Author : Binta Umar Abbale Category : Hausa Novels Story
kafadar ta sake mayarwa wannan karon gabadaya ta zuba hannayenta a cinyarsa.
Kallonta yayi babu walwala a tare dashi yace." Wane magani ki kasha."?
Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya nauyi da kunya ya hana ta magana.
A fusace! yace." Ko bakya ji ne."?
Ta kalleshi ruwan hawaye na kokarin zuba tace." Bafa magani nasha ba ka daina min tsawa! ka
kyaleni naji abunda ya dameni."
Ya sake tuge kafadarsa kanta ya sauka a karo na biyu, kallon ido da ido yayi mata kafin yace."
Zaki k'aryata maganar Likita kenan."?
Kasa had'a ido tayi dashi saboda kunya.
Yace." Ki fada min maganin da kika sha domin salwantar min da gudan jinana.
Hannu tasa ta share gumin saman hancinta sai ta fara inda-inda........."Bafa magani bane
gish.......Ta kasa karasa maganar sai shine ya 'karasa da fadin." *Gishiri!"?* kai ta daga alamun
"Eh."
Ya dinga girgiza kansa yana mata kallon mamaki kafin yace." Ya akayi kika san gishiri yana
zubar da ciki ko dama can kin ta'ba zubarwa."? yana sane yayi mata wannan tambayar.
Aikuwa ta kad'u! ta zuba masa ido tana masa wani irin kallo, maganar kawai take maimatawa
a zuciyarta *"Ko dama can kin ta'ba zubarwa.''?* shin me yake nufi?
Wasu zafafan hawaye masu azaba suka fara sauka asaman fuskarta sam ta kasa tsayar dasu
saboda zubarsu ne kwanciyar hankalinta
Ya kalleta sam bata bashi tausayi ba, saboda duk sanda zai kalli fuskarta sai ya tuna
ta'addancin da take kokarin yi masa.
Ya sha mur! babu fara'a yace." Ke shagwabbiya ko? daga anyi magana sai ki bude baki kina
kuka alhalin kice baki da gaskiya to ba kuka nace kiyi min ba cikakken bayani zaki min."
Tayi namijin kokarin had'iye kukan ta share fuskarta, zuciyarta na wani irin tafarfasa! tace."
Kace nayi abortion ko."?
Ya girgiza kai da fadin " Aa ni tambayarki nayi amsa zaki bani.
Ta had'iye wani kuttun takaici kafin tace." Kai zaka shedawa jama'a cewa ga yanda ka same ni
dan haka bani da lokacin yi maka bayani."
Tana gama maganarta ta tashi ta bashi guri. zuciyarta kamar ta fashe saboda bacin rai.
Tabbas da ta san irin zargin da zai biyo baya kenan to da ba ta dauki shawarar Sakina ba domin
tun farkon faruwar al'amarin tayi shawara da ita kuma itace ta tabbatar mata da cewa gishiri
yana zubar da ciki *Subahanallahi! ciki ko na haram ne ba'a san zubar dashi, ballanatana na
halak! dan haka a kiyaye dan Allah abi dokar Allah dan a samu zaman lafiya.*
*Ayi min afuwa banyi posting akan lokaci ba muna matsalar wutar NEPA ne NAGODEí ½í¹í ¼í¿»*
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:55 PM] Matar Malamí ½í¸Š: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*99&100*
Wani sanyi ne ya ziyarceshi yayin da yayi tozali da ita a hakimce tayi ado irin wanda yake
bala'in burgeshi, in ban da kamshi babu abunda take........Gabadaya wata irin kasala ta rufeshi
tsananin sha'awarta ya sake kamashi, shi dai yana bala'in son kamshin jikinta.
Kusa da ita ya zauna ya jifanta da wani irin kallo, ta marairace fuska tana kallonsa kafin tayi
masa barka da zuwa.
Ya dubi hannun da ya kone! tsigar jikinsa ta tashi, a hankali ya rike hannun ya fara tofa mata
addua ya gama ya kalleta cike da kulawa yace." Ke zanyi wa sannu duba da irin tsautsayin da
kika samu ta dalili na, tunda kika sheda min hankalina ya tashi ina Allah-Allah na iso gida naga
halin da kike ciki, amma abun mamaki sai na sameki cikin koshin lafiya kinyi ado da kwalliya irin
wanda nakeso ina mai tabbatar miki da cewar ina alfaharin kasancerki a matsayin matata."
