SARKIN SADAUKAI Littafin Yaki Complete By Mansur Usman Sufi .pdf

Author :  Mansur Usman Sufi Category :  Taskar Novels

Chapter   7 / 8

18K to 21K   out of 23.6K words

har sau huɗu,
Aljani ya bayyana gare sa ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa
Aljanin yakasance gabjejen kato mai tsawo da kwarjini sosai,
Komai jarumtakar Mutum idan yayi arba dashi sai ya ɗimauce saboda tsanin munin sa
Boka ƙarzum ya dubesa yace
"Yakai Darmanu ibn kauƙas kayi sani cewa bakomai ne yasanya na kirawo ka izuwa nan ba
Sai domin ina so ka ɗauke mu ni da wannan tawagar 
Kabi sahun aljani Marhutul-Azab da halin yanzu ya durfafi dajin Baitul-shamshan,

Ina so ka cimmu su a Kowa ne, ya Darmanu ibn kauƙas kayi sani cewa matsawar ka gudanar
da wannan aiki yadda na buƙata,
To zan yan taka da bauta da ka shafe tsawon shekaru kana yi agareni,
Koda jin wannan umarni daga bakin boka ƙarzum sai Aljani Darmanu ya sake risina agareshi
yace 
"An gama ya shugaba na yana Gama faɗin hakan sai ya shimfiɗe gadon bayan sa take sarki
uslaim da boka ƙarzum suka hau bisa kan sa suka zauna,
Dakarun rakiya, guzuri gami da kuyangi suka koyi koyi dasu suka hau bisa gadon bayan Aljani
Darmanu,
Cikin kuzari da karfin damtse Darmanu ya yunkura ya tashi izuwa sararin samaniya tare da
kaɗa manyan fuka fukan sa,
Jama'a na ɗaga musu hannu tare yi musu fatan samun nasara har suka ɓace ɓat a cikin
gajimare tamkar basu taɓa wanzuwa ba,
Wannan shi ne abinda ya faru da sarki Uslaim na Birnin bahren
wanda sarkin bokayen duniya ya sace masa yar sa gimbiya zarifa
Kuma a halin yanzu ya fito farautar yaro Humair makaho domin ya samu nasarar saduwa
Hibairu SARKIN SADAUKAI.
Lokacin da aljani Haulatul-infal ya ɓace ɓat daga ɗakin sirri domin zartar da umarnin sarkin
bokaye Dargas,
Kamar yadda boka Dargas ya umarce sa haka al'amarin ya kasance domin cikin abinda bai
huce daƙiƙa hamsin ya bayyana a kofar gidan sarauta ɗauke da sarki shazwan da tawagar sa,
Bayan Haulatul-infal ya sauke su sarki shazwan sai ya yunkura ya sake tashi izuwa sararin
samaniya ya ɓace ɓat
Sarki shazwan bai samu ganawa da Hushriba ba sai da gari ya waye bayan ya kammala kalaci
sannan Hushriba da waziri Rufyan Sarkin bokaye da sauran tawagar matsafa suka iske sa a
cikin turakar sa ta ganawa da baƙi,
A wannan lokaci sarki shazwan na zaune bisa wata ƙasaitacciyar kujera ya caɓa ado irin na
hamshakan sarakai,
Kyawun surar sa ya bayyana a fili, jikin sa na fitar da wani irin kamshin turare mai daɗin gaske,
Lokacin da gimbiya Hushriba tayi arba da fuskar sarki shazwan sai taji zuciyar ta ta buga da
karfi a karo na farko ta kasa gane shin mene ne abinda ya sanya zuciyar ta zata buga da karfin,
Shin ta faɗa farkon soyayya ne ko kuwa tsananin kwarjinin sarki shazwan ne 
Amsar tambayoyin da Hushriba ta kasa bawa kanta kenan
Ta samu waje ta zauna bisa kujerar da aka tanadar mata dake fuskantar sarki shazwan,
Bayan kowa ya zauna ne bisa wajen zamansa 
Sai sarki shazwan ya shiga kallon su ɗaya bayan ɗaya kamar mai nazarin wani abu,
Duk wanda sarki shazwan ya kurawa idanu sai kaga ya sunkiyar da kan sa ƙasa,
Amma bisa mamaki koda ya haɗa idanau da Hushriba sai ya ga ita ma ta ƙura masa idanun ko
kiftawa bata yi,
Al'amarin da yayi matukar ba sa mamaki kenan yace a ransa shin wannan jarumi bata san
Mene ne matsayi na ba ne ta ƙura mini idanu batare da ladabi ba
Wani ɓangare a zuciyar sa kuma na cewa shin baka lura da nau'in kallon da Hushriba ke yi
maka ba ne,

