GOJE part 3 Complete Document by Binta Abbale-1.pdf

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Hausa Novels Story

Chapter   12 / 13

33K to 36K   out of 37.7K words

kwanakin baya mahaifinta ya sameni da maganar muka tattauna kuma ya fahimce ni
sosai amma na sheda masa cewa sai kazo tukkuna za'a tsayar da magana."


Yayi shuru yana nazarin maganar...sam! baya san gaggawa acikin al'amarinsa, amma yana
ganin dole ya amince musu dalili bashi da kwakwkwaran hujjar da zai bayar.

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Ni kaina al'amarin yana damuna, kuma na san da yawa daga
cikin mutanan gari sun dauke ni kamar mara amana da cika alkawari! tabbas Allah ke tsarawa
bawa rayuwarsa amma a mafarki banyi tunanin auran wata mace bayan Hamra'u ba, akwai
abinda Allah yake nufi da faruwar hakan, saboda haka yau nake da niyyar komawa bakin aiki
amma zan bar komai a hannuku duk abunda ya kamata ayi na neman aure a tabbatar an
gabatar zan turo kudin hidima da sauransu idan yaso sai a tsayar da lokaci."


Gabadayansu farin ciki ya lullubesu dama babban burinsu ace yaron ya dawo gida yayi aure,
domin auran da yayi a baya sam bai kwanta musu a rai ba sai kuma gashi had'uwarsu ta farko
da sukayi da yarinyar ta nuna k'yama! a garesu wannan shine dalilin da yasa gabad'aya suka
d'ora mata karan tsana basa kaunarta ko kad'an.

Kawu Haruna yace." Allah yayi maka albarka Umaru yanda kayi mana biyayya Allah ya
azurtaka da yaran masu albarka, Allah ya jikan mahaifinka yayi masa gafara."

Ya amsa da "Ameen ya Allah Kawu Allah ya saka da alkairi."

Kawu Ado yace." Yanzu kai ya kamata ka tsayar da lokaci domin mu shedawa mahaifin
yarinyar."

Yayi jim! yana nazari kafin yace." Shekara guda yayi."

Kawu Haruna yace." Haba Umaru wane irin shekara kuma? me ka nema ka rasa da har zaka ja
lokaci haka."

Shuru kawai yayi yana kallonsa shi a ganinsa shekarar shine dai-dai lokacin matarsa ta haihu
hankalinsa zai fi kwanciya baya so yanzu ta samu labari matsala ta afku.

Kawu Adon yace." Kayi shuru kana tunani Umaru ka duba lamarin nan da kyau."


Yace." Kawu akwai dalilin da yasa nace a sa shekara guda domin iyalina na da juna biyu kasan
mata da kishi bana so wata matsalar ta biyo baya idan ta samu labari."


Kawu Haruna ya 'bata fuska tsanar yarinyar ta sake nunnukuwa a ransa yace." Umaru na
dauka ai tuntuni ka shedawa matarka tsakaninka da yarinyar nan Hamra'u, ai bai kamata kaja
bakinka kayi shuru ba tunda tilas ta san ba zata zauna ita kad'ai ba."


Ya tsirawa Kawun nasa ido yana mamakin furucinsa.....Idan ban da kaddara baya tsammanin
kara aure domin bai tashi da ra'ayin haka ba, mace daya ta isheshi rayuwa mutukar ta cika
abunda yake bukata, amma yanda ya tsara rayuwarsa ba haka Allah ya tsara masa ba,
wannan shine dalilin da yasa yake mamakin furucin kawun nasa.
Kawu Haruna yace." Wata shida za'a sanya shine dai-dai."

Yace." To shikkenan Kawu Babu damuwa Allah ya tabbatar mana da alkairi."

Gabad'aya suka amsa da "Ameen ya Allah."

Ya d'an gyara kafin yasa hannu cikin aljihu ya fito da kudi 'yan dubu-dubu saffi kar guda ashirin
ya ajiye gabansu da fadin.'' Ga wannan babu yawa bayan haka akwai kayan abinci a can gidan
Uwale idan na koma yanzu zan sanya yara sukai gida."

Suka dinga godiya suna shi masa albarka gabadaya bakinsu yaki rufuwa sai fatan alkairi suke
masa. sallama yayi musu kafin ya bar gurin cike da tararrabi da damuwar abunda zai biyo
baya.


Kawu Ado ya shiga gidansa bakinsa kamar gonar audiga.

Matarsa Taburni tana tsintar shinkafa ta kalleshi tana mamakin annushuwar da ya shigo dashi
gidan


Kusa da ita ya zauna da fadin." Kina da labarin zuwan Umaru ko."?

