babu abinda za ki yi hatta gyaran ɗakinki da wankin bayinki duk za su yi akwai mai girki,wato Uche kenan. Sai dai duk abinda ki ke so ƙya iya sanar dashi ga kitchen ɗin nan,za kuma a zo a saka miki wayar cikin gida a ɗaki saboda kiran masu aiki,in kin yi baƙi haka,ko dai wata matsalar,aikinki ɗaya ne jal shi ne gyaran ɗakina,wato shinfiɗa ta, to amma na ɗauke miki wannan tukunna don ba zaki iya ba.

Ta dube shi kamar zata yi magana, amma sai tayi shiru,na ta ganin menene abin wuya a gyaran gado? Nata ganin komai girman gado zata lailaye shi. Jummai ta ce, gaskiya kam, amma dai ka raba mana kwana saboda ko bata gyara maka shinfiɗar ba, saboda ƴan matsalolin ta kaga sai ka rinƙa ji,ya ce haka ne.

Bayan sun gama jawabansu, tana dai jin su,ta ƙosa ta koma ɗaki don jinta take tamkar kan ƙaya,ba don komai ba sai don Jummai,don haka ta soma hamma,ya ce je ki ƙwanta ai kafin ya rufe baki har ta miƙe ta nufi ɗakinta.

Jummai ta dube shi, Alhaji ni ko nawa ganin ba yi bane kace zaka ƙyale ta,ka san yaran yanzun da wayonsu sarai,mu da muke son yara ka tsaya renonta? Ya yi shiru, sannan ya ce ni abubuwan ne sun min yawa dubi fa yarinyar zan cutar da ita,ƙirjin ma babu komai sannan sai in dinga ganin tamkar in na ƙwanta da su ne suke mutuwa,shi yasa nake tsoro.

Jummai ta zaro idanu "kada fa asirinta ya tonu,ta ce mishi haba dai to da haka ne dani yanzun sai dai labarina ka daina wannan tunanin." Shiru ya yi yana nazarin maganarta,sai dai shi kam nashi ra'ayin ba zai taɓa ɗanɗana nauyin juna ba yanzun a tsakaninsu,yana ganin in ya ɓullo da haka ɗan sakin jikin da take mishi zata daina, amma sai ya bar wannan a ranshi don sirrinshi ne. Ya dubi Jummai ya ce haka ne,shi kenan sai ku riñƙa yin ƙwana bibbiyu in na gama ƙwanakina cike da jin daɗi ta ce Allah ya taimake mu ya bamu Sa'a, ya ce amin.

Abinda ya soma ɗaga hankalin Jummai shi ne,yau satin amarya biyu, kullum tana jiran ta ji Alhaji Saddiƙ ya ce jama'a ku zo, har yau shiru. In ta kira Karima ta mata magana sai ta ce bata da haƙuri ne sun taɓa yin wannan abin ya yi musu gaddama? Ta ce ko dai har yanzun bai ƙwanta da ita bane? Jummai ta ce oho amma yau zan bugi cikinta. Matsiyaciyar yarinya kina ganinta haka na kula zata yi salo don yanzun kin san kullum daga Ofis sai ya aiko an karɓar mishi wani zoɓo da take mishi?" Kari ta ce daina bani labari, zan dai zo gidan gobe.

A'isha kam yanzun tafi ƙosawa da karatunta,don haka sai ta ɗebo littattafan ta na makaranta tana ta karantawa, Uncle ya shigo ta ajiye ta miƙe tare da yi mishi sannu da zuwa,da sha'awa ya dubi takardun me ki ke karantawa ne Beby ? Ta ce ina ɗan duba books ɗina ne na school,ya ce kin tuna min,an kusa a koma hutu ko? Ta ce ni da jiya ma zan koma Sunday. Ya zauna kina son makarantarki ne ko in samar miki wata? Ta yi shiru sannan ta ce duk yanda kace bani da zaɓi Uncle,daɗi ya ji sannan ya ce to shikenan,nan da ƴan ƙwanaki zaki ƙara zama student ko Bebyna? Ta yi dariya har kumatunta suka loɓa. Abinda yake burge shi sosai.

