Aisha Saddiqa Part 1 by Sumayya Takori.pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   12 / 14

33K to 36K   out of 41.2K words

Shine babba cikin family duka, amma yafi duk kannensa basu wahala akan maganar aure da
janyo musu magana daban-daban daga al’ummarsu duk akan rashin aurensa”.
Prince AbdulRasheed Idris Akanni, tunda iyayensa suka fara wannan cece ku ce din yake
sauraronsu, ya rasa irin amsar da zai bayar da zata gamsar da iyayensa maza hujjarsa ta
gudun aure a yau. Cewa mata sun dade da sire masa, bashi da wani buri a kan diya mace
yanzu, ba macen da zai kara so a rayuwarsa. Shin shi mai maganar cewa yazo ga kannensa nan a gida ya bashi wato, Abdulfatahi
Akanni, yanada masaniyar cewa dansa ne ya raba shi da mata bakidayansu???
Ko yanada masaniyar cewa dansa Adetokumbo ne yayi masa cin amanar data sa ya tsani
mata koda gold aka kerasu tun daga kan Hasinah Ambursa???
He is speechless a lokacin, sai zufa, jibi, da gumi da yake ta yankawa daga zaune cikin
kurkukun idanun iyayensa da suke zazzare masa su daya bayan daya irin nasu na jiga-jigan
yarbawa.
Da suka takura da jin ta bakinsa sai yace musu yana jin nauyin dukkanninsu, su yi masa
alfarma ya gayawa Nenne amsarsa in yaso ta gaya musu.
Ganin irin halin da ya shiga ne na rudu mai yawa da gigita yasa suka kyaleshi, domin sun
tado masa kwantaccen bacin ransa, aka yi addu’a aka rufe taron a haka.
Suka ce lallai a gobe suna jiran jin amsa daga bakin Nennensa, in ba haka ba, zasu dauki
matakin da ya dace ne kawai wanda shine aura masa kannensa mata hudu kuma a rana daya
daga cikin ‘ya’yansu mata.
Ita kanta Nenne din zille mata yayi ta yi basu hadu ba har ya koma Qatar. Ya san kuma
bazata jira zuwansa ba don a ranar da asubah zata tashi zuwa pilgrimage (aikin hajji) daga
hukumar alhazai ta jihar Lagos, kuma in ta tafi Hajj sai tayi kwanaki arba’in wato jirgin karshe
sannan take dawowa gida. Kafinnan ya samu ya yanke mai fishsheshi, su kuwa kannen Ubansa yasa a ransa bazasu
kara ganinshi nan kusa ba.

Bayan tashin Nenne zuwa Hajj, ya koma Qatar, ya cigaba da fuskantar aikin sa na (Oil
Refinery), wata irin rayuwa Prince Abdulrasheed keyi ta cikawa kai aiki a gida da ofis da
daukewa kai kewa a ‘stable’ din dawakansa a kowanne yammaci ta hanyar bankawa cikinsa
Nescafe (coffee) alhalin likita yayi limiting shan (coffee) dinsa, a cewarsa in ya sha yana jinsa
fresh babu damuwa ko kankani a cikin ransa, shan coffee yana kara masa kuzari, kwana biyu
dai bai hau Doki ba don har zuwa lokacin hadewar karayar jikin sa bata bar dan motsa masa
lokaci zuwa lokaci ba.
**** **** ****
ZAMAN HEMAR ALHAZAI A MINNA
N
enne Sappa, ta sauka a kasar Saudiyyah domin sauke farali na wannan shekarar tare da
diyarta autarta Princess Firdausi.
A zaman Hema ne na kwana uku da ake yi a Minna, ana zuwa jifan shaidan ana dawowa
Hema a huta ko ayi kwanan ibada, Nenne ta hadu da Haj. Zainab. Wadda tazo daga jihar
Gombe, maigidanta Malam Yunus ma’aikacin hukumar alhazai na jihar Gombe.
Ba Hemar su daya ba, don kamar yadda kowa ya sani ne Hema din (is state by state), Haj.
