SARKIN SADAUKAI Littafin Yaki Complete By Mansur Usman Sufi .pdf

Author :  Mansur Usman Sufi Category :  Taskar Novels

Chapter   4 / 8

9K to 12K   out of 23.6K words

na hagu yana ɗauke ne da kuturta kowane
dare Abidatul-auliya bata iya barci saboda raɗaɗin da kuturtar ke yi mata
Ta samu wannan lalura ne tun tana da shekaru goma sha biyu a duniya wata rana ta shiga
izuwa dajin dake makwabtaka da birnin Tehran domin yin farauta,
Abidatul-auliya na tafe bisa kan ingarman doki ja sanye cikin gagarumar shigar yaƙi mai
matukar kwarjini daban tsoro,a gadon bayan ta tana rataye da waɗansu zaratan takubba masu
kaifi da tsinin tsiya,. Ta wanzu tana tsala Azababban gudu a cikin dajin ma'abocin dogayen
bishiyoyi duwatsu,da koramu, Sai da ta shafe tsawon Sa'a ɗaya tana tsala Azababban gudu batare da haɗu da wani abu mai
cutarwa ba, hatta kukan yan kananan tsuntsaye bata ji, al'marin da yayi matukar ɗaure mata kai
kenan kuma ya bata mamaki
Domin tunda take fita farauta hakan bai taɓa faruwa ba,
Tana cikin wannan hali ne sai wani tunani ya faɗo mata tunanin kuwa shine anya kuwa bawai
gudun da take yi bane abisa dakin ta shine ya sanya namun dajin suka gudu,
Koda tazo nan a tunanin ta sai kawai ta cigaba da sassarfa ,
Abu kamar wasa sa gashi ta shafe wata sa'a ɗaya batare da taji motsin komai ba,
A dai dai lokacin yaki bawali don haka sai taja linzamin domin ta ta tsaya cak!
Sannan ta kama ta sakko kawi sai ta durfafi wata ƙorama mai ɗauke da ruwa garai-garai gwanin
ban sha'awa don haka sai ya tsugunna a gefen tayi bawalin,. Sannan ta sanya hannun ta da
nufin ta ɗebo ruwan ƙoramar amma sai ta lura cewa fitsarin da tayi ya shiga cikin ƙoramar ya
canza launin ruwan, Sannu a hankali sai kalar ruwan ƙoramar ya canza launi izuwa ja,

