Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
ba shine mummunar illar da incidence din yayi a zuciya da
tunaninsa, ya riga ya gurbata psyche na tunanin sa akan mata da soyayyar dukkan diya mace
in general.
Ranar da suka kwana bakwai tare dashi Taiwo da ‘yarta suka juyo gida Lagos cike da
kewarsa. Da alkawarin sai sun zo bikin kammala karatunsa nan da ‘yan watanni masu zuwa.
***** ***** ****
WACECE NENNE SAPPA?
N
enne (na nufin ‘Uwa’ kenan), da harshen fulatancin Arewacin Najeriya na sassan Gombe,
Adamawa da Taraba, wanda Hajiya Sappa ta fito daga cikinsu, kuma da shi yaranta ke kiranta,
Nenne Sappa, irin iyayen mun nan ne na zamanin da, masu halin zuhudu (gudun duniya),
taqawa, da tsananin yawan ibadah wadanda duk halaye ne na NANI OUMMANA. Mahaifiyar ta Nani Ummana ta kasance mace mai yawan kaskantar da kai, da gudun rudin
duniya, wadannan sai suka zamo halaye ne wadanda dasu ta raini Sappa, duk wani halin
tawali’u wato humbleness (a down to earth personality) Nenne Sappa ta hada shi cikin
kyawawan halayenta. Nenne Sappa ta kasance kyakkyawar dattijiya, fara ce kal, jazur da ita mai yalwar sumar kai,
gira data idanu, mahaifiyarta Nani bafullatanar garin Gombe ce don haka kusan zamu ce
kamanninta Sappa ta debo, wadda yawan shekaru baisa kyawunta ya gushe ba sabida hutun
da take ciki kuma jikinta mai boye shekaru ne, yanayin jikinta ya nuna cewa an zuba kyau da
farin jinin manyan sarakuna a zamanin kuruciya.
Kai kace Sappa ita ta zabarwa kanta duk wata kankanuwar halittar dake jikinta don kyawun
fasali, har zuwa yanzu data baiwa sittin da biyar baya, Nenne Sappa, na nan da extra added
beauty dinta (zallar kyawunta).
Kenan a takaice sai mu ce Nenne, (Hajiya Sappa) ta samo personality dinta na (Down to
Earthiness) ne daga mahaifiyarta Nani Oummana, wadda ta kasance uwargida a cikin duka
matan Maimartaba Uban Kasar Gombe, Sarkin Gombe na goma, wanda duk da kasancewarsa
basarake to gawurtaccen Shaihun malami ne shima. Nenne itace ‘ya ta biyu cikin ‘ya’yan da ya
haifa masu tarin yawa da matansa na aure hudu.
Cikinsu duka yafison Oummana da suke kira Nani wadda ta kasance mahaifiya ga Haj.
Sappa. Bayan rasuwar Sarkin Gombe wato mahaifinsu Nenne a dakinsu ne aka gaji sarautar.
A halin yanzu Yayanta da suka fito ciki daya ne akan karagar mulkin Gombe wato
Maimartaba Sarki AbdulYassar Jalloh Umar (CFR).
Tsohuwa Oummana ta cigaba da zama ne a dakinta bayan rasuwar sarkin Gombe Ahmadu
Jalloh Umar, yayinda sauran matan da yake da sauran kuruciyarsu duk suka fita suka sake
aurarraki. Don haka ta zama uwa ga ‘ya’yan sarkin Gombe bakidaya wadanda ta haifa da
wadanda bata haifa ba wato diyan kishiyoyinta duk ta hada ta rike ta mayar nata don yanzu
babu iyayensu mata a gidan.
Sarki AbdulYassar babban dan Nani Oummana shi Hajiya Sappa ke bi haihuwa, sai autan
Nani Abdulmajid wanda ke kasar Morocco da iyalinsa, sukenan ‘ya’yan da Nani ta haifawa uban
kasa, sauran ‘ya’yansa maza da mata guda goma sha biyu duk na kishiyoyinta ne amma
bazaka taba iya banbance wadanne ne wanda Nani Oummana ta haifa da wadanda take rikewa
marigayin mijinta ba, saboda adalci da halin dattaku irin na mutanen da.