Zainab na Hemar Alhazan Gombe, Nenne tana Hemar Alhazai Yarbawa na jihar Lagos.
Wajen tafiya jifan Shaidan ne suka tafi tare, tafiya ce da alhazai ke yi mikakka wadda bata
karewa kamar bata da karshe, zuwa inda za’a jefi la’anannen Allah. Suna tafiya suna Hailala,
Princess Firdausi bata biyo su ba yau, tana kwance a Hema domin rashin tsarki da ya sameta a
ranar. Jiki na girma, tafiya tayi tafiya sai Haj. Zainab taga Nenne na neman faduwa, domin ba
karamin jigata tayi ba.
Sai ta kama hannun Nenne, ta karfafeta, tace “baiwar Allah don Allah mu dan tsaya mu sha
zam-zam ko ma samu karfin cigaba da tafiya.”
Nenne tace “kin kyauta diyata, ni fitsari ma nake ji”.
Suka sha zam-zam suka koshi, suka zagaya bayan wata Hema don shiga bayan gida.
Nenne Sappa ita ta fara shiga ta fito ta gama zata wuce ba tareda ta jira Haj. Zainab ta shiga
ba, don dama ba wai tare suke tafiyar ba a’ah, hanya ce kawai mai hadin zumuntar dole.
Da ta fito, bayan sun yi sallama ta kuma gode mata bisa kulawar data nuna mata. Har ta
gaya mata ita daga Lagos tazo, ita kuma tace mata daga Gombe tazo.
“Ashe ‘yar kasata ce, madallah dake. Nima asalina ‘yar Gombe ne, aure ne ya kaini jihar
Lagos”.
Sukayi sallama, Nenne ta wuce ta cigaba da tafiyar ibadah, Haj. Zainab kuma ta shiga toilet
din.
Har ta gama abinda zatayi ta fito, ta lura da bakar jakar nan ta guzurin mahajjata ta matar can
‘yar Lagos rataye a jikin kofar bandakin. Wato ta manta guzurinta gabadaya.
Ta dauka ta bude, yawan dalolin data gani ‘yan dari-dari a ciki ya firgitata, domin ya zarce
normal dalolin guzurin mahajjata da ake basu, daloli ne tsura abin tsoro da firgitarwa, domin ita
dai da idonta bata taba ganin irin wadannan takardun kudin a zahiri ba.
Da sauri Haj. Zainab ta fito ta duba hagu da dama, gabas da yamma, kudu da arewa babu
Hajiyar lagos babu alamarta, ta bace a cikin dubunnan mahajjata masu sanye da fararen kaya
da bakake kusan bakidayansu, kalar kayan jikin maza fari, na mata baki ne tako kasa gane ko

mai kama da ita.
Haka ta daure jakar nan a cikin jikinta taje ta karasa jifanta ta dawo Hemarsu, tana ta addu’ar
Allah Ubangiji ya hada fuskarta da Hajiyar Lagos kafin su gama zaman Minna su koma Makkah.
Dadin abun ma ba’a sayen abinci a Minna, da bata san yaya Hajiyar zatayi ‘coping’ a wannan
lokacin ba.
Duk inda ta ga ‘yar Najeriya sai tayi kokarin ganin fuskarta, ko Allah yasa ta dace da ganin
wannan kyakkyawar bafullatanar baiwar Allah, wadda haka kawai ta shiga ranta domin ta ga
tsantsar mutunci da kamala a tareda ita.
Washegari Haj. Zainab din tayi wani tunani, me zai hana taje Hemar alhazan Lagos ta duba
ta a can? Sai ta kira maigidanta wanda tare sukazo kasancewarsa ma’aikacin hukumar alhazan
jihar Gombe, sun samu kujerar Hajji ne ma sanadin aikin nasa ba karfine dasu cancan ba.
