Author : Halima K Mashi Category : Complete Novels
zuwan? Inji Hajiya Jummai,ta cigaba "Kuma sai dai mu je da direbanki, kamar kowane lokaci" "Eh,ai ina sane ba zamu bar wata kafa ko ya ya take wadda zata tona mana asiri ba,ke dai ki shaƙi kuɗi don bokan dutse yanzun idanunshi sun buɗe da son kuɗi,da, ko akan dubu biyar ma sai ya yi kisan rai." Jummai ta ce,"A sosai ma kuwa, ɗan iska ni har yau ma ban sai mashi motar da yake naci ba". Hajiya Kari ta ce "ke dai bar ɗan iska ko ina ruwan wanda ke cikin daji da mota?" Jummai ta ce,"nima shine na gani, shiyasa na share shi,rabo na da zuwa gun shi tun aikin ƙarshe da ya yi mana,na matar ƙarshe da Alhaji ya aura." Hajiya Kari ta ce, "ƙyale shi wannan karon sai ki sai masa ko ƴar starlet" Hajiya Jummai ta ce "hakan za mu yi" nan dai suka ci gaba da shirya ranar da zasu tafi.
Da gudu suka rungume juna suna murna.
*A'isha Mustapha kin ɗan rame." Inji Suwaiba Ringim.
"Nayi rashin lafiya ne, Zainab K.T bata iso ba?"
Sam, A'isha ba tayi niyyar sanar da Aminan nata batun auren nata ba, saboda kunya take ji, duk cika bakin da takeyi na cewa ita karatu zatayi kamar ba gobe,don Doctor zata zama yanzun ma har Doctor Aisha suke ce mata,in ko suka ji ta san zata sha tsokana, sai dai su shafa su ji bata dawo ba, Zainab ma ta iso kuma sun duƙufa karatu babu wasa.
Alhaji Saddiƙ ya yaba da yanda Abba ya tsaya tsayin daka, aikin kamfanin ya kammalu. Guri ya yi ƙyau duk mutane sun yaba,don haka shima bai yi wasa ba wurin kawo duk wani abu da kamfanin ke buƙata don fara aiki.
Alhamdulillah,tuni kamfani ya soma aiki, Abba kuwa ya samu kujerar manaja, yanzu sunturi yake yi tsakanin Dutse da Jigawa, Alhaji Saddiƙ ya ce mishi ya nemi gida nan Jigawa sai a siya, sannan ya saya mishi ƴar mota,ba a jima ba suka samu gidan suka dawo Jigawa.
[12/1, 19:47] Ummi Tandama😇: ____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 6*
Aisha tana makaranta ba ta san ana yi ba.
Gurin Abba Alhaji Saddiƙ ya ji cewa satin da zamu shiga ne visiting day ɗin su mutuniyar shi,ya ce "To Friend ka bari ni zan je mu da Nafisa" Abba ya ce,"shiyasa na sanar da kai don tasan cewa magana tana nan.
Waya ya yiwa Nafisa cewa,ta shirya zasu je visiting tana jin haka ta soma murna. Sun ɗau hanya in da Yahaya direban shi yake jan su. Aikin shi yake yi a bayan mota cikin laptop, harkokin business ɗin shi yake ta yi. Nafisa ko sai dai kallon ƙauyuka take yi, sai da suka isa garin Kano sannan suka tsaya bakin Sahad Store ya yi mata tsaraba mai ban mamaki, sannan suka ɗauki hanyar Munjibir.
Da tambaya suka isa makarantar,Henesy baƙa wul tana ta sheƙi,ta ɗauki hankalin da yawan ƴan makarantar,gilashinta masu duhu ne,don haka suke ganin mutane. Ya dubi direbanshi ya ce "Yahaya fita ka samo mana ofis ɗin (PC) ɗin makarantar."
"To ranka ya daɗe" inji Yahaya.
Jim kaɗan ya dawo.
"Ranka ya daɗe ga ofis ɗin can, har ma na yi mishi bayanin cewa maigidana yana son ganinshi,kuma ya ce mu shigo" "To ai shi kenan." Inji Alhaji Saddiƙ, tare da Nafisa suka fito. Ƙwarjinin Alhajin ya sa ya zama abin kallo gurin ɗaliban tare da masu ziyara. Kai tsaye ofis ɗin (PC) ɗin suka nufa,suna shiga shima (PC) din ya miƙe tare da ba Alhaji Saddiƙ hannu,don daga ganin shi ya jiƙe da Naira. Sun gaisa, sannan suka zauna kan wasu kujeru da ke gefe,ya nuna ma Nafisa wata kujera ya ce, "Bismilla Malama" shi ko Yahaya cewa ya yi,bari ya koma gurin mota.
