Author : Halima K Mashi Category : Complete Novels
ganni ba. Kari ta ce "a'a kada ki damu,zai ganki ɗan iska nufin shi zai rama wulaƙancin da mukayi mishi na aikin ƙarshe da ya mana na ƙin sai mishi motar da ki kayi?" Jummai ta ce "shiyasa yanzun na taho mishi da makullin motar su Suby,don ba zan sai mishi sabuwa ba,yana kan tsauni ban da iskanci me zai yi da wata mota?" Kari ta ce "saka ai mata penti ki bashi ya ƙarata da ita". Jummai ta ja tsaki,"Ni tunanina me zan ce ma Alaramman nawa in ya ce ina motar su Suby?" Kari ta ja tsaki, "Jummai kina bani haushi,mu da muka nufi gurin masu biyan buƙata cikin gaggawa shakkar me zakiyi,ai ki sa a rufe mishi baki yanda ba zai tuna motar ba,su kuma shegun yaran masu ɗan iskan rawar kan tsiya sai kurum ki ringa haɗa su da na Mashinko direba ya dinga kai su."
https://hikaya.bakandamiya.com/muazzam-babi-na-daya/
*💃💃💃💃💃Wata garabasa sai tsarin bakandamiya ki sayi littafi daya ki samu damar karanta littafai sama da arba'in,akwai litattafan manyan marubuta kamar su RUFAIDA UMAR,LUBNA SUFYAN,MAIMUNA IDRIS SANI BELI,FATIMA DAN BARNO da sauran su,yi kokari kada wannan garabasa ta wuce ki akan naira 500 kacal,wacce take bukata ta yi magana ta wannan number 09068032427*
____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 9*
Jummai ta ce, "sun raina Tinau direba, kullum rigima shi yasa fa Alhaji ya sai musu ta su", Kari ta ce "ƴan iska to su fito da miji mana ki musu aure,ki huta can sa ƙarasa karatun a ɗakunan su" Jummai ta ce "yaushe suka nutsu har zasu samu mazan ƙwarai? Sai dai masu rarake su kuma ƙanana sa'o'insu.
Kari ta ce,"nima gidana matsalar kenan,Safina tamkar ƴar Akuya ko ince karya maza wannan ya aje wannan ya ɗauka". Jummai tasa dariya, sannan ta ce bata yar ba,kin tuna lokacin muna school?" Kari ta ce "kema ai Allah ne yaso ki gurin cire cikin da Mr.Joseph ya yi miki,mahaifarki ta nakasa,da ba don haka ba ƴarki ko ɗanki ba ƙaramin tataccen ɗan iska ko ƴar iska za'ayi ba."
Jummai taja tsaki "bar tuna min ɗan iska Mr.Joseph, shi ne ya yi min sanadi da ko ƴan iskan na samu ai da ban Yi wahalar ɗaukar rayukan jama'a ba,tun da nasan don rashin ƴaƴa ne yake ta wannan aure-auren." Kari ta ce, haka ne. Suna ta ƴan hirarrakinsu, har suka isa ƙauyen da zasu je, hanya ce mara ƙyau mai cike da ƙwazazzabai tare da dutsina.
Suna isa suka fito suka rufe motar, sannan suka soma hawa dutsen wata ƴar bukka ce a saman dutsen nan suka nufa ashar suka zunduma ita ce sallamar shiga gurin Bokan dutse,shima daga ciki ya ce maraba da ƴan tselan uwa,ku shigo dan abu takazar ubanku.
Suka samu guri gefe suka zauna. Ya dubi Jummai da jajayen idanunshi,kafin ki ce komai ki fara cika min alƙawarina,don tsakaninmu babu ƴar ɗaga ƙafa yanzun ga wuri ga waina zamu dinga yi, tunda ke na lura ƴar rainin hankali ce. Dodo ya ce in kin sake kuskure alƙawarinsa za ki sha mamaki."