Da irin wadannan kyawawan halaye Nani Oummana ta raini diyarta Sappa mace daya
(Nenne Sappa) cikin maza har itama ta girma suka aurar da ta ga zuri’ar Akanni’s tun
mahaifinta yana raye, har itama a yanzu gashi ta tara nata bataliyar iyalin.
A yadda Hajiya Nenne take gudanar da rayuwarta wajen kula da tarbiyyar ‘ya’yanta hudu
dake gabanta, sak halin mahaifiyarta Nani Oummana, ba bazaka taba cewa ita din ‘yar Sarki
kuma jikar Sarki, sannan matar babban dan Sarki, uwa ga jikan Sarki na farko bace.
Sabida yadda take nuna musu gudun duniya da mantawa da madaukakiyar nasabarsu, ita
dai burinta shine su bi Allah, su kasance masu tausayawa mara karfi, su kiyaye sallah akan
lokaci, su nisanci zinah kowacce iri kowanne nau’I ce, wannan itace tarbiyyar Nenne kullum ga
yaranta hudu, duk wani burinta a yanzu shine ya zamo cewa halinta suke kwaikwayo, halin
kankan da kai da tawali’u, shi takeso Taiwo da Kehinde da kannensu twins mata guda biyu wato
Firdausi da Fatima su siffantu dashi.
Amma me? Cikin ‘ya’yan nan nata guda hudu kowa halinsa daban da nata, babu mai irin
halinta na kaskantar da kai. Suna gudanar da rayuwarsu ne bisa tsari na ‘ya’yan manyan
sarakuna da irin tarbiyyar gidansu na Akanni’s wato yadda suka taso suka tarar a masarautarsu
ta Ilorin. Kakansu Sarki Abdulrasheed da kansa ya taba cewa Nenne ta haifo masa jikoki masu
halaye daban-daban da yake tinkaho da dabi’unsu na sarauta. Abdulrasheed baya rayuwa irin
wadda take so, baya zama a kasarshi, rayuwa ce yake yi daidai data ‘ya’yan gata kamarsa,
domin Kakansa ya tsaya masa.
Taiwo kuma miji ya tsaya mata don ba karamin dukiya Toufeeq ya mallaka a turai ba.
Sannan Fatima da Firdausi Yayansu Abdulrasheed da suke kira Hamma wato (Prince) ya
dade da tsayawa rayuwarsu matuka, tun shigarsu jami’a yake dawainiya dasu, bai yarda Dade
(mahaifinsu) ya kashe komai akan karatunsu da bukatunsu ko dawainiyarsu tayau da kullum ba,
shine komai nasu, baya so su kannen sa su nemi wani abu komai tsadarshi su rasa tunda shi
ba iyali ya ajiye ba, so kusan zamu iya cewa komai na Prince na ‘yan uwansa ne baida wani
buri bayan walwalarsu da wadatuwarsu.
Princess Fatima da Princess Firdausi nada albashi mai tsoka duk wata kai tsaye daga
account dinsa zuwa nasu. Haka Kiki da Hakeem ‘ya’yan Taiwo.
Hajiya Sappa kullum tsaye take a kansu da addu’a, shine kadai saukinta. Musamman shi da
yayi nisa da ita, kullum ko a waya bata fasa tunasar da shi bin Allah, kaunar musulunci da
kiyaye sallah, ko yana dauka ko baya dauka ita dai Nenne bata fasawa kuma bata fasa yi masa
addu’a ta musaman a duk inda yake cikin duniya Allah ya kare mata shi daga rudin zamani
dana kuruciya, kasancewarsa namiji daya tal a cikin mata uku da Allah ya bata.
A yadda Hajiya Sappa take rayuwa cikin yawan ibadah kullum, da kula da bautar aure da
mijinta uban ‘ya’yanta, kai sai kayi tsammanin ita din wata waliyya ce. Shigarta kullum cikin
hijabai (jilbabs) kala-kala kamar bata da alaqa da kowacce sarauta.
