Author : Mansur Usman Sufi Category : Taskar Novels
Nuwairat duk shekara tana yin hawa na musamman da kan ta,
Ta kai mamayar bazato da rundunar mayakan ta,
Kwatsam a kashe garin ranar da Nuwairat zata yi wannan fita yaki ne,
Ta yi wani mafarki da ya firgita ta ya hana ta sukuni,
Ba wani abu ta gani har ya hana ta barci ba face surar wani kyakkyawan saurayi,
Wanda tun da take a rayuwar ta bata taɓa ganin bil'adama mai kyawu tamkar sa ba,
Tun a daren sarauniya Nuwairat ta ƙasa rintsawa bisa yadda zuciyar ta kamu da matukar
kaunar saurayin da ta gani a Cikin barcin ta,
A lokacin tashi Manzo ta aika aka kirawo mata bokan masarauta mai suna jadwar ibn zairum,
Lokacin da boka Jadwar ya bayyana a gaban sarauniya Nuwairat a Turakar ta barci sai ya zaɓe
ƙasa ya kwashi gaisuwa a gare ta,
Sannan daga bisani ya ɗago da kan sa sama,
Saadda yayi arba da halin da sarauniya Nuwairat ke ciki sai ya ɗimauce dakyar ya samu sake
sunkiyar da kan sa ƙasa a karo na biyu amma sai jikin ya kama kyarma,
Ba a Kowa ne hali boka Jadwar yaga Nuwairat ba har ya ɗimauce face bisa arba da yayi zahirin
kyakkyawar surar ta bayyana a fili
Domin a wannan lokaci ne tana sanye ne da rigar barci shara-shara wacce bata kai ƙwaurin ta,
kuma bata rufe rabin kirjin ba, hasken fitilun dake turakar ya kara bayyana kyakkyawar surar ta
ya mace dake cikin rigar barcin shara-shara.
Cikin alamun matukar damuwa sarauniya Nuwairat ta dubi boka Jadwar cikin sanyayyar murya
mai ɗauke da damuwa tace"ya abin dogaro na shin ina dalilin wannan kyarma taka da kuma
sunkiyar da kanka ƙasa batare da ka dube ni ba?,
Koda jin wannan tambaya sai boka Jadwar ya buɗi baki Muryar na rawa yace "Ya shugaba ta
na rantse da kyawun surar ki,
Bazan iya kallon ki a cikin wannan yanayi ba koda kuwa na daƙiƙa goma ne domin,
Domin kallon kyakkyawar surar ki zai iya sanya wa na manta da kai na da ma dukkanin sirrikan
tsafi na,
Koda jin amsar waɗannan tambayoyi daga bakin boka Jadwar,
Sai a sannanne ta lura cewa ashe rigar barci a jikin ta kawai sai tayi wuf ta janyo wani mayafi na
alhariri ta rufe jikin ta,
Sannan ta sake duban boka Jadwar ta buɗi baki a karo na biyu ta buɗi baki da nufin ta ce wani
abu amma sai boka Jadwar ya ɗaga ma ta hannu yana mai nuna cewa ta dakata,
Sannan yayi gyaran murya a karo na biyu cikin kakkausar murya yace"ya shugaba ta ba sai kin
wahalar da kanki wajen sanar da ni abin da kika gani a cikin mafarkin ki ba, hakika duk na gani
a cikin madubin tsafi na kuma nayi bincike,
Ya sarauniyar kyawawan duniya kiyi sani cewa haƙiƙa kin faɗa tarko mai wahalar fita,
Domin saurayin da kika gani a cikin mafarkin har kika kamu da soyayyar sa ba wani ba ne face
Wani hatsabibin jarumi da ake kira da suna Hibairu wato SARKIN SADAUKAI na duniya,
Hibairu wani irin mutum ne daya rayu a cikin daji da dabbobi da aljanu bai iya kowane irin yare
ba,
A halin yanzu ba zai fito daga daga cikin dajin Baitul-shamshan da yake zaune a cikin sa ba
face ya kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRI a ranar da zai bayyana a
wannan duniya ta mu zai yaƙi biladama ne domin ya kare martabar dabbobi,
Babu wani mahaluki da zai iya magana da Hibairu har ya fahimci Yaren sa face wani yaro
makaho mai suna Humair,
Wani abin baƙin ciki da na gani a cikin madubin tsafi na shine akwai wata budurwa guda ɗaya
wacce ita ce mace ta farko da SARKIN SADAUKAI zai fara yin arba da ita a cikin dukkan
biladama,
Don haka ita ce wacce HUBAIRU zai kamu da ƙaunar ta fiye da komai a rayuwar sa,
Saboda tasirin cewa ita ce jinsin mace ta farko daya fara gani a rayuwar sa,
Sa'adda boka Jadwar yazo nan azancen sa sai sarauniya Nuwairat ta cika da matukar al'ajabi,
Amma sai ta dube da cikin alamun matukar damuwa tace "shin wace ce wannan budurwa da
zata fara saduwa da SARKIN SADAUKAI,
Hakika duk inda take sai na farauto ta na hallaka ta domin ya zamo cewa nice mace ta farko da
sarkin sadaukai zai fara arba da ita,
Har ya kamu da tsananin kaunata,. Boka Jadwar ya yi ajiyar zuciya a dai dai lokacin da zufa ta
keto masa.
