Author : Mansur Usman Sufi Category : Taskar Novels
Koda ganin hakan sai mahayin ya sanya hannun sa ya ɗauko wannan kasusuwan zaki yana
nazarin su har tsawon dakika arba'in
Daga can sai ya sanya kashi ɗaya a jikin kafafun zakin take ƙashin ya fara motsawa wani irin
haske naban al'ajabi ya gauraye sassan jikin sa,
Koda ganin hakan sai mahayin da saurayi Huzmal suka ja da baya a tsorace
Sannu a hankali kwarangwal ɗin ya dunga sauya launi har ya dawo izuwa cikakkiyar halittar sa
ta zaki,
Kawai sai ya takarkare ya kurma wawan ihu kai ko ganin girman zakin ya isa ya tsorata mutum,
Kafin ɗaya daga cikin su yayi wani yunkuri zakin ya dako suma izuwa inda suke,
Koda ganin hakan sai saurayi Huzmal ya yi koyi dashi suka tari zakin aka ruguntsume da
azababban yaƙi mai ban tsoro,
sakamakon saukar ruwan sama a daren jiya,
Hakan ne yasan ya tun da duku- dukun safiya mutane ficewa daga cikin gidaddajin su su ka tafi
izuwa kasuwa domin tallata hajar su,
Manoma suka fita gona domin yin noma, babban abinda ya kara sanya mutane farin ciki shine
yadda garin yayi lullumi saboda Rashin fitowar rana,
A wannan lokaci fadar kasar ta cika ta batse da al'umma babu masaka tsinke yara, da manya
maza da mata
Gaba ɗaya ginin fadar an yi shine da waɗansu irin duwatsu na zubar daju da yakutu, fadar ta
ƙawatu da nau'ikan kayan kawa da alatun jin daɗin duniya har da ma abinda idanu basu taba
gani ba,
Shimfidar fadar anyi tane da wani koren kilishi mai taushi wanda idan mutum ya taka shi sai yaji
tamkar kafar sa zata nutse a cikinsu saboda haushi.
A ɓangaren yamma na fadar aka kirke wata ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'an ta ta da
zallar mulmulallan jauhari aka yi mata feshi da farin ruwan zinare mai fatsi - fatsi, tana sheƙi da
ɗaukar idanun duk mai kallon ta,
Zaune a bisa karagar mulkin wani shirgegen mutum ne fari,mai tarin saje da ƙasumba kirar
samudawan farko, yana da mitsitsin kai mai ɗauke da yan mitsi-mitsin idanu jajaye da faffafɗan
hanci mai manyan kofofi tare da wani tafkeken baki tamkar kofar gari,. Cikin sa rundememe ne
tamkar an kifa masa kwarya, A jikin sa yana sanye da wata doguwar koriyar alkyabba da aka yi mata cin baki da zaren
Lu'u'lu'u
Takalmin dake ƙafarsa yakasance mai ban sha'awa domin idan ka kalle sa sai kaga yana canza
launi lokaci - zuwa - lokaci, sanye a kansa akwai lambu na sarauta,
Tabbas wannan mutum ya cika mai kwarjini kuma mai ban tsoro, domin komai dakewar jarumi
idan yayi arba dashi dole ne tsoro ya ɗarsu a zuciyar sa,
Kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci cewa yakasance gwarzon mayaki mai tarwatsa maza a filin
daga,
Ba wani bane wannan mutum ba face sarki uslaim ibn kahmar,
Sarki uslaim yakasance gawurtaccen mayaki kuma mashahurin attajiri ya hau karagar mulkin
kasar Baharen tun da yana da shekaru sha biyar a duniya,
A rayuwar sarki uslaim babu wani abu najin daɗin rayuwa daya rasa domin a kullum yana
samun kuɗin shiga da adadin su yakai dinare miliyan ɗari,
Batun dabbobin ni'ima kuma yana da sama da miliyan dubu, ballantana gonaki da kadarori,
Duk wannan abubuwan More rayuwa daya tara bai hana sa jin kamar ya hallaka kansa ba
saboda baƙin ciki,
Bakomai ne ya haddasa masa hakan ba sai domin duk sa'adda ya tuna cewa 'yar sa daya fi so
fiye da komai bata tare dashi,
Dalilin rabuwar sarki uslaim da yarsa gimbiya zarifakuwa shine kamar haka ,
Wata rana gimbiya zarifa na zaune a cikin turakar ta, Turakar ta ƙawatu ainun da nau'ikan
kayan ƙawa da alatun jin daɗin duniya,
A wannan lokaci dare ya tsala yayi duhu dunɗum babu abinda kunne keji face kukan gyare da
haushin karnuka,
Tana cikin wannan haline sai kawai taji kukan jariri ya cika bangaren Turakar baki ɗaya,