Duk shekara Hajj da umarah basa wuce Nenne Sappah, bata azumin Ramadhan a gidanta
dake Lagos sai a birnin Makkah da Madinah duk shekara, wani abun burgewa da Nenne in zata
je Hajji bata bin International saidai Pilgrims duk cikin halinta na (down to earthiness) da
kaskantar da kai, wanda take bi duk shekara daga hukumar alhazai ta jihar Lagos zuwa
Saudiyyah.
Shekarun Nenne Sappa a halin yanzu sun kai kusan sittin da biyar a duniya. Yayin da
mahaifiyarta Nani tayi tsufa mai inganci saboda ibadah, har yanzu cikin koshin lafiya Nani
Oummana take rayuwa a Gombe da jinta da kuma ganinta garau.
Tun Nene Sappa nada shekaru akalla sha biyar take gidan aure, kamar yadda na fada a
baya mahaifinta Uban Kasar Gombe Ahmadu Umar Jallo, ya bada aurenta da hannunsa ga dan
abokinsa kuma babban amininsa wanda ya kasance Bayeraben Ilorin (dan kabilar Yoruba).
Saida Prince AbdulRashid ya cika shekaru ashirin a duniya, bayan Nenne Sappa da
Waziri Idrisu sun fidda rai da sake haihuwa, sannan kuma yaki kara auren kowa saboda son da
yake ma Nennen Prince Hajiya Sappa, AbdulRasheed shi ya saka mata suna (Nenne).
Kwatsam bayan fidda rai rana daya sai Allah ya kara baiwa Nenne Sappa haihuwa. Cikin ikon
Allah wannan karon Nenne Sappa ‘yan biyu mata ta haifa kyawawa son kowa fara da baka,
wato daya ta debo kalar dangin mahaifinsu Bayeraben usuli, dayar kuma ta debo Nenne, amma
fa ko kusa ‘yan biyu basu kama kafar Yayansu Prince AbdulRasheed a kyau da farin jini gun
iyaye da dangi ba, sabida shi nasa kyawun surki ne na ruwa biyu; wato duk uwar da kuma uban
ya debo ya hada, don haka kamanninsa kamar na half-caste (ruwa biyu) suke. Aka kira su
Princess Fatima da Princess Firdausi (Princess na nufin Gimbiya da harshen hausa).
Daga kan ‘yan biyunnan ba’a kara ko batan wata a gidan su AbdulRasheed ba. Har kawo
recently, da Princess Fatima da Princess Firdausi sukayi bikin cikar shekarun haihuwarsu
ashirin da hudu a duniya a gidan iyayensu dake yankin Banana Island a jihar Lagos.
Daga Princess Fatima har Princess Firdausi sun kammala karatun jami’a a Jami’ar Nsukka,
kuma kowacce da zancen aurenta a kanta.
Gidan Engnr. Idris Akanni, yana nan a Banana Island wani bangare na (offshore) din Ikoyi,
waje ne da masu arzikin kasar Najeriya da masu sarauta ke buya su zabga gininnuka na gidaje,
su zauna suna cikin arzikin da suka tara ta yaki-halak yaki-haram tareda iyalansu tsakiyar a
jihar Lagos. Banana Island, na nan a Ikoyi, inda acan aka haifi ‘yan biyun; Princess Firdausi da
Princess Fatima.
**** **** ****
BAYAN SHEKARU GOMA SHA HUDU
Y
a zama cewa a halin yanzu Engnr. AbdulRasheed (Prince) ya cika shekaru 44 na rayuwarsa,
shekaru ne da suka zo suka wuce kamar kiftawar ido cikin tarin nasarori masu dimbin yawa da
budi da falala a gareshi da bazasu lissafu ba. Wace duniya Haseenah take bai sani ba, don
bayan kammala Masters dinsa sai ya bar Japan kwatakwata. Ya koma Argentina yayi PhD a
jami’ar da ayayi karatun digiri na farko. Daga baya ya koma Qatar inda ya samu aiki da ‘Qatar
Refinery’.
