GOJE part 3 Complete Document by Binta Abbale-1.pdf

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Hausa Novels Story

Chapter   8 / 13

21K to 24K   out of 37.7K words

'baci amma ai basu tsira ba da ikon Allah sai bukatarmu ta biya a
kansu.


Kasa hakuri tayi ta karasa gurin tana tambayar Asp din abunda yake faruwa.........kasa bata
amsa yayi domin a lokacin burinsa kawai yaga ya samu kan abokin nasa.

Da 'kyar ya iya zaunar dashi gefan gado ya mayar da wukar gidanta rataye ta yayi a gurinta, ya
dawo ya zauna a kusa dashi.

Sai suka sanyashi a tsakiya, dukkaninsu babu wanda baya jin sautin fitar numfashinsa huci
kawai yake yana hura hanci!

Ita kam jikinsa kawai take kallo domin ganin koda akwai rauni babu wata matsala fatar jikinsa
tana nan a inda take.


Asp hannu yasa cikin aljihunsa kwalin Sigari ya fito dashi da leta ya kunna masa, aikuwa zuka
uku yayi mata ta kare, ya sake kunna masa wata, a kalla sai da yasha kara biyar sannan ya
dawo hayyacinsa...............Asp ya kalleta da fadin." Ta had'a masa ruwan wanka.

Da sauri ta kama hanyar band'akin duk jikinta a sanyaye!

Ya kalleshi da rinannun idanuwansa a kausashe yace." Jiya nayi magana kace ina da gaggawa!
yanzu me jinkirin ya haifar."?


Ya dafa kafad'arsa da fadin." Kai dai da kawai akwai lauje cikin nad'i! domin Wali Nasiru ya
sheda min duk abunda ke faruwa akwai sanya Hannun manyanmu dangane da faruwar
al'amarin.

Yace." Kai wa kake zargi."?

Shuru yayi na minti biyu kafin yace." Commissioner domin har yanzu bai kira ni yace min komai
ba, kuma ina da tabbacin cewa yasan abunda yake faruwa.


Yace." Shikkenan yanzu mutanan sun dinga samun nasara da sa'a kenan! me yasa ba zamu
sadaukar da rayuwarmu akan ganin mun kawo karshen su ba......Akan wannan dalilin fa wallahi
zan iya ajiye wannan aikin."


Yace." Haba kada kayi haka abokina kabi komai a sannu a hankali, insha Allah komai zai
daidaita za kuma mu samu nasarar kama wa'innan mutane, saboda haka mu cigaba da addua
da kuma bincike akansu."


Shuru kawai yayi masa domin har yanzu akwai sauran takaici a tare dashi...............Ta fito daga
toilet din tana sheda masa cewa ta hada ruwan.

Ba tare da yace komai ba ya tashi ya kama hanyar toilet din, sai ta rufa masa baya, ganin haka
yasa Asp din tafiya gida gabadaya shima ranshi a bace yake da faruwar al'amarin.


Taimaka masa tayi yayi wankan suka fito a tare.


A sanyaye take goge masa jiki da towel sai kallonsa take tana wasu tunane tunane a ranta
mutum sai kace mai aljanu ita yanzu tsoro ma yake bata.


Kallon da take masa ne ya dameshi ya juyo suka hada ido.


Sunkuyar da kanta tayi ta shafo mai a hannunta ta fara shafa masa a gadon bayansa.


A hankali tace." Wai me ya faru ne hankalina yana tashi a duk sanda ka shiga irin wannan
yanayin bana so ko kadan."


Hannunta ya riko yana kallonta idonta ya tara kwalla, da gaske bata so domin ya ga hakan a
cikin kwayar idonta.

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya shiga warware mata abunda yake faruwa.


A tsorace take kallonsa kafin tace." Kayi wa Allah da Annabi kada kasa kanka a cikin wannan
al'amari domin muna sonka kada ka mayar damu marayu." Murya na rawa take maganar.


Ya dunga kallonta yana jin wani irin sonta na ratsa jikinsa!

Fad'uwar gaba asarar namiji! dashi da *UBAN DABA!* Yanzu aka fara! har sai yaga abunda ya
turewa buzu nadi........a zuciyarsa yake wannan maganar, a zahiri kuwa ganin yanda duk
hankalinta ya tashi yasa ya sassauta muryarsa yana rarrashinta, sai ya kasance suna rarrashin
juna ita dai burinta yay mata alkawari cewa ya bar harkar *TAURI!* Kuma bai zai tunkari *UBAN
DABA!* ba.


Alkawarin gaibu yayi mata domin ta samu nutsuwa! amma baya tsammanin zai janye kudirinsa!
harkar *Tauri* kuwa wannan a jinin jikinsa take.