Maigidan nata Malam Yunus, tsohon malamin (federal government) ne da ya jima yana koyarwa
a makarantar sakandiren ‘yammata ta Bajoga, shekaru biyu baya Allah ya tarfawa garinsa nono
aka dauke shi aiki a Gombe State Pilgrims Board (ma’aikatar alhazai ta jihar Gombe).
Tun daga lokacin ne kuma suka samu damar da duk shekara yake samun kujerar hajji biyu,
karkashin hukumar alhazai don su zo su kula da mahajjatan Gombe a Saudi. Shine yake baiwa
maidakinnasa.
Da kyar ta samo Hemar ‘yan Lagos, bayan ta ci tafiya da zagaye a cikin Minna har ta gode
Allah. Haka Haj. Zainab tayi ta bin fuskokin mata Yarabawa daya bayan daya tana dubawa
amma ko mai kama da wannan kyakkyawar dattijiyar bafullatanar bata gani ba, ita gashi ko
sunanta bata sani ba balle ta tambaya, amma tabbas ta rike kamannin fuskarta da kyau. Ita
gani take ma fuskar na mata yanayi da wata popular fuska data sani ko a hoto ne ko a zahiri,
amma ta kasa gane inda ta san fuskar Hajiyar Lagos. (A rashin saninta, fuskar Haj. Sappa na
mata yanayin kama ne data Sarkinsu na Gombe, wato Uban Kasar Gombe na wannan lokacin,
wanda suke kamar an tsaga kara da Nenne Sappa, don shi ya sha nono ya saki ta kama.
Allah bai tashi hada su ba sai ranar hawan Arfah a kan dutsen ARFAH. Bayan Haj. Zainab ta
fidda ran ganin Nenne Sappa don damka mata dukiyarta. Har ta fara tunanin kaiwa hukumar
kasar Najeriya ta Saudiyyah kudin tayi musu bayani. Haduwar tasu a filin Arfah ya zo ne
indirectly ba tareda zaton kowaccensu ba. Addu’ar data ji matar bayanta ta daga hannu sama tana yi a fili ne ya ja hankalinta gareta.
Hannayenta biyu matar ta daga cikin kaskantar da kai ga Ubangiji da tsananin ikhlasi da
tawali’u cikin addu’arta, sannan cikin zubar da hawaye mai yawa a kan dutse mai alfarma na
Arfah, ranar da Ubangiji yayi alkawarin baya juyar da addu’ar bayinsa akan wannan
tsarkakakken dutse, taji matar tana yin addu’a ga haularta (abinda ta haifa) a fili cikin harshen
fulatancin Gombe ziryan.
“Ya Ubangiji ga Dana ABDURRASHEED dan IDRIS ABDURRASHEED (Kehinde),
managarcin bawanka mai kyautatawa iyaye da kula dasu, mai tsantseni wajen ibadarka da
kulawa ga ‘yan uwasa mata, mai yawan alheri ga danginsa da kyakkyawar zuciya ga kowa, mai
tarin halayen kwarai na kyautata zumunci. Na roke Ka, Ka dubi halin da Kehinde yake ciki na rashin aure. Ya Ubangiji ka yanke masa,
kasa yana da rabon yin aure a rayuwarsa, ka kare min shi daga duk wani nau’I na aikin sabon
ka a dalilin rashin aure, Ya Allah”.
Ta shafa addu’arta a daidai lokacin da take ji a zuciyarta Allah ya amsa mata, Mala’iku sun ce

Ameen Abdurrasheed zai yi aure, kamar yadda Hajiya Zainab dake bayanta ma tace “Ameen” a
fili, ta kuma tayata da shafa addu’ar itama zuwa tata fuskar cikin tausayawa, ganin yadda
Nenne ke kuka tana addu’ar.
Sai Nenne taji an dafa kafadarta a hankali ta baya, anyi mata sallama cikin nema mata
amincin Ubangiji.
Da far’a ta juya ta amsa tana share ido, kuma nan da nan suka gane juna. Suka rungume
juna suka sauko daga kan dutsen Arfah tare rike da hannun juna.
