Mummunan Zato 1 Complete Hausa Novel

Author :  Halima K Mashi Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 10

6K to 9K   out of 29.6K words

ɗansa mahalaka,don ni da kaina sai in rinƙa ganin tamkar gidan nawa mahalaka ce, Allah ya yi maka sakamako ya sa itace sanadiyyar warwarewar al'amurana."

"Amin" inji Abba. "To yanzun yaushe ka ke son matarka?"

Alhaji Saddiƙ sai ya samu kan shi da jin nauyin Abokin nashi,ya yi shiru, Abba ya dube shi "Don Allah Friend kada ka ji komai,ba wata kunya" Alhaji Saddiƙ ya ce "abin ne sai yana ba ni mamaki, ashe zaka haifi ƴa ni kuma in aura?" "To ai abin Allah ne," inji Abba,"yanzu dai yaushe ne za ka turo sai a saka rana in ta dawo hutu ayi bikin in ya so zan roƙi alfarma koda je ka ka dawo ce don Allah ka yarje mata,don tana son karatu,burinta shine ta zama Doctor."

"Don wannan kada ka damu Friend, insha Allahu ba tun turowa daga naje zan masu Alhajinmu bayani." Daga nan suka ci gaba da hirar aikin gyaran kamfani, bayan sun gama tare da cewa su zo su je gidan nashi, Alhaji Saddiƙ yace"an ya sai nake ganin yanzu kamar gidan zai min wuyar zuwa" Abba ya miƙe "to tashi muje ku gaisa da yarinyar,don tuni na yi mata bayani" Alhaji Saddiƙ ya dubeshi da sauri "Ta amince?" Abba ya yi murmushi "A'isha ba ta musu ko gardama,ƙwarai zaka ji daɗin zama da ita,ko dana sanar da ita ba ta yi musu ba, amma ta yi zancen karatunta,in kaje yanzun ka ga sai ka shaida mata karatun nata yana nan, insha Allahu" "to na gode,sai dai in har bata so dole ne mu bar wannan maganar," murmushi kawai Abba ya yi, sannan ya miƙe tare da faɗin "shiryo mu je, bari na yi waya" ya fita. Umma ya kira ya ce mata ga su nan zuwa su da Alhaji Saddiƙ, kuma yana buƙatar zoɓo mai ɗan sanyi.

Falon Abba suka shiga Umma ta leƙo sun gaisa tare da tambayar Iyalan nashi da kuma su Hajiyarshi,ya ce duk suna lafiya,ta koma kicin inda A'isha ke harhaɗa abinci kan babban tire. Umma ta ɗauka tare da faɗin "Shiryo musu zoɓon bari na kai wannan." Tana direwa Abba ya dube ta, "Ni fa dake zaki haɗa min,Ummansu shi Friend sa mishi nashi shi ɗaya, wannan zuwan ba nawa bane,na ƙawallinki ne." Murmushi Umma ta yi,ba ta ce komai ba ta fita. Ta isko A'isha kicin tana ƙoƙarin fitowa,ƙasa-ƙasa ta yi mata magana.

"Ki natsu ban da wauta, Alhaji Saddiƙ zai yi magana da ke,kada ki ba Abbanku kunya." Ta ce "to" dama tsaf take. Ta nufi falon Abba,ta yi sallama ta shiga.

Daddaɗan ƙamshin sa ya gauraye falon, ta ɗan saci kallon inda yake yana sanye da wani farin shara-sharan yadi wanda har ana iya ganin bes ɗin shi ta ciki. Ƙyan yadin ne ya bayyana tsadar shi,hular shi ƙube ce wadda aka yi ta da farin zare. Ta dire tire sannan ta zauna ƙasa,kanta sunkuye ta ce, "Ina yini Uncle?" Tun shigowarta ya ke kallonta, duk da cewa sanye take cikin hijabi bai hana shi ganin rashin jikinta ba, shi kanshi tausayinta ya ji ya amsa da cewa, "lafiya lau ƴar Abbanta." Ta miƙe ta soma ɗauko plate don zuba mishi cous-cous, ya ce "bar shi Nana A'isha,ba ni zoɓon nan nasha bana jin yunwa," ta ce "to" ta soma zuba mishi cikin kofi ta rage tsawo ta bashi,hakan ya burge shi, sannan ta koma mazaunin ta ya dube ta,ke ce kikayi wannan zoɓon?" Ta ɗaga kai alamar "Eh" ya kuma kafa kofin a bakin shi ya shanye ragowar na cikin kofin.