Kwatsam bazato babu tsammani sai Abidatul-auliya ta ji an dakamata tsawa mai ban tsoro
Saboda matukar razana bata san sa'adda ta kife a ƙasa ba tana baƙi gami numfarfashi, kuma
hantar cikin ta kaɗa tsoro Yakamata ainun,
Daga bisani sai taga wani mutum tsoho tukuf ya bayyana a tsakiyar ƙaramar tamkar yana tsaye
ne akan turba,
Mutumin yakasance dogo tamkar bishiyar turare, gashin kansa da gemun sa farare ne solko
ɗigon baƙi babu, idanuwan sa jajayene tamkar garwashin wuta, hancin a taɓe yake tamkar ba
dashi yake shaƙar numfashi ba, yana da tafkeken baki tamkar kofar gari, yana da faffaɗan kirji
tamkar faranti, A kwiɓin hannayen sa biyu yana maƙale da waɗansu fuka-fukai guda biyu daga kasan gadon
bayan sa yana sanye da wata irin murtukekiyar jela irin ta kifi,
Sanye a ƙugun sa yana sanye da bante na fatar damisa mai ɗauke da guraye da layu na tsafi, a
tsakiyar kansa yana ɗauke da manyan ƙaho guda biyu irin na ɓauna,
Tabbas wannan mutum ya cika abin tsoro domin babu wani mutum da zai yi arba dashi face ya
ɗimauce,
Sa'adda Abidatul-auliya tayi arba da mutum sai jikin ta yakama kyar ma tamkar mazari har tana
sakin fitsari a wando saboda tsananin tsoro da razani,
Yayin da mutumin yaga halin da Abidatul-auliya ta shiga sai ya takarkare ya bushe da dariya
mugunta,mai kama da kukan baƙi sai daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da
Sakon mutuwa sannan ya buɗi baki cikin kakkausar murya yace "yake wannan bil'adama kiyi
sani cewa kin aikata mini laifi wanda ahalin yanzu babu wani mahaluki da ya taɓa yi mini shi
kisani cewa wannan ƙorama da kika yi mini fitsari a ciki ba ruwa bane face JININ SARAKAI na
baƙaƙen aljanun duniya na shafe tsawon shekaru dubu arba'in ina sihirce wannan jini domin in
samu nasarar mallakar gaba ɗaya sarakunan ma'ana na zamo SARKIN SARAKAI na aljanu,
A yau ne zan kammala wannan aiki nawa sai gashin kin wargatsa mini wannan buri na wa a
cikin Abin da bai gaza daƙiƙa goma ba wanda na shafe tsawon shekaru dubu arba'in,
Lokacin da mutumin yazo nan azancen sa sai hawayen baƙin ciki suka zubo masa,
Sannan daga bisani ya cigaba da cewa "Na rantse da rayuwar mahaifina sai na yanke mini
hukuncin da har abada bazaki taɓa mantawa da ni ba
Koda gama faɗin hakan sai mutum ya a nuna Abidatul-auliya da ɗan yatsan sa na hagu take
wani irin koren haske yayi fitar burgu daga gare sa ya shiga jikin Abidatul-auliya
Nan take taji wani irin tsananin zafi a tsagin jikin ta na hagu tamkar ana ƙonata da wuta,
Nan fa ta fara ihu da kururuwar neman taimako
Sannan daga bisani mutumin ya ɗauke hannun sa na dubi Abidatul-auliya yace "yake wannan
bil'adama kiyi sani cewa har abada baza'a taɓa samun magani lalurar ki ba domin nemo
maganin dai dai yake da barkewar YAKIN DUNIYA na uku,
Koda mutumin yazo nan a zancen sa take ya bace bat tamkar bai taɓa wanzu wa ba.
Adai-dai wannan lokaci ne Abidatul-auliya tajiyo karar takun sawayen dawakai da haniniyar su,
Ai kuwa koda ta duba sai tayi arba da dakarun masarauta su kimanin dubu biyu sun durfofi inda
take, da zuwa su ka ɗauke ta batare da ɓata lokaci ba, suka juya suka nufi hanyar da zata kai
su birnin Tehran,
Tun daga wannan rana tsagin jikin Abidatul-auliya ya kamu da ciwon kuturta,
Kuma sai dare yake yi mata raɗaɗi, sarki ya nemi bokaye da matsafa a sirrance akan su gano

masa maganin cutar dake damun gimbiya amma abu yaci tura , domin duk bokan da yajewa da
maganar sai yace masa shima bai san maganin lalurar ba,
Har sarki ya mutu aka ɗora Abidatul-auliya akan karagar mulki amma ba'a gano maganin cutar
ba,
Kuma yazamana cewa gaba ɗaya birnin Tehran babu wanda yasan cewa Abidatul-auliya na
ɗauke da wannan cuta ta kuturta, hatta dakarun da suka ɗauko ta daga cikin wannan daji a
lokacin da al'amarin yafaru,
Tun daga ranar da wannan abu yafaru bata ƙara bari wani mahaluki yaga jikin ta koda kuwa
hannayen ta da kafafunta face fuskar ta kaɗai, ko wanka da kwalliya zata yi da kanta take yi
bata bari kuyangi su yi mata,
Wata rana Abidatul-auliya na zaune acikin Turakar ta bisa ƙasaitacciyar kujera ta tafka uban
tagumi, a wannan lokaci dare ya tsala kuma yayi duhu dunɗum babu abinda kunne keji face
haushin karnuka da kukan gyare tsilli-tsilli.
Abidatul-auliya na cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai wani kyakkyawan
tsuntsu ya bayyana agare ta a cikin iska yana mai ƙura mata idanu,