Hajiya Zainab ta kwanto lalitarta daga cikin jikinta, ta damkawa Nenne Jakarta hannu da
hannu.
“ga nan kudinki ne masu yawa da kika manta nake ta nemanki in baki. A bandakin da muka
shiga a Munna kika mantasu, na nemeki kamar ba gobe, har Hemar ku ta ‘yan Lagos naje
nemanki Allah baiyi haduwarmu ba, inata addu’a dai da rokon Allah ya hada mu cikin sauki in
baki, don in aka shiga Makkah bansan halin da zaki fada wajen sayen abinci ba idan babu
guzuri a tare dake, don kamar dukkan guzurinki yana cikin jakar nan.”
Baki Nenne ta saki tana mamaki. Ta tuna zunzurutun dalolin dake cikin jakar. Sai ta kara rike
hannun Haj. Zainab gam. Tare suka zauna akan kananun katifunnan na filin Arfah Haj. Sappa ta
rasa da bakin da zata godewa wannan baiwar Allah.
Abinda ya bata mamaki shine na farko da ganin matar ba wata wadata ce irin tasu a tareda
ita ba, amma ta iya wannan halin na mutanen kwarai, mai wuyar samu a wannan zamanin.
Dala na gugar dala da har dala dubu biyar ne a cikin battar, data kirga suna nan cif yadda ta
lankwasasu ta ajiye a cikin zip ko guda daya bata yi ciwon kai ba.
Ashe dama har yanzu akwai mutane masu wadatar zuci da gudun abun duniya irin haka?
Nenne Sappa, ta tambayi kanta domin kwarai Haj. Zainab ta burgeta. Kudine da Abdulrasheed
Kehinde ya bata domin tayi guzurin aikin Hajjinta dasu kamar yadda ya saba bata duk shekara.
Da ta tabbatar ta yar da su taji babu dadi amma bata yi mamaki ba sabida irin gajiyar datayi da
tafiya a lokacin a Munna, ji take kamar ta yanke kafafunta bakidaya ta yar, don suma sun mata
nauyi da kyar take iya cirasu, balle jakar guzuri.
Nenne da Hajiya Zainab basu rabu ba daga filin arfah ba sai da suka karbi adireshin junansu
na hotel din da kowacce take zaune a cikin Makkah.
Bayan sun koma Makkah Nenne ta soma tunanin me zata baiwa wannan matar a matsayin
kyauta ta jinjinawa, sabida taji dadin wannan halin kwarai data gwada mata har fiye da kudin
data maido mata. Nenne Sappa na matukar son mutum mai tsoron gamuwa da Allah, mai
gudun duniya mai cin halal. Don haka da taje sayawa Princess Fatima warawaran zinaren data bata sautu a kasuwar
Jiddah, sai ta sayi wasu warawaran (bracelet) again, sak irin na ‘yan biyunta Firdausi da Fatima
wadanda kudinsu mai kima ne da daraja sosai.
Data dawo daga Jiddah shagon zinaren kai tsaye ta wuce gidan ‘yan Gombe wato masaukin
‘yan jihar Gombe a Makkah.
Da yake ta rike lambar dakin da haj. Zainab ta gaya mata, sai ta hau lifta (elevator) ta isa har
kofar dakin, ta danna ‘door-bell’ daga ciki akayi mata iznin shiga sannan tasa kai ta shiga dakin
da sallama abakinta.
Nan ta tadda Haj. Zainab ita kadai a dakin dawowarta kenan daga Dawafi. Haj. Zainab tana
ganinta nan da nan ta shaidata, ta kuwa shiga lale marhabin da hidima da ita da duk abinda

take dashi a dakin na sakawa a baka, itace kawo Laban(Al-mara’i) itace kawo ‘Aseer’ wato jus
mai sanyi. Kai har Gahwah data koyi sha a kasar ta hada mata wadda ake kira (Gahwah
Al-Arabiyyah) ta zuba musu a kananan kofunan karau suka zauna a gefen gadon Haj. Zainab
suna sha sai suka balle da hira. Ko daga yadda Nenne Sappa take magana kadai cikin yanayi na kasaita Haj. Zainab ta
alakantata da Sarauta mai girma cikin zuciyarta, in kuma ba sarauta ba to da arzikin da ya
zauna a muhallinsa, komai na jikinta kadai dake walwali cikin zobban zinare ya fallasa hakan.
