Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
waka saita koma gefe cikin muzanta kamar mujiya a
cikinsu, don yadda Aisha tasa ‘yan dakinsu suke nuna mata wariya da kyama wai don
kasancewarta bayarabiya daya tal a hostel dinsu, cikin dalibai masu yawa hausawa da fulanin
Gombe da suka fi yawa a FGC Billiri, wadda aka kawo daga jihar Ibadan, aikin asibitin federal
government ne ya kawo iyayenta garin Gombe, har yayi sanadin da aka yi mata transfer zuwa
FGC Billiri.
Bisola Akanbi musulma ce gaba da baya. Yarinya mai hakuri da rashin sakewa da hausawa.
Har ya zamnto daga zuwanta Billiri zuwa yanzu su Aisha da gang dinta su Amintako, Ramatu
da Zannura suna neman jaza mata ciwon damuwa, sabida yadda Aisha ke nuna kamar itaba
cikakkar mutum bace, ko kuma ba daya take da sauran dalibai ba, wai tunda ita bayarabiya ce.
Kabilanci muraran a wurin Aisha abin ba’a cewa komai.
Yau dai abinna Aishatu-Siddiqah Yunus, ya kai Bisola Akanbi bango, duk hakurinta Aisha ta
kaita karshe, don ta sa an wareta daga cin abinci tare dasu a dakin, sabida itace gang leader ta
dakin gabadaya, ‘yan dakin tun kan a kawo Bisola suna yin ciyayyar abinci a dakinsu. Da aka
kawo Bisola daga baya suna ci har ita, yau Aisha tace idan har basu cire Bisola daga ciyayya
ba ita zata daina ci tareda su, don ita bata son cin abincin yarbawa ko ci tare dasu, alhalin taji
ana fadin suna kashi a kwano, don haka Bisola ita kadai aka zuba mata nata a plate, aka tura
mata gefe wai don ita bayerabiya ce. A cewar Aisha Yunus, gang leader ta ‘yan aji hudu (SS 1)
bazata ci abinci da Yarbawa masu cin dodon kodi da hannunsu ba.
Wannan abu yaima Bisola ciwo. Kasancewar ta dade tana shaqa daga Aisha, ta yi hakuri mai
yawa da Aisha, hakurin da ya hada da dan tsoro-tsoro, kasancewar Aisha nada wasu ilhamomi,
watau kwarjininta da kyawunta da kaifin harshenta dake sawa aji ana shakkarta, sannan duk
‘yan gang dinta su Amintako halinsu daya da ita na tsokana da fin karfin wanda bashi da baki
kamar Bisola. Amma yau? Dama aka ce mai hakuri bai iya fushi ba.
Da kuka Bisola taje (staff room) ta gayawa Discipline Master duk abinda Aisha ke yi mata a
hostel, a aji, a library, a wajen wasa ne dama duk inda ta ganta tun zuwanta FGC Billiri.
“This is Mockery! Derision!”
Inji Malamin cikin bacin rai.
Discipline Master Uncle Sayyadi ya cika da mamaki, ransa kuma dana sauran malamai ya
baci sosai, ace a makaranta ta gwamnatin tarayya (unity school) ta Najeriya ake irin wannan
abin Allah wadai su malaman basu sani ba? Nan ya aika Head Girl Hasiya Mato, yace
maza-maza ta kawo masa Aisha-Siddiqah Yunus ofishin malamai (dead or alive), sannan yace
Bisola ta zauna a gefe, yau sai ya ga uban Aisha. Bisola ta koma gefen Teacher din tana sharar
hawaye domin hakika Aisha Yunus, ta zame mata matsala cikin makarantar, ta dade tana cutar
da feeling dinta.
Head girl Hasiya din taje har dakinsu ta sako Aisha a gaba har ofishin malamai, duka
malaman sun hada kai a ofishin suna tattauanawa akan al’amarin da Bisola ta kawo kara tana
neman ayi mata iyaka da Siddiqah Yunus. Discipline Master yafi Bisola jin bacin rai, koda yace
a kawo masa ita, kafin sui so ya shirbinawa dorinarsa man shanu sau uku kuma dama gashi
lokacin san yi ne, yace a ransa yau zai ga karshen kabilancinta, zai gani idan ubanta ne ya
wanzar da hausa bakwai da banza bakwai.
Malaman kowa na tofa albarkacin bakinsa akan kabilancin ‘yan arewa ga ‘yan kabilar Yoruba,
da yawa ana samun hakan, wanda ko kadan bashi da amfani musamman ga yara masu tasowa
ana saka musu wani nagetive tunani daban a ransu akan kabilar Yarbawa. Kamar su din wata
halitta ne daban da hausawa da Fulani. Ko Hausa/Fulani din sun fisu wata martaba ne. Aisha ta
iso sumui-sumui da ita don tasan kiran Malam Sayyadi ba alheri bane, ganin Bisola a gefensa
tana kuka yasa ta gane kwabarta tayi ruwa yau, wato yau Bisola ta kai kararta, ai kuwa nan da
nan cikinta ya duri ruwa.