Ta buɗe jakarta tana cewa,"kai ko gashi ka cika gajen haƙuri, gashi" ta miƙa mishi makullin motar, ya ce "riƙe tukunna ina motar?" Ta ce "a'a tana can ni ba zan iya jan zuwa gurin nan ba, kuma bana son in ce direba ya jawo asirina ya tonu,ko ba haka ba ne? Yace don wannan babu ji ko su Ifiritu sai su ɗauko, amma sabuwa ce ko?" Suka dubi juna ita da Kari, har suna haɗa baki gurin cewa dal ma kuwa,ya ce shi kenan. Ya shiga haɗa wasu abubuwa yana surkullenshi har ya gama ya ce,to ke ma fa kina da aiki a gabanki, domin wannan aikin ya banbanta da na baya.saboda ita wannan yarinyar tana yawaita ambaton Ubangijin musulunci, saboda haka sai mun dage."
Jummai ta ce,gara kam a dage Boka, saboda wannan in son raina ne ta mutu a ranar da aka kawo ta.
Hajiya Karima ta ce "in ma ta mutu ranar ya kiyaye aure," Boka ya ce "ba zata mutu sanda ku ke so ba, domin Aljani ba zai samu aiwatar da aikinsa ba, sai lokacin da take fashin sallah, saboda tana tsananta ambaton Ubangiji.
Tana yawan kusanta kanta da Ubangiji, sannan ke kuma zaki daina sallah daga yau har sai lokacin da Dodo ya ce kici gaba da yi. Ya miƙa mata wani ruwa gashi nan ki yayyafa cikin ɗakin da za'a saka amaryar, kullum sau uku a rana har tsawon kwana baƙwai. Ya bata wani ɗan gwangwani,ki binne shi a ƙofar ɗakin amaryar in ana sauran sati ɗaya bikin," ta ce "Boka ko'ina tiles,ya ya zan yi in saka? Ya ce "ruwan ki in kin matsu ki sa a fasa, sannan zaki dawo in ana sauran ƙwana tara bikin" ta ce "to sai batun mijina ya ya zanyi na sameshi a hannuna? Ya ce"wannan ba zan gaji da gaya miki ba,ba zaki taɓa samun shi yanda kike so ba, kasancewarshi mai tsayuwa akan duk dokokin Ubangijinshi, sannan tun yana ƙarami iyayanshi suna matuƙar tsaye kan shi, duk bokan da ya ce zai kama miki shi to ƙarya yake yi ba zai iya ba, sai dai ki haɗa da kissarku ta mata,to zuciyarshi tana da tausayin mace, amma ba dai asiri ba,in ma ya kamashi ba za aje ko'ina ba, zai karye.
Jummai ta ce, "shikenan zan ga me zanyi. Suka tashi suka fita yana me ƙara tuna mata ban da Sallah ban da Sallah. Wa'iyazu billa,kaji mushirikan mata.
Alhaji Saddiƙ ya dubi Fatima, "Sister ki duba dai ko za'a ƙara wani abu" cikin dariya ta ce, "sun yi fa Brother,sai dai in kana son ka ƙara zaka iya." Nafisa ta ɗaga wani takalmi mai igiya ta baya ta ce, "haba Brother wallahi wannan takalmin ya yi ma A'isha kaɗan na yara ne fa?" Ya dube ta kaji ki to ai itama yariyar ce,she is fourteen or fifteen,sa'ar ƴarki ce fa sister" ya dubi Fatima. Nafisa ta ce "amma ai tafi Nana tsawo," ya ce "to ai Kuma Nana ta fita ƙiba ma," ya miƙe yana cewa, "kisa direbanku ya ƙwasa ku kaima Hajiyarmu,in ta ce komai ya yi shikenan,sai kusa ranar tafiya tunda gaba ɗaya yau sauran kwana sha shida bikin. Suka ce "To" bayan ya fita suka soma dariya Fatima ta ce "ni nama rasa me zan ce ma Brother babu fa brezia ko ɗaya,ya dai saka pants da skat zuwa su bess, amma babu bra. Nafisa ta ce "nufin shi bata da nonon sakawa ne ko?" Suka sa dariya, Fatima ta ce "kin san shi da kanshi ya siyo undes ɗin, zannuwa da sauran kayan duk ni ya ba zaɓi amma ko takalma sai gashi da su" Nafisa ta ce "shikenan in ta zo gidan ya siya," suka soma shirin ƙwasar kaya don zuwa gidan Hajiyarmu.