Tabbas kallo mai ɗauke da alamun shauƙin so
To kai ma meyasa ka cigaba da ƙura mata idanun fiye da ƙima
Sa'adda sarki shazwan yazo Nan a tunanin sa sai yaji kunya ta kama sa,
Kawai sai ya dawo da duban sa ga Sarkin bokaye yayi gyaran murya sannan ya fara magana
akaro na farko cikin nutsuwa
"Da farko ina yiwa dukkan waɗanda suka hallara a wannan waje Barka da zuwa tare da yiwa
bakuwar jaruma maraba,
Bayan haka dalilin daya tara ku wannan waje shine domin na saurari dukkan bayani game da
wannan musiba da ta afka mana ta GOBARAR DAJI da kuma karin bayani akan hanyar
magance wannan al'amari,
Koda jin wannan batu daga bakin sarki shazwan sai sarkin bokaye Dargas ya yi gyaran murya
yace"Ya shugaba na dukkan wani bayani da Ya kamata nayi maka nayi maka shi game da
bayyanar wannan jaruma wato Hushriba,
Abinda ya rage dai yanzu kawai shine mu saurari bayani daga bakin Hushriba akan hanyar da
zamu kawar da wannan annoba,
Sa'adda sarkin bokaye Dargas ya zo nan azancen sai jaruma Hushriba tayi gyaran murya tace
"Yakai sarki shazwan kayi sani cewa babban muhimmin abinda ya kawo ni wannan ƙasa taka
kuma har na ceci rayuwar al'ummar kasar ka daga ANNOBAR GOBARAR DAJI
Shine yaro Humair da kuke nema domin ku yanka da ku bayar da jinin sa ga abin Bautar ku
domin kare kanku daga GOBARAR DAJI
A halin yanzu ni ma shi na fito farauta domin na cika burina na mallakar tsumin tsafi dake fadar
Sarkin bokaye, 
Hakan kuma ba zai tabbata ba face na sadu da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI na bayyana
masa buƙata ta ta zuwa fadar Sarkin bokaye domin ya samo mini tsumin tsafi
Yaro Humair shine kaɗai yasan Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI
Kun ga kenan a halin yanzu ina matukar kaunar ganin Yaro Humair makaho a raye saɓanin ku
da kuke yunkurin hallaka sa,
Hanyar da zaku kawar da wannan guguwar annoba kuwa shine,
A halin yanzu saura kwanaki ɗari uku da sittin da uku SARKIN SADAUKAI HUBAIRU ya
kammala bawa tsuntsun tsafin sa horan yaƙi domin ya samu nasarar fito wa daga dajin
Baitul-shamshan ya bayyana a wannan duniya tamu
Ya kai wannan sarki kayi sani cewa kasar ka ce ta farko da SARKIN SADAUKAI zai fara bajewa
daga doran ƙasa,
Kuma yaro Humair ne kaɗai ne zai iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI har ya
fahimci hanyar da zai roƙar muku alfarma a wajen sa,
Kaga kenan a halin yanzu idan ma kun mallaki yaro Humair kun yanka sa kun bayar da jinin sa
ga abin Bautar ku
Dai -dai da kun dabawa kanku wuƙa domin dazarar SARKIN SADAUKAI ya fito daga dajin
Baitul-shamshan zai baje Birnin ka baki ɗaya babu wata halitta mai rai da zai bari ta cigaba da
numfashi,
Sa'adda jaruma Hushriba tazo dai- dai nan a jawabin ta sai hankalin gaba ɗaya jama'ar dake
cikin turakar ya dugunzuma ainun
Kuma ɗakin yayi shiru tamkar Mutuwa ta gifta,

