GOJE part 3 Complete Document by Binta Abbale-1.pdf

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Hausa Novels Story

Chapter   1 / 13

1 to 3K   out of 37.7K words

[3/26, 9:55 PM] Matar Malam😊: *GJSR*
*77&78*
*PROBLEM!*
Sakamakon tsintar gawar matashiyar budurwa a bakin hanya ya tashi hankalin duk wanda ke
zaune a cikin 'kauyen *KUYAN TA INNAH!* saboda abu ne dai ta'ba faruwa ba, shiyasa
hankali kowa ya tashi mussaman maigari da uban yarinyar, cikin tsantsar tashin hankali da
damuwa suka nufi cikin gari domin sanar da hukuma don ta gabatar da binkice akan gawar
yarinyar da kuma abunda ya janyo mutuwarta.

A nan binkice ya nuna cewa fyad'e akai mata wanda ya janyo har ta rasa rayuwarta, maihafin
yarinyar dai kasa daurewa yayi kawai ya zube a gaban gawar yana share hawaye hakika
wanda ya aikata wannan ta'annati ya cika mara imani, mara tsoron Allah domin kuwa idan ba
mai bushewar zuciya ba to babu wanda zai aikata wannan mugun ta'addanci...........Duk
binkicen da ake gudanarwa an kasa gane wanda ya aikata mummunan aikin, domin wanda ya
aikata mugun abun dashi da jama'arsa dasu ake gudanar da binkicen kuma suna sawun farko
gurin nuna alhininsu da kuma tashin hankalinsu, domin dai dasu din ake binkice shiyasa babu
wanda ya d'ora zarginsa a kansu domin duk sun rufe wata kafa da zata nuna cewa su d'in
bara gurbi ne a cikin al'umma.
Wannan al'amari ya girgiza jama'ar dake cikin wannan 'kauye kasancewar abu ne da bai ta'ba
faruwa ba, sai dai su ji labarai a redio da sauran kafafan sadarwa.

******
Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ya gama cinye hutunsa ya fara shirye-shirye komawa
bakin aikin...........A cikin kwanakin da sukayi a tare sun d'an samu jituwa da juna sun rage fad'a
kusan koda yaushe suna tare idan dare yay kuwa sai sunyi romancing din junansu suke jin dadi
wannan shine mataki na farko da ya janyo musu samun jituwa a tsakaninsu.
Wani irin so take masa a can kasan zuciyarta, wanda take jin bala'in kishin duk macan da zata
kusance shi, sosai da sosai ta sanya ido a kan sa da duk wani motsinsa.........Ganin haka yasa
shima ya kiyaye baya amsa kiran Hamra'u a gabanta, amma suna tare da juna kuma har yanzu
da akwai kudirin auranta a zuciyarsa.
Tana sonsa amma ta kasa nuna masa son a aikace, ta sake shi sasakai bata san ci da shan sa
ba, ba tasan idan ya dawo daga aiki ta masa sannu da zuwa ba, ba tasan tayi masa kalamai
masu dadi ba, akwai gyara masu yawa a cikin al'amuranta.......Yanda ya fahimceta ita kawai
su shiga bargo daya suyi romancing shine abunda take so a gare shi, wanda shi kuma a nasa
bangaran ba haka yake da bukatar rayuwar auransu ya kasance ba, yana so ta zama
*Mar'atussaliha* wato mace tagari mai ladabi da biyyaya da kuma kiyaye dokokin ubangiji.

Tun yana yaro yake da burin auran nagartacciyar mace mai hankali da nutsuwa da sanin ya
kamata, sai gashi kuma hakan bai samu ba, wacce Allah ya had'ashi zama da ita tana da
nakasu a kowane 'bangare, domin ba ta cika addininta ba, ballanatana ta san meye
hukunce-hukuncen aure..........To wannan shine dalilin da ya sanya yake da burin auran

Hamra'u domin duk ta tara abubuwan da yake da bukata, amma kuma a can k'asan zuciyarsa
ya fi jin uwargidan nasa.