A'isha tana ta gyaran ɗakinta domin tunda take sau ɗaya ƴar aikinta ta taɓa zuwa ta gyara mata daga nan bata dawo ba,don haka sai ta ci gaba da aikinta,dama ba ta ɗauke shi aiki ba,ta gama ta jona na'urar da ake saka turaren wuta,ta zuba nan fa ƙamshi ya soma tashi. Hajiya Jummai da Hajiya Kari suka yi sallama,ta amsa nan take gabanta ya shiga faɗuwa ta soma karanta Allahumma kafihim bima shi'ita,domin yanzun addu'ar da ta koma karantawa Jummai kenan.

Suka shigo ta zauna ƙasa ta sunkuyar da kai,su kuma suka zauna bakin gado. Ta gaishe su kanta yana ƙasa suka amsa cikin fara'a, sai kurum suka ji an bugo ƙofa a tsorace A'isha ta ɗago kai. Suwaiba ce cikin rashin kunya ta ce Hajiya ki zo kinyi baƙi,me kike yi ne ɗakin wannan ƴar ƙauyen? Jummai ta miƙe tana cewa ubanki nake yi kin ji ko? Ta bita suka fita. Hajiya Kari ta girgiza kai tare da cewa, Allah wadaran irin wannan tarbiyya da Jummai ta koyawa yaran nan, ta dubi A'isha ƴar nan sai fa haƙuri kin dai ga abinda nake gaya miki nan,ta sake matsowa gaya min yanda kuka yi da Alhajin naki,baki dai gudun shi ko?" A'isha ta ɗaga kai amma zuciyarta cike da tsanar matar, ta ce yauwa ƴar nan,to ya ya kukeyi ɗakinshi ki ke zuwa? Ran A'isha ya ɓaci ta yi mata banza tana ta tambayarta A'isha tayi shiru, da ta matsa mata sai ma ta saka kuka.

Hajiya Karima ta ce yau na shiga uku daga tambaya? To yi haƙuri,wayar A'isha ta soma ringing ta share hawayenta ta ɗaga Uncle ne ya ce na turo direba, ya amshi zoɓon nan na ji shi shiru, ta ce bai zo ba ko ƙila yazo bai samu wanda zaya aiko ba, ya ce to bari na kira Uche ya amsa ya bashi,ta ce to sai ka dawo, ya ce ba wata matsala ko? Ta ce a'a babu komai ta ajiye wayar bayan ta kashe ta kalli in da Karima take, tana nan zaune ba ta koma ta kanta ba, sai kawai ta shiga haɗawa Uncle ɗinta zoɓon da ta riga ta haɗa cikin wani ɗan ƙyakƙyawan ƙwando,yau har da cin-cin da diblan ta haɗa irin na bikinta ta zuba cikin wani ɗan ƙwanon tangaran saiti ne da jug ɗin ta zuba kofunan jug ɗin Uche ya ƙwanƙwasa ƙofar ta buɗe mishi sannan ta bashi tana juyowa taga Hajiya Kari ta miƙe ta ce, to sai anjima tunda kin ƙi mu yi hira A'isha can ƙasan maƙoshi A'isha ta ce to ta shige toilet.



########
[12/6, 16:20] Ummi Tandama😇: *📗 Page 15*



Cike da al'ajabi Kari ta isa ɗakin Hajiya Jummai da sauri, Jummai ta miƙe ta ce ta sanar dake komai? Karima ta ce, ina fa, wannan yarinyar tana da shegen wayo, na lura muna mata kallon biri ne ita kuma tana mana kallon ayaba.

Jummai ta dafe ƙirji ya ya ku kayi ne? Karima ta zauna,yarinyar da na matsa mata sai kurum ta saka min kuka,can kuma in gaya miki sai Alhajin ya kira ta,zo kiga kashe murya don sanabe Uncle ma take ce mishi an haɗa su soɓo da cincin an kai mishi.