Yayi mata alkawarin ya bari, amma abun mamaki taji yana waya da babban yaronsa *ALBA*
yace lallai - lallai gobe ya kawo masa maciji yana bukatarsa.

Cikin faduwar gaba take kallonsa har ya 'kare wayar ya ajiye a gefansa.......Ta 'bata rai da
fadin." A'a ina za'a kawo maciji kuma me za kayi dashi."?


Yace." Ina bukatarsa ne babu ruwanki dashi."

A raunane! tace." Yanzu fa kayi alkawari ka daina wannan harkar, me yasa duk ga dabbobi ne
wanda Allah ya hallata ba zaka ci ba sai maciji me kukeji a jikinsa."?


Ya d'aga mata hannu da fadin." Kinga *ZINA* kada ki dameni dan Allah ba fa zaki ha nani
aikata abunda na taso dashi tsayin shekaru da yawa ba, saboda haka ki cire kanki daga
wannan sabgar."


Rai a b'ace! ta kama hanya ta fice daga d'akin, tana Allah wadai da al'amarin.

Tsayin sati suna 'yar tsama a tsakaninsu domin tun ranar da ta fita daga dakinsa bata sake
shiga ba, kowa a dakinsa yake rayuwa, shima bai nemata ba sai da ya tabbatar da cewar ya
cinye miyar macijinsa sannan ya nemi in da take da bukatarsa domin dauriya kawai yake a
tsayin kwanakin.

Tace bata san wannan ba, domin data kalleshi zata dinga hasaso shi yana cin maciji sai
zuciyarta ta tashi, takai ta kawo ma duk sanda yayi yunkurin sumbatar bakinta sai ta kwara
amai na bam mamaki!


Al'amarin ya dinga dugunzuma masa zuciya yana bala'in jin haushi yaje da bukatarsa ta dinga
gudunsa gashi sam baya son ya dinga gwada mata k'arfi! yafiso suyi komai cikin walwala da
farin ciki.



Yau dai shiri na mussaman yayi kafin ya tunkari inda take sai da yayi wanka da turaruka
bakinsa sai kamshi yake fitarwa shigar da yayi ma ta mussaman ce, domin wasu kayan bacci
yasa masu kyau da daukar hankali.


Tana kwance kan gado abun duniya ya isheta kwana biyu ta kasa gane kanta, komai na duniya
yayi mata zafi ta rasa yanda za tayi da rayuwarta.............Yawan tashin zuciyar da take yana
damunta.


Shigowarsa dakin yasa da sauri ta juyar da kanta, sam bata san Kallon fuskarsa.


Cikin bargon da take ciki ya shiga yana lumshe mata ido, kokarin janyota yake tayi sauri tashi
tana yamutse fuskarta........Yawu ne ya taru a bakinta ta sauka daga gadon toilet ta nufa ta
zubar da yawun ta dawo.


Abun ya bashi haushi mutuka! ya rufeta da fada ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba.


Hannu ta daga masa da fadin." Don Allah ka kyaleni haka, ni wallahi gabadaya yanzu bana san
damuwa, kai kuma na lura duk sanda ka shigo dakin nan sai ka 'bata min rai! kawai ka daina
shigo min daki."

Ya mike zaune yana mata wani irin kallo kafin yace." Iskancin banza da wofi! meye abun k'yama
a jikina da har kike tara yawu! na dauka yau kwana takwas rabon da ki bani hakkina na aure
ina ruwanki da tsarin rayuwata maciji ni naci abina mai zai dameki kuma."


Tace." Ni fa ba maganar maciji nake maka ba, kai din ne kawai bana son gani." da gaskiyarta
take maganar.


Takaici da bacin rai sukayi masa katutu! ya daina jin tausayinta kuma duk abunda za tayi sai ya
biya bukatarsa.


A daran bai saurara mata ba ya turmusheta ya zage dukkakin karfinsa a kanta, ya galabaitar da
ita sosai domin dama yakan dade kafin ya kawo haka hallitarsa take da nisa.

Aikuwa da ciwo ta tashi dan rasa gane kanta yayi.....babu shiri ya kira likiti domin ya duba masa
ita.

Kallon farko likitan ya gane abunda ke da akwai amma bai tabbatar ba sai da ya auna
fitsarinta.....nan ya tabbatar da zarginsa, ciki ne sati bakwai da kwanaki.

Sai ya rasa ina zai sanya ransa yaji dadi, kawai ya shiga godewa likitan kamar shi yayi masa
kyautar cikin, kudi ya fito dasu daga aljihu ya bawa likitan yana godiya.