Lafiya kalau suka rabu ya fita daga aiki, ta koma sashenta cikin farin ciki da annushuwa yanzu
ta manta da boyayyan masoyinta tunda tana samun abunda take kulafuci a gurin mijinta,
shiyasa ko ya turo mata da text bata kula shi dama a rashin uwa akanyi uwar daki.......Ta iske
hadimanta na aikace-aikace a falon, suka zube har kasa suka gaisheta kafin ta wuce
ciki........Shigarta dakin da minti biyar Marakisiyya ta shiga, ta kalleta da fadin." Lafiya."?

Sunkuyar da kanta tayi kafin tace." Ranki ya dade ni kam wannan al'amari ya ishe ni wallahi,
shiyasa kawai na yanke shawarar fada miki domin kiyi wa tufkar hanci."

Gabadaya ta mayar da hankalinta gare ta da fadin.''Marakisiyya fada min ko meye."?

Tace." Kullum sai bayan kin fito daga can bagaran maigidanki ita kuma nake ganin gilmawarta
a gurin ban san me yake kai ta ba, ranki ya dade ya kamata ki tsawatar mata."

Gabadaya yanayin ta ya sauya gabanta banda faduwa babu abunda yake kishi ya rufe mata ido
tace." Wai kina nufin Hamra'u ko kuma wa."?

Tace." Kwarai ranki ya dade ita nake nufi kullum da safe sai ta shiga sashen."

Wani irin gumi ya fara karyo mata mussaman a saman hancinta.

Tsaye ta mike ta gyara lifayar dake jikinta, hanyar fita ta nufa ranta a masifar 'bace!


Aikuwa a bude ta samu sashen bayan tare suka fito dashi ya rufe har bakin mota ta raka shi sai
da ta tabbatar da cewa ya fita daga Barack din sannan ta nufi gurinta , ashe munafurtar ta
suke, a'ina yarinyar ta samu key din gurinsa.

Ta tura dakin ta shiga ido suka had'a tana tsakiyar gadonsu da sunan tana gyarawa, ganin
Gimbiyar yay bala'in gigita ta, mara gaskiya ko a ruwa gumi yake, itama ta san abunda take
bata kyautawa amma ta na yin hakan ne domin ta kafa gwamnatin ta.

Ta sakko daga gadon da rigar fillo a hannunta, a sanyaye tace." Aunty Ina kwana."?

Ba ta amsa ba, ta nufi inda take cikin tafiyar isa da k'ama.!


Ta daure ta tsaya domin bata tsammaci cewar hukuncin mari ne zai biyo bayan zuwanta gurin
ba kawai taji saukarsa a kumatunta, ta zabura! ta dafe gurin da fadin." Me nayi miki zaki mare

ni."?

"Ubanki ki kayi min."! tafad'a jikinta na wani irin rawa!!

Ta nuna kirjinta da fadin." Ubana fa ki kace."?

Tace." Eh don ubanki! waye ya baki ikon shigo min turakar miji."!

Ranta ya 'baci! tace." Kada ki kara zagina domin idan ki ka sake zan rama turakar mijinki kuma
dama tun kafin kizo gidan nake shigowa ina gyara masa saboda haka ke baki isa ki hana ni
shigowa ba."

Tace." Ban isa na ha naki shigowa ba.''? kai ta gyada alamar E.

Tarin belt din da suke rataye a jikin hanga ta fizgo daya, kawai ta shiga zabga mata a jiki ta
ko'ina.................. Wannan shi ake kira ba zato! ba tsammani, Hamra'u da gudu ta fice daga
dakin, itama ta bita da gudun tana cigaba da zabga mata blet din da fadin.'' ' Yar iskar yarinya
mara kamun kai kawai ni zanyi maganin ki duk sanda na k'ara ganin kafarki a dakin nan sai nayi
miki abunda yafi haka."
Hamra'u na kukan bakin cikin ta isa sashensu kawai sai ta zube a kujera tana rusa ihu!
kafafunta da saman wuyanta shatin belt rad'au! ya fito..
Jin kukanta yasa Uwale fitowa daga daki, hankali a tashe take tambayarta abunda yake faruwa.