A'isha tana ƙwance kan katifa, zuwa yanzu ta gama sadaƙarwa ta dangana ta kuma ɗauki ƙaddara, sannan ta amince ƙwananta ne ya ƙare. Don haka ko yaushe zaka same ta da casbaha tana ja. Istingifari ta ke yi, domin Allah ya yafe mata zunubanta.
Wayarta da ke gefanta ce take ruri, bayan ta ɗauka tare da sallama, ya amsa, sannan ta ce, "ina ƙwana Uncle? Ya ce lafiya lau Beby, baƙin sun taso na san yanzun ma sun sauka a Kano, saboda jirgin Kano suka hau, ta ce "Allah ya kawo su lafiya," ya ce "Amin" ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Beby duk abinda be yi ba cikin lefen ki gaya min kin ji ko? Saboda bata son dogon bayani sai kurum ta ce "To" ya ce "shikenan sai na kira ko? Ta ce,to na gode, ya ce nima haka.
Gidan cike yake da ƴan'uwa ta gefen Umma da kuma gefen Abba. Shi yasa yawancin baƙin duk ƴan Gumel ne, sai ƴan Garki, sun zo ne don karɓar lefe kamar yarda akayi waya aka sanar da su. Anyi girke-girke don tarbar baƙin Katsina. Su kan yiwa amarya tsiya da cewa duk gudun auren ne ta ƙara ramewa, ita dai tana kallon su tana kuma jin su,nata addu'a ne a zuci, Umma ma dai tana ƙarfin hali ne domin kada ta karya ma A'isha guiwa.
Sun iso cikin motoci guda uku fararen Acadami su uku motar farko matan abokanshi ne na Kano,ta tsakiya kuma kaya ne a ciki, sai direba ta bayan mata huɗu ne Fatima a gaba, sai Nafisa sai kuma ƙanwar Hajiyarmu, da ƴaƴarta Talatu.
Ƴan unguwa da suka taru da kuma ƴan'uwa sun sha mamakin ganin kayan da aka kawo, suma sun sha tarba kuma sun ga karamci sun kuma yaba. Nafisa kuwa ɗakin A'isha ta shige lokacin A'isha tana wanka. A'isha tana fitowa taga Nafisa zuciyarta tana son Nafisa. Ta saki murmushi tare da cewa "dama har da ke aka zo? Ta ce,eh mana aini Brother ya yi ma ƙawance. A'isha ta zauna tana shafa mai, Nafisa na kallonta, lallai kam yanzun nononta suke fita ashe ya kula ne. Ta ce, Nafisa ya ya Hajiya fa dasu Aunty Fatima?" Nafisa ta ce, "ai tare da Anty Fatima, muka zo Hajiyarmu kam tana gaishe ki ba ki ce ina Uncle ba? A'isha ta ɗan yi murmushi kawai.
Nafisa ta ce, "Naga kin rame ne" A'isha ta ɗan yi murmushi, sannan ta ce "Na sha jinya fa tun a school har yanzu." Nafisa ta ce Allah sarki, to Allah ya ƙara lafiya. Amin inji A'isha, tare da zura wata duguwar riga, sannan ta soma ɗaura ɗan ƙwali. Nafisa ta ce Allah yasa ki haifa mana Beby mai irin gashin nan naki. A'isha dai ta sunkuyar da kai, Nafisa tayi-tayi ta zo su gaisa da su Anty Fatima, amma ta ƙi,Fatiman ce ma tace ai nima ƙanwar ta ce, bari naje mu gaisa,Talatu ma tabi Fatima dan su ga A'isha.
A'isha ko rufe fuskarta ta yi, har dai suka gaji suka tafi, Nafisa ma nan ɗakin ta ci abincinta, Abba yayi-yayi su ƙwana amma suka ce a'a, Kano zasu ƙwana don zasu shiga kasuwa goben da safe,sai su wuce. Da zasu tafi an basu tukuici suma yanda ya kamata. Nafisa ta raɗa ma A'isha a kunne, cewa ki rage bacci,ki tsaya kan addu'a.tsayuwar dare zaki dinga yi kina roƙon Allah alkhairin da ke cikin auren ya kuma kare ku da duk masu sherri da hassada kin ji ko? A'isha ta ce, na gode Nafisa zan kiyaye insha Allah.
