Author : Mansur Usman Sufi Category : Taskar Novels
a cikin dajin
Baitul-shamshan.
Al'amarin su saurayi Hizmal kuwa sa'adda suka samu nasarar shiga izuwa gidan tsira sai suka
tsinci kan su a cikin wani kasaitaccen gida da aka kawata sa da nau'ikan kayan ƙawa da alatun
jin daɗin duniya, gaba ɗaya ginin gidan anyi sane da zallar duwatsun zubar daju yana sheƙi da
walwali, ko ina an kawatashi da furanni da furanni da shuke-shuke gwanin ban sha'awa. Gidan yana ɗauke da manyan falo guda arba'in kowanne na ɗauke da kayan alatun jin daɗin
duniya daya bambanta da ɗayan,
Haƙiƙa babu wani Basarake ko attajiri da zai tsinci kansa a cikin gidan face ya raina kansa ya
tabbatar dacewa ya shiga cikin maƙurar aljannar duniya,
Bayan su saurayi Hizmal sun sauka a cikin wata ƙasaitacciyar turaka sai kowa ya shiga kimtsa
cikin sa bayan an kammala an samu nutsuwa ne sai Hizmal yayi gyaran murya sannan ya kawo
gwaron numfashi ya ajiye ya dubi mahayin nan yace"ya kai wannan jarumi ma'abocin karfin
damtse lokaci yayi da ya kamata ka bani amsar tambayoyin da nayi maka a baya, Koda jin wannan batu sai Mahayin ya ɗora hannun sa a kansa ya cire rawanin sa fuskar sa ta
bayyana a fili ƙarara,
Sa'adda saurayi Hizmal yayi arba da fuskar mahayin sai ya cika da matukar al'ajabi da mamaki,
Bakomai ne ya basa mamaki ba sai bisa ganin cewa mahayin yakasance tsaleliyar kyakkyawar
budurwa,
A iya tsawon rayuwarsa bai taɓa ganin mace mai kyan diri tamkar mahayin ba,
A karon farko Hizmal yaji soyayyar ya mace ta shiga zuciyar sa,
Kyakkyawar budurwar ta jefi Hizmal da wani irin kayataccen murmushi mai ɗauke da alamar
tambaya,
Sannan ta buɗi baki cikin zazzakar murya mai daɗi tamkar sarewa tace"yakai Hizmal a yanzu
na bayyana maka wace ce ni
Yanzu kuma zan sanar dakai dalilin da ya sanya taimaka maka wajen ceton rayuwar yaro
Humair,
Da farko dai suna na Husnaila bintu ishwar, mahaifina ƙasurgumin matsafi ne kuma ƙasaitaccen
sarki da yayi shura a yankin ƙasashen yamma ta tsakiya,
Dalilin rabuwa da mahaifina da ƙasar mu kuwa shine ,
****. *****. *****
Kimanin shekaru arba'in bayan shuɗewar KARSHEN ƘARNI na shida da yin YAKIN DUNIYA na
biyu,
An yi wata ƙasaitacciyar ƙasa da ake yiwa laƙabi da Baitul-Mausul,
Ƙasar Baitul-Mausul ta bunƙasa a harkar kasuwanci,noma da kiwo daɗin daɗawa sun tara
zaratan Jarumai masu juriya a filin daga,
Sarautar ƙasar na karkashin mahaifina sarki ishwar,
Sarki ishwar yakasance gwarzon mayaki mai tarwatsa maza a filin daga, ya na da tarin
dukiya,gami da sanin ilimin tsafi,
Mutum adali mai tausayin talakawan sa, bisa wannan dalili ne yasan ya jama'a ke matukar
kaunar sa da yi masa biyayya,
Kuma sarakunan dake nahiyar suke shakkar sa basa yunkurin kawo masa farmaki,
Mahaifina yana da matan aure guda huɗu kuma dukkanninsu sun haifa masa ya'ya
Yarima ubaiyu shine babba, sannan Hushriba,yarima Zaiyum sai ni yar autar su Husnaila,
A kaf cikin ya'yan mahaifin mu ni kaɗai ce na gajeshi a fagen halaye na kwarai, saɓanin yan
uwa na su yarima ubaiyu,
Yayin da yan uwana suka ga cewa sarki da ma sauran juma'ar gari sun ɗora soyayyar agareni
kuma suna nuna cewa nice zan gaji karagar mulki sai yan uwa na suka fara bayyana mini