Kasa yi mata bayanin komai tayi ta tashi ta shige d'aki tana share ha waye.......Wayarta ta
dauka ta kira shi...........Ya daure ya bar abunda ke gabansa ya daga wayar, jin alamun kuka a
tare da ita ya sanya shi mamaki yace." Hamra'u menene ya faru kike kuka kiyi shuru kiyi min
bayani."
Da k'yar tai shuru tana sauke ajiyar zuciya ta shiga sheda masa irin cin mutuncin da matarsa
tayi mata.

Ransa a 'bace a kan me ta dauki belt ta zane ki, ke kina me har zaki zauna ta doke ki."

Hanci ta shaka kafin tace." Kawai dan ta same ni a dakin ka ina gyarawa shikkenan tayi min
wannan cin mutuncin."


Yace." Kiyi hakuri wannan ba hujja bace, kuma idan na dawo gidan zanji dalilinta nayi miki
wannan tozarcin! saboda haka kiyi hakuri insha Allah zanyi maganin abun."


Ajiyar zuciya ta sauke da fadin."Shikkenan tunda kace haka Allah ya dawo da kai lafiya."

Ya amsa da "ameen ya Allah kafin ya kashe wayarsa."

Sosai ransa ya 'baci da abunda tayi, a ganinsa ai ba wani abu bane, tunda ita ta kasa d'aukar
ragamar ayyukansa to bata da hujjar da zata hana wani yayi masa hidima dole ya nuna mata
kuskuranta idan bata so wata mace ta kula dashi to tayi gaggawar gyara kuskuranta.


Yana ganin kiran wayarta yaki d'auka, ta kira ya kai sau goma amma bai daga ba, hankalinta
ya tashi mutuka domin ta tsani ta kira waya a share ta a ganinta da gayya yayi mata hakan.

Hawayen takaici ta share kafin ta kira Aunty Zeey sama-sama suka gaisa da juna, ashe
kowacce da abunda yake damunta aunty Zeey din ce ta fara yi mata complain akan Madam
uwargidanta sai d'ura mata ashar take tare da fadin." Ta asirce Asp din sai abunda tace yake
aikatawa.

Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Aunt Zeey ni a ganina naki mai sauki ne tunda kishiyarki ce
kuma ke kika sameta a gidan, ni kuwa fa wata 'yar iskar yarinya 'yar 'kauye tana cin
dunduniyata ban sani ba, ashe kullum tana tare da mijina kamar matarsa tana zuwa sashensa
ta hau gadonsa da sunan gyara wannan abu ya 'bata min rai mutuka da gaske."
Aunty Zeey din ta dinga kurma ashar kamar bamagujiya tace." Kici uwar shegiya! wallahi kada
ki saurara musu gabadaya ki tashi hankalinsa har sai kinji abunda yake tsakaninsu."


Ta ciji yatsa da fadin." Aunty Zeey ni kadai na san irin bala'in da za muyi a yau wallahi sai naji
dalilin zamanta a gidan nan sannan zai sheda min dalilin da ya ha nashi daukar waya ta."


Tace." Yaushe kuwa zai dauki wayarki bayan ta ki rashi ta sheda masa karya da
gaskiya.........Kada ki saurara musu wallahi."

Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke cikin ranta take raya irin dambarwar da zasu buga idan ya
dawo gidan.



Tsaf ta shirya tayi gayu cikin wata dakkakiyar shadda dinkin sinigal aiki a ko'ina wuya hannu da
kasan rigar, ta zuba gold a ko'ina hatta da yatsun k'afa babu wani cikakken kwalliya a fuskarta
amma tayi wani bala'in kyau tamkar fure kowane dressing tayi yana kar'bar jikinta.........rufaffen
takalmi tasa a kafafunta ta yafa mayafi irin na sarauta kai tsaye sashen nasa ta nufa tana
zabga k'amshin turare fuskarta babu walwala ko ta gamin gafara.

