Author : Binta Umar Abbale Category : Hausa Novels Story
garin.
Ya mayar da hankalinsa kan takardar yana karantawa.
Rahoto ne daga gidan jaridar *AMINIYA* cewa wasu 'yan gudun hijira da suka samu masauki a
k'auye *KUYAN TA INNAH* ana zarginsu da ta'addanci tare da yiwa k'ananun yara
fyad'e........Ana dai binkice a kansu domin tabbatar da gaskiya magana.
Ya share zufar saman goshinsa, ya kalli Asp din da fadin." Ko shakka ba nayi zasu aikata
abunda yafi haka, babu wani maganar binkice! wai shin me yasa jami'an tsaron *KANO!* suke
da sakaci ne? to ni da kaina zan shiga Kanon domin a gudanar da binkicen dani idan ba haka
ba zasu iya kyaleshi ya cigaba da ta'addanci tare da kashe rayukan da basu ji basu gani ba." Murmushi Asp din yayi kafin yace." Kai ka fiye gaggawa! yanzu idan akayi wani yun'kuri zasu
ankara su samu damar tserewa.....wannan rahoton babu wanda ya san dashi sai ni da kai sai
kuma Commissioner.......Domin Abokina *Wali Nasiru* dake *KANO* tare da sauran abokan
aikinsa ne suka shiga 'kauyen suna binkice akan matsaltsalun dake faruwa.....nan suka samu
cikakkaken bayani daga bakin wani dattijo cewa tsayin shekara dari da wani abu wata
gagarimar matsala bata ta'ba faruwa ba a 'kauyen sai dalilin zuwan 'yan gudun hijirar.......Dalilin
da yasa kenan suka tsananta binkice akansu domin gano gaskiyar lamari.......Kasan abokina ne
sosai tare mu kayi karatu to yana bani labarin abunda ke faruwa sai na bukaci da ya turo min
rahoton domin ni kaina sai da na zargin wani abu, saboda haka muyi hakuri kada muyi
gaggawa domin hakan zai zaburar dasu, su gudu! a nutse zamu kamasu. ina kuma kara
tabbatar maka da cewar babu wanda ya san wannan rahoton daga ni sai kai sai kuma mai
gayya mai aiki don bana tsammanin ma gwamnati tasan da abunda ke faruwa domin yanzu
muka gama tattaunawa commissioner din akan hakan."
Dogon tsaki! yaja ransa duk a dagule! wane irin aikin gaggawa ai a ganinsa jinkiri shi zai cutar
dasu, ya ga dama sun samu amma za suyi wasa da ita! ya dinga jan tsaki! kansa ya cigaba da
sarawa! tabbas da ba dan a karkashin gwamnati yake aiki ba to da babu shakka yau zai yiwa
garin *KANO* dirar mikiya duk inda *UBAN DABA!* Da yaransa suke sai ya lalubo su domin
gwabzawa!
Asp din yace." Ya kamata kaje gida ka huta idan zai yuwu ma gobe ka zauna ka sake jin
'kwarin jikin ka Allah ya sawwake."
Ya amsa da "Ameen yana duba agogon dake daure a hannunsa, uku da rabi na yamma....Asp
din ya mike da niyyar fita shima mikewar yayi, ya dauki gilas dinsa ya sakaye idonshi kafin yabi
bayan Asp din da niyyar zuwa gida ya sha magani ya kwanta ya huta.
'Bangaranta kuwa tunda ya fita ta kasa samun nutsuwa, tana ji kamar ta kira shi a waya tana
kuma tunanin kada ta zubar da ajinta.....Haka ta dinga juye-juye a saman gado sa'i da lokaci
tana share hawayen takaici! ita kanta ba'a son ranta ta aikata masa hakan ba, kawai ya b'ata
mata rai ne.
Kafin ya shiga gidan sai da ya gabatar da sallar la'asar tukkuna.........Ya duba gurin su Uwale
domin ya tabbatar da cewa sun fito daga asibitin saboda a d'azu da safen Likitan yake tabbatar
masa da cewa zai sallamesu zai kuma sanya direba ya kai su gida.