Aisha da Bisola suka gurfana gaban Discipline Master, kan Aisha a sadde da ganinta kaga
maras gaskiya. Discipline Master ya daka mata tsawa yace “maimaita tsokanar da kike mata
kullum a kunnen mu muji, isashshiya diyar barbushe da tsimbirbira”.
Aisha tayi narai-narai da sexy eyes dinta akan malamin bafillacen, wadannan idanun na
Aisha masu kama da hawaye ne fal ya taru a cikinsu, shi kansa Discipline Master din sai da ya
kauda kai sabida kwarjinin idanun Siddiqah, ya taba cewa wani Teacher dan uwansa mai suna
Malam Tafida ya daina kallonta, Malam Tafida yace shima bai san meyasa yake yawan kallonta
ba, Uncle Sayyadi yace da Malam Tafida cikin takaici, “yarinyar nan in ka cika kallon ta
musamman wadannan maganadisun idanun nata alwala bazata zauna a jikinka ba”. Bai manta
dariyar da malam Tafida yayi ta yi ba a ranar, to yau ma hakan ce ta kasance. Discipline Master
da Aisha tayi masa narai-narai da ido cikin rokon ta tuba bai san sanda ya zabura don kwato
kansa daga tasirin idanun Aishah ba, ya buga dorinarsa a kasa cikin barazana.
“Zaki fada muji ko ba zaki fada kowa ya ji me kike yi mata ba?”
Maimakon Aisha ta bada amsa sai ta soma tumami a kasa tana kuka tana shura kafafu.
“Malam in ka dake ni Asma ta tashi zata yi, Malam ni asthmatic ce. Ummana kafin a kawo ni
tace ayi mata alkawarin ko me zan yi za’a bani punishment, na aiki ko kneel down kowanne
irine a bani, amma kar a taba mata lafiyar jiki na.
Wallahi Malam nima a bakin yaran unguwarmu naji”.
Discipline Master da sauran malamai duk suka saki baki da ido galala! Suna kallon
Aisha-ikon Allah, irin kukan da take yi da tumami a kasa na shagwaba kamar karamar yarinya
alhalin tayi 15, bayan ko dukan nata ma bai yi ba ya hanasu sake ce mata komai. Ta sake sakin
kuka tana cewa Bisola ta mata sharri. Ai kuwa Disdipline Master ya fusata ya zuba mata dorinar
a gadon bayanta guda daya, kafin ta farfado ya daddage ya sake zuba mata wata akan siraran
kafafunta, yace “bari in saki kukan shagwaba da hujja, ko kinga Umman naki anan da zaki
mana shagwabar banza da wofi? Tukunnama makarantar nan ta Babanki ce da zaki uzzurawa
‘yar mutane?”
Aisha suma ne kawai bata yi ba, don bulalar ta shigeta yadda ya kamata, muryarta fal kuka
tana mutsu-mutsu tace “Na tuba Uncle, na tuba nabi Allah na bi ka, na daina wallahi Uncle,
daga yau bazan kara yi mata ba, kuma na daina cewa Yarbawa masu kwalo-kwalo ne”.
Malam Sayyadi ya kara shimfida mata lafiyayya wadda tafi ta baya shiga tsokar jikinta, Aisha
tayi flat a kasa wannan karon sabida yadda bulalar ta shigeta har wani dan karamin fitsari ta
saki ta cikin uniform dinta.
A wahale ta ce tayi “na maida kalamai na, Bisola ki yi hakuri, Yarbawa basa tukin tuwo da
duwawu, Yarbawa basa kashi a kwano, ke ba bayerabiya bace mutum ce ‘yar najeriya kamar
mu, na tuba na bi Allah na maida kalamai na Uncle”. Daga malaman dake gefe har Discipline
Master din saida Aisha ta basu muguwar dariya amma suka hadiye don so suke sata a saiti. Suka rufu wajen yi mata fada da nasiha cewa abinda take yiwa Bisola ba daidai bane ko a
addini, Bisola musulma ce kamarta, ‘yar kasa cikakka kamarta, abinda takeyi din kabilanci ne
da wariyar launin fata.
Sannan a matsayinmu na ‘yan Najeriya dole mu kaunaci juna, mu cire banbancin yare da na
al’ada har ma dana addini inta kama, in har ana son a samun cigaba da hadin kai a tsakanin
al’ummar Najeriya.