Sun dade suna hira kafin Nenne ta ce zata koma hotel dinta, don ta baro autarta Firdausi a daki
kwance bata jin dadi tun dawowarsu Arfah a nasu Fundaq (hotel) din. Ta ciro warwaron data zo
dasu a cikin battarsu ta damkawa Haj. Zainab a cikin hannunta.
Ta ce kyauta ce tayi mata don su rinka tuna juna in su koma garuruwansu mabanbanta. Tana
son mutane masu irin halinta na gaskiya da rikon amana. Sama da komai tsoron abin duniya.
Haj Zainab ta ce “ba’a maida hannun kyauta baya, don hakata gode”. Kuma duk da bata san
darajar wadannan warawaran ba, amma ko ba komai aka ce ido ba mudu ba ya san kima.
Tayi godiya mai yawa sosai ga Nenne, tanakokarin gwada warawaran, cikin ‘yar dariyar jin
dadin alkhairin da aka yi mata Haj. Zainab tace da Nenne.
“Yo ni wannan ai bazasu shiga hannu na ba, sun min kankanta na yara ne, sai dai in kaiwa
PETEL (AISHAH-SIDDIQAH), yafi kama da na ‘yan mata”. Nenne ta ce “har nawa kike da
bazakiyi kwalliya da awarwaro ba?” Nan ta daga nata hannun tana nuna mata nata warwaron
guda shidda tace “bana rabo dasu a hannayena don su din adon diya mace ne. suna karawa
kwalliyar mace kima su da zobuna, wacece Petel-Aisha-Siddiqah kuma? Halan kinada ‘ya
budurwa ne kema kamar su Fatima?
‘Yan biyuna (Firdausi da Fatima) na sayawa, shine kema nayi miki sha’awarsu”.
Cike da far’a Haj. Zainab tace “eh, inada Petel-Siddiqah a gida, itama ‘yan biyu ce, su biyu
aka haifa tun lokacin Hassanar ta rasu a wurin haihuwa, ita kadai ta saura mana.
Allah ya dora min iftila’in WABI, domin kuwa haihuwata goma amma AISHA-SIDDIQAH ce
kadai Allah ya bar mana a raye”.
“Allahu akbar!” Inji Nenne, “lallai dole ki so AISHAH-SIDDIQAH. Har nima yanzu zan tayaki
son nata, naji a raina ina son SIDDIQAH. Ajinta nawa yanzun?”
Murmushi sosai Haj. Zainab tayi tace “Petel na ajinta na biyar a makarantar gwamnatin
tarayya ta Billiri Gombe”. Sun dade a bakin kofar suna hirar Aishah, kafin Nenne ta karbi lambar
wayar Haj. Zainab ta gida Najeriya, da alkawarin duk ranar da Allah yayi mata shigowa Gombe
(kasancewar tana yin shekaru kusan biyu bata zo ganin gida ba), zata nemi Haj. Zainab har
unguwarsu su gaisa. Kafin dan lokaci kakkarfan kawance ya kullu tsakanin matan biyu a aikin
Hajjin bana.
Sati daya bayan nan Alhazai suka soma shirin komawa gida.
Ranar Asabar Nenne da Princess Firdausi suka koma gida Lagos. Yayinda Haj. Zainab jirgin
kusan karshe suka bi suka koma gida Gombe don saida aka gama kwashe ‘yan jihar su kaf.
**** **** ****
Tunda Haj Zainab ta koma Gombe Kusan kullum sai ta baiwa Maigidanta Mal. Yunus labarin
kawarta mai karamci Hajiya Sappa ta Lagos da suka hadu a Minnah, kawar da tayiwa Petel
dinta

12 / 14