Sosai yayi farin cikin ganinsu A falo suna hira har ita Hamra'u domin ta wartsake kamar ba ita
ba, hakan duk ya faru ne dalilin kwantar mata da hankali da Uwale keyi ta tabbatar mata da
cewa suna zuwa k'auye manya zasu tsayar da maganar daurin auransu, wannan ne dalilin da
yasa ta samu nutsuwa ta kuma kwantar da hankalinta.
Gabadaya suka dinga bin sa da kallo har ya samu guri ya zauna.......Uwale ce ta magantu, cikin
damuwa tace." UMARU mai ya samu 'kafar ka."?
Shuru yayi na minti biyu kafin yace." Na d'an taka k'usa ne kin san tana da dafi! shine dalilin da
yasa kafar ta kumbura!
Sosai tayi mamaki kafin tace." Cikin wannan uban takalmin da kake sanyawa har kusa ta iya
huda maka 'kafa UMARU anya kuwa."?
Murmushi yayi da fadin." Uwale ki bar tsautsayi kawai! Allah ne kawai ya takaita min wahala
'kusar bata shiga sosai ba ku cigaba da yi min addua."
Tace."To Allah ya kiyaye ya tsare gabanka da bayanka."
Ya amsa da "Ameen ya rabbi kafin ya kalli Hamra'u da tunda suka fara maganar ba tace komai
ba.
Ya dan saki fuskarsa da fadin." Ya jikin naki."?
Tace." Da sauki Yaya na, kai ma ya jikin naka? Allah kiyaye gaba."
Ya amsa da "Ameen ya rabbi nagode sosai amma kin dai ji abunda likita yace miki ko? ki rage
tunani dasa damuwa a ranki."
Tace." To Yaya na insha Allah zan kiyaye nagode Allah ya saka da alkairi."
Bece komai ba ya kalli Uwale da fadin." Uwale a dan bani abinci zanci kafin nasha magani."
Ko kafin Uwalen ma tace komai zumbur ta mike ta kama hanyar kicin......Gabadaya suka bita
da kallo suna girgiza kai, tausayi take basu.
Yaci abincin sosai yayi godiya ga Allah kafin ya wuce sashensa dan beyi niyyar shiga gurinta ba
gudun b'acin rai! abunda baya bukata kenan.
Marakisiyya dake shanya kayan data wanke a harabar gurin ita taga wuce war sa, ta dur'kusa
har kasa tana gaisheshi ya amsa ba tare da ya kalleta ba, ya wuce ya bar ta a gurin.
Ita din ke shedawa uwar dakin nata dawowar mijin nata.........Tace mata ta ganshi ya fito daga
sashen masu gidan ko za'a kai masa abinci."
Ranta ya 'baci! ta kalli Marakisiyyar ta watsar kafin ta buga mata tsawa! had'e da nuna mata
hanyar fita.
Da sauri ta mike ta kama hanyar fita gabanta na faduwa! sam ba tayi tsammanin cewar
maganarta zata fusata! Uwar dakin nata ba, a ganinta kamar gwaninta tayi.
Ita kuwa har Marakisiyyar ta fita ba daina hararar hanyar data bi ba.......Wani irin kishi ne yake
damunta. wannan ai abun kunya ne mijinta ya dawo amma ace mai'aikinta ce ke sheda mata,
bayan haka kuma tana jin haushin abunda ya kai shi sashen masu gidan, hakan baya rasa
nasaba da mutsiyaciyar yarinyar data tsana a rayuwarta.
Sabon wanka tayi....... sosai tai gayu tayi cikin kananun 'kaya masu daukar hankali, masifaffun
turarukan da take d'aukar hankalinsa dasu tasa a kowane sassah na jikinta, kai tsaye sashen
ta nufa zuciyarta cike da wasiwahsi!
Idar da sallarsa kenan domin tun daga magaribar har isha'in a gida ya gabatar bai samu shiga
massalaci ba dalilin matsanta masa da kafarsa tayi, koda yake yasha magani da sauki akan
da.
Kamar bata so tayi masa sallama, shima babu yabo babu fallasa ya amsa, yana bin ta da kallo
har ta samu saman kujera ta zauna.
Shuru tayi tana dan wasa da yatsun hannunta!.....shi kuma bai fasa kallonta ba, da carbi a
hannunsa yana ja yana nazarinta.
