Aisha Saddiqa Part 1 by Sumayya Takori.pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 14

15K to 18K   out of 41.2K words

sha’awar soyayya ba, bai
kara sakawa ransa son yin aure ba, ya tattara maganar aure da mata ya tura su can wani gefe
mara amfani na shafin rayuwarsa, ya zamo yana cigaba da playing Polo for fun and pleasure da
kuma debe kewa kadai. Amma aikin da ya samu da (Qatar Petroleum Refinery) bayan kammala
PhD dinsa akan (Oil and Gas Engineering) yasa dole ya bar kasar Polo ta Argentina ya tare a
Qatar, sabida aikin refinery yafi cinye lokacinsa yanzu fiyeda wasan Polo.

A halin yanzu da yake da shekaru arba’in da biyu a duniya, Engnr. AbdulRasheed Idris
Akanni, zamu iya cewa ya gama accomplishing komai na daukakar aiki akan Oil and Gas, tunda
yana kan matsayin ‘Star Engineer’ na ‘Qatar Refinery’, AbdulRasheed ya gama cika duk wasu
burika na rayuwarsa, saura kaiwa makura a gasar Polo wato (10+ goal handicap). Kudi yake samu kawai daga kasashe daban-daban ta harkar Polo da kuma aikinsa, har bai
san abinda zai yi dasu ba, babu Da, ba jika, balle matar da zata taya shi mora (babban tashin
hankalin iyayensa kenan). Don haka AbdulRasheed ya himmatu wajen aikin alkhairi ga ‘yan
uwansa mata guda uku musamman Taiwo, ya tsaya musu, ya tsayawa cigabansu, baya barin
iyayensu su yi musu hidimar komai ta karatu kota yau da kullum, balle mijin Taiwo da yake da
kankamo sai ya zamanto komai nata shine, har ila yau yana raba arzikinsa da iyaye da ‘yan
uwansa na Uwa dana Uba (duk da kasancewarsu ba mabukata ba). A gefe kuma a boye,
Prince Abdulrasheed ya dage wajen tallafawa gidajen marayu dana gajiyayyu a kasarshi
Najeriya inda a irin haka ya samo HASEENAH.
A halin da ake ciki yanzu (he mainly consults for the refinery) fiye da zama a ofis yayi aiki.
Don haka ne yake samun lokacin da yake fita ‘tournaments’ kadan-kadan, to really play his
passion which is ‘Polo’. Amma dai rayuwarsa yanzu tafi yawa a birnin Qatar.
Wannan shine tarihinsu Prince AbdulRasheed da iyayensa, ‘yan uwansa, da komai da ya
shafi rayuwarsa ta yau da kullum, rayuwar da kowa yake kallo masa a matsayin ‘incomplete’
wato wadda ba cikakkiya ba, mai wawakeken gibi, duk da tarin achievements din da ya cikata,
da tarin arzikin dake cikinta musamman mahaifiyarsa, Kakarsa da mahaifinsa da ‘yan uwan
haihuwarsa gabadaya suke cikin damuwa da rashin cikarta, domin kuwa har zuwa wannan
lokacin da ya tasamma shiga shekaru 43 ba wanda ya san dalilin sa na kin yin aure ko yin
budurwa in ka cire Murjanatu.
Wanda ya zamo na jikinsa sosai ne kadai zai iya gane cewa, duka lokutansa na yanzu ya
mallakawa wasan ‘POLO’ ne, da kuma aikinsa na matatar man fetur, sannan Prince yana
ibadah musamman ta yawan azumi a gidansa, ba abinda duniya ke zarginsa dashi ne a
gabansa ba. ​ **** **** ****