Murmushi tayi tare da jin dadin kalamansa, dama kuma babban burinta bai wuce ace ta siye
zuciyarsa kaf ya daina ganin ko wace mace a gabansa ba sai ita, ta lura yana da sau'kin kai!
kuma ta fahimci ya kamu da tsananin sonta wannan abin alfahari ne a gurinta.
*****
Da safe kafin ya fita gurin aiki yake sheda mata tafiyar da za suyi, sam ba tayi tunanin cewa har
da ita za'ayi tafiyar ba, sai da taji yana fadin." Za ku kwana biyu a k'auyen domin kisan 'yan
uwana suma su sheda ki sosa.''
Sai ta kasa 'boye bacin ranta! ta dan 'bata fuska tana kallonsa.
Ya fuskanci ba tayi na'am da tafiyar ba, ransa bai masa dadi ba.
Ganin taki yin magana ya sanya ya tashi da niyyar fita.
Ta kalleshi a lokacin da yake gyara f-cap din kansa. da kyar tace." Sai ka dawo."
A dakile ya amsa ya kama hanyar fita zuciyarsa duk babu dadi, sam bai ji dadin abinda tai masa
ba, ya lura har yanzu ba ta k'aunar a halinsa, a ganinsa duk soyayyar da take nuna masa a
banza take, mutukar ba zata kaunaci yan uwansa ba.
Ya saba kiran wayarta idan ya samu saukin aiki amma a ranar sai ya share ta yana so ya nuna
mata kuskuranta
B'angaranta kuwa ba wai zuwa 'kauyen ne ba taso ba,cewar da yayi zata zauna tare dasu har
na tsayin wasu kwanaki shine abinda ya 'bata mata rai! gaskiya bata tunanin kwana a kauyen
'kafarta-'kafarsa.
Da taji shuru bai kira ta ba, sai ta kira shi, ya daga yana shan k'amshi.
Murmushi tayi kafin tace." Fushi kake ko darling."
Gyaran murya kafin yace." Fushi akan me? a halinki ai ba sabo bane a gurina."
A shagwabe tace." Au! mugun hali ne dani."?
Yayi shuru bai ce mata komai ba.
Ajiyar zuciya ta sauke a sanyaye tace." Kayi hakuri ba wai bana so naje bane naji kayi maganar
kwanaki shine bana so."
Ya fusata! yace." Kin ga idan ma ba zakije ba kiyi zamanki okey." Kawai ya kashe wayarsa.
Ta dinga bin wayar da kallon mamaki! ita fa yanzu kwata-kwata bata bukatar abunda zai shiga
tsakaninsu, amma ta fahimci akan 'yan uwansa zai iya cin mutuncin kowa.
A'a! abu kamar wasa 'karamar magana na nema ta zama babba! fushi yake da ita sosai! dan
koda ya dawo daga gurin aikin bai shiga gurinta ba, ya gama duk abunda yake ya nufi
sashensu Uwale, zuciyarsa duk babu dadi.
Koda taji shuru bai shigo ba, sai ta yanke shawarar zuwa gurinsa, tunda zuwa yanzu ta san ya
dawo, ita sam ba taga abun fushi da 'bacin rai ba, bata gudin 'yan uwansa. halinsu ne kawai
abun gudu.
Koda ta shiga gurin nasa, Babu shi babu dalilinsa. amma akwai alamun ya dawo yayi wanka
sannan ga 'karamar wayarsa nan a saman drowar.
Kai tsaye gurinsu Uwale ta nufa domin tana da tabbacin yana can.
Abunda taci karo dashi ya kusa tarwatsa mata zuciya, amma sai ta jajurce! tayi kokarin danne
mugun kishin da yake taso mata.. tayi musu sallama.
Su biyu ne a falon, Uwale na daki domin gabatar da sallar magariba, shima dawowarsa kenan
daga massalancin, ya samu Hamra'un ta shirya masa lafiyayyan towon farar shinkafa da miyar
kubewa d'anya wacce taji bushashshen kifi da man shanu!
Ya dinga shi mata albarka domin yini cur bai ci abinci ba, tun breakfast din safe, b'acin ran da
ya fita dashi ya ha nashi cin wani abu.