Tace." Eh na samu labari a bakin yara Allah yasa da alkairi yazo mana."

Ya fito da sabbin kudin ya ajiye a gabanta, ta dauka tana lissafawa ta kalleshi da fadin." Dubu
goma ne."


Yace." Kwarai kuwa haka ya bani ya kuma bawa Haruna sannan yace yanzu zai turo mana da
kayan abincin.


Ta washe baki da fadin." Kai masha Allah ashe yau za muyi miya da nama! mun gode sosai
Allah ya saka masa da alkairi."


Ya amsa da "Ameen yana tattara kan kudinsa yasa a aljihu da fadin." Bayan haka kuma mun
tsayar da magana wata shida masu zuwa za'a daura auransa da Hamra'u 'yar gidan 'kawarki
'Dayyiba.

Taburni ta rangad'a bud'a farin ciki kamar ya kasheta tace." Lallai Allah yayi aure da mara
kwabo! yanzu kuwa zan je na shedawa kawata halin da ake ciki."

Yace." Ai yanda na lura da yaron kamar yana tsoron matarsa ne idan ba haka ba mai zai sanya
yace sai ta haihu sannan za'ayi maganar aure a take a gurin Haruna ya nuna masa fushinsa.


Taburni ranta a bace tace."Au! ciki ne da matar tasa."?

Yace." 'Kwarai kuwa ciki ne da ita har yayi kwari mana."

Taja tsaki da fadin." Hegiyar yarinya mara mutunci ai duk sanda na tuna abunda tayi mana
sai raina ya 'baci! bana k'aunarta ko kad'an ."

Yace." Duk cikinmu babu mai k'aunarta! wannan ne dalilin da yasa muke so yayi auren cikin
gida domin mu samu wacce zata mutuntamu ta kuma daraja mu."

Tace." Wannan shine gaskiya, naji dadin faruwar wannan al'amarin, Allah kuma ya tabbatar da
alkairi." Ya amsa da "Ameen." Yana kokarin kishingida a gurin.

Ita kuwa da sauri ta tashi ta fara aikace-aikacen ta tana Allah-Allah ta kammala taje ta shedawa
'Kawarta albishir mai dadi.
Da wata iriyar kasala ya koma gidan, gabadaya kansa ya daure ya rasa wane irin tunani zai yi.

Bacci take sosai duk gumi ya ji'kata! da sauri ya dage labulan ya dora saman 'kofar dakin, kai
tsaye dakin Uwale ya nufa ya samo mafici ya fito wanda yayi dai-dai fitowarta daga kicin, ta

kalleshi da fadin." Har ka dawo."?

Yace." Eh yanzu nan na shigo Zinatu taci abinci."?

Tace." A'a ai bayan fitarka na leka dakin sai na sameta tana bacci, shine dalilin da yasa ban
tasheta ba.

Yana kokarin barin gurin yace." Yanzu zamu shirya tafiya insha Allah."

Kallo ta bishi da kallo tana mamakin maganarsa.

Rigar jikinsa ya cire ya zauna kusa da ita tare da kokarin cire mata rigar jikinta.

Ido ta bud'e cikin alamun bacci take kallonsa. sai ta fara kokarin tashi zaune.

Ya taimaka ta tashi burinsa kawai ya rabata da rigar saboda gumin da take.

Ha nashi tayi domin tsarguwa tayi ganinsa babu riga sai take tunanin wani abu zai yi mata.

Da ya fuskanci haka sai ya girgiza mata kai da fadin." Babu abunda zanyi miki ki cire rigar
saboda zafi.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara kokarin tashi........hanyar fita ta nufa ya bita da kallon
mamaki!

Bandaki ta shiga ta kama ruwa kafin ta fito ta daura alwala.

Uwale ta fito daga kicin hannuna rike da farantin silba da kwanukan abinci a jere, ta kalleta da
fadin." Kin tashi kenan."

Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba ta fara kokarin kar'bar kayan abincin.

Ta janye da fadin." A'a ki bar shi na k'arasa lada na mana."

Murmushi tayi tana kallonta, hakika matar nada kima da daraja a idonta.


Ta ajiye Tire din da fadin." Umaru ashe sai da ka tashi yarinyar nan .''

Yace." Uwale tashin shi yafi alkairi tayi sallah ta kuma ci abinci domin mu dauki hanya da wuri.

Tace." Tun dazu kake magana a 'boye me kake nufi ne."?

Yace." Uwale kiyi hakuri tare zan koma da ita."

Ta 'bata rai da fadin." Okey ta saka ka a d'aki ta nuna maka rashin yarda ta kenan."
Maganar tayi dai-dai da shigowarta dakin.

Itama Uwalen sai da ta fadi maganar sannan kuma tayi dakace.