"Kice zaki dinga haɗa min in kin koma gidana can Katsina? Ko ba za ki je Katsina ba?" Cikin cinyoyinta ta tura kanta,ya ce "Gaya min in ba ki son zuwa don bana son ki takura." Ta ɗago kanta ta ɗan dube shi "in dai zan dinga zuwa makaranta ai ba komai," ya ce "da gaske ki ke yi?" Ta ɗaga kai ya ce, "To za ki yi karatunki in ma makarantar da ki ke,ki ke so zan bar ki kiyi abinki,yanzun yaushe zaki koma?" Ta ce"jibi" ya ce "to shikenan,in na kai jibi a garin nan sai na kai ki." Ta ce,"To" bai san me zaice mata ba ma,yana jin nauyin yi mata magana, hannu yasa cikin aljihun rigarshi ya ciro bandir ɗin ƴan Naira ɗari biyu "Gashi kiyi shopping" ta ce,"A'a,ka barshi na gama shopping ai" ya yi yayi taƙi amsa,ta nufi cikin gida. Abbanta ya ce har kun gaisa?" Ta ce "Eh," ta shige ɗaki bakin gadonta ta zauna. Mutumin yana burge ta, ya iya gayu mai ƙyau da shi, tunda ya ce zatayi karatu ba ta damu ba, sai dai zata yi kewar Ummanta da Abba.

Washegari tafiyarshi ta kama,don haka ba zai samu kaita makaranta ba, Abba ya ce kada ka damu,dama da akwai motar da ke kai su, kuma ita ce ke ɗauko su. Ya ciro ƙwalin waya ƴar mai ƙyau ƙirar (Nokia), "Gashi ka ba ƴar gidan tawa in dai babu damuwa, saboda kasan ba zan dinga samun zuwa ba, duk da na san ba za ta da ita makaranta ba,in ta dawo ma ringa gaisawa,don na bata kuɗin ne taƙi amsa shiyasa na siyo mata da na fita ɗazun," Abba ya ce "ita da zata koma makaranta ka sai mata waya?" Alhaji Saddiƙ ya ce ka dai bata ƙila ma zata fi amsa min magana a cikin wayar," "shikenan" inji Abba, Allah ya biya maka da gidan aljanna,bari na turo ta kuyi sallama," "a'a ka barta tana jin nauyina yarinyar tana da kunya bana son matsa mata," "shikenan". Suka sake yin musabaha, sannan ya shiga mota sai Kano,ya bar motar a gidanshi na nan Kanon, sai ya hau jirgi.

Labarin da Alhaji Saddiƙ ya zo ma su Hajiyarmu da shi sun ji daɗi, amma suna fargaba sai dai Alhajinsu ya kawo shawarar a miƙe da roƙon Allah,tun kafin bikin,ya ce zai samu malamai kuma zai sanar Masallatai a saka su a cikin addu'a.

Nafisa auta itama cewa tayi Yaya Saddiƙ nima insha Allah zan soma tsayuwar dare tun daga yau. Ya dube ta "kin yi alƙawari fa?" Ta ce "insha Allah,Yaya zan cika" shima dama Allah ya ke gayamawa kullum sai dai ya sha alwashin dagewa.

Ya dubi Hajiyarmu wadda har yanzun ba ta ce komai ba, sannan bai karanci wani abu game da zancan a fuskarta ba,ka ra Hajiyarmu ta yi don haka bata furta komai ba. Amma zancan ya yi mata daɗi, duk da tana fargaban abin, ganin kallon da yake mata yasa ta ce "Allah yasa ma abin albarka."

Yayi ajiyar zuciya tare da miƙewa,can ƙasan zuciyarshi kuwa cewa ya yi "Amin Hajiyarmu".

Nafisa kuwa, dariya ta yi.

Sau da yawa tana mamakin yanda Hajiyarmu da Yaya Saddiƙ suke jin nauyin juna,tamkar surukai. Yace "to ni zan tafi,ban riga na sanar da Jummai ba tukun, sai na koma yanzun."

Nafisa ta ce, "Yaya don Allah kada ka gaya mata".

Kafin ya yi magana, Hajiya ta ce "Don me? Ke Nafisa kin cika fitina," shiko ƴar dariya ya fita yana yi, Nafisa ta bishi tana cewa "Yaya bani lambar A'isha,zan kira ta," ya ce "ayya Nafisa, A'isha yarinya ce ƙarama, gobe ma zata koma makaranta (S.S 1) take a Munjibir, kuma ba wai shekarunta ne suka kaita (SS) ɗin ba, ƙoƙari ne,she is fifteen."