ƙiyayya,
Sau babu adadi sun kawo mini hari domin su cutar dani amma sai na tsalleke,
Haka ma a bangaren mahaifiyata tana fuskantar tsangwama daga kishiyoyin ta
A wasu lokutan haka zamu zauna ni da ita suna kukan baƙin cikin abinda ake yi mana
A kwana a tashi wata rana sai mahaifin mu ya kamu da matsananciyar rashin lafiya da aka kasa
gane kanta,komai na jikin sa ya daina motsi sai dai idanunsa da bakin sa da yake iya magana,
Nan fa manyan bokayen ƙasar suka dukufa gudanar da bincike domin su gano musabbin
abinda ya haddasa cutar da kuma maganin dazai warkar da cutar,
Amma mahifina bai taɓa sani ɗaya daga cikin matayen su sun sa abin da binciken ya bayar ba,
Wata rana tunda dukun safiya ni da sauran Yan uwa na muka shiga turakar mahaifin mu domin
mu duba sa,
Da shigar mu mu ka tarar dashi kwance abisa kan gadon sarauta,
Kai idan ka gansa sai kayi tsammanin cewa gunki ne domin komai na jikin sa ya daina motsi
idan ka cire idanuwan sa dake kiftawa,
Sa'adda mu kayi arba da halin da mahaifin mu ke ciki muka shiga zubar da hawaye
Tsawon daƙiƙa hamsin a cikin wannan hali sannan Daga bisani muka miƙe tsaye domin ficewa
daga Turakar,
Yarima Ubaiyu ne a gaba sannan Gimbiya Hushriba yarima Zaiyum sai ni a ƙarshe,
Har na sanya ƙafa ta ɗaya a waje sai naji bisa mamaki mahaifina ya yi gyaran murya yace"ya
yata dawo izuwa gareni domin in sanar dake wani sirri,
Koda jin wannan batu daga bakin mahaifina sai na dawo da baya nazo na tsugunna a gaban
mahaifina,
Kawai sai abbana ya buɗi baki ya karanto waɗansu dalasiman tsafi take wani haske ya bayyana
yaje ya shiga jikin kofofi da tagogin turakar take suka rufe kansu,
Kana haske ya dawo ya cure waje guda ya rikiɗa izuwa wata fitilar haske,
Nan fa Turakar ta gauraye da wani irin haske na ban mamaki wanda koda allura ce ta faɗi
mutum yana dubawa zai ganta.
Kana daga bisani mahaifina ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai tattare daban tausayi yana
mai cewa "ya yata abar alfahari na kiyi sani cewa bakomai ne ya sanya na keɓe da ke ba sai
domin na sanar dakai wani boyayyen sirri guda ɗaya game da wannan cuta da ta same ni,
Ya yata kiyi sani cewa binciken da bokayen wannan ƙasa su kayi ya tabbatar dacewa wannan
cuta tawa Yan uwan ki su yarima ubaiyu ne suka yi mini Shirin tsafi domin su hallaka ni su gaji
karagar mulki na,
Saboda da mugun shirin da su kayi mini ne yasan ya na umarci waziri daya tura ku izuwa
sassan duniya domin ku nemo mini maganin cutar,
Duk wanda ya samu nasarar nemo maganin shine zai gaji karagar mulki na,
Ya yata kiyi sani cewa kece kaɗai na fi kauna a cikin yan uwan ki da mahaifiyar ki,
Saboda haka ne nake so na sanar dake maganin dazai warkar dani daga wannan cuta,
Domin ina son ki gajeni bayan raina na ta tabbata cewa jama'a zasu samun farin ciki da zaman
lafiya har abada, saɓanin yan uwan ki,
Maganin dazai warkar dani daga wannan cuta shine sihirtaccen DAMARAR SIHIRI ta Sarkin
bokayen duniya dake sanye a ƙugun sa DAMARAR SIHIRIn na dauke da waɗansu sirrika na
sunayen Ubangijin wadansu ma'abota wani addini da ake kira da suna Musulunci,