Koda tayi arba da tsuntsun take ta dawo cikin hayyacin ta daga duniyar tunanin da ta shiga
zuciyar ta cike da matukar mamaki da al'ajabi
Bisa mamaki sai Abidatul-auliya taji tsuntsun ya bushe da dariya tamkar yakasance bil'adama
sannan daga bisani ya fara magana cikin murya mai ɗan karan daɗi tamkar ana busa sarewa
Yana mai cewa"Barka da warhaka ya sarauniyar kyawawan duniya Abidatul-auliya bintu
shafwaz,
Ya ke wannan sarauniya mai daraja nasan cewa a halin yanzu zuciyar ki cike take da matukar
mamakin yadda akayi nake magana alhalin nakasance tsuntsun ba bil'adama ba,
Tabbas ni bil'adama ne kamar ki sai dai na boye miki siffa ta ne saboda waɗansu muhimman
dalilai,
Ya ke wannan sarauniya kiyi sani cewa bakomai ne yakawo ni gareki ba sai domin na taimaka
miki wajen samun maganin lalurar da ta addabeki atsagin jikin ki na hagu tsawon shekaru masu
yawa,
Koda jin wannan batu sai Abidatul-auliya ta dubi tsuntsun cike da mamaki tace"Kace mini kai
bil'adama ne to shin wane ne kai? Kuma mene ne ribarka idan ka taimake ni na samu maganin
lalura ta?
Koda jin waɗannan tambayoyi sai tsuntsun yayi ajiyar zuciya sannan yayi gyaran murya
yace"Haba ranki ya daɗe me kike ci ne na baka na zuba ai cikin bayanin dazan yi miki za kiji
duka amsar tambayoyin ki amma tun da kina buƙatar su bari na fara sanar dake.
Da farko ni suna na shubairu ibn mauzur mahaifina mashahurin boka ne da yayi shura a yankin
nahiyar larabawa,
Duk cikin ya'yan mahaifin mu ni ne kaɗai na gaje shi tun banfi shekara goma sha biyar ba da
rasuwar sa,
Game da amsar tambayar ki ta biyu kuwa zakiji amsar acikin bayanin da zan yi miki,
Binciken da na gudanar bisa halarar tsafi na ya tabbatar mini dacewa tun mahaifin ki yana raye
ya ziyarci bokaye da dama domin samo maganin lalurar ki amma abu ya ci tura,
Yake wannan sarauniya mai daraja kiyi sani cewa har abada bazaki taɓa warkewa daga

wannan lalura taki ba face kin sha wani tsumin tsafi dake ajiye a cikin wata salka a fadar Sarkin
bokayen duniya,
Bincike ya kara tabbatar mini da cewa babu wani mahaluki da ya isa yaje fadar Sarkin bokaye
ya ɗauko tsumin tsafi face wani hatsabibi kuma taƙadirin jarumi da ake yiwa laƙabi da SARKIN
SADAUKAI,
Hibairu wani irin mutum ne da yake rayuwa ta daban domin ya taso ne a cikin dabbobi da aljanu
tun yana jariri, bai taɓa ganin wani bil'adama ba ballantana ya iya Yaren su,
An kira sa ne da SARKIN SADAUKAI saboda tsanin jarumtakar sa ya huce hankali,
Bazai taɓa fitowa daga dajin Baitul-shamshan ba face ya kammala karanta waɗansu dalasiman
tsafi dake jikin wani ZOBEN SHIRI dake hannun sa wanda adadin sirrikan tsafin shine adadin
dabbobin dake cikin dajin,
Game da amsar tambayar ki ta uku kuwa akan mene ne riba ta idan na taimaka miki wajen
samun maganin lalurar ki shine
Sai domin na gano cewa kece kaɗai wacce zata taimaka mini wajen biyan tawa Bukatar,
Kamar yadda kike ɗauke da lalurar tsagin jiki
Ni ma ina da irin ta sak amma a tsagin dama kuma na samu tawa lalurar ne alokacin da nake
fafata artabu da yan uwana a ƙoƙarin su na rabani da muhimman sirrikan tsafin mahaifin mu,
Bisa wannan dalili ne yasan ya nake so mu haɗa karfi da karfe domin mu sadu da sadauki
Hibairu a lokacin da zai fito daga dajin Baitul-shamshan domin mu bayyana masa buƙatar mu ta
zuwan sa fadar Sarkin bokaye,
Koda tsuntsun ya zo nan azancen sa sai kawai ya rikiɗa izuwa wani zabgegen kyakkyawan
saurayi ba ya sanye da riga ko wando face bantai na fatar damisa da ya rufe al'aurar sa zuwa
kwaurin sa,
Sa'adda sarauniya Abidatul-auliya tayi arba da saurayin nan take taji zuciyar ta buga da karfi
kuma tsikar jikin ta ta tashi,
Bakomai ne yasanya sarauniya Abidatul-auliya taji zuciyar ta ta buga da karfi ba sai domin
tunda take a rayuwar ta bata taɓa ganin wani ɗa namiji mai kwarjini da kyan diri tamkar saurayin
ba,
Abinda yasanya tsikar jikin ta ta tashi kuwa shine Yayin da ta kalli saurayin sai taga barin jikin sa
na dama na zubar da wani ruwan mugunya na kuturta,
Daga can sai saurayin ya sake rikiɗa izuwa wannan kyakkyawan tsuntsu ya buɗe baki a karo na
uku yace "Na barki lafiya ya sarauniyar kyawawa sai mun sake saduwa a ranar da jarumi
Hibairu SARKIN SADAUKAI zai kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRI a
dajin Baitul-shamshan, Koda gama faɗin hakan sai ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Nan take sarauniya Abidatul-auliya ta cika da matukar farin ciki maral misaltuwa yazamana
cewa a kullum idan dare ya tsala sai ta zauna a wannan baraba ta Turakar ta koda wannan
tsuntsun zai sake bayyana gareta wato shubairu ɗan boka mauzur
Wannan shi ne abinda ya faru da sarauniya Abidatul-auliya ya birnin Tehran dake yammacin
duniya.