Yace." Ko d'aya kawai nayi wani tunani ne, shiyasa na sanja shawara."


Ba tace komai ba ta kama hanya ta fita ranta a 'bace!


Tana idar da sallar ta kalleshi da fadin." Ka bari kawai zamu dawo tare dasu kayi tafiyarka.''


Yace." Saboda me? shin kin san damuwa da nake ciki kuwa."?


Tace." Kayi hakuri ka danne damuwarka duka kwana nawa za muyi zamu dawo."

Shuru kawai yayi mata a ransa sam beso hakan ba dan dai sun fi karfinsa ne.


Tare suka ci abincin sai jifanta yake da wani irin kallo na mussaman wanda ya kashe mata jiki
babu shakka akan ga'ba yake tana jin tsoron suyi abun kunya.

Aikuwa dai abunda yake shirin faruwa kenan, dan fafur! yaki tafiya lokacin yayi kwanciyarsa
sai bayan da ya biya bukatarsa tukkuna! kunyar duniya ta isheta, ba ta iya wanka a lokacin ba
sai da ta tabbatar cewa duhu yayi sannan ta tsarkake jikinta ta gabatar da magariba da
isha'i......Lokacin shi kuma ya gama shirin tafiya.
Zuciyarta ce ta karye ta kasa kallonsa sai kokarin mayar da hawaye take.

Koda ya fuskanci halin da take ciki sai ya rungumeta yana rarrashinta......Yanzu bashi da
damuwa tunda ya kawar da abunda ke damunsa.

Sosai ta b'oye damuwarta duk dan kada Uwalen ta fahimci wani abu ta saki jikinta sosai! suka
dinga hira a tsakaninsu. Har take tambayar Hamra'u, nan take sheda mata cewa ta tafi gidansu
a can zata kwana.

Allah sarki Uwale mace mai karamci da kanta ta gyara mata shimfida sabon zanin gado ta
shimfida akan gadon katifar audigar dake shimfide akan gadon karfenta irin na mutan da , ta

kunna mata turaran wata na tsinke! dakin ya dinga kamshi mai dadi, bata kwanta ba sai da tayi
wanka tukkuna ta sanya wata doguwar riga cotton mai tausa sai tasa hula da yake duk tayi
gurizin abinda zata bukata....Sosai taji dadin kasancewarta a d'akin, tayi kwanciyarta kan
lallausar katifa iskar hadari na kad'a labulan dakin.
Mijinta kawai take gani a lokacin da idonta yake lumshe, ta kira wayarsa ba adadi taki shiga da
alama gidan bashi da network ko kad'an ! gabadaya ta shiga damuwa, muryarsa kawai take
bukatar saurara a kunnanta.




*Ayi hakuri da rashin posting akan lokaci wallahi kanwata ce za tayi sauka al'kur'ani Gobeí ½í¹í ¼í¿»*



*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:55 PM] Matar Malam😊: _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._



*107&108*
Sai gefin magariba ta tashi daga baccin daya d'auketa, jiki babu kuzari ta tashi zaune da sunan
Allah a bakinta, shiru tayi tana tunanin irin wuyar da tasha a d'azu, tabbas da kwananta ya 'kare
babu wanda ya isa ya hana Allah zartar da Allah ikonsa, sam ba tayi tsammanin cewar zata
sake wata rayuwar ba, duba da irin siradin data tsallake, a mai da gudawa ba karamin cuta
bane, yanzu ma gabad'aya bata jin dadin jikinta, duk yayi laushi akwai bukatar karin ruwa a
tare da ita.

Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta fara kokarin sauka daga gadon, kira ya shigo wayarta dake
saman gadon, ta dauka tana dubawa, a kalla ya kira yafi sau ashirin tana bacci, tausayinsa ya
rufe ta, tasan yana can a dame kamar yanda take a takure! ko kuma jikinsa ne yake fada masa
cewa akwai matsala.
Ta daga wayar cike da so taji muryarsa, network yayi tsiya dan sai magana take masa amma
shi ba yaji.....Ta kashe wayar ta sake kira anan ma ba babu biyan bukata, kamar zata fashe da
kuka ta ajiye wayar takaici duk ya isheta.

Uwale ta shigo dakin, ganinta a zaune yasa ta sauke ajiyar zuciya tace." Kin tashi ko ya jikin
naki."?

Tayi kokarin danne damuwarta ta amsa da fadin." Naji sauki sosai na gode."

Tace." Haba ai babu godiya a tsakaninmu Gimbiya Allah dai ya kiyaye gaba."

Ta amsa da "Ameen ya Allah."

A sanyaye tace." Amma don Allah ina neman alfarma a gurin ki."