Dariya ta yi.
"Yaya kana son ƙananan yara."

Ya ce,"to Nafisa ƴar abokina ce, shi ya bani duk da yasan matsalar gidana,ki bari in lokacin ziyarar ɗaliban makarantar ta zo in kina gari sai muje ko?"

Ta ce, "to Yaya," Ta koma ciki,shi kam ya shige mota. Ya lura kowa yana son Aisha a dangin nashi, yanzun saura Jummai.

*** **** **** ****
Umma ta ce, "Ga wayarki can jikin chaji in ji Uncle ɗin naki, har ma da layi ya saka miki." Ta kalli wayar, "kai tana da ƙyau wayar, sai dai na san Abba ba zai bari na riƙe waya ba, kuma makaranta ma ba zasu bari ba ai".

Umma ta ce,"to ai Abban naki ne ya kawo" ta ɗauki wayar tana jujjuyawa,ga ta ƴar mai ƙyau,na gode. Umma ta yi dariya.

"A'isha kenan,dama ga ki da son yin (Game)."

Tayi dariya,ta zauna tana cewa, "Bari na gani zan gane kan wayar kuwa?" Ba tako gane ba, sai da Yaya Abdurrahman ya shigo, sannan ya koya mata.

Bayan sallar Isha'i,sun ɗan taɓa hira ta ce "bari na ƙwanta Umma,don gobe tashin wuri zan yi saboda komawa makaranta."

Jafar ya ce, "Yaya A'isha ko dai kina son ki buga (Game) ne da wayar?"

Ta ce,"Jafar ka raina ni ko?" Ta shige ɗakinta, gado ta haye tana buga (Game) ɗin (Bounce) kusan goma na dare wayar ta shiga ringing,ta saba da wayar Umma don haka ba taji komai ba,ta ɗauka. Da ƴar zazzaƙar muryarta ta ce,"Salamu alaikum" ya amsa da "wa'alaikis-salam, A'isha ce?" Gabanta ya faɗi saboda ta gano Uncle ne,ta amsa "Eh." Ya gyara ƙwanciya, "kin san mai magana?" Ta ce "Eh," ya ce to wanene?" Ta yi shiru ta rasa me zata ce,kina jina? Ta ce Umh,ya ce kiyi magana mana A'isha...

#######
[11/30, 21:03] Ummi Tandama😇: ____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*

*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*


*Ɗandano page 5*


Ya ce kiyi magana mana A'isha,wa ke magana da ke? Ta daure ta ce, Uncle ne. Yayi murmushi, "zan zama mijinki kuma kina ce min Uncle? Gara kin kira sunana" ta ce "bazan iya kiran sunanka ba". "To ki samin wani sunan mana ban da Uncle". Ta yi shiru, ya ce "to ba mu gaisa ba" ta yi maza ta ce "Ina yini?" Ya ce "lafiya lau Nana A'isha Saddiƙa,ya ya su Abbanki da Ummanki?" Ta ce"suna lafiya." Ya ce "za ki jini ina kiranki da sunaye duk na ki ne", ta yi shiru, shima ya kan rasa me zai ce mata,can ya ce, to bani labari" ta ce "Na me?" Ya ce, "Na komai mana" ta yi shiru,ya ce "To bani na ƙawayenki na makaranta."

Tamkar ya mata susa,ta ce "ƙawayena biyu ne,da Suwaiba Shehu Ringim,sai kuma Zainab Shitu Katsina, duk suna da kirki."

"Ashe har da ƴar garinmu? Ki ce shi kenan in kin zo Katsina kina da ƙawa, sai kuyi ta wasanku ko?".

Kalmar ta bata dariya, har ma ta ɗan dara kaɗan, sannan ta ce "wasa kuma?" Ya ce, "Eh mana,ko baƙwa wasa a makaranta?" Ta ce "sai ka ce ƙananan yara?" Ya ce "Au,na manta ashe fa ku manya ne,ni da har ina son in saya miki kayan wasa su Tedi, haka su Cartoons." Ta ce "Haba dai?" Ya ce, "To shi kenan bari in bari sai kin haifa mana Beby sai in saya mata ko?"