Alhaji Saddiƙ ya ce,"mun zo ziyarar yarinya ne."
"Ya ya sunanta?" Inji P.C.
"A'isha Mustapha, daga Gumel ta jihar Jigawa."
P.C ya ce,(S.S) take ko JS?"
"S.S one." Inji Alhaji Saddiƙ.
"Ok" ya miƙe yana fita ya kira shugabar ɗalibai ya aike ta neman A'isha,ya dawo ya ce bari a kira ta.
Alhaji Saddiƙ ya ce,"Ba komai" ya zauna tare da cewa, "Ranka shi daɗe ƴar ka ce?" Alhaji Saddiƙ ya amsa da cewa "Eh,ƴar abokina ce", wayarshi ta shiga ruri,ya ɗauka yana magana.
Shugabar ta gano A'isha ne tare da ƙawayanta Zainab da Suwaiba,in da Yayan Zainab ya kawo mata ziyara daga Katsina, ta ce kece A'isha Mustapha ko?" Ta amsa da "eh,ni ce."
"To ki zo inji P.C"
A tsorace ta ce,"lafiya?"
Nima ban sani ba" ta ce "Ina jiran ku" ta nufi ofis ɗin shugabar ce ta shiga,ga ta nan Sir,ya ce ta shigo, nagode miki ta fita sannan ta ce A'isha ta shiga, ita kuma ta tafi. Tana shiga ta ji hancinta ya shaƙi daddaɗan ƙamshin turaren Uncle,gabanta ya faɗi amma ta daure ta shiga,sanye take da wando da riga haɗe da gyalen su, kayan mutanen Pakistan masu kalar sararin samaniya, kai tsaye teburin P.C ɗin ta nufa, inda ta gaishe shi cikin harshen Turanci, sannan ta ce gata,ya nuna mata Alhaji Saddiƙ da ke waya.
"Ga masu visiting na ki." Ya miƙe "Bari na barku, ku gaisa ko?" Ya fita.
Duk sai taji kunya ta rufe ta, har ma ta ja gyalenta ta rufe gefen fuskarta. Ta dubi Nafisa,ga zatonta matarshi ce. Cike da dariya Nafisa ta ce, "zo mu gaisa A'isha." Ta isa gurinta ta zauna, sannan ta ce "Ina yini? Ya ya hanya?" Nafisa ta ce "lafiya lau,hope kema kina lafiya?" A'isha kanta a ƙasa ta ce "lafiya ƙalau." Nafisa ta ce "Hajiyarmu da Alhajinmu sun ce mu gaishe ki" A'isha ta ce, "ina amsawa, na gode."
Dai-dai sannan Alhaji Saddiƙ ya gama waya ta ɗan saci kallonshi da gefen ido. Wata jiƙaƙƙiyar shadda ya saka kalar ƙasa,ya yi ƙyau sosai ta zamo daga kan kujera don ta gaishe shi.
"Ina yini Uncle?"
"Bana cin miƙe A'isha, daga nan za ki gaishe ni?".
Ta saka gyale ta rufe fuskarta, sannan ta miƙe taje gefenshi ta tsugunna,muryarta ƙasa-ƙasa ta sake gaishe shi. Ya amsa yana dariya.
Nafisa ma dariya take yi, sannan kunyar A'isha ta burge ta, A'ishan ta mata ƙyau,sai dai yarinya ce ƙwarai, ya ce "Nafisa yau dai ga ki ga A'isha" Ya dubi A'isha ya ce, "Ga ƙanwata Nafisa." Ta kuma duban Nafisan.
"Sannu da hanya"
"Yauwa," Nafisa ta amsa da fara'a.
A'isha ta miƙe tana kallon Nafisa, "Bari na kira ƙawayena." Har za ta fita, ya ce "Zo" Ta dawo ta tsugunna.
"Wa zaki ce musu ya zo?"
Ta rufe fuska,tana ɗan murmushi. Ya ce, "Umh,wa zaki ce musu? Ko har kin basu labarina ne?" Ta girgiza kai, sannan ta ce, "Ce musu zan yi Uncle ɗina ne." Ta miƙe ta fita da sauri. Dariya Nafisa ke musu, ta ce "Yaya Saddiƙ duk da A'isha yarinya ce kun matuƙar dacewa, Allah dai ya yi mana jagora tare kuma da shige mana kan matsalarmu." Ya ce "Amin sister."