Ya fito daga wanka,wankan da ya zama mishi ƙa'ida, duk dare koda da ya yi shi ne zai kusanci matarshi ya fi gane yayin in yaso ya sake. Matsawar bai yi wankan nan ba,to ko ba zai samu bacci ba, kasancewar yanayi ne na zafi shiyasa. Yana fitowa ya warware (AC) turarukan shi na ƙwanciya ya faffesa, sannan ya saka kayan baccin shi riga da wando.
Ya zauna bakin gado yana son jin muryar A'isha ne kawai,yau ƙwana biyu kenan ba su yi waya ba,bai san mene ne yasa yake son Yarinyar ba,yana tsoron fa kada Yarinyar ta mutu tamkar sauran matanshi. Ya soma neman layin yarinyar,yana yi yana kallon agogo goma ta gota a ranshi, ya ce ko kin yi bacci zaki tashi. Dai-dai lokacin ko ita tana kan darduma, nafila take yi sanda ta sallame sannan ya sake kira.
Ta ɗauko wayar ta ɗaga tare da sallama, ya ce "oh sorry Bebyna, na tashe ki kina bacci ko?" Ta ce, "a'a bana bacci, ya ce me ya hana ki? Ta yi shiru, ya ce to ko abinda ya hana ni bacci ne kema ya hana ki? Ta ce um,ya yi ƴar dariya kin san abinda ya hana ni ne? Ta ce a'a, ya ce in gaya miki? Ta ce eh,ya ce ni tunanin kine ya hanani ke fa? Ta yi shiru ya ce Beby kina ji na kuwa? Ta ce,ina jin ka,ya ce oh gaya min, ta ce ni ina sallah ne, ya ce good,me kike roƙo? Da sauri ta bashi amsa da cewa cikawa da imani da rahamar kabari, tare da samun Aljanna maɗaukakiya." Ya ce "Umhum? Yana son jin ƙarin bayani, ta ce "Shikenan nake roƙo," ya ce "batun aure fa baƙya yi mana addu'a? Shiru ta yi jikin shi ya yi sanyi ya ce A'isha in tambaye ki wani abu? Ta ce eh, ya ce zaki sanar dani gaskiyar maganar? Ta ce,in har na sani ba, ya ce "kin ji wasu maganganu ne a kaina?" Ta ce kamar me? Ya yi ɗan jim sannan ya ce koma na me? Ko kirkina ko akasin haka?.
Ta rasa me zata ce ya ce ina jinki nasan duk mai irin sunanki in dai ta ci sunan bata ƙarya. Sanar da ni. Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce "Uncle duka biyun na ji da kirkin da kuma akasin hakan. Ya ƙwanta rigingine jikinshi ya yi matuƙar sanyi sannan ya ce "Beby tsorona ki ke yi ko? Kin tsane ni ko? Kina zargina kema ko? Na sani na dai na burge ki ko? Muryarshi ta soma rawa, shi kenan ba zan matsa miki ba Beby zan barki kema kina tsoron haka bana son ki mutu domin kin shiga raina sosai" ya kashe wayar ya jefar da ita a kan gado sannan ya ɗauko filo ya rufa akan fuskar shi tare da matsewa yana jin wani pain a cikin ranshi.
*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*
```1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account ɗin namu ya samu matsala ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*
____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 10*
A ɓangaren A'isha kuwa duk sai ta ji babu daɗi har ma ta yi da ta sanin amsa shi, sai ma duk ta ji tausayin shi ya kamata,ta ji kamar yana kuka. Abbanta zai ji daɗi in yaji labarin nan kuwa? Ƙila ma ya ce ba zai yafe mata ba. Da sauri ta tashi ta duba agogo,sha ɗaya saura, ta ɗauki ɗari biyu ta fita, da sanɗanta ta fice bakin titi ta siyo kati ta dawo ta shige. Sai da ta kulle ƙofarta ta hau katifarta ta loda katin, gabanta yana ɗar-ɗar ta soma kiran layin shi kasancewar wannan ne karo na farko da ta taɓa kiran shi.