Zancan ya yi mata nauyi, har ma ta kasa magana,ya ce "A'isha" ta ce "Umh" "kin ji me nace?" Ta ce "Um," "to kin yi shiru" ta ce "Uncle Ina jin bacci," ya ce"shikenan yi baccinki, sannan ki yi mafarki mai ƙyau na ƙyawawan yara masu kama dani" ya kashe wayar.

Shiru ta yi tana mamakin zancan da Uncle ya yi mata,ta yi addu'a ta shafa ta runtse idanu, har bacci ya yi gaba da ita.



Hajiya Jummai wadda ta jima tsaye kanshi tana sauraron surutun da yake yi, sai jikinta ya hau rawa,ta san tabbas da budurwa yake magana, kenan Alhaji aure yake nema? Cabdi! Daga gani kuma ko ma wacece yana sonta,dubi yanda yake wani kashe murya tamkar shima ɗan matashin saurayi ne? Lallai yana neman tada zaune tsaye ne, amma don ta san in har ta nuna ɓacin ranta yanzun ba zata san komai game da yariyar ba,don haka sai ta sako makirci da kisisina.

"Alhajina kai kuma da wa kake samartaka a waya?"

Cike da walwala ya dube ta,sanye take da rigar bacci mai santsi, ɗan gashin kanta da ya rage ta tufke shi da ƙyar ma yake tufkuwa saɓanin da da take da gashin da yawa, tsabar ƙalƙalin da take ma gashin duk ya karye.

Ya miƙa mata hannuwanshi alamun ta zo, sai ta basar ta zauna gefenshi, ta kuma cewa da shi.

"Kai da wa kake waya?"

Ya ce, "ƙanwarki to be insha Allah." Ta danne wani abu da ke son taso mata.

"A ina ka samo ta? Nifa ina jin tsoron ka ƙara aure yanzu in ina tuna baya."

Ya ce"to ni kaina a tsorace nake,ƴar abokina ce na Jigawan nan,wato Mustapha Gumel."

Ta miƙe da sauri tare da faɗin "Dama na san za'ayi haka,wato yaga kuɗi za'a ɗora shi manajan kamfani ba dole ba, kai ma in baka so cutarshi ba ai sai ka gaya mishi cewa gidanka duk wadda ka auro mutuwa suke yi."

Ya dube ta, "To menene na tada jijiyar wuya? Har kina gaya min cewa In ba na so cuta ba, wato ni ne macucin ko?"

Shiru ta yi ranta yana tafasa.

Ta miƙe tsaye "wallahi wannan karon ba zan yarda ba,ban amince da auranka ba, shiyasa ka ke waya har kana wani cewa zata haifa maka yara? Sai dai ka zaɓa ko ni ko ita, haka kawai kana auro matan suna mutuwa,ƙila ma ana can ana zagina ana cewa nice ke kashe su to ba zan iya ba."

Ya dube ta,"zan auro ta, itama ta zo ta mutu,batun yarda kuma bana neman yardarki tunda bake bace Hajiya Sa'adatu uwata ba,kin ji ko? Batun kamfani kuwa da kike magana naga ba naki bane,bana kuma son shiga sharo ba shanu,in ma kyauta na bashi ba ruwanki sannan ki sani rashin mutuncinki da ki ka iya kada ki yarda ya zo kaina."

Fuu! Ta fice ta bar mishi ɗakin, kallo ya bita da shi, cikin mamakin ɗaga hankalin ta da tayi. Sam bai za ci haka daga gareta ba, saboda duk auren da ya yi a baya bata taɓa nuna damuwarta ba sai wannan.

Ita ko cikin ɗakinta safa ta ringa yi tare da marwa, lallai ta kula Alhaji da gaske auren nan zai yi,ta soma magana, wallahi-wallahi ba zan gushe ba zan cigaba da ɗaukar alhakin rayukan duk wadda ta yarda ta yi kishi dani, shima wannan karon ko nawa zan kashe sai nasa an kama min shi, aikin banza kawai in ko ba zai gaji da aure-aure ba nima ba zan gaji da aikawa da duk matar da ya aura barzahu ba."

Ta ɗauko wayarta, Hajiya Kari ta soma nema,tana ta ringing ba ta ɗaga ba,ta ja tsaki itama ƴar iska ko gidan uban wa ta shiga ni ban ma sani ba,Ta Kuma kira, cikin yanayin bacci ta ɗauka, tare da faɗin "lafiya Hajiya Jummai?" Ta ja tsaki "to kasa sarkin bacci in ce dai kin wartsake? Magana zamu yi."