Ta d'ago kai suka had'a ido! bai janye idonsa ba bai kuma ce mata komai ba......Itace dai ta
janye idonta sakamakon dafin idanuwansa dake kokarin kassara ta!
Da 'kyar ta iya bude baki tace." Ashe ka dawo."?
Uffan bece mata ba kawai dai ya zuba mata idonsa dasu yake hukuntata!
Ta kalleshi a karo na biyu idonsu ya sake had'uwa.......Wani abu mai yuwar fassaruwa take
hange a cikin kwayoyin idanuwansa, gabadaya jikinta ya mutu sai kawai hawaye ya kwace
mata! suna zuba tana sa hannu tana sharewa tare da shak'ar hanci! tabbas da tana da iko da
sai ta dawo da ciwon jikinta a ganinta ma kamar ta fishi damuwa!
Gyaran murya yayi kafin yace." Me kuma nayi miki? zaki sanya ni a gaba kina kuka! ai ni zanyi
kuka duba da ta'addancin da ki kayi min."
Ta kalleshi hawaye share-share! "Nice 'yar ta'addah."? tafada tana nuna kirjinta.
Kansa ya daga da fadin." Eh mana baki da imani! idan ba haka ba mai zai sanya ki farfasa min
kwalabe a daki ai kinso ki cutar dani ne."
Taja hanci tana goge ragowar hawayen daya rage tace." Okey kai yanzu a ganinka abunda ka
aikata shine dai-dai."?
Ya ajiye carbin dake hannunsa sosai ya mayar da hankalinsa kanta yace." Me nayi ? ina so kiyi
min cikakken bayanin abinda nai miki ko'ina akaje baki da hujja!
"Shikkenan tunda haka kace ni bazan yi wata magana da kai ba a yanzu amma ina mai
tabbatar maka da cewa wallahi idan baka daina ba nima ba zan fasa ba."!
Yace." Idan kuma ta hanyar halak nayi fa? shin ko zaki hana ni aikata sunnah da matata."?
Shuru tayi tana kallonsa gabanta in banda faduwa babu abunda yake.
Yace." Ki kiyaye domin kishin hauka babu inda zai kai ki, sai halaka hakan kuma da kike bashi
zai ha nani abunda nayi niyya ba."
Jikinta duk ya mutu da maganarsa, a sanyaye tace." Kayi hakuri."
Wani sanyi ya ziyarci zuciyarsa.......Lallai ya yarda da maganar Uwale da Asp in da suke cewa
cikin laluma ake nusar da mutum idan yana aikata kuskure......gashi kuwa yayi amfani da damar
bukatarsa ta biya bai ta'ba tsammanin zata bashi hakuri ba, koda yake yabi hanyar da hakan
zata kasance!
Yace."Na yafe miki Allah yayi miki albarka."
Ta amsa da "Ameen Nagode."
D'akin yayi shuru na 'yan mintina kafin tace." Kaci abinci."?
Yace." Eh naci gurinsu Uwale yanzu kwanciya kawai nake bukata."
A hankali ta mike ta iske inda yake zaune.........Hijab din jikinta ta cire kafin ta zauna kusa
dashi..........Kallonta kawai yake yana sha'kar kamshin jikinta da yake masifar so!! idonta kuri
kan k'afarsa kafin ta kai hannu gurin ciwon!
Da sauri ya janye yana ya mutse fuskarsa!
Tace."Da zafi ko."?
K'amar karamin yaro ya daga kansa!
Sai kawai ta taya 'bera 'bari ta janyoshi jikinta kansa ta rungume a kirjinsa tana jijjigashi tare da
shafa sumar kanshi kamar k'aramin yaro!
Tabbb! ☺️ ai neman ciwo yayi ya rasa irin wannan soyayya! haka mai neman kuka an jefeshi
da kashin awaki! mutumin da ake rarrashi! domin yayi bacci sai kawai ya 'buge da kusurkusur
yana motsi tamkar yaron dake tsananin bukatar nono! haka ya dinga cusa fuskarsa a kirjinta da
wayo da dubara ya 'balle bireziyar ya sa'bule! 'karamar rigar dake jikinta........Daga nan labari ya
sauya.