Al'marin da yayi matukar bata mamaki kenan kuma ya ɗaure mata kai domin a iya sanin ta a
gaba ɗaya gidan sarautar babu wacce ke ɗauke tsohon ciki,ko mai shayarwa tsakanin kuyangi
da barorin gidan,
Abin tambaya anan shine daga ina wannan kukan jariri yake,
Amsar tambayoyin da gimbiya ta kasa bawa kanta kenan
Abu kamar wasa sai gimbiya zarifa tafi sautin kukan jaririn yana ƙaruwa,nan take taji zuciyar ta
bazata iya jurewa ba sai taje ta ceci wannan jariri gama tunanin hakan keda wuya sai kawai ta
miƙe tsaye ta nufi kofar fita daga Turakar,ta tura kofar ta fita
Ai kuwa sai taga dakarun dake tsaron wajen sun kamu da barci mai nauyi,
Batare da fargabar komai ba ta cigaba da durfafar inda take jin kukan
Amma abu kamar wasa sai gashi ta har ta fice daga lambun shaƙatawar ta batare da taga inda
jaririn yake ba,
Haka dai ta cigaba da tafiya zuciyar ta cike da matukar mamaki da al'ajabi, kawai sai ta ƙara
azama domin ta isa inda wata farar kwalba take mai haske,
Yayin da yazamana saura taku goma tsakanin ta da kwalbar ba sai taga cewa wannan kwalba
na ɗauke da wani koren ruwa mai yauƙin gaske kuma kukan daga cikin ta yake fitowa,
Al'amarin da ya yi matukar ɗaure mata kai kenan tace a cikin ran ta ya akayi kukan jariri ke fito
daga cikin ta kuma wane ne ya ajiye kwalbar,
Haƙiƙa al'amari ne na sihiri, yanzu zan buɗe kwalbar domin naga mene ne a ciki domin dai
masu iya magana na cewa da a baka labari gwara ka bayar,
Koda kamma ayyana hakan sai kawai ta ɗauki kwalbar ta buɗe murfinta,
Kaico! Hakika rashin sani yafi dare duhu, inda ace zarifa tasan abinda zai faru da bata yi
gangancin bude kwalbar ba ,
Domin koda buɗewar ta sai wannan koren ruwa ya rikiɗa izuwa wani narkeken baƙin aljani mai
matukar muni ban tsoro daban al'ajabi, gaba ɗaya jikin sa cike yake da gashi, yana ɗauke da
manyan fuka-fukai,
Koda gimbiya zarifa tayi arba da aljanin sai ta ɗimauce ta buɗi baki da nufin ta kurma wawan
ihu amma kafin takai ga aikata hakan aljanin ya busa mata wata iska daga bakin sa take barci
mai nauyi ya ɗauke ta,
Kawai sai ya suret ta ya luluƙa izuwa sararin samaniya ya ɓace ɓat a cikin gajimare,
Tun kafin ƙetowar alfijir gaba ɗaya gidan sarautar ya hautsine da gujegujen jama'a bisa jin
labarin ɓatan gimbiya zarifa,
Abangaren sarki uslaim kuwa lokacin da labarin ya riske sa sai ya haukace ya kama kashe
kuyangi da barorin sa,
Al'amarin da ya sanya gidan sarautar ya hautsine kenan kowa ya shiga gudun ceton rayuwarsa,
A cikin wannan haline bokan masarautar ya bayyana ga sarki uslaim a lokacin da yake kai
komo a Turakar gimbiya zarifa hannunsa riƙe da takobin sa na digar da jini, fuskar sa a murtuke
babu annuri tamkar an aiko masa da sakon Mutuwa,
Koda sarki uslaim yayi arba da boka ƙarzum sai ya bude sa cikin matukar fushi da bai taɓa yin
kamar sa ba yace "yakai ƙarzum shin wane shirmen banza kake yi har wani ya shigo gidan
sarauta ta sace gimbiya, yi maza ka gano mini wane ne shi kuma ina ya kai ta,
Na rantse da darajar iyaye na sai na yi masa kisa mafi muni da ba'a taɓa yiwa wata halitta ba,
Koda jin wannan batu daga bakin sarki uslaim sai boka ƙarzum ya zube ƙasa ya kwashi
gaisuwa cikin ladabi cikin kakkausar murya yace"ya shugabana kayi sani cewa zuwa inda
gimbiya zarifa take a halin yanzu dai -dai yake da mutum ya sayi ajalinsa da kuɗin sa bakowa
bane ya ɗauke ta ba face Sarkin bokayen duniya wanda a halin yanzu babu mashahurin
matsayi kamar sa walau mutum ko aljan,
Ya shugabana kayi sani cewa duk faɗin duniya babu mahalukin da isa yaje inda gimbiya take
har ya ceto ta face wani mutum guda ɗaya hal! Wannan mutum kuwa ba wani bane face.