Bisola ta dinga basu labarin irin uzzurawar da Aisha ta dade tana yi mata, ta ce komai tayi sai
Aisha ta kushe, tana jin dadin kiranta “bayerabiya” a cikin yara ‘yan uwansu, kai sai ka rantse da
Allah kiran bayerabe da Aisha ke yi cikin ‘mockery’ na nufin bayeraben mutum ba cikakken
mutum bane wani abu ne daban, (kusan haka yake a idon Aisha-Siddiqah) a kabilancin data
dade da sawa ranta akan Yarbawa.
Ita a tunaninta Bayerabe wani kalar mutum ne daban wand bashi da katabus a cikin hausawa
da Fulani, kamar wani alien take kallonsa. Ko kuma ka dauka wani ‘yanci bahaushe ko
bafillacen mutum yafi bayarabe in dai a idon rigimammiya… ‘yar Ummanta, Aisha-Siddiqah
Yunus ne. **** **** ****
Labarin jinyar da AbdulRasheed yayi bayan fadowa a Doki ta kai kunnen Kakansa Emir of
Ilorin, ai kuwa ya tubure sai an shirya masa tafiya har Qatar don gano jikin Kehinde. Inda su
Turaki da Mutawalle da Shettima har ma da Waziri mahaifin Kehinde din suka taru suka ki
amincewa da hawansa jirgi a yanzu, don a lokacin jikin girma ya fara motsawa ba lafiya ce ta
isheshi ba, in ya sa rikici kan yana son yayi abu, su duka goman damuwa suke shiga saboda
basa iyawa rikicin tsufansa.
Daga baya suka yanke shawarar su kira Abdulrasheed din yazo kawai sai dai Kakan ya
ganshi ba tare da an gaya masa zai zo ba.
Turaki shi ya kira dan nasu Engnr. AbdulRasheed a waya, yace lallai yazo cikin satinnan
Emir ya ganshi hankalinsa ya kwanta ko suma nasu ya kwanta da rikicinsa.
Bai jima da komawa Qatar ba, yanada tarin ayyuka a gabansa amma kuma, baya hada
lamarin Kakansa da komai, don haka Abdulrasheed ya ajiye komai dake gabansa ya shirya
zuwa Ilorin a sati mai zuwa don ya ga Kakansa.
**** **** ****
Sarki Abdulrashid ya rika ina yaka-saka-ina-yaka-aje da jikansa mafi soyuwa a gareshi Prince
AbdulRasheed (Kehinde) ta bakinsa, lokacin da ya sauka a Ilorin, tarba ta girma aka shirya ma
babban jikan na Sarki Prince AbdulRasheed, kuma takwaransa.
Basu samu kebewa ba shida Sarki sai da daddare kasancewar saukar safe yayi, ya gaya
masa raunin da dokinsa mai tarihi wato SAHEEB yaji sosai sanadin tsautsayin da ya samesu
shida dokin. Yanzu haka ya daina wasan Polo dashi sai sauran dawakansa.
Sarki da karawa aya zaki wajen taya jikan nasa son Polo da duk abinda yake so nan take
yayi alkawarin sayawa AbdulRasheed sabon yaron Doki (Criollo Horse), a karshe yace.
“Baka hau doki ba kayi me jikana? Ride it with passion the great Prince of the Ilorin
Emirate!!!
Tsautsayi na Allah ne don ka fadi doki sai ace ka daina Polo kwata-kwata? To wa tsautsayi ya
bari inace abu ne da baya wuce ranarsa? Rabu dasu takwara duk jinsu nake kawai ina biye
musu don a zauna lafiya, amma ba mai hanaka yin abinda kake so kaji. Don duk sun hada baki
wai na hanaka hawa Doki daga yau, fau-fau. Allah na tuba “Prince” din duk da bai hau doki ba ai bai cika “Prince” din ba”.
Shiyasa fa AbdulRasheed ke matukar son Kakan nasa, yake kuma amsa kiransa a duk
lokacin da ya bukaci ganinsa a ko’ina yake kuma kome yake komai muhimmancin abun zai bari
yazo. Sabida a duniya ba mai son farin cikinsa irin Sarki.
A daren ranar sunyi hirarraki iri-iri wadda ta shafi lafiyar Kakan nasa, da cigaban rayuwar
AbdulRasheed kacokam. Wani abu da yasa Abdulrasheed yake sakewa da Kakansa yake kuma
yin doguwar hira dashi saboda shi baya matsa masa akan maganar aure, kullum addu’a yake
masa don ya yarda rashin auren AbdulRasheed har zuwa yanzu ba haka kawai bane, akwai dai
abinda Allah ya boye a ciki, ko dai aljana ta aureshi, ko kuma akwai wani boyayyen dalili da
kowa bai sani ba.