"Ina jin ki" inji Kari, "kin ji na da wannan sarkin ɗaukakkiyar" "Wa fa?" Inji Kari, "Alhaji mana, aure ya kuma ƙirƙirowa, duk abinda ya faru baya bai ishe shi saduda ba." Kari ta ce, "ke ki bari, aure kuma ya ƙara lakatowa?" Jummai ta ce, "ke dai bari, sai ma kin ji yanda ya wani canza murya yana magana da ita a waya, ina zaton da farko ma bai yi niyyar sanar dani ba, kawai na kama shi suna waya."

Hajiya Kari ta ce, "To ya ya kikayi?" Ta ce, "buɗe wuta mana, yanzun nan in gaya miki kaca-kaca mukayi da shi". Hajiya Kari ta ce, "Kash! Ai ke kin ji matsalar ki,ke da zakiyi kwanto kamar yanda muka saba,me ma kika sani game da yariyar?" Hajiya Jummai ta ce, "Me kuwa? Abinda na sani kawai ya ce min ƴar abokinsa ce,kishi ya rufe ni na hau masifa." Hajiya Kari ta ce, "lallai kin so ki kwafsa,ko sunanta ba muji ba, saboda haka da safe ko kuma yanzu ki je ki bashi haƙuri ki ce masa zafin kishi ne, daga nan sai ki bugi cikin shi muji komai."

Hajiya Jummai ta ce, "sai dai goben, amma yanzun kamar ba zai saurareni ba,na san shi sarai ina ganin wannan karon ko boka na dutse ba zai iya aiki kan Alhaji ba, zan nemi wani tunda har yau bana juya shi yanda nake so,sai yanda ya ce, dole haka za'ayi."

Hajiya Kari ta ce, "kada ki damu, zan zo gobe sai mu yi magana a tsanake, amma don Allah ki kwantar da hankalinki" ta ce "zan yi ƙoƙari."

Yana saka kaya ta shigo da sallama. Ta ci gayu cikin shadda mai kalar ja, ƙyan shaddar da tsarin ɗinkin shine ya toni asirin tsadar kayan,ƙamshinta ya cika ɗakin,cike da salo ta iso gurinshi ta amshi (Nect tie) ɗin tana gyara mishi tare da faɗin, "ka ganka kuwa Alhajina? Kai ka yi ƙyau." Bai ce mata komai ba, haka nan bai saki fuska ba, kuma bai katse ta da gyara mishi (Nect tie) ɗin ba, sai da ta gama yana kallonta,ta ɗauko turarenshi Matador ta fesa mishi kaɗan, sannan ta ce sauran ka (break) ya ce na ƙoshi,ta dube shi da sauri ban gane ka ƙoshi ba? Kana nufin ba zaka ci ba zaka fita?"

Ya soma tafiya,tasha gabanshi cikin yanayin tausayi,ta ce "Haba Alhajina, kayi haƙuri na san ban ƙyauta ba laifin kishi ne, sonka ne ya sani na yi maka haka." Ya tsaya yana dubanta, sannan ya ce "Don kina kishina sai ki min rashin kunya? Har kina gaya min cewa ni macuci ne?" Ta zube ƙasa guiwa biyu.

"Kai min afuwa,ba zan sake ba." Ta soma hawaye, mai tausayi ne musamman ga mata,don haka ya ce "naji tashi shi kenan, amma kada ki sake,batun Break kuwa na yi latti,in na dawo zan ci na dare" cikin shagwaɓa ta ce,"ka kula min da kanka." Ta rakashi zuwa ƙofar falo,yana fita ta ce,zaka sani ne, tunda ka ce mata kasa gaba.

Hajiya Kari ta dubi Hajiya Jummai.

"Ina jin ki."

"Wai kin san da ya ya ma ya faɗa min sunanta?" Ta ɗan dakata,kafin ta cigaba "sai da siyasa,na ce haba Alhaji ko baka huce ba ne? Kana ji ina tambayarka sunan ƙanwar tawa amma ka min banza."

"To me zan ce miki" haka fa ya ce min sai daga baya yake ce min "A'isha." Yaƙi gaya min ma lokacin bikin."

Hajiya Kari ta ce, "ki bar shi,ai dai in lokacin ya matso dole muji, tunda mun samu sunanta shi ne kawai abin buƙata, yanzu kuma mun ji."

Yanzun sai mu sa ranar tafiya maguzawan, "To yaushe ne

3 / 10