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:55 PM] Matar Malam: *Assalamu alaikum warahmatullahi masoya yan uwa na
musulmai...*
*Tabbas wani kaya sai amali ,busa sai sarewa jiniya sai a gidan gomna ,ina kuke mata ma'abota
tambayar ina wannan shahararriyar y'ar mutan nijer wato mali ,wacce akafi ma lak'abi
da...*```BUZHUWA EMPIRE```
*Ina kuke matan Aure n mu masu fuskantar tangard'a tare da k'alubale a gidan mazajen Auren
mu??.*
*Ina kuma y'ammata masu buk'atar farin jini ta hanyar samun mijin Aure?? Don raya sunnar
manzon mu SAW...Nasan duk kunce gamuuu!!!.* *Gafa BUZHUWA EMPIRE ta* *taho
maku duk don share hawayen dake kwaranya akan fuskokin ku ta hanyar kawo maku sirrin
mallaka tare da* *magani ,haka ma y'ammata ga sirrika nan da maganin shi ,wanda anyi
mutane babu adadi kuma anzo anyi* *godiya....ki tambaya wacece Buzhuwa empire ga dukkan
wanda* *yasanta ,zakuji karin bayani daganan. Muna bada mallaka ta hanyayoyi dabam*
*dabam ,wanda da alfarman annabin rahma xamu sha mmki.* *Mallakar tamu akwai na 3k
akwai na 5k ,akwai na 10k da sama ma da haka. Mudai fatan mu shine babu cuta babu cutarwa
, kamun mu biya* *maki bukatanki sai kin mana rantsuwa akan bazaki cutar dakowa* *ba
,mallaka matan aure muke ba zallah. Na farin jini kuma na y'ammata ne ,shi munayin shi akan
5k ne da kuma na 10k.* *Zakuna iya tuntu6an wannan numbern domun karin
bayani...09061466409/08081202932.*
*Ga kad'an daga cikin mallakar da muke amfani wajen yinsu.*
*Mallaka ta hanyar K'wai.*
*Mallaka ta hanyar nono*
*Mallaka ta hanyar zobe*
*Mallaka ta hanyar guru*
*Mallaka ta hanyar turaruka da dai sauran su.... Sai kin taho domun share hawayenki daga
kunci zuwa farin ciki....* ```BUZHUWA EMPIRE taku ce!!!```
~08081202932 ko 09061466409~
*93&94*
A daran rigima ce ta kaure tsakanin Asp da Zeey sosai yayi mata jan ido ya kuma tabbatar mata
da cewar kwa'bar ta tayi ruwa, amma ta kwana da shirin cewa mutukar da sanya hannunta
auran yar mutane ya mutu to itama ta kwana da shirin nata auran sunansa matacce.
Al'amarin ya bata mamaki sosai, domin ba tayi tsammanin matakin da zata dauka ba kenan,
tasan dai sunyi zantuka da yarinyar, ta kuma bata shawarwari! amma kuma koda wasa ba tayi
tunanin cewa za ta cutar da mijin nata ba.
Jikinta duk ya mutu dan tunda take da mijinta bai ta'ba ci mata mutunci irin yau ba, lallai babu
shakka dole tayi takatsantsan gudun faruwar wata matsalar domin ta fahimci mijin nata a
fusace yake, hakuri ta bashi da fadin.'' hakan ba zata sake faruwa ba, ko sauraranta beyi ba ya
kama hanya yayi tafiyarsa gidan Madam tunda dama a can yake.
Karfe uku da rabi na dare.....Gidan jaridar *AMINIYA* ya tashi da wuta! wacce ba'a san
abunda ya haddasa ta ba, tashin hankali kenan! wutar sai da taci mutum hudu masu aikin
kwana 'kurmus! suka mutu dan da 'kyar aka samu gawarsu........Wannan ibtila'in da ya faru ya
tashi hankali jama'ar gari gabadaya gari ya dauka da maganar...... mahukunta kuwa sun
tsananta binkice domin gano abunda ya haddasa tashin wutar.