Bayan sunyi sallama da Kakan kan zai je ya kwanta, kafin AbdulRasheed ya kai ga isa
turakarsa dake gidan sarautar Ilorin, Kawunsa Turaki, wato mai bin mahaifinsa a haihuwa ya
aiko ace dashi lallai suna son ganin shi su duka gobe (kannen mahaifinsa Akanni’s
gabadayansu) kafin ya koma Qatar. Tun daga nan AbdulRasheed ya sha jinin jikinsa, cewa ganawa ce ta musamman iyayen
nasa maza zasu hada a kansa, ayi masa taron dangi a titsiyeshi kuma ba’a kan komai ba sai
akan maganar aure da baya ko son jin an alaqanta shi da ita.
Ya so ya gudu cikin daren kafin wayewar garin, to ‘booking’ dinsa sai akayi rashin sa’a na jibi
talata ne. Haka yayi ta kokarin canza ‘booking’ don dai ya samu ya kubucewa wannan haduwar
wadda yasan bazata yi masa dadi ba, Akannis sun gama zura masa ido da bata yawun bakinsu
akan maganar aurensa, duk yadda yayi kokarin barin Ilorin a daren don gujewa fushin iyayensa
maza bai samu damar hakan ba.
A washegari mahaifin Prince wato Engnr. Idrees Akanni da shima suka gayyato don ayi
zaman tare dashi ya iso Ilorin, a ranar taron ya iso don ta jirgin sama ya taho daga Lagos.
**** **** ****
THE TEN AKANNIS’
S
u goma dinnan, wato kannen mahaifinsa da mahaifin nasa haka suka saka shi a tsakiya yau
suka zagayeshi a fadar Maimartaba Sarkin Ilorin, akan yau ba inda zaije sai ya gaya musu
‘exactly’ me ya hana shi aure a rayuwarsa?
Duk kannensa na cikin family dinsu sunyi aure, ga albarkar ‘ya’ya, daga mai yara hudu sai
mai biyar. Wannan masifa a cewar Akanni’s, sun kasa gane mata. Yo masifa mana?!
Rashin aure babu dalili wanda addini ya yarda dashi ga mai shekaru sama da 40 ya zama
masifa a cikin zuri’arsu.
Suka hada baki wajen cewa “bazasu amince ya bata musu ‘image’ na gidansu da maluntarsu
ba, don kawai ya ga Sarki yana daure masa gindi yana abinda yaga dama, ba don komai ba sai
don yana gudun bacin ransa.
Suka ce Sarki yafi kowa damuwa da son yayi aure ya dauki ’ya’yansa yana raye, kawai
baya nuna masa ne don ya ga baya so, amma su sun sani, Sarki baida damuwa a halin yanzu
sai ta rashin aurensa, suka taru akan cewa bazai kashe musu tsoho da damuwa ba dole ya
bashi tattaba kunne ya dauka yana raye. Mutawalle Abdulfatahi ya ce “idan macece bai samu ba, su iyayensa maza zasu bashi ko
guda nawa yakeso a cikin ‘ya’yansu mata matasa da basu kai ga yin aure ba.
Idan kuma baya son auren gida, ya fadi duk diyar Sarkin da yake so a masarautun Najeriya,
na kudu dana arewa, su kuma za suje su auro masa.
In kuma lafiyar yin aure ce bashi da ita, itama yau dai sunaso su sani, zasu shiga ko’ina su
fita daga nan har birnin Sin, su nema masa magani, su iyayensa ne da suka haifeshi, ya yarda
cewa babu boye-boye yau a tsakaninsu.
Tunda ya nuna Ubansa wato Waziri bai isa dashi ba, saboda Polo da abunda yake samu
cikinta dake rudarsa, suka ce to Waziri Idreesu ya basu dama su yanke masa duk hukuncin da
suka ga ya dace da shi yanzu.
Su kuma a adalci irin nasu da Allah yace musu su yiwa ‘ya’yan su, bazasu yanke masa
kowanne hukunci ba, sai sun bashi dama sun ji ta bakinsa tukunna, wato sai sun ji hujjarsa ta
kin yin aure daga bakinsa. Alhalin mahaifinsa nada shekaru 25 mahaifiyarsa Sappa nada 15
aka yi musu aure, wanda albarkar hakan ne har suka sameshi cikin kuruciyarsu suka girma tare
dashi.
Shi yau Abdulrasheed shekaru 43 yake nema, me kuma ya rasa a rayuwarsa?
The Akannis’ suka kara da cewa; wannan rashin auren nasa masifa ce babba a garesu da
zuri’arsu. Suka kuma rufe zancen da cewa, “idan har bashi da hujjar kin yin aure, bashi kuma
da wadda ta kwanta masa da yake ganin zai iya aure, gobe-goben nan zasu aura masa mata
hudu, akai masa su gidan sa, kuma sun yi rantsuwa da Allah dole ya zauna dasu gabadaya in
yana son albarkarsu, bijirewa wannan umarnin na nufin zasu cireshi cikin ‘ya’yansu tunda dai
Allah yasa ba shikadai suka haifa ba.