A ranar sai bayan azuhur yaje gurin aiki, yana tare da ita yana rarrashinta da kalamai na so da
k'auna, ita dai jinsa kawai take tana mamakin al'amarin, dama jikinta sai da ya b'ata cewa
hakan na iya faruwa aikuwa gashi hakan ta kasance.....ita kam bata shirya haihuwa yanzu ba,
tunda beyi k'wari ba tasan yanda za tayi ta zubar dashi.

Koda ya dawo daga gurin aiki sashenta ya nufa domin dubata, ya same ta fes da ita domin duk
jin jikin da take bata fasa ado da kwalliya ba hakan kamar ya zame mata jiki.


Ya zauna kusa da ita yana nanikar jikinta, shi yana bala'in san kamshin ta ita kuma tana
gudunsa, ba komai ne ya janyo hakan ba, sai d'an tayin cikin dake kwance a kasan mararta.

Be damu da yanda take kauce-kauce ba, ya dinga sumbatar fuskarta yana ta so ya hada
bakinsa da nata tana kaucewa.......da kyar ya samu nasara! tunda ya kama harshen be saki ba
sai da ya gamsu tukkuna.

Idonta ya ciko da ruwan hawaye harara kawai take zabga masa ta rasa wane irin mara zuciya
ne shi.


Ido jawur! yace." Ya jikin ina fatan kin wuni lafiya tare da babyna."

Shuru tai masa tana dauke kanta.

Ya sauke zazzafar ajiyar zuciya tare da kallon agogon dake daure a hannunsa, magariba ta
gabato, tsaye ya mike ya dan kalleta tana ta yamutse - yamutse! huci ya fesar! kafin ya kama
hanyar fita, tabi shi da kallo tana zum'bura bakinta.


Kasa daurewa yayi ya bar maganar a ransa a daran ya shedawa Uwale, farin ciki kamar ya
kasheta, tace." Lallai kace da kwarin gwiwarmu za mu shiga k'auyen *K'afur!* ai wannan abun
alkairi ne da ya kamata ace yan uwa sun sani.

Murmushi kawai yayi da fadin." Saura kwana nawa bikin ne."?

Tace." Ashe baka lissafi ai yau saura kwana uku mu tafi dan duk wasu shirye-shirye mun
kammala."

Yace." To Allah ya kaimu amma ni ina tsammanin a ranar zan dawo bayan an daura aure.''

Tace." To babu damuwa amma ita matar taka sai ka bar ta tare damu domin 'yan uwa su kara
sanin ta."

Yace." Shikkenan haka za'ayi insha Allah."

Sallama sukayi da juna kai tsaye da ya fito sashen Gimbiyar ya nufa cike da farin cikin
kasantuwa da ita.





*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:55 PM] Matar Malam😊: _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin

karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._




*97&98*
Wani irin bacci sukayi mara dad'i sakamakon damuwar da suke ciki. da yake namiji ne shi
yakan iya danne damuwarsa ita kam ta kasa dannewa domin gabadaya jin kanta take a takure!
ita akan kin kanta tasan yun'kurin da tayi ba mai kyau ba ne, shiyasa take bala'in jin kunyar
hada id'o dashi!
Kwance ya sameta saman gado tun bayan sallar asubahi ta kwanta tana k'okarin gayyatar bacci
yaki zuwa babu shi ma gabad'aya a idonta tunani yafi yawa a tare da ita.

Ido ta tsira masa har ya k'araso bakin gadon, ya shirya tsaf da niyyar fita gurin aiki.

Babu yabo babu fallasa ya kalleta da fadin." kin tashi lafiya."?

A hankali ta amsa tana dan lumshe idonta.

Kallonta yake yana ayyana abubuwa da yawa a kanta, yanayin ta ya nuna kamar mara lafiya.

Ya daure zuciyarsa yace." Ko kina da damuwa ne."?

Zuciyarta ta karye hawaye naso ya zubo tana mayar dashi bata bukatar tayi masa kuka tunda
yana kiranta da shagwababbiya.


Shuru tayi ba tace masa komai ba. sai da ya sake maimata maganar sannan tace." Lafiya na
kalau."

Ya kalli agogon dake daure a hannunsa da fadin" Okey haka nake so ni zan fita amma idan kinji
wani guri nai miki ciwo ki kira ni a waya."

Ta kalleshi k'auna da sonsa na kara nunkuwa a zuciyarta, a jiyar zuciya ta sauke a hankali tace
" To."

Ya kama hanyar fita jikinsa duk babu dadi, yarinyar ta tsaye masa a rai.

"Haka zaka fita ba kayi breakfast ba."?

Maganarta ta katse masa hanzari. juyowa yayi yana kallonta.

Ta sunkuyar da kanta domin bata jurewa kallon kwayar idonsa.

" Kada ki damu zan samu abunda zan ci buri na ki tashi ki nemi abinci kici ko dan abunda ke
cikin ki idan kinyi min haka kin gama min komai."