HEARTBREAK
K
wanaki uku kenan da yin wayarsa da ‘yar uwarsa Murjanatu. Kwatanta halin da Abdulrasheed
yake ciki a kwanaki ukunnan bazai yuwu ba, he is frustrated and heartbroken, kasancewar babu
kowa a tare dashi shikadai ne a gidansa sai mai yi masa hidimar share-share da goge-goge da
girkin abinci, daga shi sai zuciya da kwakwalwarsa suke aiki a kwanaki ukunnan, don haka suka
taru suke ta kitsa masa duk abinda suka ga dama akan mata da al’amarinsu. Mai kyau da
maras kyau. Shaidan ma yana taka rawarsa wajen gaya masa mata duka mazinata ne ya fita
harkarsu. Babu wata soyayyar gaskiya in existence. Hakan yasa tunaninsa mafi rinjaye duk ya
gurbace akan diya mace.
Abdulrasheed ya kullaci mata da soyayyarsu kowace iri ce, ta aure kota watsewa duk ya
barranta kansa daga ciki, daga yau ya nesanta kansa da kowacce iri. Ya tsani taimako, duk da
in tunanin hakan yazo masa yana cewa (astagfirullah). Ya zo ya tsani yarda da duk wata mace.
Shaidan ya cigaba da ribatar sa yana gaya masa ai duk mata irin Hasinah ne marasa godiya,

maciya amanar kauna, kuma marasa tsarki na jiki dana zuciya.
Saboda shi mahaifiyarsa ta dade tana cusa masa wani irin tsoron zina, tun sanda ya fara
balaga, ta taso dashi da upbringing mai kyau cikin hikima da lallami take cusa masa kin zina,
sau tari tana yawan gaya masa cewa ko mata nawa yake so kuma ko ‘ya’yan wa yake so a
sarauta da arziki, haka kona talakawa ne yakeso zasu aura masa indai akwai nagarta da
kykkyawar nasaba.
Amma ya taimaki kansa da su kada ya kusanci zina a rayuwarsa, sabida ita zina bashi ce
wato dattinta naso yake yi a cikin zurri’a, da wannan belief din ya girma a ransa, duk da
Haseenah taso ta wargaza wannan tufkar da Nenne ta dade tana yi a zuwanta Japan.
Amma yau Hasinah tasa abin ya shafi har mu’amalarshi da kowa, don gani yake duk ‘yan
uwansa na wajen Uba ma irin Tokumbo ne wato mazinata ne (subhanallah), marasa la’akari da
girman ‘yan uwantaka da abokantaka da yarda da aminci in dai akan mace ne, idan babu tsoron
Allah ai ana barin halas don kunya. Watakila shiyasa iyayensu maza (musamman Dan Iyan of Ilorin, Babansu Tokumbo) ya damu
sai yayi aure cikin ‘ya’yansa mata kuma yafii kowa damuwa a takura masa yayi auren cikin gida,
ashe ya san ‘ya’yan nasa watsatstsu ne marasa tarbiya.