Jarumi Hibairu wanda ake yiwa laƙabi da SARKIN SADAUKAI na duniya
Bincike ya tabbatar da cewa ahalin yanzu babu gwarzon mayaki kamar sa,
Domin an ce yana iya gudun Sa'a goma ɗauke da zakanya a kafadar sa batare da ya gaji ba,
Kuma duk girman zaki idan suka bangaji kirjin juna sai dai zakin ya faɗi ƙasa,
Duk abin da bokaye zasu faɗa game da SARKIN SADAUKAI sai dai su faɗa kawai amma yace
yadda ake tsammani,
A wannan lokaci Hibairu na rayuwa ne a cikin daji da ake kira da suna Baitul-shamshan,
Bai taɓa ganin bil'adama face dabbobi da aljan,
Bazai taɓa fitowa daga cikin dajin Baitul-shamshan face a ranar da ya kammala bawa tsuntsun
tsafin sa horan yaƙi,tare kammala karance sirrikan dake jikin ZOBEN SHIRIN sa
Tabbas tunkarar Hibairu da buƙatar ceto rayuwar gimbiya zarifa a can fadar Sarkin bokaye dai
dai yake neman jaki mai ƙawo,
Ko kuma nace maka dai dai yake da mutum ya siyi ajalinsa da kuɗin sa, domin Hibairu yana
magana ne da wani yare guda ɗaya dashi ne kaɗai ya iya shi a duniya domin mahaifiyar sa ta
rasu bayan dakika goma da Haihuwarsa,
Sa'adda boka ƙarzum yazo dai dai nan ajawabin sa sai idanun idanun sarki uslaim suka
zazzaro kuma hankalin sa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe,
Ya dubi boka ƙarzum tamkar zai fashe da kuka yace
"Ya samanin ilimin tsafi yanzu mene ne mafita, tabbas zan iya bayar da komai da na mallaka
domin ceto gimbiya ?
Da jin wannan batu sai boka ƙarzum yayi shiru yana mai dogon nazari gami da sunkiyar da
kansa ƙasa,
Daga bisani ya ɗago da kansa sama ya dubi sarki uslaim sannan yaja dogon numfashi yayi
ajiyar zuciya yace "ya shugabana kayi sani cewa mafita ɗaya ce in cigaba da gudanar da
bincike bisa halarar tsafi na domin gano yaushe ne jarumi Hibairu zai fito daga dajin
Baitul-shamshan da kuma hanyar da zamu bi mu bayyana masa buƙatar mu, Lokacin da boka ƙarzum yazo dai dai nan zancen sa sai zuciyar sarki uslaim ta ɗan samu
nutsuwa,
Daga wannan furuci boka ƙarzum ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba ,
Wannan shi ne dalilin daya sanya sarki uslaim ke zubar da hawaye a kullum
Tun da daga wannan rana sarki uslaim yakasance cikin shirin zuwa dajin Baitul-shamshan
domin saduwa da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI
Haka dai sarki uslaim ya cigaba da tafiyar da sha'anin mulkin sa kamar yadda ya saba,
Lokacin da aka kacame da azababban yaƙi tsakanin su saurayi Huzmal da zakin sihiri a cikin
gidan tsira a bakin kofar shiga ta uku
Yazamana cewa saurayi Huzmal da mahayin na kaiwa zakin hare hare cikin matukar zafin
nama juriya da bajinta,
Shi kuwa zakin ya wanzu yana mai kai musu hare tamkar wani ifritu,
Nan fa su Huzmal suka fahimci cewa tabbas yau sun gamu da gamon su
Ana cikin wannan fafatawa ne zakin ya shammaci mahayin ya yakushe sa da faratan sa a
cinyar sa ta hagu
Take inda ya yakushe san ya haddasa wani lafcecen rauni jini yayi feshi yayi tsartuwa
Kafin shudewar wata rabin sa'a zakin ya samu nasarar yiwa Huzmal da mahayin miyagun
raunuka sama da ashirin,
Duk wannan artabu da ake yi wannan yaro makaho na goye a gadon bayan saurayi Huzmal
yana jin duk abinda ke wakana ,
Ana cikin wannan gumurzu ne kwatsam bazato babu tsammani sai akaji kofa ta biyu ta buɗe
dake bayan su,
Sai suka yi arba da su sarki shazwan, kafin ɗaya daga cikin su yayi yunkuri boka Dargas ya cire
wani dogo mashi a damtsen sa mai tsawo kaifi da jinin tsiya ya cillawa saurayi Huzmal da nufin