Ina da ace JARUMAN DUNIYA zasu taru waje guda baza su iya raba Sarkin bokaye da wannan
DAMARAR SIHIRI ba matsawar yana tare da ita
Ya yata kiyi sani cewa bazaki taɓa samun nasarar mallakar ɗamarar ba face kin nemi taimakon
wani hatsabibi jarumi da ahalin yanzu yake zaune a dajin Baitul-shamshan,
Ana kiran jarumin Hibairu bincike ya tabbatar da cewa a halin yanzu Hibairu shine SARKIN
SADAUKAI na duniya domin babu jarumi mai karfin damtse kamar sa,
Hibairu bai taɓa ganin bil'adama a rayuwarsa ba domin ya na rayuwa ne a cikin dabbobi da
aljanu, don haka ya taso da wani yare da wanda ya iya yinsa a duniya face yaro Humair
makaho,
A halin yanzu makahon Yaron yana ajiye a hannun saurayi Hizmal yana kula da
https://youtu.be/bq_-9I3FtnA sa tun bayan mutuwar mahaifan sa,
Lokacin da mahaifina yazo nan a zancen sa sai yace ya yata na umarci da kika kara matsowa
kusa da ni
Koda jin hakan sai na daɗa matsa kusa dashi
Kawai sai abbana ya buɗe bakin sa take wani dunkulallan farin haske ya fito daga bakin sa da
girman sa bai huce na kwan jimina ba
Take hasken ya dunga shiga jikina lokacin da hasken ya kammala shiga,
Take naji wani irin gagarumin karfi ya shige ni naji tamkar zan iya yaƙar duniya baki ɗaya,
Mahaifina yayi guntun murmushin ƙarfin hali sannan yace ya yata Kiyi sani cewa ahalin yanzu
kina ɗauke da sirrikan tsafina guda miliyan biyu,
Haƙiƙa babu wani al'mari da za ki sanya a gaba face kin samu nasara,
Saboda haka sai ki jira nan da kwanaki domin kiji bayanin da waziri zai bayyana.
Sa'adda mahaifina yazo nan azancen sa sai hawaye suka shatato daga idanuwan sa
Al'amarin daya sanya na rungume mahaifina kenan na fashe da kuka saboda da mutukar
tausayi,
Sa'adda jaruma Husnaila bintu ishwar tazo dai dai nan a labarin ta sai hawaye suka zubo daga
idanuwan ta,
Al'amarin da ya sanya saurayi Hizmal yaji ya kamu da matukar tausayin ta kenan har kwalla ta
zubo masa,
Shi kansa yaro Humair daya kasance makaho baya gani sai da yaji ya kamu da tausayin
Husnaila,
Tsawon daƙiƙa hamsin Husnaila tana cikin wannan hali sai daga bisani ne ta sanya hannayen ta
biyu ta share hawayen ta sannan ta cigaba dacewa
Kamar yadda mahaifina ya faɗa haka al'amarin yakasance ranar da kwana uku suka cika waziri
yayi umarni akayi shela a cikin birni da kauye akan cewa sarki zai tura ya'yan sa izuwa nemo
maganin lalurar sa duk wanda ya samu nasarar nemo maganin da ya warkar da shi da jinyar sa
Shine zai gaji karagar mulki, yayin da jama'a suka ji wannan shela sai sukayi cincirindo a fadar
babu masaka tsinke kowa ya hallara,
Mu kaɗai ake jira, ana cikin wannan hali ne kwatsam sai yan uwa na su yarima ubaiyu suka
shigo fadar shirye shirye cikin matsananciyar shigar yaƙi mai matukar kwarjini da ban tsoro,
Yayin da jama'a suka yi arba da su sai suka miƙe tsaye domin girmama wa a gare su,
Har sai da suka je suka zauna a wajen da aka tanadar mu su sannan fadar tayi tsit
Bayan shuɗewar Kamar daƙiƙa hamsin ne sai na shigo fadar tare da dakarun rakiya masu
tsaron lafiya
Sa'adda jama'a suka yi arba dani nan take fadar ta rude da shewa da tafi inda wasu ke cewa ni
ce zan gaji karagar mulki, wasu nace ni ce zan zamo shugabar su,.