Bai dawo ba tukkuna ta samu kujera ta zauna tana cika da batsewa sa'i da lokaci tana kallon
agogo wani sa'in shida na yamma a gida take masa amma yau har ta gota shiga da ashirin bai
shigo ba.

Ta mike kai tsaye window ta nufa, tana daga labulan motarsa na shigowa barrack
din..............Ta sauke ajiyar zuciya tare da kurawa motar ido har ta isa gurin da aka tanada
domin ajiye motoci.

Direban shi ne ya bude masa motar kafin ya fito da wasu takardu a hannunsa, ya tsaya suna
magana da direban kafin ya bashi hannu sukayi musabaha da juna.

Labulan ta saki ta koma ta zauna kan kujera tana tsumayin shigowarsa.


'Kamshin turaranta ne ya daki hancinsa, ya dan lumshe idonsa kafin ya bude ya saukesu a
kanta tana hakimce! 'kafa daya kan d'aya.

Abunda yake 'kara rikita shi a kanta gayu da iya ado yana san irin kwalliyar da take
masa.......Munanan halayenta ne kawai abun gudu.


Yanayin sa ya gyara domin shi din ma bai shigo da wasa ba, ya bude baki yayi sallama cike da
karsashi! da kwarin gwiwa!

Ta amsa a ciki kamar ba taso.

Bai saurareta ba kai tsaye bedroom d'insa ya nufa ba tare da ya kalli inda take zaune ba.


Tayi 'kwafa tare da bin bayansa.

Yana kokarin cire uniform din jikinsa ta shiga ta same shi, ya kalleta itama ta kalleshi dauke
kansa yay yaje ya rataye kayan, toilet yake kokarin shiga maganarta ta katse shi.

." Ina so zanyi magana da kai."

Ya juyo ya kalleta na second biyu kafin yace." Ina da uzuri a gabana yanzu sai an jima tukkuna."

Wani malolon abu yazo ya tsaya mata a wuya! ko kafin ma tayi wani yunkuri ya shige toilet ya
bar ta da b'acin rai!


Koda ya fito bai kalli inda take ba ya fara hidimar shirya jikinsa, yana jin ciwon yanda ta bar shi

sasakai komai shi yake wa kansa.

Ta iske inda yake cikin bala'i! da neman fitina! tace." Kasan abunda ya faru shiyasa kake wani
dauke kai saboda rashin gaskiya, to da kai da yarinyar duk zanyi maganinku dan bana shiri da
munafiki."

Ya kalleta da bacin ran maganarta yace." Eh na san irin rashin mutuncin da ki kayi wa 'yar
mutune me ta tsare miki daga gyara kayan ki zaki dauki blet ki doke ta, meye hujjarki ta aikata
hakan"?


Tana numfarfashi! tace." Saboda ta shigo min turakar miji shiyasa nai mata wannan hukuncin
kuma wallahi ko yau ta sake shigowa dakin nan sai naci ubanta."!!

Ya ja mata tsaki! tare da kokarin ratse ta ya bar gurin......Tare shi tayi har jikinsu na
had'uwa......Murya na rawa tace." Wallahi ba zan yarda da wannan munafurcin ba sai ka fada
min tsakaninka da ita domin tun baya yau ba na fahimci akwai wata alaka a tsakaninku."


Ya jima yana kallonta da tsananin 'bacin rai a tare dashi yace." Kin ga *ZINA* bana bukatar
'bacin rai a yanzu kada kiyi sanadin da zai janyo mana samun matsala, tsakanina da Hamra'u
idan lokaci yayi zaki sani."


Tace." Bana jin tsoro ko shakkar 'bacin ranka munafurci ne bana so kawai ka fad'a min abinda
yake tsakaninka da ita idan babu wata alaka to wallahi sai ta tattara kayanta ta bar gidan nan
domin zamanta bashi da amfani."


Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Ke baki isa kisa Hamra'u ta fita a gidan ban ba, domin tun kafin
ki zo muke zaune da ita, alakar dake tsakanina da ita kuma lokaci ne zai nuna miki."!


Ta fashe! da kuka tana dukan kirjinsa da fadin.'' Wallahi na fad'a maka sai dai ka za'ba koni ko
ita domin ina zargin wani abu, wallahi kaji na rantse da Allah ba zan hada kishi da ita ba."

Tana kuka sosai take maganar tana kuma cigaba da dukan kirjinsa!

Gabad'aya jikinsa ya mutu ya dinga kokarin rik'e hannuwanta ta fuzge da karfi! ta kama hanya
da sauri ta fice daga dakin tana share hawaye........Gefan gado ya zube tare da dafe
kanshi.......Hohoho!! *ZINATU PROBLEM!!😃*

*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:55 PM] Matar Malam😊: *GJ*
*79&80*
Ya jima dafe da kai yana tunanin hanyoyin da zai bi gurin ganin ya kawo gyara da zaman lafiya
gidansa, maganar gaskiya dole yarinyar nan ta gyara kuskuranta mutukar tana so ta zauna
lafiya dashi to tilas ta kula dashi da duk bukatunsa, amma baya tsammanin zai hana Hamra'u
hidima dashi mutukar ita din ba tayi wani abu akan al'amarinsa ba, idan yaga ta mayar da
hankali gurin bashi kulawa to da wayo da dubara zai iya dakatar da ita Hamra'un akan abunda
take cewa ta bari tukkuna har sai an daura musu aure.

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke yana yun'kurin tashi kiran Asp ya shigowa wayarsa, sai ya
koma ya zauna yana laluben wayar a cikin aljihun rigar dake jikinsa.

Sam bai tsammaci jin maganar daga gare shi ba kawai sai yaji yana tuhumarsa akan abunda ya
faru a tsakaninsa da yarinyar.


Ransa yayi mutukar baci da jin irin tuhumar da Asp din yake masa dan haka sai yayi saurin
katse shi a kaurare yace......."Asp kada fa ka manta da cewa wannan yarinya da ake magana
akanta itace za'bi na tuntuni ita nake da ra'ayin aure kafin maganar Gimbiya ta sanyo kai, mai
yasa kullum idan yarinyar nan zata kawo maka k'orafi baka bin ba'asi idan an bi ta 'barawo to
abi ta mabi sawu, yarinyar nan har yanzu bata cika mace a gidanta ba, domin kuwa akwai
sangarta da lalaci a tare da ita, duk wasu hanyoyin kula da miji ba ta san su ba, shin laifi ne dan
Hamra'u tayi min hidima? dama can ita take kula dani kafin wannan al'amari ya faru saboda
haka don Allah mu bar maganar nan domin kai kanka kasan gaskiya kake takewa saboda
gudun bacin ran mara gaskiya."

Asp din jikinsa yayi sanyi yace." Umaru duk abunda ka fada gaskiya ne to amma ba kayi la'akari
da gidan da yarinyar nan ta fito, kasan dai gidan sarauta ba komai sukewa kansu ba, komai yi
musu ake dole ta samu na'kasu ta wannan bangaran, ba wai ina goya mata baya bane nima
nasan gaskiya, amma lamarin mata akwai rikici bana so wannan matsalar ta hargitsa maka gida
domin 'karamar magana tana iya zama babba! shine dalilin da yasa nake baka shawara kayi wa
tufkar hanci tun kafin lamari ya 'baci abunda nake nufi anan shine ita Hamra'u ta janye jiki daga
duk wani abu da ya shafe ka ta bari tukkuna ku mallaki juna ina ganin shine maslaha a
tsakaninku."


'Karamin tsaki yaja da fadin." Asp dacewa ne ace yarinyar nan ta d'auki belt ta zane yar mutane

dashi? ko kuma dacewa

1 / 13