Author : Mansur Usman Sufi Category : Taskar Novels
budurwar ta
bushe da yar karamar dariya
Sannan daga bisani ta tsuke baki tayi gyaran murya cikin tattausar lafazi mai daɗin sauraro
tace
"Yaƙi waɗannan SARAKAI kuyi sani cewa ceton rayuwar al'ummar ku a waje na tamkar
taimakon kai na ne,
Nasan za kuyi mamakin jin na faɗi haka, amma zan sanar ɗaku abinda zai shafe mamakin a
cikin amsoshin da zan baku anan gaba,
Da farko dai ni suna Hushriba bintu ishwar mahaifina ƙasurgumin matsafi ne da yayi shura
A halin yanzu na fito ne bisa umarnin mahaifina na ne mo masa maganin cutar da ke damunsa
Bisa binciken da na gudanar bisa halarar tsafi na na gano cewa maganin dana fito nema tabbas
yana da alaƙa da musibar da ta addabe ku ta ANNOBAR GOBARAR DAJI.
Don haka nake so mu haɗa karfi da karfe domin kowanne mu ya amfana
Ina nufin bani ƙishiri na baka manda, domin duka mu samu tsira,
Sa'adda Hushriba tazo dai dai nan azancen ta, sai sarkin bokaye Dargas ya dube ta cikin farin
cikin matukar farin ciki maral misaltuwa yace
"Ya jaruma ma'abociyar abubuwan ban al'ajabi tabbas munyi matuƙar farin ciki da bayyanar ki a
cikin wannan birni,
Akwai bukatar akai ki masauki ki samu hutu kiyi kalaci sannan daga bisani sai mu tattaunawa,
Koda jin wannan batu daga bakin Sarkin bokaye sai Hushriba ta gyaɗa kai alamar gamsuwa,
Gama faɗin hakan keda wuya sai sarkin bokaye yayi wa wani badakare inkiya ta da hannu take
badakare ya zaburi dokin sa ya shige gaba yana mai yiwa jaruma Hushriba nuni da ta biyo
bayan sa,
Batare da wani jinkiri ba Hushriba ta sakarwa dokin ta linzami ta mara masa baya,
A sannanne Sarkin bokaye ya dawo da uban sa ga waziri ya dubesa cikin ladabi yace "ya
shugaba na shin me ka fahimta game da wannan bakuwar jaruma Hushriba?
Koda jin wannan tambaya sai waziri ya nisa Sannan yayi ajiyar zuciya yace"Ya Sarkin bokaye
kayi sani cewa duk da irin taimakon da Hushriba tayi mana baza mu saki jiki da ita ba
Lallai akwai bukatar ka gudanar da bincike bisa halarar tsafin ka domin ka tabbatar AAA, kuma
wajibi ne mai martaba sarkin yasan da wannan al'amari
Dajin wannan batu sai sarkin bokaye yace "Maganar ka haƙƙun yakai waziri zan zartar da duk
abinda ka umarta, 08137237071
Daga wannan batu ne kowa ya kama gaban sa waziri ya huce izuwa cikin gidan sarauta,
Sarkin bokaye da sauran Yan uwan sa bokayen suka durfafi ɗakin sirri domin gudanar da
bincike game da jaruma Hushriba,
****
SARKIN SADAUKAI
Book 2 page 2
Littafin Yaki
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071
BIRNIN TEHRAN
Acan birnin Tehran kuwa, tun sa'adda sarauniya Abidatul-auliya ta gana da boka shubairu
wanda ya bayyana gare ta acikin surar kyakkywan tsuntsu
Sai ta kasance a koda yaushe cikin zaƙuwa take domin ta ga cewa ranar tafiya izuwa dajin
Baitul-shamshan tazo domin saduwa da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI,
Bangare guda kuma zuciyar ta cike take da tsananin begen saurayi shubairu,
A kowa ne dare sai ta zauna a harabar turakar ta tana tana kallon inda saurayi Hibairu ya
bayyana a gare ta tana mai karanta waƙoƙin so da bege,
Kaico ! Haƙiƙa so shine shammatar zuciya, tabbas Abidatul-auliya ta kamu da tsananin kaunar
shubairu wacce baza ta misaltuwa ba,
Kuma wani abin mamaki shine raɗaɗin da ciwon ta ke yi mata sai yazamana ta samu sassauci,
Haƙiƙa SO yana tasiri matuka wajen ba wa jikin ɗan adam wata garkuwa ta musamman.