Sai daga bisani Hushriba ta cigaba da cewa "A halin yanzu zama bai same mu ba, 
Dole mu sake bazama farautar yaro Humair makaho domin ya zamo cewa mun mallake sa,
Domin hakan ne kawai zai sanya dukkan mu mu kai ga cika burikan mu, 08137237071
Wani abu da baku sani ba shine wannan mahayi da ceci rayuwar yaro Humair da saurayi
Hizmal ba wani ba ne face yar uwa ta gimbiya Sunaila,
Nasan cewa ko wace yar uwa ta kuma nasan hanyar da zan rabata da yaro Humair
Lokacin da gimbiya Hushriba ta sake zuwa nan azancen ta sai kowa ya cika da matukar farin
ciki gami da mamaki,
Hushriba tayi ajiyar zuciya ta ɗora da cewa "A daren yau nake so kayi umarni ga dukkan
al'ummar wannan birni da su hallara a fada a lokacin da zamu tafi izuwa farautar yaro Humair
domin masu iya magana na cewa da zafi-zafi akan daki ƙarfe,
Tabbas a lokacin da jama'a suka hallara zai basu wani sinadaran tsafi da zasu nasu kariya daga
GOBARAR DAJI har zuwa lokacin da zamu dawo daga abin da muka fita farauta,
Koda jin wannan batu daga bakin Hushriba sai sarki shazwan ya cika da matukar farin ciki
maral misaltuwa,
Nan take batare da wani ɓata lokaci ya umarci shamaki ya sanar da zagi cewa sarki yana son
ganin kowa a fada kuma ba'a ɗauke wa kowa ba koda jariri ne sabuwar haihuwa,
Bayan sarki shazwan yayi wannan umarni nan take ya sallami su waziri Rufyan domin kowa
yaje ya kammala shiri kuma yayi bankwana da iyalan sa,
Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin jaruma Hushriba da su sarki shazwan.







Lokacin da aljani Darmanu ya tsala da azababban gudu a sararin samaniya ɗauke da sarki
Uslaim,boka ƙarzum,da dakarun rakiya domin rabi sahun aljani Marhutul-Azab dake ɗauke da
yaro Humair,saurayi Hizmal da sunaila domin ya cimmu su,
Sai Darmanu ibn kauƙas ya wanzu yana tsala Azababban gudu babu sassauci yana keta
gajimare,
Ana cikin wannan tafiya ne sai yazamana cewa rana ta kwalle tayi tsananin zafi,
Don haka sai boka ƙarzum ya umarci Aljani Darmanu da ya yada zango,
Koda jin wannan umarni sai Darmanu ya saki fuka- fukan ya sauka ƙasa luuuh!
Ya sauƙa a bisa turba, inda ya saukan ya kasance daji ne mai yalwar duwatsu, koramu haɗe
kwazazzabai,
Har wasu daga cikin tawagar rakiya sun yunkura zasu sakko daga kan Aljani Darmanu sai boka
ƙarzum ya daka musu tsawa yana mai nuna cewa su dakata,
Kawai sai ya dubi gabas,yamma,kudu da arewa,
Sannan ya juya ya dubi Sarki uslaim cikin ladabi yace
"Ya shugaba na wannan daji jikina bai kwanta da shi ba, da alamu akwai wani tarko mai cutar
wa, ina ganin zai fi kyau mu sake cigaba da tafiya har sai mun samu waje mai cikekken tsaro

sannan sai mu haɗa zangon,
Kafin boka ƙarzum ya gama rufe bakin sa sai kawai akaga waɗansu waɗansu ayarin gwaggwan
birrai na fito wa daga kowace kusurwa a dajin waɗansu na dirowa daga saman bishiyoyin dajin
waɗansu daga cikin ƙarƙashin ƙasa,
Kafin kace me yarin birran sun yi musu ƙawanya
Su dai birran suna da girma tamkar toran Giwa munin fuskokin su kuwa ya huce misali,gaba
ɗaya jikin su cike yake da gashi buzu-buzu babu kyan gani gaba ɗayan su na shanye cikin
sulken yaƙi nau'i daban -daban tamkar sun kasance bil'adama,
A hannayen su kuwa suna dauke da miyagun makamai masu barazana da dukkan wata halitta
mai numfashi.
Lokacin da aka fara kallon- kallo tsakanin ayarin gwaggwan birrai da su sarki uslaim,
Sai aka shafe tsawon daƙiƙa goma a cikin wannan hali,
Sai daga bisani ne su sarki uslaim suka yi wuf suka zare makaman yaƙin su,
A lokacin da ayarin gwaggwan birran su kayi kukan kura suka yi ɗauki kansu,
Lokacin da aka haɗu da juna nan take waje ya kare da azababban yaƙi,
Bangarorin biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da
bajinta
Ana fara wannan artabu ne fa su sarki uslaim suka fara gane kuren su
Domin duk inda ɗaya daga cikin gwaggwan birran ya sanya a gaba sai dai kaga dakarun rakiya
na zube wa ƙasa matattu,
Wani abu da ya ɗaurewa su sarki uslaim kai kuma ya basu mamaki shine yadda akayi
makaman su suka kasa yin nasara akan gwaggwan birran
Abangaren boka ƙarzum kuwa ya wanzu a tsakiyar birran tamkar wani ifritu,
Sai dai aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana wannan fafatawa ɗaya daga cikin su sarki uslaim bai
samu nasarar koda hallaka gwaggwan birran ba,
Al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankalin su kenan suka shiga damuwa ainun bisa ganin
cewa
Tabbas wankin hula zai kaisu dare,
Sa'adda boka ƙarzum yaga cewa idan aka cigaba da wannan yaƙi a haka zasu rasa rayukan su
baki ɗaya sai kawai ya shiga amfani da karfin sihirin tsafi domin ya ga ya ragargaji birran,
Amma sai abu ya ci tira,ya zama na cewa yayi amfani da sirrikan tsafi fiye da dubu biyu amma
basa tasiri akan birran,
Abangaren sarki uslaim kuwa lokacin da ya zurfafa izuwa cikin Kogin tunani domin samun
mafita,
Koda samun mafitar sai sarki uslaim yayi wuf ya mayar da takobin sa izuwa cikin kube,
Cikin wani irin baƙin zafin zafi ya suri wani reshen bishiya dake wajen ya shammaci wani
gwaggwan biri ya maka masa akai,
Bisa mamaki sarki uslaim yaga gwaggwan birin ya kurma ihu ya faɗi a ƙasa magashiyan,
Koda ganin hakan sai sarki uslaim ya zage karfin sa ya shiga yaƙar gwaggwan birran da
wannan reshen bishiya,
Duk inda ya sanya a gaba sai kaga birran na zubewa kasa magashiyan, wasu sun sheƙa
barzahu,
Koda ganin yadda sarki uslaim ke samun nasara akan birran sai suka yanyame sa tamkar