Tana zaune durshan a gabansa bayan ta zuba masa abincin yana ci tana bashi labarai sai
dariya yake sai kace mata da miji.
A zabure! ta kalli bakin kofar! suka had'a ido, bahaushe yace (Mara gaskiya ko a ruwa gumi
yake) duk sai ta daburce! tayi gaggawar matsawa daga kusa dashi, shi kam ko gezau!
abincinsa kawai yake ci amma ya amsa sallamar bai dai kalleta ba.
Ta zauna kujarar dake kallonsa da fadin.'' Ranka ya dade ashe ka dawo."?
Ya dago kansa yana kallonta da mamakin sunansa da ta kira shi, sam bai mayi tunanin za tayi
masa magana ba, saboda ya san azabar kishinta.
Da yake Namijin duniya ne babu kunya yace." Eh na dawo kina raina yanzu nake maganarki a
zuciyata."
Taji kamar ta fada masa bakar magana! amma sai tayi shuru kawai tana masa wani irin kallo na
tuhuma!
Saurin sunkuyar da kansa yayi! duk dadin towon a bakinsa yaji ya fice masa daga rai!
Hamra'u kam! simi-simi ta kama hanyar d'akinta! tana ta wani kumbura fuska shigowar Gimbiyar
ya 'bata mata rai mutu'ka! domin ta katse mata jin dad'inta.
Ya kalleta da fadin." Ya zaki tafi baku gaisa ba.
Ya'ke tayi ta juya da fadin." Aunty Gimbiya ina wuni."?
Tace." Lafiya lou ina Uwale."? Kafin ma ta bata amsa Uwalen ta fito da carbi a hannunta, ganin
Gimbiyar yasa ta washe bakinta, sosai tayi farin cikin ganinta a zaune babban burin ta ace
Gimbiyar ta saki jikinta dasu.
Hamra'u kasa tsayuwa tayi a gurin da sauri ta shige dakinta, ranta idan yayi dubu ya ba'ci, ita
dai tana kishin yanda Uwale ke nuna kauna da kulawa akan Gimbiyar.
Cikin mutuncin da girmamawa suka gaisa da juna.
Ta kalleta da fadin." Ya jikin naki jiya Ai yake fada min kin 'kone a hannu har nake cewa zan
shiga na dubaki Allah bai bani iko ba."
Tace." Ai ba sosai na k'one ba, kuma tunda yayi min addua gurin ya bushe ya daina ma zafi."
Tace." Duk da haka dai ai kin tsallake tsautsayi! kin ma yi kokari abunda ba ka saba a kansa ba,
ai dole ka sha wahala."
Murmushi tayi amma ba tace komai ba.
Da farin ciki a maganarta tace." Mijinki ya sheda miki gobe za muje 'kauye ko "?
Fuska a sake ta amsa " Eh ya fad'a min Allah ya nuna mana goben lafiya."
Tace." Ameen ai yana da kyau kema ki saba da dangi shiyasa da yace shi ba zai kwana ba,
nace to ya zama dole ke ya barki tare damu domin 'yan uwa su sheda fuskarki ai riga an zama
d'aya."
Tace." Hakan yayi insha babu matsala ta b'angare na, ina tare daku."
Kallonta yayi yana mamakin furuncinta.
D'auke kanta tayi dan tunda suke maganarsu bata kalleshi ba saboda masifar haushinsa da
take ji.
Uwale sarkin hira da labarai na ban dariya ta dinga bata labarai irin na da! ta dinga dariya tana
mamakin kokari irin na mutan da! ace Mace ta haihu amma unguwar zoma ta fita yawan nama!
ita abun ma dariya ya dinga bata.
Ganin kamar sun manta dashi a gurin yasa ya tashi domin zuwa ya kwanta a gajiya yake tilis!
Ta kalleshi da fadin." Ya zaka tashi kuma."?
Yace." Eh mana to zaman me zanyi kun manta dani kuna hira bakwa sani a ciki zanje na
kwanta ne."
Dariya tayi irin ta tsaffi! kafin tace." To ai gwara ka kwanta ko ka tashi da wuri nima nafiso muyi
sammako."
Yana kokarin fita yace." Uwale ai ke yau bana tsammanin zaki iya bacci ."
Ta fashe da dariya da fadin." Me zai hana zanyi wanda ya sawwa'ka dai ai dole nayi zumudi
UMARU wata da watanni ba tare da 'yan uwa ba." Da al'ajabi ta k'arasa maganar.