Bayan wancan incidence din da ya faru dashi shekaru goma sha hudu a baya still yana nan
akan ra’ayinsa na tafiyar da rayuwarsa yadda yake yinta ba tare da tunanin aje iyali ba, sannan
ba wani aikin ashsha ne a gabansa ba sabida hardly Prince ya zauna baya komai in ba lokacin
barci ba, bashi ma da lokacin kansa kona tunanin abinda ya dace a gareshi don koyaushe baka
raba shi da yawon fita tournaments kasashen duniya da ake ji da wasan Polo.
Polo a kasashen da ta karbu babbar sana’a ce mai matukar farin jini kuma ta manyan ‘ya’ya,
Prince Abdulrasheed ya samu duk abinda ake nema a cikin Polo zuwa yanzu saura taki daya ya
rage masa.
Polo na jika shi yadda ba’a zato har fiye da aikinsa na matatar mai, domin yana cigaba da
dauko kofin zinare a yawancin tournaments dinsa, sunansa da shararsa na kara harbawa yana
shawagi a sararin samaniyar duniyar wasan Polo na duniya.
Saidai kuma duk dan adam mai lafiya ai baka raba shi da feelings. Ya yarda shi dan adam
ne ajizi kamar kowa, amma kuma mai iya controlling feelings dinsa, by making himself always
busy da harkar Dawakansa a cikin gida, da aikinsa na matatar man fetur idan yana birnin Qatar,
da kuma tseren doki idan ya fita tournaments sauran kasashe. Yafi rayuwarsa a kasar Argentina
inda acan yafi yin wasan Polo, kasar data zame masa uwardaki bayan kasar haihuwarsa,
Argentina.
A yau tana zaune a ranch house dinsa cikin wata kujera sakar kaba ta hannu, yana kallon
ingarman dokinsa da ya kira da suna ‘SEHEEB` wato ‘ABOKI’ daga can nesa dashi.
A tsaya fadin cewa Dokinsa Saheeb mai muhimmanci ne da tsohon tarihi a cikin rayuwarsa
bata baki ne, kasancewar shine dokin da ya fara mallaka a rayuwarsa, kuma wanda yafi so cikin
duka sababbin Dawakansa.
Dokin na cin korran ciyayin da suka mamaye gidan daga korran shuke-shuke masu ban
sha’awa da kayatar da idanun wanda duk ya kusanto su. Daga can gefe yana iya hangen duk
wani motsi na hadiminsa Pareto wanda ya dukufa aiki, saurayin dake kula masa da Doki
Saheeb da sauran Dawakan dake cikin stable din gidansa. Saurayin yana rage tsayin ciyayin gidan ne da inji, yana daidaita tsayinsu da cutlass, yadda
zasu fi bada sha’awa. Sannan yana kwashe kashin Doki a abin shara na musamman.
A sa’ilin ba komai Prince Abdulrasheed ke yi ba sai kurbar sassanyar ruwan Inibi a tambulan
na glass mai garai-garai, yana cikin tunanin yadda tournament dinsa na gobe zai kasance. Wani
wasan tseren Doki ne wanda ya jima yana jiran zuwan lokacinsa, da yi masa kyakkyawan shiri.
Ba don komai ba sai don kasancewar wasa ne da zai gama daga darajar sa a duniyar wasan
tseren Doki, da shahararsa a Polo a kasar da yake yiwa Polo tana biyansa (Argentina). A
wannan wasan ne yake saka ran kaiwa sauran taki kadan din daya rage masa…. In Allah yasa
yayi nasara, zai samu ya kai matakin karshe na kwarewa a wasan Polo da ya dade yana harin
kaiwa wato (10+ goal Polo Handicap).