Hakika Tokumbo yaci amanar tarbiyyar gidansu. Ya saka a ransa ba shi ba aure a duniya
balle cikin zuri’arsu, kai duka matan duniya daga yau ya yafe su koda diamond aka kerasu, zai
rufe ido ya kauda kai daga kansu in dai tawali’unsa wajen zaben macen aure (did not yield a
positive result), wato indai kaskantacciyar hanyar da yabi wajen zaben macen aure bata sa ya
samu abinda yake tsammanin samu na macen da zata so shi ta girmama shi, ta kaunace shi
domin Allah ba.
Ya yardarwa kansa a can baya ‘ya’yan marayun sune zasu fi zama nagari saboda rashin
gatansu zasu iyawa maraicinsu, fiyeda ‘ya’yan masu arziki dana sarauta, wadanda yake ganin
baza’a samu masu tarbiyyar da yake so a cikinsu ba, da irin yadda yakeso matarshi ta kasance
ta so shi tsakani da Allah, sune yafi tunanin a cikinsu babu nagari, to ashe matan daga
kowanne tushe suka fito ba kwarya bane balle ya kwankwasa cikinsu ya zabi ta kwarai. Babu
wadda zaka ci wa alwashi akan soyayya, haka babu macen da zaka iya baiwa amanar
zuciyarka da soyayyarka a wannan zamanin ba tareda ta ci don abin duniya ba, a karshe zata
kekketa zuciyarka tabi ta kai ta tattake ba tareda tayi la’akari da tarin alkhairorinka gareta ba.
Da daddare Prince Abdulrasheed yana zaune a karamin falon gidansa da na’ura mai
kwakwalwa a gabansa da sunan aikin project dinsa zai cigaba, wanda ya dade da jinginarwa
saboda harkokinsa na Polo. Yau bacin zuciya da rashin abinda zai debe masa kewa yasa ya
dauko project dinsa yana son karasawa ko ya samu ya bar kasar Japan bakidaya, ko ya samu
ya huta da binbinin da Haseenah ke masa kullum na neman sulhu. Amma abin takaici ya kasa
tabuka komai daga aikin da yake son yi. Har zuwa lokacin zuciyarsa bata koma daidai ba,
amma dai ta rage tafarfasar da take yi.
Gidan Prince Abdulrasheed na Japan wanda ya kasance karamin ‘Penthouse Apartment’ ne
cikin birnin Tokyo, Kakansa Emir ne ya kama masa hayar gidan shikadai don kawai ya zauna
yayi karatu babu takura, baya son duka abunda zai takura takwaransa kuma jikansa na farko da
yake kira “Kehinde” wato Hussaini, don haka ne ya gwammace ya kama masa wannan
tsadadden gidan ya zauna a cikinsa shikadai yayi karatunsa cikin nutsuwa, maimakon ya zauna
cikin gidajen dalibai yana manejin rayuwa irin wanda galiban kowanne dalibi da yazo kasar ke