Dai-dai lokacin shi kuma yana ta neman layin Abba don ya shaida masa ya haƙura da auran, amma wai layin is switch off,sai ga call ɗin A'isha Beby kamar yanda ya rubuta a cikin wayar tashi. Ya tsura ma sunan ido, kada dai idanunshi ne suke mishi gizo? Ya dai ɗauka ba tare da yin magana ba,ta ce "Uncle" ya ce "Na'am" ta ce "nifa ban zarginka,don Allah kada kayi fushi dani ko da na samu labarin tun a school ne na san dai an confuse amma ba dai na yarda bane,don Allah in nayi laifi kayi min afuwa." Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce "ba ki da laifi Beby, domin nima sai da nace a'a Abbanki ya ce babu damuwa, amma bari kiji wani abu,kin ga ke yarinya ce ko? Amma zan rantse miki da wallahi-wallahi ban taɓa shan jini ba, duk wani laifi game da sicret cold zargi ne,ban san shi ba, batun mutuwar matana ƙarar ƙwana ce kurum,kin yarda da haka? Jikinta a sanyaye ta ce na yarda,ya ce "to Beby ki ƙwantar da hankalinki, addu'a za ki dage da yi Allah ya zaɓa mana abin da ya fi zama alkhairi kin ji ko?" Ta ce "to,kaima ka daina fushin? Ta ci gaba kada fa ka sanar da Abbana," ya yi ƴar dariya bana fushi da ke, kuma insha Allah ba zan taɓa yi ba, itama ta yi ajiyar zuciya, sannan ta ce "to sai da safe,ka kwanta. Ya ji daɗin kalmarta, sannan ya ce "to zan yi yanda ki ka ce,kema ki ƙwanta tare da mafarki mai daɗi na twins ma su kama da face ɗin ki,ta kashe wayar da sauri.
Hajiya Jummai ta kalli kayan, sannan ta kalle shi.
"Me ka ke nufi da waɗannan kayan?" Ya dube ta "Na ki ne mana" ta taɓe baki, "Ni fa gaskiya duk zannuwan nan ba suyi min ba,babu kala ta, maimakon ka bani kuɗin na saya da kaina? Kuma ina son canza kayan ɗakina, sannan ga su Suby." Ya ce, "Jummai, gaskiya ni dai ba zan bada kuɗin wasu kaya ba,kin san nawa na siya waɗannan kayan? Game da gyaran ɗaki dai zan baki dubu ɗari,su Suwaiba kuwa dubu hamsin zan bada kada a kuma damuna,cefanen gida kuwa mun gama magana da Uche,ya rubuta komai." Ta sake fusata, domin ta kula ma ƙwangilar da take so ta yi bazata samu ba kenan, komai ƙit da ƙit? Ta dube shi "don kurum zakayi aure, sai ka dinga komai faɗa-, faɗa? Ga wani maƙo da ka koya,da Uche ne yake faɗin abinda ake so?" Ya ce,"to ke ko yaushe baki gida kin ma fi ƙarfin ki ce min zaki guri kaza,koda a waya ne sai dai na dawo baƙya nan, lokaci ya ƙure min dole na sauke abubuwan dake gabana, Uche kuwa shi ne yake girkin nan,don haka shi ne yasan abinda za'a nema.
Ta ce, "Kana lokaci ya ƙure,ba saura sati uku bane bikin? Ta ce, "batun lefe fa? Sai ka kawo a haɗa" ya ce ai lefe ya daɗe a gidan su amarya." Ta miƙe cike da masifa.
"Lallai Alhaji Saddiƙ aurenka na wannan karon ya banbanta da na baya, wannan karon aƙwai ƴar zargi." Ta soma kuka, "maƙiyana sun samu galaba,wato lefen ma ban isa ko gani inyi ba, na gode." Ta fita tana cewa gara daka nuna min babu ruwana abinda babu ruwan mutum