Ta je gurin su Suwaiba ta kira su, ce musu ta yi Uncle ɗinta ne daga Katsina, suka shigo suka gaishe shi,ya tambayi sunayen su suka gaya mishi,ya ce "Har da ƴar garinmu? To sannuku,ku dage da karatu ko?" Suka ce, "To mungode" ya ce "nima na gode." Suka fita suna mamakin dama A'isha tana da Uncle a katsina, Amma ba ta taɓa gaya musu ba? Zainab kam so take ta tuna inda ta san shi.
Nafisa ta miƙe, "A'isha bari na bi ƙawayenki na ɗan miƙe ƙafa," A'isha ma ta miƙe ta fito, kira ta ƙwalawa su Zainab.
"Ga baƙuwa ko zaku je school shop."
Suka ce, "To" ta dawo ofis ɗin ta zauna, ya dube ta "Ya ya bayan rabuwa?" Ta ce "Da godiya, shi Abbana ba zai zo ba?" Ya ce,in gaishe ki ba zai samu zuwa ba, saboda aikin shi ya koma Jigawa. Kuma yanzun Jigawan ku ke" ta dube shi, "Mun tashi daga Dutse?" Ya ce "Haka ne,to yanzu yaushe ne zakuyi hutu?" Ta ce, "Nan da sati biyar zuwa shida." Ya ce, "To so nake a shirya komai kafin kuyi hutu, cikin hutunku za'a ɗaura aure tare da bikin." Gyale taja ta rufe fuskarta. Ya ce, "Me kika ce?" Ta ce, "Duk yadda ku ka yi,ni dai karatuna na fi ji" Ya ce, "wannan babu komai, sai makarantar da ki ke so ita zan kai ki" ta ce "Bari na samo maka wani abu." Ya ce, "No,bar shi am ok." Ya dubi agogo bari muyi sallah mu zo mu tafi." Ta ce, "To."
Bayan sun yi Sallah,ya dawo ya yi ma P.C alkhairi mai yawa,P.C ya rako shi har gun motarsa. A'isha taje ta kira su Zainab su yi sallama,har ma ta ce ma Sani Yayan Zainab,ya zo ya bi su Uncle ɗin ta mana tunda suma Katsina za su je.
Sanda suka iso gurin motar Yahaya,yana ta aikin jibge ƙwalaye a ƙasa daga boat ɗin motar,Sani yaja baya ya tsaya yana mamakin ganin Alhaji Saddiƙ K.T. mutumin da ya yi kuɗi da jinin mutane, yanzu kuma dabarar da ya sake kenan? Ta shigowa makarantu yana son shan jinin ƴan makaranta? Sun gama sauke kayan suka shiga mota.
Alhaji Saddiƙ ya miƙa ma Nafisa bandir ɗin kuɗi yace ba ƙawayan nata. A'isha ta leƙo tana cewa, "Nafisa ku sauka lafiya,ku gaida ƴan garin." Ya ce, "Ni fa ko Nafisa kaɗai ki ka sani?" Nafisa ta ce, "yauwa ga Yayan Zainab shima Katsina zai je". Alhaji Saddiƙ ya ce, "To ya shiga mu je." Ta zo gurin su, ina Sanin?" Yana daga bayansu ya ce,"A'a su tafi ni dama sai gobe ina da aboki nan cikin Munjibir,ta je tace su tafi su Zainab ma suka je sukayi godiya.
Suna tafiya sai ya zo gurin su ya nuna A'isha, "wannan mutumin ne Uncle ɗin ki?
Zainab ta ce, "Ka san shi ne? Nima ina ta mishi kallon sani."
"Sani ya ce, "kin san shi mana, Alhaji Saddiƙ Usman K.T ɗin ne baki sani ba."
Zainab ta dafa ƙirji da ƙarfi.
"Kana nufin me kuɗin jini?" Ya ce "shi ne mana."
A'isha ta zaro ido,me kuɗin jini kuma?" Sani ya ce, "tabɗi,ke da baki san halin Uncle ɗin na ki ba? Koda yake ai basa cin na gida sai bare."
Jikin A'isha ya soma rawa, cikin matsanancin tsoro ta ce, "Don Allah ku gaya min gaske ne?" Zainab ta ce, "kada ki damu zan baki labari,ku zo mu ƙwashe kayan nan." Ta ce, "ai ni bazan ɗauki wani abu ba har sai naji labarin Uncle." Suwaiba da Zainab har ma da Sani suka shiga ƙwashe kayan. Zama tayi bakin gado tana tunanin baƙon al'amarin, har suka raka Sani suka dawo.