yadda dandazon kudaje ke yanyame kwallon mangwaro,
Domin a tarihin su babu wata halitta da taɓa yi musu barnar da sarki uslaim yake yi musu,
Sa'adda su boka ƙarzum suka hango Yadda sarki uslaim ke samun nasara akan gwaggwan
birran,
Sai kawai su kayi koyi dasu suka shiga ɗaukar rassan bishiyoyin dajin suka shiga dukan birran,
Wohoho! Kaico haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da su ka ce inda babu ƙasa nan ake
gardamar kokowa, kuma idan rawa ta kiɗa ya canza dole ne rawa ta canza,
Nan fa yazamana cewa filin yaƙin ya hautsine da ƙarar karafniyar ƙarafa da ihu haɗe da
kururuwar birran,
Ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, bishiyoyi suka dunga rangaji suna faɗuwa ƙasa,
Duwatsu kuwa suna karo da juna suna bindiga suna farfashewa,
Abangaren aljani Darmanu ibn kauƙas kuwa ya wanzu a tsakiyar birran tamkar GOBARAR DAJI
domin duk inda ya kai damƙa da hannun sa sai kaga ya cafko birrai guda biyu ya ɗaga su sama
ya maka kansu a jikin duwatsu sun faɗi ƙasa matattu,
Lokacin da gwaggwan birran suka ga cewa bala'i yakai ba'a'i sai suka fara kokarin tserewa,
Amma sai da su sarki uslaim suka dunga binsu a baya suka ƙure musu gudu suna rafkewa,
Kafin shuɗwar Sa'a ɗaya su sarki uslaim sun samu nasarar hallaka ayarin gwaggwan birran,
A sannanne ƙura ta lafa kuma kowa ya dawo cikin hayyacin sa,
A sannanne sarki uslaim ya lura da irin muguwar barnar da ayarin gwaggwan birran sukayi
musu,
A kalla sun kashe dakarun rakiya mutum ɗari biyar
Batare da bata lokaci ba a kasa shiga kwashe gawarwakin tare da duba lafiyar waɗanda suka
samu raunuka,
Aka kafa tantuna domin a yada zango, kuma kuyangi suka shiga hidimar dafa abin kalaci,
Wannan shi ne abin da ya faru da sarki uslaim da tawagar sa akan hanyar sa ta farautar yaro
Humair,
*****
Zaratan ƴan mata ne su biyar, kyawawa na gaban kwatance, waɗanda kallo ɗaya zasu iya
ɗimauta zuciyar duk wani ɗa namiji,
Ke ta faman falfala azababban gudu bisa duga-dugan su tamakar zasu fice daga duniyar, 
Suna gudun abisa cikin kasaitaccen daji mai ɗauke da manyan bishiyoyi, duwatsu, koramu
haɗe kwazazzabai,
Kallo ɗaya zaka yi wa yan matan ka fahimci cewa sun kasance ma'abota bota rayuwa a cikin
daji 
Saboda tufafin da ke sanye a cikin su yakasance an sana'anta sa ne da fatar damisa,kafafun su
ko takalmi babu,
Duk sa'adda da yan matan suka ɗaya ɗaga kawunan su izuwa sama sai kaga sun sake zage
damtse sun ƙara karfin gudun su fiye da ɗazu suna cikin wannan gudu ne sai kawai suka ji an
suri ɗaya daga cikin su an yi sama da ita,
Nan fa suka tsaya cak suna haƙi da numfarfashi, tamkar ran su zai fita,
Hawaye na zubo wa daga idanun su, su ka shiga dube- dube da kalle-kalle suna masu kwalawa
yar uwar tasu kira tare da kiran su nan ta,
Daga can kwatsam sai suka an jefo da gangan jikin ta babu kai,