yayi masa kisan farat ɗaya ya hallaka shi,
Cikin wani irin bakin zafin nama Huzmal ya wurkila ya zamewa harin
Bisa rashin Sa'a sai mashin ya soke ɗaya daga cikin idanun zakin
Take zakin ya kama kururuwa,sannan ya rikiɗa izuwa wata bukatar haske take kubar ta tashi
sama cikin iska ta shiga izuwa mazaunin da ke jikin kofar ta murɗa kanta. Har sau uku kawai sai
ta buɗe
Cikin matukar farin ciki saurayi Huzmal goye da yaro Humair makaho da mahayin suka kunna
kai izuwa ciki
Kafin sarki shazwan waziri Rufyan Sarkin yaƙi,da Sarkin bokaye da sauran tawagar su suyi
wani yunkuri, kofar ta sake rufe kanta ruf , wannan farar kuba ta sake rikiɗa izuwa wannan
kwarangwal ɗin zaki kamar yadda yake a ɗazu..
Sa'adda su saurayi Huzmal suka shige izuwa cikin kofa ta huɗu,
Sai suka tsinci kansu a cikin wani katon fili mai yalwa,
A yammacin filin akwai waɗansu ɗaku na guda biyar,
Ginin ɗakunan an yi sune da manyan duwatsun wuta masu kwarin gaske, kofofin su kuma an yi
sune da mulmulallan jan karfe, inda za'a sanya karti majiya karfi mutum hamsin bazasu iya ture
ɗaya daga cikin kofofin ba,
A kofar ɗaki na farko an ajiye wani ƙatuwar akwatu ta baƙin ƙarfe,
Ɗaki na biyu kuwa an ajiye waɗansu akwushi guda huɗu, kowane akwushi na ɗauke da ruwa
garai-garai kuma ya bambanta da ɗayan wato wani fari,baki,shuɗi da ja,
Kofar ɗauki na uku kuwa yana ɗauke da waɗansu kwalabe da girman su bai huce na gwanda
ba,
Suna da ɗauke da wani koren ruwa a cikin su
Kofar daƙi na huɗu da na biyar kuwa an ajiye waɗansu gumaka na waɗansu irin tsuntsaye
masu ban tsoro,
Idan mai kallo ya ɗaga kan sa sama izuwa saman kowace kofa ɗakin zai yi arba da waɗansu
alluna masu ɗauke da rubutu da aka sassaƙa su da wani itace bishiya,
Lokacin da saurayi Hizmal dake goye da yaro Humair makaho da mahayin sukayi arba da
waɗannan ɗakuna biyar sai suka cika da matukar mamaki,
Kuma ya dugunzuma ainun suka kama kalle-kalle da dube dube domin su gano wane ɗaki ne
daga cikin ɗakunan biyar ɗin su shiga ga domin isa gidan tsira,
Tsawon daƙiƙa Ɗari da Hamsin ɗayan su bai ce uffan ba, sai daga bisani saurayi Hizmal yayi
gyaran murya sannan ya kawo gwaron numfashi ya buɗi baki ya dubi mahayin cikin alamun
tsananin damuwa gami da tashin hankali yace yace"ya abokina shin yanzu wane ɗaki
Yakamata shiga daga cikin ɗakunan biyar domin mu shiga izuwa gidan tsira tabbas hankali na a
tashe yake tunda idan mu kayi rashin Sa'a a karon farko bamu shiga izuwa ɗakin da zamu tsira
ba,
To babu makawa abokan gabar mu zasu iya cimma mana har su samu nasara akan mu,
Koda jin wannan batu daga bakin saurayi Hizmal sai mahayin yayi shiru yana mai sunkiyar da
kansa ƙasa yana mai zurfafa cikin Kogin tunani,
Sai da ya shafe tsawon daƙiƙa hamsin a cikin wannan hali sannan ya ɗago da kansa sama ya
dubi Hizmal sa idanunsa waɗanda su kaɗai Hizmal ɗin ke iya gani ya buɗi baki yace"yakai
Hizmal kayi sani cewa a iya tsawon rayuwa ta babu abinda zan sanya a gaba face na cimma
nasara akansa, Naji a jikana cewa wancan ɗauki na biyu shine ɗakin da zamu samu tsira,
Koda jin wannan batu daga bakin mahayin sai Hizmal ya gyaɗa kai alamar gamsuwa, kawai sai
mahayin ya shige gaba, saurayi Hizmal na biye dashi a Baya goye da yaro Humair,
Suka durfafi kofar wannan ɗaki na biyu, da isar su daf da kofar sai suka shiga nazarin
waɗannan akwushi masu ɗauke da ruwa kala- kala a cikin su.