Shi kansa Saheeb kamar ya san shirin da ubangidansa keyi akan fitarsu ta gobe, da
burinsa akan tournament din gobe, don haka in ka ganshi sai kayi mamakin yadda yake
annashuwa, sai harbin iska yake da haniniya cikin sabo da yanayin da koshin lafiya a tare
dashi. Hausawa suka ce wai rana bata karya saidai uwar diya ta ji kunya, kome aka sawa rana cikin
yardar Allah zai iso kamar kiftawar ido, gobe ne wannan ranar da Prince Abdulrasheed
(Kehinde) Idris Akanni ke ta dakon zuwanta wadda yake yiwa wannan babban shirin da
kyakkyawan fatan, wato ranar tseren Dawaki na duniya da Argentina ta shirya tsakaninta da
sauran kasashen Polo na duniya. Amma shin ba masu azancin magana ta tsinkaye sunce mafarkai kamar dan da ba’a
haifa bane? Wani a haife shi a raye, wani kuwa a mace ake haifarsa.
Ba kowanne fata, ba kowanne buri ne yake tabbatuwa a lokacin da mukeso, ko muka tsara
yuwuwar tabbatuwarsa ba! Sai lokacin da Allah ya so, ko ya ga damar tabbatuwarsa.
**** **** ****
RANAR GASAR KOFIN TSEREN DAWAKI NA DUNIYA A KASAR AJANTINA (ARGENTINIAN
INTERNATIONAL OPEN POLO TOURNAMENT)
S
ahu biyu ne na mahaya Dawakai zaka iya hange, suna masu kallon juna sashe-sashe sun jeru
reras akan layi. Duka Dawakai goma ne a kawanne sahu, nashi dokin yana tsakiyar sahun
farko, Dawakan sun tsaya car da kafafuwansu, suna kartar kasa da kofatonsu gwanin ban
sha’awa cikin koshin lafiya sai faman ragaji da harbin iska suke tsabar koshi, sai sheki suke
kamar zasu fashe sabida tsaftar da suke samu, ‘Polo Riders’ din (mahayan) sun yi irin tsayuwar
nan ta jiran umarni daga ‘umpire’ bisa ingarmomin Dawakan tseren Doki na musamman
wadanda ake kira (Polo Horses).
Dawakan duka murdaddu ne kuma kosassu, sannan dogaye sambal, kalolinsu sun hada da
farare, bakake da ruwan kasa, ga gashi yala-yala a kansu, da ka gansu kaga lafiyayyun
Dawakai rainon gidan gona saboda koshinsu da cikar tsokar naman jikkunansu.
Wadannan Dawakai ana rainonsu ne musamman don wasan tseren doki (Polo Tournament)
na kwatankwacin irin wannan da ake yi yau, ko kuma don mallakar manyan Sarakuna da masu
kudin gaske, dake da sha’awar wasan tseren Doki a matsayin ‘hobby’ dinsu ko ‘sport’ dinsu.
Irin wadannan Dawakan zaka samu ba’a ko’ina ake kiwata su ba, kuma ba’a sayar dasu a
ko’ina kamar yadda ake sayar da sauran normal Dawakai na kasar Hausa. Su din Dawakai ne
na musamman, da sai a wannan babbar kasa kuma hamshakiya a sha’anin wasan Polo
(Argentina) kadai ake kiwata su, wadda sanin kowa ne ta shahara fiyeda kowacce kasa a
duniya in dai akan sha’anin wasan Polo ne, wato birnin Buenos Aires (Capital of Argentina).
Ana kiran wadannan Dawakan da suna;
‘Thoroughbred Argentinian Horses’.
Gabadaya mahayan nan suna sanye da kaya iri daya, wanda ya zame musu (uniform) na
wasan tseren dawaki wato; fararen riguna masu kwala da farin wando (Polo t-shirts and white
Trousers).
Kamar yadda na fada a sama ‘team’ din mahaya Dawakan guda biyu ne, sukayi sahu-sahu
suna masu fuskantar juna cikin jiran a kada kararrawa, su fara.
Kawunansu sanye da ‘polo helmets’ wadda itama fara ce kal da ratsin shudi kamar kalar
kayan jikin su. Yayinda kafafunsu ke sunke cikin fararen takalmannan tsadaddu da ake kira
‘Brogues’ da 'Chukka boots' da kuma ‘loafers’.
Umarnin ‘umpire’ kawai suke jira ya kada kararrawar bada umarnin farawa, su kuma su fafari
dawakansu ta hanyar baiwa Dawakan umarnin tafiya, wato daga nan za’a