Jummai ta ce,ni yanzu zama bai ganni ba,Kari shirya kawai mu nufi maguzawa in ko Boka na kan Dutse ya yi kuskuran aikin nan ne to ya cuceni,Kari ta ce daina wannan zancan kema kin san ba zaya ƙi yin aikin nan ba sai dai in tanan ne aka samu mishkila, amma yanzun ki bari sai gobe mu je muji dalili. Jummai ta ce bana bacci fa Karime, kullum sauraron ganin gawar yarinyar nake yi. Kari ta ce ki dai haƙuran ma goben.

Washegari tun safe ta fice ta riga maigidan fita, gidansu Kari ta nufa, shi dama ba'a ɗakin ta ya ƙwana ba, amma ga tsarin shi ko ba kece da shi ba zai shigo har ɗaki ku gaisa. To ya shigo ɗinne su Suwaiba suka ce mishi ta fita. Ya kalli agogon hannunshi,baƙwai da ƙwata ya dube su ina taje? Suka ce ba su sani ba,ya yi tsaki sannan ya fita. Ya samu A'isha tana gyaran gadonta, ya ce a'a Beby ina mai aikin naki ne? Ta ce Uncle ni na ce ta barshi bana son zama bana aikin komai shi ne dalilin,ya ce good,ta rusuna ta gaishe shi, ya ce zai fita,yau dai ta daure ta ce to Uncle kace ma Uche in aiki ya yi mishi yawa ni zan dinga taya shi, domin bai dace kana fita baka karya ba, kallonta ya dinga yi some times tana ɗaure mishi kai in tayi wata maganar domin sai ya ji tafi Jummai wadda ta haifeta hankali. Ya ce Beby kina son in dinga karyawa a gida ne? Ta ɗaga kai alamar eh,ya ajiye jakarshi ta Ofis ya zauna kan kujera je kitchen ki haɗo min ko menene zan ci,ta ce to amma kana ganin Anty Jummai ba zata ga kamar na canza mata tsari ba? Nan ma kallonta yake yi,ya girgiza kai sai ta saka takalmi to bara na zo ta fita ya bita da kallo zuciyarshi tana ta kai kawo an ya kuwa in ya ce zai bar A'isha sai zuwa wani lokaci ba zai ƙwaru ba? Shi yana mata kallon yarinya amma komai nata irin na masu hankali. Koda yake haka Allah yake ikonshi, sai ka ga yaro da hankalin manya.

Ita ko tana shiga kitchen ta samu Uche yana ta aiki suka gaisa nan ta tsaya tana kallon na'urorin girkin da yake amfani da su. Ta ce,ya ɗora mata ruwan zafi, sannan ta ɗebi dankali zata fere da wuƙa nan ya amsa yasa na'urar fere-fere nan da nan sai ga shi cikin lokaci ƙanƙani ya gama nan dai ya dinga taimaka mata ta shirya mishi abin kari mai sauƙi tunda sauri yake yi ta cika tire.

Ta zauna gabanshi tana cewa Uncle yi haƙuri na tsaida kai, ya ce Beby kenan,nan ta haɗa mishi tea tare da baje mishi dankali da ƙwai, duk da yana cewa tea bai dame shi ba,ya sha sosai, har ma ya gano ba wai baya son tea ɗin ba ne,ba a iya haɗawa bane. Ya dubi A'isha ya ce Beby kin san da can ina shan tea lokacin ina gidan Hajiya, daga baya sai na ji ban son shi,ta ce la ban sani ba shine kasha da ka gaya min me ka fi so da nayi maka shi. Ya ce a'a wannan ya yi min daɗi ina son irin shi, amma yaushe za ki min irin kunun gyaɗannan da Ummanki take yi? Ta ce gobe in ka fita ka ce Uche ya zo zan rubuta abubuwan da zana yi amfani da su sai ya siyo zan maka gobe,ya ce na gode.



