Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
dauki hawa Dokinnan da
muhimmanci bana jin ko aikinka kana maida hankali haka a kansa.
Balle kuma sallah da ibadar Allah, na tabbatar suna wuceka, alhalin kana bisa sabgar
Dawakai, wadanda su kadai zasu tserar da dan adam ranar lahira ba wasan tseren Doki ba”.
Sai kuma Nenne ta dakata kadan sannan ta sassauta murya ta koma yin magana wannan
karon cikin lallashi da lumana, ganin yadda Prince ke wani irin yamutsa fuska akan zantukanta,
baya so take cewa baya ibadah sai hawa Doki.
A ganinsa yana baiwa kowanne lokacinsa yana kokari kwarai wajen kiyaye sallah a duk inda
ya samu kansa. In akayi la’akari da irin schedules dinsa. Yana irin nasa kokarin a ganinsa.
“Magana ta domin Allah, Hammansu, ka maida kan ka kamar wani tsuntsu mai tashi
sama kan fiffike, yau baka nan gobe baka can duk don hawa Doki?? Ni menene a cikin hawa
doki ne? Ka ki tsugunnawa a wuri guda ka fuskanci rayuwa ta reality. Saboda Allah yaushe
rabon ka da zuwa aikin Hajj don sauke farali balle umarah da take sunnah? A tunanina duk wata daukaka, ko suna da kake nema cikin wannan sana’ar ina ganin zuwa
yanzu daka mallaki kofunan Zinare sau ba adadi a sanadinta, in ban yi kuskure ba kofunanka
sun kai biyar, ko shidda, ina ganin ai ka gama samun daukakar Polo kuma Hammansu.
Ko tunanin aure da aje iyali baka yi wanda shine wajibinka a rayuwa ta hakika kuma mai
ma’ana ga dan adam, ba don komai ba sai don saboda hawa doki ne kadai a ranka, ka manta
cewa harka fita shekarun kuruciya da jimawa ka shiga na girma, don ma dai bakayi kama da
shekarun ka ba; you are still looking fit and healthy”. Nenne ta kara kwantar da murya yadda dole dan nata ya tausaya mata, tace “Abdulrasheed
ko tausayina baka ji, duk faccalolina sun ajiye jikokin ‘ya’yansu maza ni ko daya babu, ba don
Taiwo ta bani ba, jikoki ba da saidai kowa ya riga ni tarawa, har wadanda sukazo a bayana, ga
maganganun nan marassa dadi da duniya ke yi akan ka suna dawowa kunnenmu, haka ‘yan
uwan ubanka suma suke yimin irin tasu tijarar a kanka, suna ganin ni na hana Ubanka kara
aure har tsufansa, haka zai mutu da mace daya kamar rai sai kace auren zobe, kai kuma dana
haifa mun daure maka gindi kana yawon tambada da lalata a duniya ka ki cika Sunnah, kana
gudun aure wanda yake sunnar Annabi SAW.
Ka ki ko tsayawa kayi tunanin ya kamata ace a wannan matakin na rayuwarka kana da yara
lafiyayyu har guda uku ko hudu.
Yau dai tunda Doki ya kusa hallaka ka kana ji kana gani, ina ganin ya kamata ka hakura
dashi haka Kehinde! Babu sauran alfanu kuma a cikin hawansa”.
Prince AbdulRasheed ya muskuta ya gyara kwanciyar sa cikin jin azabar zafin ciwo irin
na hadewar kashi, yace.
“Nenne bana so ko kadan kike sakawa kanki damuwa akan abinda at least kin riga kin san
bazan iya bari da sauki ba.