https://youtu.be/bq_-9I3FtnA
Al'amarin da ya harzuƙa zukatan yan uwana kenan suka kama tafarfasa tamkar zasu kone,
Duk wanda ya kalla ne daga cikin su sai naga ya kada mini uwar harara
Sai da kowa ya zauna abisa kujerar da aka tanadar ma sa Sannan waziri ya miƙe tsaye ya ɗaga
hannun sa fadar tayi shiru tamkar Mutuwa ta gifta,
Sannan ya fuskanci jama'a yayi gyaran murya yace
"Da farko mu na yiwa jama'a Barka da zuwa wannan fada mai albarka barka da zuwa,
Bayan haka koda cewar mutane sun san abinda ya tara mu anan,
Amma akwai bukatar nayi ƙarin haske akai,
Sanin kanku ne cewa mai girma sarki ishwar ya kwanta jinyar rashin lafiya tsawon lokaci
Bisa wannan dalili ne yasan ya sarki yayi umarni da a tura su yarima ubaiyu su shiga izuwa
duniya domin su nemo maganin da zai warkar da cutar mai martaba,
Dukkan wanda ya samu nasarar nemo maganin da ya warkar da cutar mai martaba to fa shine
zai gaji karagar mulkin wannan birni mai albarka,
Saboda haka yanzu za muyi wa su yarima rakiya har izuwa kofar gari tun da dama tuni an
tanadar musu dawakai da abin guzuri,
Koda waziri ya zo daidai nan azancen sa sai muka miƙe tsaye daga wajen zaman mu muka nufi
kofar fita daga fada, waziri,yan majalissa da sauran jama'ar gari suka mara mana baya,
Yayin da aka fita sai muka kama dawakan mu muka sakar musu linzami,
Sai da aka yi mana rakiya har izuwa kofar gari sannan kowanne mu ya debi dakarun rakiyar sa
guda Ɗari biyu da ɗoriya ya nausa cikin daji,
Ma'ana yarima ubaiyu ya nausa izuwa bangaren yamma, Hushriba gudu,yarima zafiyar arewa,
ni kuma nayi gabas,
Kowa ya rabu da ɗan uwan sa, sai na shafe tsawon Sa'a uku i na gudu tare da dakaru na
sannan na yada zango,
Bisa mamaki sai naga dakaru na na rakiya sun zare makaman yaƙi sun afka mini domin su
hallaka ni dakyar da siɗin gishi na tsira da raina bayan na samu manyan raunuka.
Wannan shi ne taƙaitaccen labari na da kuma abinda ya sanya na fito farautar yaro Humair
kuma na taimaka maka wajen ceton rayuwar sa domin ya taimaka mini na sadu da Humairu
SARKIN SADAUKAI.
Sa'adda jaruma Husnaila tazo dai dai nan a labarin ta sai saurayi Hizmal ya kamu da matukar
tausayin ta ya dube ta a nutse yace"yake Husnaila haƙiƙa labarin ki cike yake da ban tausayi,
Ina mai tabbatar miki dacewa matsawar ina numfashi zan taimaka miki wajen cika burin
mahaifin ki,
Sa'adda Husnaila taji wannan batu daga bakin Hizmal sai ta cika da matukar farin ciki maral
misaltuwa,
Daga wannan ne kuma sai fira ta ɓarke a tsakanin su,
Wannan shi ne abinda ya faru ga baƙon jarumi wato jaruma Husnaila,da saurayi Hizmal a cikin
gidan tsira bayan sun samu nasarar tseratar da Yaro Humair makaho daga sharrin sarki
shazwan wanda yake son ya hallakashi domin ya bayar da jinin sa ga abin Bautar su don
tseratar da jama'ar birnin sa daga saharrin GOBARAR DAJI. *****. *****. *****
Duk wanda ka gani a birnin tsakanin maza, mata, yara da manya kowa gudu yake domin ya
tsira da rayuwar sa,
Kaico! Haƙiƙa tashin hankali ba'a sama sa rana kuma ita GUGUWAR ANNOBA idan ta taso
babu mai ɗauke ta face Ubangiji,
Babu abinda zai karya zuciyar mutum kuma ya sanya shi zubar da hawaye
Face idan yaga yadda wata irin guguwar Wuta ke kama jikin yara ƙanana da mata suna ci da
wuta suna ihu da kururuwar neman taimako amma babu mai ceto,
Wani abin takaici shine hatta kwalbati da hanyoyin ruwa wuta ke ciki babu wani waje da mutum
zai sami fakewa,
Kafin shuɗewar rabin sa'a gaba ɗaya birnin ya cika da gawarwakin yara da tsofaffi,
Gidaje duk sun rushe sun ƙone kurmus,ihu da koke-koken ƙananan yara da mata ya cika dodon
kunne, mutane suka dunga guje-guje gami da ifice-ifice,
Komai rashin imanin mutum idan yaga wannan ƙazamar musiba dole ne ya zubar da hawayen
tausayi.