Daga can sai mahayin ya dubi saurayi Hizmal yace"ya Hizmal ina ganin wannan koren ruwa
dake cikin akwushi shine zamu ɗauka mu zuba a cikin wannan mazirari dake jikin kofar sannan
ta buɗe,
Koda gama faɗin hakan sai Mahayin ya tsugunna a ƙasa da nufin ya ɗauki wannan akwushi mai
ɗauke da jan ruwa a cikin sa,
Sai kawai a kaji yaro Humair yayi magana akaro na farko da fara wannan tafiya,
Al'amarin da sanya mahayin ya fa sa ɗaukar akwushi kenan domin yaji me yaro Humair makaho
zai ce.
Yaro ya buɗi baki cikin murya mai daɗi Yace"yaku yan uwana kuyi sani cewa duk da
kasancewar bana iya gani da idanuna na kasance makaho amma na fahimci cewa wannan
ruwa ja dake cikin akwushi ba shi ne mabuɗin kofar ba domin kuwa duk inda ja yake tashin
hankali ne da rashin zaman lafiya, Ina ganin akwushi mai ɗauke da farin ruwa shine mabuɗin kofar domin duk inda farin abu yake
akwai zaman lafiya da kuma alkairi,
Sa'adda mahayin da saurayi Hizmal suka ji wannan batu daga bakin yaro Humair sai suka cika
da matukar mamaki da al'ajabi bisa wannan fasaha d hikima da yayi ,
Batare da wani ɓata lokaci ba Mahayin ya sake tsugunnawa aƙasa ya ɗauki akwushi mai ɗauke
da farin ya zuba a cikin wannan mazirari dake jikin kofar,
A Birnin Tehran anyi wata gawurtacciyar sarauniya,kuma Basadaukiya da ake yiwa laƙabi da
Abidatul-auliya,
Abidatul-auliya takasance kyakkyawa tagaban kwatance da bokaye da su hasashe suka
tabbatar dacewa,
A wannan KARSHEN ƘARNI babu wata mai kyan diri da sura tamkar ta,domin labarin kyawun
ta ya bazu a ko ina a duniya,
Daɗin daɗawa kuma ta shahara ainun a fagen sanin alƙalumman sihiri,
Tun sarauniya Abidatul-auliya tana da shekara sha huɗu a duniya ta hau karagar mulkin birnin
Tehran,kuma a halin yanzu tana da shekaru talatin cif, amma bata taɓa yin soyayya da wani ɗa
namiji ba ballantana tayi maganar aure,
Sautari manyan sarakuna, bokaye, attajirai kan bijiro da bukatar soyayyar su ga sarauniya
Abidatul-auliya amma basa samun nasara,
Al'amarin da yayi matukar ɗaure mane ma auren nata mamaki kenan,
Su ka ce aransu anya kuwa sarauniya Abidatul-auliya tana da cikakkiyar lafiya,
Ya za'ace mace takai waɗannan shekaru masu yawa batare da tana son wani ɗa namiji
ballantana ta buƙaci namiji a kusa da ita,
Bisa hakan yasanya boka suka shiga gudanar da bincike domin su gano dalilin faruwa hakan
Amma haka suka gama binciken su babu wani cikekken bayani daga gare su,
Abinda basu sani ba shine bakomai ne yasanya sarauniya Abidatul-auliya bata soyayya ba ko
batun aure ba sai domin wata matsananciyar lalura da ta addabeta tsawon shekaru masu yawa
tun kafin ta hau karagar mulki,
Wannan lalura dake addabar ta Ita ce tsagin jikin ta