Nan fa sauran Yan matan suka sake ɗimauce wa suka sake falfawa izuwa cikin daji domin tsira
da rayukan su,
Komai rashin imanin mutum idan yaga yadda yan matan ke gudun tsira dole ne ya zubar da
hawaye.
Su dai waɗannan yan mata bakomai ne ke biye dasu ba face waɗansu miyagun halittu masu
ɗauke da siffa irin ta ƙurar
Kuma yan matan sun fito ne daga wani birni da ake yiwa laƙabi da Garul- mausul ,
Birnin Garul-mausul ya kasance kasaitaccen birni da ya shahara ainun a fagen
kasuwanci,noma da kiwo
Daɗin daɗawa kuma sun tara zaratan Jarumai masu juriya a filin daga,
Sarauniya Nuwairat bintu Darhaz ita ce ke rike da Sarautar birnin 
Nuwairat takasance kyakkyawa tagaban kwatance wanda labarin tsananin kyawun ta ya watsu
a ko ina a sassan duniya,
Mace ce mai matsakaicin kaurin jiki, ba doguwa ba ce ba gajere ba,fatar jikin ta wankar tarwaɗa
mai sheƙi da taushi tamkar ta jariri sabuwar haihuwa,
Tana da dara-daran idanuwa farare ƙal, masu haske tamakar tatacciyar madarar shanu, kwayar
cikin su takasance baƙa sidiƙ,tamkar an ɗiga tawada,
Hancinta dogo mai lankwasa da kyau, a ƙasan sa an tsaga wani ɗan madaidaicin baki da
laɓɓansa suka kasance jajur, haƙoran sa cikin su masu haske da sheƙi,
Wuyan ta dogo mai kyau tamkar na barewa, kirjinta kuwa a cike yake kuma a tsaye ƙyam bai
ranƙwafa ba tamkar nunanniyar gwanda,
Cikin ta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba,
Ƙugun ta a tsuƙe yake daga gaba,
Daga baya kuma yayi tudu sosai, tamakar idan aka ɗora tuffa zata zauna akan kai saboda tudu
su,
Tana da sharɓa sharɓan Cinyoyi masu ɗaukar hankali, yatsun kafafun ta da hannaye sun
kasance zarara masu ban sha'awa,
Gashin kan ta baƙi siɗiƙ mai kyalli da sheƙi tamkar gilashi ya zuba izuwa kan kwankwason ta.
Wohoho! Haƙiƙa duk in da kyawu yake idan aka zo kan sarauniya Nuwairat to batu ya ƙare.
Gawurtacciyar Basadaukiya ce mace mai kamar maza, daɗin daɗawa kuma takasance
azzaluma tagaban kwatance,
Tsananin zalunci Nuwairat ya huce tunanin bil'adama
Domin kowa bata kyale ba babba da yaro,
Wani abu da yake tayar da hankalin jama'a shi ne yadda aka yi sihirin tsafi kowane iri baya tasiri
akan ta,
Kuma babu wani al'marin da zata sanya a gaba face ta cimma nasara akan sa,
Duk wata ƙasa da Nuwairat ta sanya a gaba sai taga bayan ta,
Ta cinye mutanen kasar da yaƙi sun zamo ganima gare ta,
Bisa wannan dalili yasanya ta zamo gagarabadau kuma kadangaren bakin tulu a tsakanin
sarakuna bokaye da matsafa,
Duk saurayin da ya bayyana soyayyar sa ga sarauniya Nuwairat baya taɓa samun nasara,
Da yawa daga cikin su ma sun rasa rayukansu bisa bakin cikin rasa Nuwairat a matsayin
abokiyar rayuwar su.

Bisa al'adar sarauniya

7 / 8