yi.
Shi da kansa ya san ko cikin zuri’arsu ta Sarki Abdulrasheed Abdullateef Akanni shi dan gata
ne, yafi kowa gata da samun kulawa da soyayyar Sarki. Prince yayi amanna da cewa, Sarki
Abdulrasheed na masa son da baya yiwa kowa cikin ‘ya’ya da jikokinsa, cikin zuri’ar Sarki
Abdulrasheed kaf dinsu shine na gaban goshin Kakan nasu. Hatta Taiwo da aka haifesu tare
saidai ta biyo bayansa a gun Emir duk da taci sunan mata mafi soyuwa a gareshi Olori
Murjanatu. Kai Sarki baima cika shiri da Taiwo ba don yakan ce halinta irin na Babanta ne bata
son shiga cikin dangi.
A kokarinsa na neman abinda zai kwashe masa damuwar da yake ciki, sai ya sake kunna
na’u’rar ya budo aikin ‘final project’ dinsa na kammala digiri na biyu, wanda shi ya rage masa, in
ya gama ya mika aka bashi certificate zai bar kasar Japan.
Wayarsa a kasha take tun jiya bayan sun gama magana da Taiwo, ya kasheta gabadaya ne
don tsira daga azababben kiran Hasinah, wanda take jefo masa shi a jejjere babu kakkautawa
sanda ya bar wayar a kunne, haka na Tokumbo ma yake shigo masa duk bayan minti, wani
zubin kiran nasu har turereniya suke yi da juna, amma ko kusa ya kasa dagawa dayansu, don
ya san maganar guda daya ce (hakuri zasu bashi) wanda bashi da amfani gareshi a halin
yanzu, me zasu ce masa bayan wannan? Ya riga ya gama (making mind) dinsa kan cewa babu
shi babu soyayyar mace bayan mahaifiyarsa! Babu shi babu soyayya da kowacce mace kuma.
Don haka tunda har zuwa lokacin zuciyarsa bata saki ba sai ya kasa tabuka aikin komai na
(project) din nasa, wanda daga shi ya hada masters dinsa a (Petro Chemical Engineering).
Har ila yau, Abdulrasheed yayi wani kuskure domin kasa furta addu’ar yayewar bakin ciki,
kamar yadda Nenne ta dade tana nuna masa cewa a duk hali makamancin wannan ya dimanci
addu’ar yayewar kunci da damuwa da Annabi SAW ya koyar, amma a yanzu bayan bakin ciki
har da shaidan ke jagorantar ragamar fushin zuciyarsa, yana controlling emotion dinsa da
grievance dinsa, yana gaya masa saboda abinda Hasinah tayi masa to daga yanzu bashi babu
kallon wata diya mace, koda da jan yaqutu (emerald) aka kerata, daga nan har gaban abada.
Daidai lokacin, kararrawar kofa (door bell) ta sanar dashi yanada bako a bakin kofa.
​ Kamar bazai tashi ba, don kafafunsa kansu sun yi masa nauyi, sabida dadewarsa a
zaune, kamar yadda zuciyarsa ma tayi nauyi mai yawa a cikin kirjinsa, ya dade gaban allon
kwamfuta (doing nothing). Baya tsammanin zuwan kowa a dai-dai wannan lokacin don a
saninsa bashi da appointment da kowa, amma ko mai yasa? Sai ya ji ya kasa kyale kiran kararrawar, don mai dannawa ya ki tsagaitawa da dannawa, ya
tashi ya taka a hankali cikin basarakiyar tafiyarsa, yana tafe cikin nutsuwa kamar bai son taka
kasa, wadda tafiyarsa ce wannan ta halitta.
Abdulrasheed ya bude kofar falon fuskarsa ba yabo ba fallasa. Ga mamakin sa sai ya ga ‘yar
uwarsa rabin ransa da bait aba kawo zuwanta a yanzu ba.
​ Doguwa kakkaura Murjanatu-Taiwo ce a tsaye, cikin bakar abayat, ta nade kanta da
dankwalin a bayar ta saka face-mask, wanda ya rufe fiyeda rabin fuskarta, Taiwo na rungume
da diyarsa (Kiki) Ruqayyat.
Kiki ta sha ado da ribbons mai kalar pink da yellow kamar ka sace ka tafi da yarinyar don
kyau.
Taiwo a Tokyo, unexpected, don kawai hankalinta ya gaza kwanciya da halin da yake ciki.
Hakika kamar yadda tayi tunani yana bukatar wani nasa kamar ta a gefensa, a dai wannan