Ana cikin wannan musiba ne su Sarkin bokaye suka bayyana a dai dai kofar fada,
Sa'adda suka ga yadda wannan GOBARAR DAJI ke hallaka jama'ar birnin su sai suka cika da
matukar tausayi da baƙin ciki,
Waziri Rufyan ya dubi Sarkin bokaye Dargas cikin tashin hankali yace
"Ya shugaban bokaye Yakamata kayi wani abu game da wannan musiba,
Domin fa idan musibar nan tayi tsamari karshe zamu iya rasa dukkan iyalan mu Bama jama'a
birnin mu kaɗai,
Koda jin wannan batu daga bakin waziri Rufyan dai sarkin bokaye ya dake murtuke fuska ya
dubi waziri Cikin alamun karayar zuci yace
Ya shugaba na shin ka manta ne cewa yau tsawon shekaru wannan musiba tana bayyana
amma duk lokacin da zata taso ilimin tsafi baya taɓa tasiri akan ta,
Duk lokacin da nayi yunkurin aiwatar da wani al'amari akan hakan zan iya rasa dukkan sirrikan
tsafi na, koda boka Dargas yazo dai dai a zancen sa sai idanun sa suka kaɗa kuma kwallar
takaici ta zubo masa,
Ana cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai a kaga wani mahayi ya bayyana
bisa kan ingarman doki sanye cikin gagarumar shigar yaƙi ya tunkaro inda su Sarkin bokaye
suke tsaye yana mai ratsawa ta cikin gagarumar wutar dake ci
Amma bisa mamaki shi dokin da yake kai wutar bata kama jikin su ba.
Al'amarin da yayi matukar ɗaurewa su Sarkin bokaye kai kenan kuma ya basu mamaki,
Kawai suka saki baki suka kura mahayin idanu,
Lokacin da yazamana tazarar dake tsakanin su bata huce taku hamsin ba,
A sannan ne su Sarkin bokaye suka fahimci cewa mahayin ya mace ce kyakkywa ta gaban
kwatance,
Lokacin da yazamana tazarar dake tsakanin bata huce taku goma sai budurwar ta ja linzamin
dokin ta ta tsaya cak,
Kawai sai buɗe bakin ta ta karanto waɗansu dalasimai
Tana mai nuna sararin samaniya da hannayen ta biyu
Tana gama rufe bakin ta sai wata walkiya da tsawa suka bayyana a sararin samaniya haɗe da
ci da
Sannan ruwan sama ya kece tamakar da bakin kwarya,
Amma wani abun mamaki ruwan bai jiƙa budurwar ba,
Cikin Abinda bai gaza daƙiƙa hamsin ba gaba ɗaya GOBARAR DAJI dake birnin ta mutu
ƙurmus,
A sannan ne jama'a suka fara dawowa cikin hayyacin sa kowa ya shiga duba irin muguwar
asarar da yayi,
A lokaci guda ruwan saman ɗauke ɗif tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Cikin alamun tsananin farin ciki maral misaltuwa Sarkin bokaye, waziri Rufyan Sarkin yaƙi suka
taka da kafafun su izuwa inda budurwar take tsaye,
Lokacin da suka isa daf da ita sai suka ƙara cika da mamaki ainun
Ita dai budurwar takasance kyakkyawa tagaban kwatance, tana da kyan diri da sura tamkar ita
ce ta ƙera kanta yadda take buƙata, fatar jikin ta wankar tarwaɗa ce ma'ana ba baƙa ba ce ba
fara ba,
A gadon bayan ta tana rataye da wata zabgegiyar takobi mai tsawo da kaifin tsiya, shekarun
budurwar ba zasu haura ashirin ba
Lokacin da aka isa sai boka Dargas ya buɗi baki cikin tattausar murya fuskar sa cike da annuri
ya dubi kyakkyawar budurwar yace
"Yake wannan jaruma ma'abociyar abubuwan ban al'ajabi mun zo ne gareki domin muyi miki
godiya bisa wannan gagarumin taimako da kika yi mana na ceton miliyoyin jama'ar birnin mu
daga musibar GOBARAR DAJI,
Sannan idan babu damuwa muna san ki sanar damu wace ce ke a cikin jerin bokayen duniya,?
Shin akwai wani abu da kike da bukata daga garemu har ya shigo dake cikin wannan ƙasa ta
mu mai albarka?
Koda jin waɗannan tambayoyi daga bakin Sarkin bokaye Dargas sai kyakkyawar