Polo ya zama wani bangare na jikina Nenne, ina yi ne kawai don jin dadina da biyan bukatar
sha’awata ga wasan Polo, amma ba don tara kofuna ba, yana debe min kewa yana hanani
tunani yana kuma hana ni damuwa da komai, ba don neman wani abu kuma nake Polo ba ko
da can balle yanzu da nake da aikin yi kwakkwara, don haka banaso kina damuwa da
ance-ance din mutane wadanda basu da gadonka. Su mutane ai al’adarsu ne damuwa da
abinda bai shafesu ba.
Abinda ka kwashe rabin shekarun rayuwarka kana yi yana da wuyar bari a dare daya kuma
farat daya Nenne. Kimin addu’a, idan inada rabon barin hawa Doki in bari a hankali.
Nenne nifa zan iya ajiye aikina na refinery dungurungum! In rungumi wasan Polo shikadai.
Idan Doki shine ajalina haka Allah ya kaddara min Nenne”.
Yayi dan shiru yana dan haki, na zafi da zogin ciwon karaya, kafin yace “Nenne tun
shigowarki bakiyi duba da halin ciwo da nake ciki ba, sannan ko jajen raunin da SAHEEB yaji
baki yimin ba kin hau ni da fadan rashin aure anya Nenne?
Ki godewa Allah da ban zarce ba, na barki da ciwon rashina bana rashin aurena ba.
Kimin addu’ar samun sauki da gaggawa kinji Nenne na, ki daina damun kanki akan abinda
banida rabo a cikinsa, ki roka min tsahon rai da lafiya mai amfani mu rayu tare, yafi min rayuwa
da wata mace, tunda ba wani abun kunya na ke yi a yawon hawa Dokin nawa ba, sha’awa ce
kawai, hobby na ne kawai yin wasan Polo. Amma ba haka kawai rana daya kice lallai in bar abinda nafi so a rayuwata ba, wai don
tsautsayi ya gitta min wand aba yau farau ba, kuma mutane suna maganar banza a kaina da
ke, ina ruwana da maganar mutane?
Ko an gaya musu inada business da mutane su yabe ni ko su zage ni?
Aure ra’ayi ne, kuma banida ra’ayin yinsa a yanzu, tunda dai auren nan Sunnah ne ba farillah
ba”.
Nanne sai ta zama speechless, ta rasa me zata ce masa kuma, duk ta inda tabi don Kehinde
ya gane damuwarta da ciwon ranta akan rashin aurensa bazai gane ba, ta yarda kuma babu
abinda zai sa AbdulRasheed barin Polo, idan wannan karairayewar da ta sameshi yanzu, basu
saka ya barta hakannan ba. Ta kuma yarda bashi da niyyar yin aure nan kusa, aure baya ransa kwata-kwata, baya cikin
burikansa da fatansa na gaba, burinta na samun jikoki daga jikinsa, bata san ranar da Allah zai
dubeta ya cika mata shi ba.
Wayar Murjanatu ce ta katse tunanin Nenne, ta boye dan guntun hawayen da ya tsatstsafo
mata. Hankalin sa kacokam ya koma kan waya da Aunty Taiwo dake ta koka jin abinda ya
sameshi ta waya tana zata taho itama yana ta zauna ai ya ji sauki, yana lallashinta da taushin
murya, yana gaya mata ta san dai ba yau ya fara faduwa a Doki ba, shi nasa ciwon bai daga
hankalinsa ba kamar lafiyar SAHEEB dinsa.
**** **** ****
Zaman jinyar Nenne da Fatima tare da AbdulRasheed a asibiti, ya taimaka matuka gaya
wajen samun lafiyarsa da wuri, sakamakon addu’o’I na (Ayatushshifa) da Nenne takeyi kullum a
ruwa tana bashi yana sha dare da rana, da kuma dorewar lafiya da take roka masa a duk bayan
kowacce sallahr farillarta. Ya fara jin sauki sosai cikin ‘yan kwanaki kalilan, har yana tashi ya zauna yayi sallah daga
zaune, bakin Nenne baya hutawa da yi masa nasiha akan bin Allah da tunasar dashi soyayyar
Manzonsa, saidai in basu kadaice a dakin jinyar ba.