Zainab ta zauna kusa da ita, A'isha dama baki sani ba,shan jini suke yi,An ce aure-aure ya ke yi, duk wadda ya aura ba ta sati biyu take mutuwa,aurenshi goma, uwargidan ce kaɗai bai cinye ba, ke yanzu fa ba a bin layin gidan shi,don ance kana cikin tafiya a layin wani abu zai ja ka zuuu sai dai ka ganka a cikin wani ɗaki a gidan,ke kina ganin gidan kin san ana cin mutane a cikinshi, ko ba ki san gidan ba?"
A'isha cikin tsananin tsoro ta ce "ban taɓa zuwa ba".
Suwaiba ta ce, "Tab! Amma ya yi ƙyan banza." Zainab ta ce "kinga gidan ne wani mahaukacin gida ga bishiyoyi."
A'isha sai kuka,lallai Allah ya so ta tana zuwa gida zata sanar da Abbanta. Duk kayan da ya kawo ta ce bata so,ta ma fita hayyacinta cikin ƙwana uku ta ƙwanta ciwo,ƙwananta biyu ta ɗan samu sauƙi. Amma duk ta rame su Zainab sun yi ta matsa mata da son jin gaskiyar lamarin ta da Alhaji Saddiƙ don sun ga yanda ta ɗauki abin da zafi ƙwarai. Ta gaji ta gaya musu cewa Babanta ya riga ya bashi ita,sun jajanta mata tare da kuma bata shawarar ta tashi tsaye da addu'a, Allah ya shiga tsakaninta da sharrinshi. Sun ce suma za su taya ta.
A daddafe dai suka yi jarabawa, Abba da Abdulrahman ne suka zo ɗaukanta, Abba ya dube ta, "A'isha ciwo ki ka yi haka? Na ganki ne babu ko ƙyan gani?" Hawaye ya soma zubo mata, cikin sanyi murya ta ce "Abba nayi ciwo ne sosai."
Sun isa Jigawa misalin ƙarfe biyar na yamma,suna tsayawa A'isha ta fito tana kallon sabon gidansu,ga dai gida mai kyau amma ta kasa jin farin ciki, kuma ta yarda cewa iyayenta suna cin kuɗin ƴarsu ne. Nan take hawaye ya soma zubo mata,ta shiga ciki.
#######
[12/2, 08:00] Ummi Tandama😇: ____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 7*
Abdulrahman yana biye da ita da kaya, cikin wani tsararren kitchen ta hangi Umma, Umma tana juyowa ta yi arba da ƴarta, da sauri ta fito tana cewa ga ƴan makaranta ga ƴan makaranta." A'isha ta faɗa jikin Umma tana kuka.
Ramarta ta tsorata Umma, ta ce, "A'isha kin yi ciwo ne?" Dai-dai nan Abba da Abdulrahman suka shigo, Abba ya ce, "ƙawallin taki ta bani tsoro, Ummansu kin ga yanda ta ƙare?" Umma ta ce "Shine ai,wane ciwo ki kayi haka?" Cikin kuka A'isha ta ce, "Nima ban san ciwon ba,ni dai duk jikina ne bana jin daɗin shi. Suka shiga falo kan kujera ta ƙwanta tana ƙara kallon yanda aka tsara falon da kuɗin jini, duk sai ta samu kanta da ƙyanƙyamin komai na gidan. Umma ta zubo mata abinci ta tasa shi ta kasa ci, har dare Umma ta yi tayi A'isha, amma ta ƙi cin komai. Hankalin Iyayen ya tashi, cikin dare zazzaɓi ya rufe ta saboda tsananin damuwa da kuka, dole da safe suka nufi asibiti, duk binciken likitan bai gano komai ba, sai damuwa. Don haka yasa mata ruwa tare da allurai don ta samu bacci.
Ƙwananta biyu aka sallame ta, tunda ta dawo ko yaushe jugum ba ta magana. Umma ta matsa mata da tambayar abinda ke damunta,don likitan ya ce tabbas akwai abinda ke damunta. A'isha tana son sanar da Umma amma tana tsoron kar ta gaya wa Abba, shi kuma ya yi faɗa. Ko ma ya yi fushi da ita,don haka ta yi shiru.