Sun isa maguzawa kai tsaye suka zarce gidan bokan dutse,sun samu wasu halakakkun ƴan'uwansu a gurin, sai da suka jira suka fito sannan su kuma suka shiga. Yana kallon su ya soma sheƙa dariya tare da cewa, kowane shege ya ci tuwo damu miyar ma ba zai sha ba, Hajiya Jummai ta kalleshi,na kan dutse me ka ke nufi? Kari tayi saurin cewa ba dai ka ɓata mana aiki ba? Ya kuma ƙwashewa da dariya,na san dole ku dawo domin na san ba zaku ga da ƙyau ba. Jummai ta zaro idanu ya ce ke ƴar tselan uwar menene na zare idanu,kin maida ni kidahumi tunda ina daji ban san komai ba,kin kawo tsohuwar mota buga-buga an kawo min,to nima shi yasa na ce zaki gani, zufa ta shiga ketoma Hajiya Jummai, ta ce kash, to yanzu ya ya za'ayi ne? Ya ce ki zube kuɗi in miki aiki, ta ce haba na kan dutse, wannan aikin ai na biya ka na motar ne kurum aka sami akasi, ya ce ban san akasi ba,ta ce to naji yanzu nawa zan ba da? Ya ce sai kin zube min dubu ɗari biyu,shiru tayi abin duniya ya ishe ta,ta dubi Karima,to yanzu ya ya kenan? Kari ta ce kawai ki nemo kuɗi kin san na dutse bai san Allah ba bare a roƙe shi," ta ce to shikenan zamu dawo ta miƙe cikin damuwa,Karima ma ta miƙe suka fita. Cikin mota Hajiya Jummai sai mita take yi har da kukanta don baƙin ciki Karima ta ce ɗan iska ko yaushe ma ya san mota da har yasan an yi mata ƙwasƙwarima ne? Jummai ta ce bar matsiyaci ni yanzu ma kuɗin cikin account ɗina da ƙyar in ya kai dubu ɗari, Karima ta ce ki ƙwaƙula jikin shi mana. Hajiya Jummai taja tsaki tare da cewa, kada ki ban haushi Hajiya Kari kina yi kamar baki san halin shi ba? Kin san fa dole sai ya san me zan yi da kuɗi kafin ya bani,ta ce ke ja can, inji Kari wani sa'in sai ki ringa yin abu tamkar wawuya,ba za ki iya ce mishi biki ko sunan ƙawa ba? Ta ce, to zan dai ƙwatanta in bai bani ba sai na saida abin hannuna (warwaro) in yaso shima sai nasa a min aikin da na tambayi kuɗi zai bani,Kari ta ce kin yi tunani haka za'ayin ma kawai. Cikin satin zuwan Hajiya Jummai maguzawa uku, kuma ta kai duk abinda boka na kan dutse ya buƙata ta koma tana sauraron abinda zai biyo baya.

A'isha tana zaune tsakar ɗakinta kallon Cartoons take yi a tashar mbc 3 amma zuciyarta tana can ga tunanin Uncle ɗinta Wanda ya tafi Angeles ta ƙasar Amerika,don kasuwancinsu tafiyar ta ƙwana uku ce yau zai dawo gashi har yanzun bai iso ba, kuma tun safe ya ce sun taso,baya da abokin hira hasali ma tunda Uncle baya nan ba ta fita, domin su Suwaibar nan dariya suke mata tare da yi mata ba a wai ƴar ƙauye, ita ko Hajiya bata zama ma bare ta ƙwaɓa musu,don haka sai ta daina ma fita tunda tana da komai kuma Uche in ya gama abinci zaya kawo. Kasa ɗaurewa ta yi ta jawo wayarta ta shiga neman layin shi na can, cewa akayi ba zai je ba ta ajiye wayar ta saka kanta cikin guiwa. Sam bata ji turo ƙofa ba,bare taku sai dai taji an dafata a bayan ta. Firgigit ta waigo cike da tsoro, tare kuma da faɗin innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un. Ganin Uncle sai taji wani shegen daɗi cikin fara'a take cewa har ka dawo? Sannu da zuwa ya ce

9 / 10