lokacin, wanda zai tunasar da shi ALLAH! Da karbar kaddara.
Ko Nenne da Dade basu san da tahowar Taiwo Japan yau ba. Daga ita sai Toufeeq wato
mijinta suka shirya maganar tahowar tata da gaggawa don ta lallashi Abdulrasheed don ta san
shi bai iya daukan frustration da sauki ba musamman in yana ganin ka masa unfair treatment
da bai cancanta ba. ​ Hannu yasa kawai ya karbi Kiki daga kafadunta ya sumbaceta bayan ya bude kofar, ya
dan yiwa Taiwo (side hug), amma ya kasa boye feeling din dake kasan zuciyarsa na hakika ya ji
dadin ganin su a wannan lokacin akan basarakiyar fuskarsa.
Taiwo ta kama hannunsa ta rike cikin nata, a haka suka karasa tsakiyar madaidaicin
hadadden falon nasa, tana mamakin fadawar da Kehinde yayi, cikin ranta tana korafin duk
neatness din dan uwan nata da kullum zaka ga komai na gidansa tsaf-tsaf yana kyalli, yau
falonsa kaca-kaca, gabadaya ya canza daga dan gayun Kehinde din data sani cikin kwanaki
biyar kacal. Ta tabbata da kyar idan a duka kwanakin nan ya ci abinci kuma yayi wanka yadda
ya saba, balle akai ga zancen gyaran fuskar da bai bari da kasumba.
​ Ta yarda soyayya masifa ce (ga wanda bai yi sa’arta ba) sannan cin amana daga wanda
kake so, ka kuma yarda dashi da zuciya daya, ka wahaltawa rayuwarsa a lokacin da yake
tsananin bukatar taimako kamar Haseenah da Adetokumbo yafi komai lahanta zuciyar dan
adam wato (butulci). ​ Balle Abdulrasheed da zata rantse bai taba cin amanar kowa a rayuwarsa ba, mai
kirkine mai alkhairi ne shi, zuciyarsa mai kyau ce kuma mai tsafta ce akan kowa da komai,
komai zai yi ma mutum yana yi ne saboda Allah ba don ya rama masa ba.
​ Taiwo ko kafin ta ko huta kicin ta shiga ta samar masa abinda zaya ci mai zafi da nauyi
wato Amalar bawon doya miyar Ewedu data ji naman turkey da smoked fish zuku-zuku. Saida
ta tabbatar ta masa favourite food dinsa ya ci sosai ya sha tea na nescafe mai zafi, sannan ya
kishingida akan sofa da Kiki a gabansa yana wasa da ita. Ko a kwayar idonsa ta lura yunwa tayi masa lahani a kwana biyar ba kadan ba,
kasancewarsa mutum mai yawan cin abinci, kullum Nenne na cewa “his best friend is food”.
Idan akwai abinda yafi karyawa namiji zuciya toh Hasinah ta karya maza, ta karya zuciyarsa
raga-raga. A daren shi da Taiwo sun zauna sun kara tattaunawa kan al’amarin da ya faru dashi da
Hasinah, kuma Taiwo bata barshi da mummunan tunanin da ya riga ya tsirga ya samu muhalli a
zuciyarsa ba na cewa duk mata haka suke, tayi ta bashi baki da kwantar masa da hankali da
bashi kyawawan misalai iri daban – daban na halin lalacewar da al’umma ke ciki a wannan
zamanin, tace don haka wannan bazai zamo wani abin mamaki daga halayyar dan adam ba.
Taiwo ta kara da cewa “ka yarda ba kuma duka mata muka taru muka zama daya ba a
halayya da dabi’a, ta kara da nuna masa cewa Hasinah ba itace karshen rayuwarsa ba, sannan
ba itace autar mata ba, wasu matan ma nagari ko haihuwarsu ba’a yi ba, tace kada hakan yasa
ya fidda kyakkyawan fata akan mata tagari. A cewar Taiwo, “mata nigari yanzu aka fara
haifarsu”.
Shirmen Kiki ma ya taimaka kwarai wajen cheering dinsa up. Ya fara murmushi,
murmushinnan nasa mai matukar kyau da aji, da Kiki ta hau jan kasumbar daya bari a fuska
wadda bata saba gani a tareda shi ba, ya dan fara sakin ransa da mantawa da damuwar
Hasinah Ambursa don ita tafi bashi mamaki fiye da Adetokumbo wanda dama su maza ai

kunyarsu ragagga ce akan macen da zuciyarsu ta kwadaita musu.
​ Shikuwa Tokumbo Akanni a ranar bai kara kwana a Tokyo/Japan ba, yana jin karshen
shigarsa kasar Japan din kenan gabadaya, har dai in Abdulrasheed yana cikinta, duk da a can
ne harkokin kasuwancinsa suka fi yawa.
Taiwo da Kiki, basu baro Tokyo ba saida suka kwashe sati tare da Prince Abdulrasheed
(Kehinde), har sai da ta tabbatar Prince din ya manta da damuwar da Hasinah ta haddasa
masa, ya koma harkokinsa da rubutun project dinsa amma ko sunanta yace kada ta kara
ambata masa. A zahiri Prince Abdulrasheed ya saki ransa sosai yadda Taiwo keso, har ya koma harkokinsa
na baya ya soma duba schedules na tournaments, yayi kokarin da ya kammala project dinsa
kaf tun kafin barin su Taiwo gidansa. Musamman da komai Taiwo ke masa cikin gidan na kula
da abincinsa da tsaftar gidansa da lallashinsa shi kawai aiki yake wuni yi akan kwamfuta. Amma abinda Taiwo bata sani

6 / 14