Abba yana zaune yana cin abinci, ya tasa ta gaba wai itama sai ta ci nata. Umma ma ta shigo ɗakin na A'isha, wanda ya ji uwar katifa sai (T.V) ance ba za'a cika ɗaki da kaya bane tunda cikin hutun nan ne za'ayi bikinta, Umma ta zauna tana cewa,ka ce kana nan na fito ban ganka ba,ya ce "eh, ina nan gurin A'isha so nake ta ci abincin a gabana in gani," Umma ta ce "to nima dama na zo ne in tsare ta, yarinya duk tasa kanta a uku" ta dubi A'isha wadda take ta ƙoƙarin ganin ta ci abincin,ko don hankalin iyayenta ya ƙwanta, ta ce, "To ko saboda aurenki da Alhaji Saddiƙ ne?" Da sauri ta kalli Abba, wanda ya tsura mata ido, sannan ta girgiza kai, "Ba haka ba ne Abba" ya ce "ai bani ne na tambaye ki ba, Ummanki za ki bawa amsa, tunda ni dai ai mun gama magana,jiya ma nake sanar da shi dawowarki, sai dai ban sanar dashi ciwon ki ba, saboda zai ce zai bar aikinshi ya zo,ya ce dai zai zo kafin su kawo kaya."
Umma ta ce "bari na saka mata wayarta ma a caji, saboda ƙila zai neme ta. A'isha ta yi ajiyar zuciya,lallai ya kamata ta sanar da Umma, domin dai ba su san komai kan Uncle ba. Sai da Abba ya fita sannan A'isha ta dubi Umma, ta ce "Umma zan gaya miki abinda ke damuna, amma sai kin yi min alƙawarin ba zaki sanar da Abbanmu ba" cikin fargaba Umma ta ce, "Sanar dani,ba zan gaya mishi ba." Ta soma hawaye, "Umma ashe Uncle ɗan yankan kai ne? Ashe duk kuɗin shi na jini ne?" Umma ta daburce tare da cewa "Wane Uncle ɗin?" A'isha ta ce, "na Katsina, kinsan ƙawata ƴar Katsina ce nan dai ta koro ma Ummanta labarin da ta ji game da Uncle ɗin nata, Umma ta shiga damuwa,zufa ta shiga keto mata duk da cewar da takeyi anya kuwa A'isha zancan nan gaskiya ne? Duk suka yi shiru kowa yana tunaninshi, can dai Umma ta yi ƙarfin hali ta ce "A'isha wannan zancan ba na shiru ba ne, dole Abbanki ya ji, domin dai duniya yanzu babu gaskiya, kuɗi suna kai mutane cikin halaka, sannan kai ka yarda da mutum shi ko yana da nashi burin a kanka".
A'isha ta soma kuka tana faɗin, "Don Allah Ummata kada ki sanar da Abba,ba zai taɓa yarda ba saboda ya yarda da Uncle ni dai na haƙura zan auri Uncle ɗin tunda dai dama na san ƙarshena mutuwa zan yi."
Abba da ke ƙoƙarin shigowa ɗakin tun ɗazun,ya ji A'isha tana sanar da Ummanta A ranshi ya ce, "shikenan sun ji zancan da ya ke ɓoye musu,ya zama dole ya shiga ya sanar da su gaskiyar lamarin domin ya yarda Alhaji Saddiƙ ba zai mishi ƙarya ba,ba zai cuce shi ba,ba zai ci amanar shi ba, kuma ba zai kasance ɗaya daga cikin masu shan jini ba.
Da sallama ya shiga duk da baya da kuzari amma ya yi ƙarfin halin cewa "kuna hira ne? Umma cikin damuwa ta ce "wane hira Abbansu zauna ka ji". Ya zauna tare da faɗin "lafiya dai ko? Umma ta ce "da sauƙi dai,dama Abbansu dama ashe irin sana'ar da yake yi kenan?" Abba ya ce "wa?" Ta ce "Alhaji Saddiƙ mana ta shiga jero mishi bayani yanda A'isha ta sanar da ita. A'isha dake ƙwance jikin Ummanta tana kuka,ta ce "Abba ka min afuwa na sani ranka ba zai so ba, amma duk da haka zan aure shi.
Abba ya ce "ku kwantar da hankalinku ni kaina na san wannan labarin kuma shi da kansa ya yi min bayanin zargin da jama'a suke masa. Tabbas tun daga kan Hajiya Jummai duk Mata da ya aura mutuwa take yi, gaske ne ya yi aure kusan tara ko goma ne? Duk sun rasu," A'isha ta zaro ido,