Ya dubi Nuwairat cikin alamun tsananin damuwa yace"ya shugabata kiyi sani cewa haƙiƙa
farautar wannan budurwa abu ne mai matukar wahalar gaske,
Domin lokacin da matasa Cikin halarar tsafi domin na gano birnin da budurwar take sai na sha
bakar wahala har da na su ma sau arba'in
Sannan na gano birnin , ana kiran sa da suna Darul-arzik,
Yana ne sa kaɗan da birnin ki. Abinda na fahimta kawai shine tabbas mutanen birnin Darul-arzik
sun kasance hatsabiban mutane masu ƙarfin sihirin tsafi tunda dai gashi tsawon shekaru kina
kai farmaki izuwa kasashe da bira ne amma ba ki iya gano wannan birni na Darul-arzik ba.
Sa'adda boka Jadwar ya zo nan a jawabin sa sai sarauniya Nuwairat ta cika matukar farin ciki
maral misaltuwa ta dui Jadwar tace "Babu ruwa na da hatsabibancin su tabbas na gano wannan
budurwa na hallaka ta
Shin ka manta ne cewa babu wani al'amari dazan sanya a gaba face na samu nasara akan sa
Tabbas ina so ne alfijir ɗin gobe ya keto Ina tsaye a bakin kofar Darul-arzik,
Daga wannan batu boka Jadwar yayi bankwana da sarauniya Nuwairat ya fice daga turakar.
Kamar yadda sarauniya Nuwairat ta faɗa haka al'amarin yaksance wato tun sulesainin dare ta
kammala haɗa rundunar mayakan ta,
Su ka ɗauki hanyar zuwa birnin Darul-arzik, tun kafin hudowar rana suka isa kofar birnin,
Lokacin da isa sai boka Jadwar ya dubi sarauniya Nuwairat cikin ladabi yace"ya shugabata ina
ganin zai yi kyau mu jira anan har izuwa lokacin da za'a buɗe kofar birnin,
Koda jin wannan batu sai sarauniya Nuwairat ta fusata ainun ta dube sa tace "wannan wata irin
maganar banza ce kake yi
Tabbas yanzu batare da ɓata lokaci zamu karya kofar birnin mu afka musu da yaƙi,
Dajin hakan sai boka Jadwar yace"ya shugabata tuba nakeyi Amma kiyi sani cewa bakomai
bakomai ne yasanya na faɗi hakan ba sai domin cewa idan har mu ka afka birnin zai zamo
cewa tamkar harin bazato mu ka kawo musu,
Tabbas dole ne a samu waɗanda zasu yi gudun tsira daga cikin al'ummar birnin wata ƙila a
samu rashin Sa'a a cikin masu gudun tsirar har da budurwar da muke nema,
Koda jin wannan ƙarin bayani daga bakin boka Jadwar sai sarauniya Nuwairat tayi ajiyar zuciya
sannan ta dube sa tace"tabbas zancen ka dutse ne ya abin dogaro na tabbas na yi maka
mummunar fahimta,
Kamar yadda boka Jadwar ya bada shawara haka al'amarin ya kasance sai aka jira dakarun
birnin Darul-arzik suka fito,
Sannan aka shiga fafata yaƙi, kasancewar masu iya magana na cewa karfin yawa yafi Sarkin
Karfi dai yazamana cewa dakarun Nuwairat sun samu nasara akan dakarun birnin Darul-arzik,
Kamai rashin imanin mutum idan yaga yadda gawarwakin ƙananan yara da tsofaffi mata suka
cika Birnin dole ne ya zubar da hawayen tausayi,
Batare da bata lokaci ba aka ribace waɗansu yan mata guda biyar dasu kaɗai suka rayu daga
cikin
Jama'ar birnin,
Bayan an kwashe dukiyoyin birnin a matsayin ganimar yaƙi
Sai aka ɗauki hanya domin komawa izuwa birnin Garul-mausul,
Tare da waɗannan kyawawan yan mata guda biyar da suka tsira daga cikin jama'ar birnin
Darul-arzik,
Inda a lokacin da aka isa birnin ne aka tafi dasu izuwa wani gida na musamman,
A daren ranar da aka kawo su ne su kayi yunkurin tserewa daga hannun dakarun masu tsaron
su bayan sun hallaka dakarun ta hanyar yi musu kisan gilla,
Bisa wannan dalili ya sanya boka Jadwar da sarauniya Nuwairat suka shiga farautar su a cikin
daji har suka turo musu waɗannan miyagun halittu domin su hallaka su,
Wannan shi ne dalilin da ya baro da waɗannan yan mata guda biyar daga birnin Garul-mausul
kuma suke gudun tsira domin kada waɗannan halittu su hallaka su,
Lokacin da zaratan yan matan huɗu suka ci-gaba da falfala azababban gudu domin tsira da