Cike da mamaki take kallon matar wace irin alfarma ce."?

Tace."Don Allah kada ki fad'awa mijinki abunda ya faru kinji ko."?


Murmushi kawai tayi kafin tace." Insha Allah kada ki damu ba zan fad'a masa ba."

Tace." To na gode sosai.''


Har ta juya zata fita daga dakin ta dakatar da ita....."Ina bukatar nayi wanka jikina bana jin
dadinsa."

Tace." Ai dole! amma kiyi hakuri ayi sallah tukkuna bari na dora miki ruwan zafi sai ki gasa
jikinki."


Tace." To shikkenan hakan yayi." Uwale ta fita daga dakin tana godiya ga Allah ganin yanda ya
gajarta musu wahala.


Cikin ikon Allah ta na yin wanka jikinta ya warware ta zauna taci abinci zuciyarta fes domin ba
tayi tunanin cewa wai abincin da taci dazu ne ya janyo mata matsala ba, itama tafi tunanin

cewa ko sauyin yanayin gari da sauransu.

Ta kalli Uwale da fadin." Ina so nayi waya amma gidan nan bashi da network yana bada
matsala."


Tace." To yanzu ya za'ayi kin ga yanayin gidajen namu ginin da ne babu tsayin katanga a daki
ga zurfi.

Tace." Zan fita waje ko Allah zai sa a dace."

Tace." To shikkenan babu damuwa.


Can wani fili ta nufa, duk da dare ne hakan bai hana gane ta ba, ido yayi caaa! a kanta, yara da
manya masu wuce wa.

Ita dai bata damu ba bukatar ta, ta samu wayar masoyinta.

Bugu daya ta shiga ya daga, abun mamaki tar taji muryarsa babu gargada.

Ajiyar zuciya mai sanyi ta sauke kafin tace " Darling ya kake? ina fatan kana cikin koshin
lafiya."


Yace." Kin san hakan ba zata samu ba, ZINAT me yasa baki d'aga wayata akan lokaci ba."


Tace." Ba laifi na bane network ne babu a garin, nima na damu da kai sosai wannan dalilin yasa
na fito waje wani fili duk dan naji muryarka."


Yace." Yanzu kina nufin ba'a cikin gida kike ba."?

Tace." Eh ai cikin gidan na fad'a maka babu network mai kyau.

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Ki koma gida bana san tsayuwar ki a gurin nan."

Tace." Haba babu fa abunda zai faru duk ga jama'a nan suna kai kawo a gurin."


Ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin wani abu a ransa, jiya kwana yayi yana munanan
mafarkai a kanta, amma yasan babu wani mahalukin da ya isa ya cutar da ita face Allah ya

mayar masa da sharrin kansa.


Hamra'u da k'awarta Zabbah suka hangota a tsaye da waya a kunne.

Hamra'u tace." Zabbah ga mutsiyaciyar can."

Zabbah ta kalli gurin da fadin." To me ya fito da ita a wannan daran ita ba 'yar gari ba."


Tace." Waya ta take na san kuma da masoyina take, yau sai naci mutuncinta in yaso duk
abinda zai faru ya faru."


Zabbah ta rike hannunta da fadin." Hamra'u kada fa ki aikata abunda zai janyo miki matsala ki bi
komai a sannu a hankali."


Ta fizge hannunta da fadin." Zabbah ni kad'ai na san irin b'akin cikin da wannan matar ta k'unsa
min, ai magana ta 'kare tunda manya sun shiga maganar har an tsayar da ranar daurin aure."


Hannunta ta fizge ta durfafi gurin da Gimbiyar take tsaye....Zabbah ta rufa mata baya.


Tace." Darling zan shiga na kwanta sai da safe." Daga d'aya b'angaran yace." Okey Allah ya
tashe mu lafiya amma ki mika min gaisuwa gurin babyna kafin mu had'u."


Tana murmushi tace." Zai ji da kyau! amma shima yayi kewarka sosai.

Yace." Haka nake so ai duk sanda muka had'u zamu gaisa sosai ki bashi hakuri."

Cikin shagwaba tace." 'Daya babyn naka ma yana bukatarka fa."

Ya lumshe ido tsigar jikinsa na tashi! ya gane abinda take nufi shiyasa gabadaya kasala ta
rufeshi yana bala'in son yanayin shagwabarta.

Yace." Wannan babyn yayi min laifi ki sheda masa cewa idan muka had'u zan hukuntashi da
kyau."!

Ta fashe da dariya da fadin." Ba ruwana amma na yarda duk sanda kuka ka had'u kayi masa
hukuncin da ya dace."

Yana sake release a kujera yace." Zan kuwa cire masa kai shine

12 / 13