Har ila yau Nenne bata gushe ba da nasiha sannan bata fasa ba. A kullum bata gajiya wajen
nuna masa muhimmancin aure da ajiye iyali ga faein ciki da cigaban rayuwarshi, cikin nasiha da
lumana, ta kan ce masa ‘ya’ya sune gatan bawa duk arzikinsa, tunda su zasu dinga yi masa
addu’a a bayan ransa. Kuma su tsaya masa a sanda yake bukatar su. Auren kuma da yakewa kallo na daban Nenne tana kokari wajen nuna masa cewa ibadah ne
ba son rai bane.
Koma meye dalilinsa na gudun yinsa bai isa dalili a wurin Ubangiji ba, tunda dai ya bashi
lafiya da abinda lafiya zata amfana.
Tace ana yinsa ko ba’a so domin katange kai daga sabon Allah da tsarkake kai daga daudar
zinah da katange zuciya daga sha’awar aikata sabo kowanne iri ne.
Wadannan sune ire-iren kalaman Nenne Sappa ga danta Prince Abdulrasheed lokacin
jinyarshi. Princess Fatima kuma ita ke bashi abinci a baki da cokali.
Yau daya gama cin abincin rana, Princess Fatima tana gyara masa filon da zai kishingida ta
bayansa, a cikin tarin sumar kansa sai ta hango tsillin ‘furfura’ a cikin gashin kansa. Ta kai waje
guda 20 a cikin lallausar sumar kansa, ta kuwa ce me zata yi ba sakin shakiyyar dariya ba.
Princess Fatima tasa hannu ta tsigo furfura guda daya daga saman kansa, tana dariya tana
kanne ido ta nunawa Nenne, tana fadi cikin yanayi na (banter) harda neman sikewa don dariya,
“someone has finished, ooh my Dear! Getting white hair before even getting a first wife…
Nenne furfura ce fal! A kan Hamma!”. (Ta kara gishiri).
To ma yanzu sabida Allah Nenne, wacece zata yarda ta auri mutum over 40 kansa duk yaci
furfura?
Ai saidai kwantan ‘yammata kamarsa dan (mid forties), irin bazawara mai ‘ya’ya biyu haka, ko
widow (wadda miji ya mutu ya barta) haka dai, amma ba dai (sweet 16) ba!”.
Nenne an sosa mata inda yake mata kaikai, sai ta gyada kai tace “in ya samu sweet 16 din
sai ki hana ruwa gudu! Furfura baiwa ce ‘yar nan, ba itace tsufan namiji ba, wani ma sai ya fara
ta yake fara jin mazantaka da karfin samartaka, rashin aure haka kawai babu dalili shine
mishkilarsa, domin tamkar izgili ne ga rahamomin da Ubangiji yayi maka Abdulrasheed. Saidai kuma bansani ba ko abinda mutane suke fadi marar dadi a kanka din, ko gaskiyane
Abdulrasheed?”
Yanayin fitar sautin muryar Nenne, a halin yanzu ya nuna helplessness din da take ciki akan
situation din, wanda hakan yayi matukar karya zuciyarsa, jikinsa yayi sanyi matuka, amma dai
bai yi magana ba.
Princess Fatima, ganin yanayin da suka shiga na damuwa su duka, sai ta dauki ipad dinta ta
bar musu dakin, ta koma can reception na asibitin ta samu kujera ta zauna tayi tagumi itama,
don taga zancen na Uwa da Danta ne, kuma yau raunin Nenne da bakin cikin ta na shekara da
shekaru akan rashin aurensa yafi na kowacce rana bayyana a tare da ita da nauyin shekarunta
da suka bayyana kan kyakkyawar fuskarta yau saboda damuwa.
Wai AbdulRasheed ya fara furfura ba aure!!!