rayukan su daga miyagun halittun da suka turo su,
Sai suka shafe tsawon daƙiƙa Ɗari biyu suna wannan tsere a dai dai wannan lokaci ne halittun
suka karfin gudun su ya fara raguwa saboda tsananin zafin rana da kishi ruwa da suka addabe
su,
Wannan shi ne abinda ya bawa halittun samun nasarar hallaka yan matan uku
Ta hanyar farke cikin su suka cinye kayan cikin,
Ya zamana cewa sauran budurwa guda ɗaya wacce har yanzu take falfala gudun babu
ƙaƙƙautawa
Sa'adda budurwar taga cewa miyagun halittun sun kusa cimma ta kuma an kashe gaba sauran
Yan uwan ta matan,
Kawai sai taja ta tsaya daga gudun da take yi ta fuskanci halittun batare da ta riƙe wani makami
a hannun ta ba,
Hawaye na zuba daga idanun ta, koda halittun suka ga cewa tayi yi gaba da gaba
Sai kawai suka diro daga sararin samaniya suna masu yi mata ƙawanya suna dalalar da wani
irin yawu daga bakunan su,
Daga can sai halittun su kayi kukan kura suka afkawa
Kyakkyawar budurwar da azababban yaƙi mai matukar muni da ban tsoro suna kai ma ta
miyagun hare hare da fuka -fukan,bakunan su da faratan hannayen su masu kaifi tamkar takobi,
da nufin yi masa kisan gilla,
Budurwar ta wanzu tana kai cewa da zillewa hare- haren miyagun halittun cikin gwanin ta da
kwarewar yaƙi,
Duk Sa'adda ɗaya daga cikin halittun ya kai ma ta hari idan budurwar ta goce sai kaga duk abin
da harin ya taɓa ya tarwatse koda kuwa dutse ne
Koda hassadar Mutum idan yaga yadda budurwar take zillewa hare haren miyagun halittun dole
ne ya jinjina mata ya tabbatar dacewa ta cika Basadaukiya mace mai kamar maza,
Su kansu halittun sai da suka cika da matukar mamaki da al'ajabi,
Domin a wannan karon ne suka taɓa fafata yaƙi da wata bil'adama da suka shafe tsawon Sa'a
batare da sun samu nasarar hallaka ta ba,
Ana cikin wannan artabu ne wani daga cikin halittun ya kai wa budurwar wani wawan hari da
fuka -fukan sa,bisa Sa'a sai ya make ta faɗi ƙasa jini na zuba daga hancin ta da baki,
Kuma numfashin ta na fita sama sama, koda samun wannan nasara,
Sai halittun suka yunkura izuwa kan ta suna wani irin gurnani da dalalar da yawu daga bakunan
su domin su yi fata fata da sassan jikin ta,
Kwatsam bazato babu tsammani sai kyakkyawar budurwar taga halittun sun kurma ihu sannan
su faɗi ƙasa suna shure shuren mutuwa,
Al'amarin da yayi matukar bawa budurwar mamaki kenan, tace a cikin ranta shin kowane ya
hallaka waɗannan halittu,
Amsar tambayar data kasa bawa kanta kenan
Kawai sai ta yunkura ta miƙe zaune da ƙyar,
Ai kuwa sai tayi arba wani narkeken baƙin aljani dauke da waɗansu jarumai guda uku mace
ɗaya namiji ɗaya sai karamin yaro
Tsaye daf da inda take zaune,
Budurwar ta ƙura musu idanu ko kiftawa bata yi
Ba wa su bane Waɗannan mutane ba face su jaruma Husnaila,
Koda su sunaila suka lura da halin da budurwar ke ciki sai ta durfafi inda take domin ta bata
taimakon gaggawa,
Yayin da ta isa sai sunaila ta firo wata jakar fata a gadon bayan ta ɗauko wani ƙyalle ta shiga
goge mata jinin dake zuba a bakinta da hancin ta,
Bayan ta kammala ne ta ɗauki wani garin magani daga cikin jakar ta haɗa a cikin wani kofi na
azurfa bayan ta zuba ruwa ta cakuɗa sai ta kafa budurwar a baki ta shanye,
Koda kammala shanye ruwan maganin nan take budurwar taji ƙarfi a jikin ta har ta iya muƙewa
tsaye
Batare da wani ɓata lokaci ba sunaila da saurayi Hizmal suka yi wa budurwar jagora har bisa
kan Aljani Marhutul-Azab suka ɗora bisa gadon bayan sa
Bayan kowa ya hau sai Marhutul-Azab ya sake yunkurawa ya tashi izuwa sararin samaniya ya
shiga keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya,
Bayan tafiyar su saurayi Hizmal tare da wannan budurwa da suka ceci rayuwar ta.