Wayewar gari a cikin k'auyen sukayi 'batan dabo! shi da jama'arsa sama ko kasa aka neme su
aka rasa.....sun gudu bayan sun tafka ta'addanci dan gabadaya sai da suka yashe jama'ar
garin, da yake k'auye ne basu waye da kai kudi banki ba, a gida suke ajiyewa, wannan dalilin
yasa suka bi dare suka haura gidajen mutane suka tafka musu sata, kudi cikin jakar baggo
suka fita daga cikin garin.
Wannan ne ya tabbatar da zargin da ake musu.....Mane ma labarai suka fara d'aukar rahotanni
daga bakunan jama'ar kauyen suna watsawa a duniya.....Jami'an tsaro kam basu zauna ba sun
bazama domin binkicen inda suke.
Wannan labarin yayi masifar 'batawa UMARU rai dan koda Asp din yake sheda masa abunda
yake faruwa, tsaki kawai yaja ya kashe wayarsa, shi kansa Asp din haushinsa yake ji domin da
yabi shawararsa a ganinsa da duk haka bata faru ba.
Ta fito daga toilet ta sameshi ya dafe kai sai sakin tsaki yake.....Cike da damuwa ta dafa
kafadarsa nan taji yanda jikinsa yake mazari da tsuma!
A sanyaye tace." 'Kafar ce take damunka."?
Kallonta yayi...sai ta kasa hada ido dashi ganin yanda gabadaya kwayoyin idonsa suka sauya
jijiyoyin kansa sunyi rad'a-rad'a! lallai da akwai abunda yake faruwa!
Tana kokarin magana ya mike tsaye.... ya kai ya kawo a dakin! fatar goshinsa duk ta tattare ta
tara zufa!
Hankalinta ya tashi domin duk sanda ya shiga irin wannan yanayin abunda zai faru ba zai kyau
ba.
Cikin dauriya ta 'karasa inda yake kokari take ta rungumeshi amma hakan ya gagara! domin
gabadaya ya kasa tsayuwa a guri guda.
Sai kawai ta fashe da kuka da fadin." Wai meye haka ? ni bana san ganinka a irin wannan
yanayin idan nai maka laifi kayi hakuri."
Bece mata komai ba gefe ya matsa yana kokarin cire rigar jikinsa......Ta tsira masa ido dake cike
fargaba da tashin hankali!
Gabadaya jikinsa ya bude mussaman kirjinsa da damtsan hannuwansa sai rawa jikin yake
ruwan gumi na diga.
Da sauri taje ta dauki wayarta, Asp zata kira ta sheda masa abunda yake shirin faruwa domin ta
tsorata da ganin ya cire riga.
Kafin ma ta kai ga kiran Asp din ya kwarma ihun!!! da ya sanya wayar hannunta fad'uwa, ta juya
da sauri! kawai sai ta ga har ya cire zabgegiyar wukar dake rataye a dakin.......Ya fara da
dadurawa! a jikinsa, mussaman wuyansa.......
Ita kam tana ganin tashin hankali a rayuwarta! a kid'ime ta nemo number Asp din sai dai a
kashe take...........Ta juya ta sake kallonsa, bai fasa dadurawa jikinsa wuka ba yanayi yana
taune bakinsa.
Auran d'an tauri akwai tashin hankali! wallahi ita ta d'auka tuntuni ya bar harkar ganin ya kwana
biyu beyi ba.
Tsabar fargaba k'afafunta kasa daukar ta sukayi kawai ta zube kasan kafet ta takure jikinta guri
daya ta fashe da wani irin kuka! babban tashin hankalinta taga yana gurzawa jikinsa wuka gani
take idan rana ta 'baci wukar zata samu nasara!
Can ta hango wayarsa saman kujera, da sauri taje ta dauka, number Asp din dai ta nemo ta
kira shi, aka ci sa'a wayar ta shiga, tana kuka take sheda masa abunda yake faruwa......da yake
weakened ne yana gida ko minti goma ba'ayi ba ya shigo gidan.......ita ta shiga dashi Dakin tana
nuna masa shi yana nan yana Aikin abu daya ko gezau! domin wani irin karfi da kwarin jiki yake
ji a duk lokacin da wukar ta sauka a jikinsa.
Asp din ya durfafeshi da fadin.'' Ya isa haka! ni da nasan abinda zai faru kenan, da ban fada
maka ba, nasan dole ranka ya