Wannan al’amari ya tsorata Hajiya Sappa matukar tsoratawa.
Fitar Princess Fatima keda wuya, sai ga hawaye mai kauri ya tsinke a fuskar Nenne Sappa.
Kamar jira take Fatima ta gusa.
Hankalin AbdulRasheed yayi tashin da bai taba yi ba yau, ba yau Nenne ta soma korafi da
kuka akan rashin aurensa ba, amma na yau yafi na kullum daga hankalinsa ko mai yasa? Don
ya ga bakin cikinta muraran a idanunta.
Abdulrasheed ya shiga rokon Nenne cikin kaskantar da kai, akan ta gaya masa menene
exactly damuwarta har haka akan rashin aurensa, take irin wannan zafafan hawayen dalilinsa,
masu barazanar tarwatsa rayuwarsa?
“Zubar hawayenki a kaina Nenne masifa ne a gareni kin sani”.
Nenne Sappa saida ta yi sharbe son ranta, tana gogewa da habar hijab dinta. Kafin ta soma
Magana cikin rauni da karaya.
“Na soma zama cikin zargi mai girma a kanka nima!
Na soma yarda da zargin da duniya ke maka, na cewa neman maza ‘yan uwanka kake yi
(you are gay) shine abinda yasa ka juyawa auren Sunnahr Ma’aiki SAW baya. Haka ne ko ba
haka bane Kehinde?”
Nenne ta tsatstsareshi da jikakkun manyan idannunta da suka rine kamar garwashi suke jike
shatab da hawaye mai yawa.
Ko kadan babu firgita kan kalamanta a tare da shi, ko don ba yau ya fara jin ana zarginsa da
hakan ba? Jin maganar yau daga bakin mahaifiyarsa shine babban abinda yafi tada hankalinsa.
Amma ko kadan babu tashin hankalin maganar akan fuskarsa sai tsantsar damuwa da
yanayin da mahaifiyarsa ke ciki.
Abdulrasheed yace (cikin despair).
“Nenne in kowa zai min wannan mummunan zargin ke UWATA (mahaifiya) ya kamata ki
kyautata min zato.
Ban taba zaton Nenne ranki zai yi bacin da zakiyi duba da wannan banzan zargin na mutane
marar tushe da hujja ba, tunda kin san irin tarbiyyar da kika yi mun da hannunki, ba wani ya
tarbiyyantar miki ni ba, kuma kinada tabbaci a kan ingancinta, na cewa ko bayan ranki bazan
zubar da ita ba, balle da ranki da lafiyarki in yi wannan mummunan aiki.
Anyway, bazan musa ko daya ba, cikin abubuwan da ake zargina dasu din.
Allah ne kadai ya san zahiri da badinin zuciyar bayinSa, da abinda suke aikatawa na fili dana
boye, kuma shaidarsa nake nema bata mutane ba Nenne, tunda ke kanki da kika haifeni kin
kasa shaidata….…”.
Yayi shiru, ya koma ya kwanta yana maida numfarfashi da sauri da sauri kamar mai ciwon
asthma. A hankali AbdulRasheed ya rufe idanunsa…. Mummunan ‘scene’ din na Hasinah da
dan uwansa kuma wanda ya rika a matsayin “amini” duk cikin family dinsu Adetokumbo akan
gadonsa na gilma masa. Abinda ya faru kusan shekaru goma sha hudu a baya, amma har yau
yake ‘haunting’ dinsa… ‘trauma’ din abun ya kasa barin ransa ya huta, zuciyarsa ta sake da
mata.
Cousin dinsa Adetokumbo Abdulfatahi Akanni da fiancée dinsa Hasinah Ambursa turmi da
tabarya, kuma a kan gadonsa sannan a dakinsa mallakinsa a gidansa dake kasar Japan.
Wani ‘incidence’ ne da kullum yake komawa ‘GREEN’ a idanunsa… ya kasa barin duhun
idanunsa su huta ko hasken wata mace ya ratsa ta cikinsu.