Wannan shi ne abinda ya faru ga sarauniya Abidatul-auliya dake birnin Tehran
Al'amarin su saurayi Hizmal kuwa sai da suka shafe tsawon kwanaki uku a cikin gidan tsira tare
da yaro Humair makaho,
Tsawon wannan lokaci da suka shafe a cikin gidan duk wani abu da suke buƙata na sha'anin
rayuwa da sun bukace shi sai suga ya bayyana gaban su,
Kuma a iya tsawon wannan lokaci shaƙuwar soyayya ta ƙara kullu wa ainun tsakanin jaruma
Husnaila da saurayi Hizmal
A ranar kwana na ukun ne da la'asar sakaliya su Hizmal suka kammala shiri domin cigaba da
gudun tsira, domin tseratar da rayuwar yaro Humair,
Bayan sun kammala shirin ne
Sai saurayi Hizmal ya giya yaro Humair a gadon bayan sa,
Sannan suka durfafi wata kofa ta musamman a cikin gidan domin su fita,
Lokacin da suka isa bakin kofar sai suka tarar da kofar a garƙame babu alamun wajen da za'a
bude ta,
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin su kenan ainun suka shiga dogon nazari,
Suna cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai suka ga wani aljani ya bayyana
gare su ya faɗi yayi sujjada,
Aljanin yakasance gabjejen kato mai tsawo da kwarjini, yana da fuka fukai guda huɗu, da jela
guda ɗaya, yana da kwalakwalan idanu jajur tamkar garwashin wuta, hancin sa kuwa ashafe
yake tamkar bada shi yake shaƙar numfashi ba, a haɓar sa yana maƙale da dogon gemu fari
sol mai tsawon kamu huɗu Hakika wannan aljani ya cika mai ban tsoro gami da muni
Su kansu su saurayi Hizmal a matsayin su na zaratan Jarumai sai da suka firgita da sukayi arba
da aljanin,
Aljanin ya ɗago da kansa sama ya dubi Hizmal da sunaila ya buɗe tafkeken baƙin sa mai kama
da kofar gari, sannan yace cikin kakkausar murya,
"Da farko dai suna na Marhutul-Azab kuma nine hadimin dake kula da wannan gidan tsira yau
fice da shekaru dubu bakwai,
Ya ku waɗannan bil'adama ma'abota gudun tsira kuyi sani cewa na bayyana gareku ne domin
na fitar daku daga cikin wannan gida na kai mu duk inda kuke bukata a fadin duniya,
Koda jin wannan batu daga bakin aljani Marhutul-Azab sai Hizmal da sunaila suka cika da
mamaki ,
Sunaila tace "Yakai wannan aljani haƙiƙa munyi farin ciki maral misaltuwa bisa wannan taimako
da zaka yi mana,
Amma fa wani hanzari ba gudu ba, ina so kayi sani cewa tafiya damu abu ne mai matukar
wahalar gaske da zai iya jefa rayuwar ka a cikin tsaka tsaka mai wuya,
Ina ganin abinda zai fi kawai shine ka nuna mana hanyar da zamu fita kai kuma ka cigaba da
gadin wannan gida kamar yadda ka saba ,
Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai Aljani Marhutul-Azab ya bushe da yar karamar
dariya mai kama da haniniyar doki sannan yace
"Yaku waɗannan bil'adama kuyi sani cewa fiye da shekaru dubu biyu nasan da labarin bayyanar
ku a cikin wannan gida dama abinda zai kawo ku nan ɗin
Da kuma abinda zaku tafi nema,
Bisa al'adar wannan gida kowa ne mai gadi zai shafe tsawon shekaru dubu huɗu ne cif,
Kuma a yau ne shekarun kammala aiki na suka cika na samu yanci zan iya shiga ko ina a
duniya
Babban muradi na shine na sadu da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI wanda shine kuka fito
ne ma
Tsawon shekaru na shafe ina jiran zuwan ranar da zan sadu daku domin na cika burina na ceto
rayukan al'ummar kabilar mu,
Wanda a halin yanzu ruhikan su ke ajiye a can fadar Sarkin bokayen duniya
DURUSUL-FANNAR
A bisa cikin wata akwatu ta baƙin ƙarfe,
Kowa ce rana Sarkin bokayen duniya sai na tsafe ruhikan kabilar mu da wani sinadaran sihiri,