3




Kwatsam bazato babu tsammani sai saurayi Hizmal da mahayin suka ji ƙarar alamun zare
sakatun wannan ƙofa daga ciki,
Daga bisani sai ƙofar ta bude sai ga wani irin haske da kamshi mai nan sha'awa ya ratso daga
ciki
Cikin matukar farin ciki maral misaltuwa mahayin ya kunna kai izuwa ciki saurayi Hizmal yayi
koyi dashi goye da yaro Humair a gadon bayan sa,
Su na kammala shiga sai ƙofar ta mayar da kanta ta rufe ruf!.
Adai dai wannan lokaci ne sarki shazwan waziri Rufyan Sarkin bokaye da sauran tawagar su
suka bayyana a wajen bayan buɗewar ƙofa ta huɗu,
Sa'adda suka bayyana sai sarkin bokaye ya dubi sarki shazwan cikin matukar takaici yace"ya
shugaba na haƙiƙa munyi babban rashi da har mu kayi kuskure su saurayi Hizmal suka ƙetare
kofa ta biyar suka shiga izuwa gidan tsira
Bisa tsarin wannan gida babu wanda ke da ikon shiga cikin gidan tsira matukar akwai wanda ya
ƙetare kofa ta biyar har sai nan da kwanaki uku,
Koda jin wannan batu daga bakin Sarkin bokaye Dargas sai kowa ya cika da matukar takaici,
shi kuwa Sarki shazwan saboda matukar takaici bai san sa'adda ya takarkare ya kurma wawan
ihu ba wanda ya firgita duk wata halitta dake wajen har da boka Dargas,
Sai Daga bisani ne ya turɓune fuska tamkar an aiko masa da wasikar mutuwa ya dubi Sarkin
bokaye a lokacin da idanuwan sa suka kaɗa su kayi jawur tamkar garwashin wuta cikin
kakkausar murya yace"ya Sarkin bokaye ina so kayi ma za ka gudanar da bincike gano mini
shin mene ne abin da ke faruwa a birni na, Koda jin wannan umarni daga bakin sarki shazwan sai idanun Sarkin bokaye suka zazzaro su
dube sa cikin ladabi yace"ya shugaba na shin ka manta ne cewa abisa ƙa'ida da dokar wannan
gida sihiri baya tasiri,