Ta yun'kura ta tashi tana d'an ya mutse fuskarta.

Saurin kawar da kansa yayi sakamakon ganin zahirinta kayan bacci ne a jikinta wanda suka
fitar da wasu sassan na jikinta.

Yay gaggawar bude kofar dakin ya fita yana jin yanda jarumarsa ke motsi har ta fara yun'kuri!
al'amarin ya bashi mamaki mutuka! koda yake ba'a abun mamaki bane idan anyi la'akari da
kwanakin da ya dauka rabon da ya hada shinfida da ita.


Yana zama a ofis kiran wayar Maimartabar ya same shi.

Suka gaisa cikin mutunci da dattako.

Maimartaban yake sheda masa cewa suna da baki da misali sha biyu jirginsu zai sauka anan
filin jirgi na Katsinan.

Farin ciki yayi sosai ya dinga godiya tare da adduar Allah ya saukesu lafiya.

Sukayi sallama cikin girmama juna.


Cike da farin ciki ya kira wayar ta.

Fitowarta daga wanka kenan tayi saurin dauka tare da zama gefan gado.

Ya sheda mata abunda yake faruwa.

Jikinta a sanyaye tace." Me yasa ka sheda musu abunda yake tsakanimu.''? murya na rawa

take maganar


Yayi shuru yana nazarin maganarta.

Tace." Shikkenan na shiga uku ka janyo min bacin ran iyaye na."

Ya kwantar da murya da fadin." Ni fa ban fada musu maganar da wata manufa ba, na fada
musu ne domin su ta ya ni neman mafita, amma bana fatan ranar da zan shiga tsakaninki da
iyayenki."


Ta share hawayen saman fuskarta kawai ta kashe wayar saboda kukan da yake kokarin kufce
mata.


Sake kiran wayar yayi tana kallo tana ringing taki dauka, ita yanzu tashin hankalinta zuwan
Mahaifiyarta tasan bacin rai ne zai biyo ba.


Babu kuzari a tare da ita ta kimtsa jikinta, ta nemi kujera ta zauna tana duba agogo sha biyu ta
gota tasan yanzu mybe sun sauka .


Wayarta ta d'auka cike da fargaba ta kira mahaifiyarta.

Murya na rawa tace."Mommy ina wuni."?.

A dakile ta amsa gaisuwar.

Ta daure tace." Kun sauka ne."?

Gimbiyar tace." Eh sun sauka dan yanzu suka kira waya, babu ni 'Yar uwata ce sai yayyunki."

Ajiyar zuciya ta sauke tana jin sanyi a zuciyarta tasan SAFAH tana da sanyi rai ba kamar
mahaifiyarta ba.


Ta katse tunaninta da fadin.'' Kin kyauta abunda ki kayi ZINA kin janyo min zagi da cin mutunci
na gode." Ba ta jira amsarta ba, kawai ta kashe wayarta.

Ita kam shuru tayi da waya a hannunta gabadaya ta rasa ya za tayi da rayuwarta.

SAFAH tare da Hassana da Hussaina da Magajin sarki suka sauka a gidan......Farin cikin
ganinsu yasa ta fashe da kuka! ta dinga rungumesu duk ta rasa yanda za tayi saboda jin dadin
ganinsu.

Magajin Sarki yace." Ki samu nutsuwa haka zuwan mu gidanki baya nufin farin cikin ki. akwai
babban dalili ne ya kawo mu gidanki."

Ta nemi kan kujera ta zauna jikinta duk a sa'bule.


Ya fara yi mata fad'a tare da kawo mata ayoyin al'kur'ani da hadisai duk dai akan abunda ta
aikata mara kyau!

Shuru tayi ba ta iya cewa komai ba, dukkaninsu kowa ya tofa albarkacin bakinsa mussaman
SAFAH da ta dinga yi mata nasiha mai ratsa jiki anan ne ta zubar da hawaye, tana kukan tace."
Mammah dan Allah ku gafarce ni wallahi tsautsayi ne da son zuciya insha Allah ba zan sake
maimaita abu mai muni irin wannan ba.

Hassana tace." To Alhamdulillhi haka muke so muna rokon Allah ya sauke ki lafiya ya kuma
inganta duk abunda zaki haifa."


Gabadaya suka amsa da "Ameen." Kafin su fara yun'kurin tafiya.

Tace." Mammah har zaku tafi ni wallahi na dauka kwana za kuyi."


Magajin Sarki ya harareta da fadin." Sai kace mahaukata ko."?

Ta 'bata rai da fadin." Aunty Hassana don Allah ku zauna ku kwana mana."


Hussaina tace." Baki da hankali ZINA daga zuwa sai mu kwana ke a ganinki hakan yayi
dai-dai"?

8 / 13