Da zarar ya kammala sihirin waɗannan ruhikan zasu koma nasa,
Ma'ana kenan zai zamo cewa yana ɗauke da rayuka guda dubu arba'in, Kowa ne ruhi guda
ɗaya zai shafe shekaru dubu huɗu kafin ya mutu,
Baban burin Sarkin bokayen duniya shine ya cigaba da rayuwa da waɗannan ruhikan bazai
mutu ba har abada, zai cigaba da kasancewa SARKIN SARAKAI,
Bisa binciken da na gudanar bisa halarar tsafi na na gano cewa babu wani mahaluki da zai iya
zuwa fadar Sarkin bokaye ya ceto ruhikan kabilar mu face SARKIN SADAUKAI Hibairu,
Sannan babu wani abu dazai iya buɗe wannan akwatin baƙin ƙarfe face ZOBEN SHIRIn dake
hannun jarumi Hibairu kuma zoben ne zai karya sihirin dake jikin ruhikan kabilar ta mu har ya
dawo zuwa gangar jikin su su cigaba da rayuwa kamar kowa,
Sa'adda aljani Marhutul-Azab yazo nan azancen sa sai hawaye suka zubo daga idanuwan sa,
Al'amarin da yayi matukar bawa su saurayi Hizmal tausayin sa kenan,
Hizmal ya dube sa cikin matukar damuwa yace
"'yakai Marhutul-Azab kayi sani cewa haƙiƙa labarin ka akwai ban tausayi duk da ka bamu shi a
takaice,
Ina mai tabbatar maka dacewa ni da abokiyar tafiya ta zamu taimaka ka har mu sadu da jarumi
Hibairu SARKIN SADAUKAI tun da dukkan bukatar mu kusan ɗaya ce
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lulluɓe zuciyar Marhutul-Azab ya buɗi baki karo na uku
yace
Yaku abokanan tafiya ta kuyi sani cewa ina farin cikin sanar da ku cewa
Ina ɗauke da dukkan taswirar fadar Sarkin bokaye,
Wacce babu wani mahaluki dazai shiga wannan fada face yana tare da taswirar,
A halin yanzu nasan cewa kowa ya ɗora idanun sa akan taswirar,
Wacce ko shi kansa Sarkin bokaye basan cewa ina ɗauke da wannan taswira ba ,
Tsawon shekarun da na shafe ina gadin gidan tsira domin na mallaki wannan taswira ne,
Na ji ajikana cewa wannan tafiya tamu cike take da nasara,
Tun da gashi muna tare da taswirar fadar Sarkin bokaye da kuma yaro Humair makaho wanda
shine kaɗai a faɗin duniya ya iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI,
Sa'adda aljani Marhutul-Azab yazo nan azancen sa sai kowa ya cika da matukar farin ciki maral
misaltuwa,
Gama faɗin hakan ke da wuya sai Marhutul-Azab ya shimfide gadon bayan sa Hizmal goye da
yaro Humair da sunaila suka hau suka zauna,
Sannan Marhutul-Azab ya yunkura ya tashi izuwa sararin samaniya ya na mai keta gajimare
cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa
wanzuwa ba,
Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin jaruma Husnaila da saurayi Hizmal a cikin gidan tsira
domin tseratar da rayuwar yaro Humair makaho,
****
Lokacin da boka Dargas da sauran tawagar matsafa biyar suka bayyana a ɗakin sirri domin
gudanar bincike bisa bayyanar bakuwar jarumar da ta ceci rayuwar al'ummar kasar daga
GOBARAR DAJI wato gimbiya Hushriba bintu ishwar,
Bayan binciken da bokayen suka yi suka gabatar da jawabin binciken su
Sai sarkin bokaye Dargas ya dube su yayi gyaran murya yace
"Bisa ga dogon nazari da kuma abinda bincike ya tabbatar shine jaruma Hushriba ba tazo
domin ya cutar da mu ba kawai dai taso ne mu haɗa karfi da karfe domin kowanne mu ya kai ga
biyan buƙatar sa,
Amma sai dai ba zamu saki jiki da ita ba domin kunsan cewa ba'a bawa mata yarda a cikin
al'amura
Matukar baku mallake su ba shin ina cewa kun taɓa karanta Littafin KUNDIN MATSUBBATA
Hikayar jarumi Hilairu da Baiwa luzra
Kun ji irin cin amana da yaudarar da tayi masa daga karshe m
Bayan ya siyar da rayuwar sa ya ceto ta da ma mahaifan ta,