Idan kuwa har ka naso na gudanar da binciken dole sai dai mu koma da baya,
Sai dai ina da wata shawara,shawarar kuwa ita ce mu kasu guda biyu kaso na farko su jira
anan har zuwa nan da kwanaki uku domin su samu damar shiga izuwa kofa ta biyar su cimma
su saurayi Hizmal,
Ni kuma da wasu zamu koma izuwa birnin mu domin mu kai ɗauki jikina ya bani cewa tabbas
bayan tafiyar mu wani mummunan al'amari ya faru sai dai bazan iya sanin ko mene ne ba tunda
bani da halin gudanar da bincike,
Yayin da sarki shazwan yaji wannan shawara daga Sarkin bokaye sai yayi shiru yana nazari
Daga bisani kuma ya dubesa yace"Ka kawo shawara mai kyau saboda ka tafi kai da sauran
Yan uwan ka bokaye mutum biyar,tare da waziri Rufyan
Ni kuma da Sarkin yaƙi zamu zauna nan mu jira cikar kwanaki uku domin mu cimma su saurayi
Hizmal.
Koda jin wannan umarni daga bakin sarki shazwan sai sarkin bokaye ya juya da baya ya shige
izuwa cikin wannan kofa ta huɗu da suka fito waziri tare da bokaye biyar suka mara masa baya,
Suka bar su sarki shazwan a tsaitsaye cirko cirko fuskokin su cike da matukar damuwa,
Wannan shi ne abinda ya faru da su sarki shazwan da su saurayi Hizmal a cikin gidan tsira,
****. *****. *****
Daji ne ma'abocin kwarjini,da ban tsoro, ya tara bishiyoyi, duwatsu,koramu haɗe da
kwazazzabai,gami da manyan tsaunuka,
Komai rashin tsoron Mutum idan ya yaga yadda dajin yakasance dole ya razana,
Domin da gani dole ne a samu miyagun dabbobi ko aljanu a cikin sa,
Tsananin shirun da ya wanzu a wajen ya ishi ya firgita Mutum
Sai dai abinda zai bawa mai kallo mamaki shine duk yadda dajin ya tara wadannan abubuwan
ban tsoro amma sai gashi wani bil'adama ya wanzu a cikin sa amma babu alamun tsoro ko
razani a tare dashi
Kyakkyawan saurayi ne ɗan kimanin shekaru sha biyar yana sanye da bante iya gwiwar sa,
babu riga a jikin sa, https://youtu.be/tsdKzDyEuVk
Hakan ne abinda ya bayyana surar jikin sa ta jarumtaka , jikin sa a murɗe yake tamkar na
ƙarfe,yana da faffaɗan kirji tamkar duwatsu aka cuccusa masa a ciki,gashin kansa baƙi ne siɗik
mai kyalli ya zuba akan fuskar sa da kirjin sa,
Kafar sa ko takalmi babu, a hannun sa yana riƙe da wani dogon mashi mai baki tamkar zarto
mai kaifi tamkar takobi,
Kallo ɗaya za ka yiwa saurayin ka fahimci cewa yana da karfi na Allah ya isa,
Tafiya yake a dajin cikin ƙasaita yana mai ratsa duwatsu koramu da sarƙaƙiyar duhuwar
bishiyoyi tamkar yana cikin turakar sa,
Yana cikin wannan tafiya ne ya jiyo alamun motsi a bayan,. Koda ya waiga bayan sa sai yayi
arba da wata zakanya da mijin ta suna tsere cikin nishaɗi,
Idan namijin ya ba wa macen tazara sai macen ta zage damtse ta tsere masa, ta mai yimasa
gurnani dake nuna cewa ta samu nasara ,
Sa'adda saurayin yaga abinda zakanyar da mijin ta ke yi sai ya kalle su yayi murmushi har suka
zo suka gifta ta gaban sa suna matsanancin gudu suka yi nisa sosai har yazama dakyar yake
iya hangosu.
Sai kawai shima ya takarkare ya falfala da azababban gudun mai ban al'ajabi daban mamaki,

Domin ƙorama, duwatsu da bishiyoyi basa tsaida sa,
Duk faɗin ƙarama tsallake ta yake yi.
A wasu lokutan sai kaga ya daga tsalle sama yana yana mai rike rassan bishiyoyi tamkar wani
ɗan biri,
A wasu lokutan ma idan yaga bishiya zatayi masa waigi sai kaga ya sanya hannun sa ɗaya ya
naushe ta ta faɗi ƙasa ya bi ta kanta ya huce,
Cikin Abinda bai gaza daƙiƙa goma sha biyar ba sai gashi ya dira a can gaba ɗaya inda
zakunan suke,
Ya yin da su kayi arbda da saurayin sai suka ja suka suka tsaya cak,
A kayi kallon kallo sai bisani sai zakanyar da mijin ta suka dako sufa izuwa kan saurayin yayin
da suka hada kirji da juna sai su duka biyun suka faɗi ƙasa tim,.
Amma saurayin ko da ƙafarsa bata motsa ba ballantana yayi gezau,
Sai da akayi haka har sau goma, koda zakunan suka ga cewa sun kasa samun nasara sai
kawai suka risina da kawunan su ƙasa suka durƙusa alamun dake nuna cewa sunyi MUBAYA'A
ga saurayin,
Ba wani bane wannan saurayi ba face jarumi Hibairu wato SARKIN SADAUKAI.
Yayin da Hibairu yaga zakunan sun risina agareshi sai kawai ya juya ya cigaba da tafiya a dajin
hannun sa riƙe da wannan mashi mai baki biyu,
Wannan shi ne abinda ya faru da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI

4 / 8