Sai sarauniya Nuwairat da boka Jadwar suka bayyana a wajen,
Sa'adda Nuwairat da Jadwar suka yi arba da gawarwakin halittun sai suka cika da matukar
baƙin ciki maral misaltuwa su shiga kallon alamun takun sawayen inda aljani Marhutul-Azab ya
sauka,
Cikin hanzari boka Jadwar ya buɗe bakin sa sannan ya runtse idanun sa ya karanto dalasiman
tsafi yana Gama rufe bakin sa sai yayi nuna da hannun sa ga wata bishaya dake fuskantar inda
suke tsaye sai ga hoton dukkanin abinda yafaru tsakanin budurwar da su saurayi Hizmal ya
bayyana a jikin bishiyar tun daga farko har ƙarshe,
Cikin alamun tsananin takaici sarauniya Nuwairat ta dubi boka Jadwar tace "ya dodon bokaye
shin yanzu Mene ne mafita
Haƙiƙa idanuwa basu taɓa rintsawa ba matsawar budurwa NIHLA tana numfashi a doran ƙasa
Kuma bazan taɓa koma izuwa ƙasa ta har sai yaga na hallaka ta na mallaki SARKIN
SADAUKAI Hibairu amatsayin abokin rayuwa ta,
Koda jin wannan batu daga bakin Nuwairat sai boka Jadwar yayi shiru Sannan daga bisani ya
buɗi baki yace"Ya shugaba ta tabbas nayi matuƙar baƙin ciki da bamu riski waɗannan jarumai
ba da su ka samu nasarar ceton rayuwar budurwa Nihla ba,
Domin kuwa sune suke ɗauke da yaro Humair makaho wanda shine kaɗai ya iya magana da
Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI a kaf fadin duniya,
Sannan aljanin dake ɗauke da su kuwa shine ke dauke da taswirar fadar Sarkin bokaye,
Haƙiƙa bakamar asarar mukayi ba da mun riske su shi kenan burin mu ya cika na duniya baki
ɗaya,
Yanzu abinda kawai za su muyi shine mu bazama farautar su domin mu cimma su,
Sai dai kuma ya shugabata wani hanzari ba gudu ba
Yanzu gashi zamu yi wannan tafiya kuma bakiyi sallama da jama'ar ki ba,
Koda jin wannan tambaya sai Nuwairat tace "nasan da hakan abinda nake buƙata kawai shine
ka tashi Manzo na sihiri ya tafi izuwa Birni na domin ya sanar da jama'a ta labarin tafiya ta,
Koda jin wannan umarni sai boka Jadwar ya sake buɗurwar baki ya karanto waɗansu
dalasiman tsafi sai ga wani saurayi ya bayyana a wajen,
Bayan Jadwar ya sanar da saurayin duk abinda ke wakana sai Saurayin na sihiri ya ɓace ɓat,
Sannan boka Jadwar ya karanta wadansu dalasiman a karo na uku take wata dardumar sihiri ta
bayyana a wajen,
Ba tare da wani jinkiri ba sarauniya Nuwairat da boka Jadwar suka hau bisa kan Dardumar
Take Dardumar sihirin ta tashi sama a cikin iska ta shiga keta gajimare cikin matsanancin gudu
tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya,
Hakika boka Jadwar yayi shura a fagen ilimin tsafi
Wannan shi ne abinda ya faru da budurwa Nihla da sarauniya Nuwairat ke son ta hallaka bayan
ta kashe baki daya mutanen birnin su,
Da kuma abinda ya wakana tsakanin ta dasu saurayi Hizmal akan hanyar su ta sada yaro
Humair makaho da SARKIN SADAUKAI Hibairu,
Mu haɗu a
GOGA SHA FAMA littafi na 1 Domin jin
cigaban wannan kayataccen labari,
Daga mai ɗebe miki kewa a kullum da ko yaushe
Mansur Usman Sufi
Sarkin marubutan yaƙi