Koda jin wannan batu daga bakin Sarkin bokaye Dargas sai sauran maysafan su kayi na.am
Boka Dargas ya ɗora dacewa "wani abun takaici da na gani a cikin halarar tsafi ma shine tuni su
saurayi Hizmal sun samu nasarar fice daga cikin gidan tsira sun bazama izuwa duniya bisa
taimakon wani hatsabibin aljani mai Marhutul-Azab da halin yanzu babu saurayin aljani mai
tashen balaga kamar sa a fagen karfin damtse da jarumtaka, Yanzu batare da bata lokaci ba zan umarci hadimin aljani na domin ya dawo dasu mai girma
sarki Shazwan domin a halin yanzu jiran gawa babu rai suke yi a can gidan tsira,
Sa'adda Sarkin bokaye Dargas yazo nan a jawabin sa shafi wani gurun tsafi a damtsen hannun
sa
Take wani aljani mai kama da tsuntsun batoyi ya Bayyana gare sa, ya kwashi gaisuwa
Boka Dargas ya dubesa ya kai Haulatul- infal kayi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin
ina so ka tafi izuwa gidan tsira ka ɗauko mai martaba sarki Shazwan da tawagar sa acan inda
ka dauko mu a ɗazu ni da jama'a ta,
Koda jin wannan umarni sai Aljani Haulatul-infal ya risina sannan ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa
wanzuwa ba.
Daga wannan jawabi ne kowa ya kama gaban sa ɗakin taron ya watse,
Wannan shi ne abinda ya wakana acan birnin zawatul-ifdal.
Lokacin da aljani Marhutul-Azab ya tsala da matsanancin gudu a sararin samaniya ɗauke da
Jaruma Husnaila,saurayi Hizmal da yaro Humair makaho,
Sai ya wanzu yana mai keta gajimare tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya,
Nan fa Saurayi Hizmal ya kama kalle-kalle yana mamakin yadda sararin samaniya yakasance
domin wannan ne karon sa na farko a rayuwarsa da ya taɓa tashi sararin samaniya bisa kan
aljani,
Tsawon daƙiƙa hamsin ana wannan tafiya babu wanda yace ƙala,
Sai daga bisani ne jaruma Husnaila ta katse shirun da ya wanzu ta hanyar buɗar baki tayi
gyaran murya sannan dubi saurayi Hizmal tace"Yakai Hizmal shin kana ganin cewa yanzu kai
tsaye zamu huce ne izuwa hanyar da zata sada mu da dajin Baitul-shamshan?,
ko kuwa zamu jira ne har izuwa lokacin da SARKIN SADAUKAI zai kammala karanta ɗalasiman
tsafin dake jikin ZOBEN SHIRI?
Koda jin waɗannan tambayoyi Daga bakin Husnaila sai Hizmal yayi gyaran murya yace
"Ya sunaila haƙiƙa kin kawo maganganu masu muhimmanci daya kamata muyi dogon nazari
akan su,
Amma dai bisa shawara ta ina ganin zai fi kyau ace mun tunkari dajin Baitul-shamshan domin a
halin yanzu,
Dalili na na faɗin hakan kuwa shi ne a Kowa ne hali bokaye,sarakai cikin farautar yaro Humair
suke
Idan muka ce zamu tsaya sai ranar da jarumi Hibairu zai kammala karanta ɗalasiman tsafin
dake jikin ZOBEN SHIRI zai kasance waɗansu sun riga mu isa dajin Baitul-shamshan,
Haƙiƙa dai masu iya magana na cewa a bari ya huce shine ke kawo rabon Wani,
Koda jin amsar tambayoyin da ga bakin Hizmal sai sunaila tayi shiru tamkar tana nazari
Daga bisani ta dubi aljani Marhutul-Azab tace"yakai Marhutul-Azab mene ne ra'ayinka akan
wannan magana,
Marhutul-Azab yace cikin kakkausar murya"Tabbas maganar da Hizmal ya faɗa shawara ce mai
kyau,
Domin abinda baku sani ba shine,
Daga nan izuwa dajin Baitul-shamshan tafiya ce ta tsawon shekaru ɗaya bisa saurayin aljani
mai tashen balaga,
Amma ni zan iya gajarce mana tafiyar cikin kwanaki sittin da huɗu,
Domin ahalin yanzu a kaf jinsin aljanu babu aljani mai tashen balaga da karfin gudu tamka ta,
A yau saura kwanaki sittin da huɗu cif jarumi Hibairu ya kammala karanta ɗalasiman tsafin dake
jikin ZOBEN SHIRI.
Kun ga kenan ranar da zamu isa dajin ranar ne SARKIN SADAUKAI zai bayyana a sararin
duniya,
Bani da tabbacin akwai wanda zai riga mu isa dajin Baitul-shamshan ɗin,
Koda jin wannan wajabi daga bakin aljani Marhutul-Azab sai Hizmal da sunaila suka cika da
matukar farin maral misaltuwa,
Daga wannan furuci ne kowa yayi shiru aka cigaba da tafiya,
Wannan shi ne abinda ya faru da Jaruma Husnaila da saurayi Hizmal da yaro Humair makaho,
Bayan aljani Marhutul-Azab ya dauko su daga cikin gidan tsira,
*****
BAHREN
A Can ƙasar bahren kuwa, al'amarin sarki uslaim kuwa tun ranar da boka ƙarzum ya bayyana
gare sa,
Domin ya yi masa bayani game da batar yar sa gimbiya zarifa,
Bai sake bayyana a gare sa ba sai wata rana da hantsi sarki uslaim na zaune a bisa karagar sa
ta mulki a fadar sa,
A wannan lokaci fadar ta cika Maƙil da al'umma babu masaka tsinke kowa na zaune bisa
kujera,
Kwatsam sai aka ga wani bakin duhu ya bayyana a tsakiyar fadar
Sannu a hankali sai duhun ya riƙiɗa izuwa wani dattijo fari kakkaura ma'abocin kwarjini,
Fuskar sa cike da ƙasumba da gemu farare sol
Sanye da jajayen tufafi, hannun sa riƙe da kwagirin tsafi dake canza launi izuwa siffa daban
daban-daban,
Ba wani ba ne wannan dattijo ba face boka ƙarzum
Da bayyana sa sai ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa
Ga sarki ƙarzum,
Bayan sarki ya amshi gaisuwar sai boka ƙarzum ya miƙe tsaye tsam ya nufi wata ƙasaitacciyar
kujera dake kusa daf da inda karagar mulki take yana mai dogare da kwagirin sa,
Ya na isa ya zauna abisa kujerar, sai ya juya ya fuskanci sarki uslaim fuskarsa babu yabo babu
fallasa cikin wata irin kakkausar murya yace"ya shugaba na kayi sani cewa bisa binciken da na
gudanar bisa halarar tsafi na na gano cewa lokacin gudanar da tafiyar mu yayi domin saduwa
da SARKIN SADAUKAI domin ka bayyana masa buƙatar ka na son ya ceto maka yarka gimbiya
zarifa daga fadar Sarkin bokaye,
Ya shugaba na kayi sani cewa a halin yanzu ilimin tsafi ya tabbatar mini da cewa babu wani
mahaluki dazai iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI face wani yaro da ya
kasance makaho ana kiransa da suna Humair,
A halin yanzu wani hadimin aljani da ake wa laƙabi da Marhutul-Azab ya dauki yaro Humair tare
da waɗansu jarumai biyu domin su isa dajin Baitul-shamshan domin saduwa da jarumi Hibairu
SARKIN SADAUKAI
Domin su ma su bayyana ma sa nasa bukatun,
Saboda a halin yanzu ba mu da wani abin farauta da huce yaro Humair makaho,
Domin dole shine zai iya magana baki da baki da Sarkin sadauki,
Ya zama wajibi agare mu mubi sahun aljani Marhutul-Azab domin mu riski yaro Humair,
Sa'adda boka ƙarzum yazo dai dai nan a jawabin sa sai sarki uslaim ya cika da matukar farin
ciki maral misaltuwa bai san sa'adda murmushi haɗe da yar karamar dariyar farin ciki suka
suɓuce masa ba
Cikin hanzari sarki uslaim ya mike tsaye zumbur ya shiga izuwa gidan sarauta domin ya kimtsa,
Jim kadan sai gashi ya bayyana sanye cikin gagarumar shigar yaƙi tare da dakarun rakiya gudu
dubu ashirin, haɗe abin guzuri da kuyangi masu hidima,
Batare da wani ɓata lokaci sarki uslaim ya miƙa rikon sarautar sa ga wazirinsa,
Sannan aka dunga aka fita izuwa wajen faɗa, bayan an fita ne sai boka ƙarzum ya kwalawa
hadimin aljanin kira