Shikuwa me zaiyi da mata yanzu? Ai ya dade da rufe babinsu daga kan Hasinah Bello
Ambursa.
A cewarsa dukkansu are nothing but ‘Gold-Diggers’, wadanda in dai namiji zai basu kudi to
ya gama samun mutuncinsu, kowanne kare da kowanne doki ma yazo ya fanshi mutuncinsu da
diyaucinsu in dai yana da kudi.
A tasa mummunar fahimtar da ya dade da yiwa mata daga kan Hasinah, wadda ta dade da
yin babakere a zuciyarsa ya gama yardarwa kansa duk matan yanzu irin Hasinah ne, masu son
holewa ta jiki data aljihu, ya yarda mafi akasarinsu namiji daya ba zai taba isarsu ba, batare da
sun zagaya sun ci amanarsa ba ko me zai musu na halacci kuwa, ko me zai basu iya karfinsa
don kula da lalurorinsu, kuma koda zai yagi naman jikinsa ya basu bazai hana su hango wanda
ya fishi samu ba, they are totally greedy, rashin wadatar zuci ya yiwa zakatan ‘yammatan yanzu
katutu, babu soyayya ta saboda Allah a zuciyarsu yanzu.
Shiyasa yake ganin bashida mata a duniya, ba’a haifi macen da zai kara gangancin so ba,
bazai kara yarda da mace a duniya da sunan soyayya ba in ka cire soyayyar da yake yiwa
Nennensa da ‘yan uwansa mata. Bai ki ba dai a gidan aljannah in yana da rabo.
Me yasa mostly kyawawan mata kamar Hasinah ne kullum suke yin dage, domin hango wani
wanda bai kama kafar mijin da Allah ya basu a komai ba? Marasa shararren kyau zaka samu
basu cika dage ba.
Me ya rasa da Da namiji ya rasa daya cancanci abinda Hasinah tayi masa? Me Tokumbo zai
nuna masa banda cikar aljihu a lokacin?
Idan har aljihun wani namiji dan uwansa ne zai sa Hasinah yi masa haka, to kuwa duk matan
duniya ya dade da yi musu jimilla da ‘gold-diggers’, kwadayayyu, hadamammu, ma’abota manta
halaccin mai halacci, wadanda burinsu kawai namijin da zai basu kudi suyi bushasha, ba wanda
zai so su saboda Allah ba, kuma wanda zai kwatanta irin soyayyar da suke so ta banza da da
sunan itace soyayyar da zata bulle dasu, koda kuwa ace babu abinda Allah ya rage ka dashi a
rayuwa.
Ya rasa wane irin jin dadi mata ke nema a wurin namiji fiyeda daya. Shi kuma Allah da ya
halicceshi yayi shi mai matukar kishin kansa da kishin macen da yake so, watakila shine dalilin
da yasa daga kan Hasinah ya daina sha’awar kowacce mace sai Polo dinsa, yanada kishin
kansa fiyeda yadda harshe zai iya bayyanawa!
Nenne ta rainesu akan turbar tsoron Ubangiji, tana tare dasu ko bata tare dasu suna tuna
Allah, ta rigada ta dorasu akan turbar gujema ketare iyakokinSa.
In aka duba kuma, a rayuwa ba abinda bai yiwa Hasinah ba, a matsayinta na wadda yaso
aure da dukkan zuciyarsa ba tareda tunanin banbancin nasabarsa da tata ba, kuma marainiyar
da ya fiddo daga gidan marayu, ya maidata daliba mai ‘yancin higher education, ta hanyar
sponsoring karatunta daga gidan marayu zuwa Lagos eventually zuwa kasar Japan ba tareda
sanin kowa nasa ba bayan Taiwo.
Bayana fara karatunta na jami’a ya zama shine uwarta shine ubanta