Girgiza kansa kawai yayi kafin yace.'' Sai da safe kenan ya kalleta bata da niyyar tashi su
tafi......."A nan zaki kwana ne."?
Ya jefa mata tambayar hannunsa na rike da handle domin bude kofar.
A nutse ta mik'e ta kalli Uwalen da fadin." Sai Allah ya kaimu." Ta amsa da "To Allah ya tashe
mu lafiya Alla ya bamu alkairi."
Kusan a tare suka amsa kafin ya bude kofar ya fita ta bi bayansa.
Kowa sashensa ya nufa, bata tsammanin bin sa domin yanda zuciyarta take a tunzure! bata
tsammanin
zasu wanye lafiya. munufiki ne har yanzu akwai abunda yake 'boye mata.
Wanka tayi ta sanya kayan bacci tayi kwanciyarta tana tunanin irin hukuncin da za tayi masa
cikin ruwan sanyi, abu d'aya za tai masa ya shiga damuwa! shine ta hana shi kanta wannan
shine babban tashin hankalinsa, tabbas zai kawo kansa anan za ta fanshe in yaso yaje gurin
yarinyar ta bashi kanta, tunda yana zuwa yaci abincinta a boye.
Washe gari da wuri ta gama shirinta sosai ta had'a musu tsaraba cikin baggo, sai da ta shirya
tsaf sannan ta zauna domin karyawa.
Lokacin ya shigao cikin farar shadda kar! wando da riga iya gwiwa da wani irin tsadaddan aiki
a wuyan rigar da hannu. yayi kyau sosai rashin sanya hula shine yai masa cikas, da alama
bashi da ra'ayi ta sosai.
Ta kalleshi ta 'kara kallo, yana da kyau sosai sai yanzu take tantancewa dole mata su rikice a
kansa, itama tana masifar sonsa saboda yana da baiwar da ba kowane namiji ne ke dashi ba.
Abinda take rayawa a kansa shima irinsa ne a zuciyarsa, duk kwanan duniya 'kara sonta da
kaunarta yake a zuciyarsa.
Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta gaishe shi a sanyaye.
Babu yabo babu fallasa ya amsa yana gyara agogon sarkar dake hannunsa, yace." Har kin
shirya kenan."?
Shuru tai masa bata ce komai ba. ta cigaba da kurbar tea din dake gabanta.
Saboda neman magana sai ya kai hannu yana so ya dauke cup din.
Ta kalleshi da fadin." Ya haka kuma."?
Yace." So nake na sha."
Murmushi kawai tayi ta sakar masa cup din.....ya dauka ya kai bakinsa dai-dai bakinta ya
shanye tas!
Ta yunk'ura ta tashi daga gurin.
Ya bi bayanta da kallo a lokacin da take kokarin shiga dakin, yawu ya had'iye ya lumshe idonsa!
bayanta kad'ai ya isa ya gigita duk wani namiji lafiyayya dama mara lafiya.
Bayanta yabi jikinsa duk yayi la'asar! ya same ta tana kokarin nad'a lifaya a jikinta.
Yaje gurin da fadin." Bakya jin zafi zaki nad'a wannan bayan kayan dake jikinki." Yana maganar
yana ha nata abunda take.
Ta kalleshi da fadin." Zafi kuma."?
Kansa ya daga da fadin."Eh ana zafi a gari ko bakya jinsa ne."?
Ta san neman magana yake da ita kawai sai ta cire lifayar ta ajiye, hijab ta d'auko amma bece
komai ba. sai abun ya bata mamaki ganinta kamar a yanzu zai magana tunda a zahiri kamar
hijab din zai fi lifayar zafi, amma bece komai ba sai aukin kallonta yake gabadaya kwayar
idonsa ta sauya! ganin haka yasa da sauri ta kama hanyar fita tare da fadin." Wannan jakar
baggo din ka fito da ita kaya ne a ciki."
Da hannu ta nuna masa, yabi gurin da kallo kafin ma yayi magana ta fita daga dakin. Zazzafar
ajiyar zuciya sauke kafin yasa hannu ya dauki bakkon ya bi bayan ta da tunanin wani abu a
ransa.
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:55 PM] Matar Malamí ½í¸Š: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita