Noor Albii Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   23 / 36

66K to 69K   out of 107.4K words

ta tashi tayi sallar la'asar tareda fitowa Palo taje kitchen ta hado cereals da Madara tadawo Palo tazauna tana kallo tana chatting tana Sha a natse sbd bayanan ya fita tun tana bacci.

Da sofia suke chatting tana Mata korafin ciwon jikinta akan Aunt siya Dake hudubantata Dan kuwa itace taqarasa zugata ta zarewa Abban gaba daya.
Tana cikin chatting din yadawo ta dago ta kallesa fuskarta a Dan sakalce da gajiyan datake ciki
Kafin ta tashi yariga ya iso inda taken ya zauna gefenta ahankali tareda kallon abin datake Sha ya kalleta yace"

Wannan abinci ne?

Gyada masa Kai tayi tana sake marairaicewa da fuska tace"

Yunwa nakeji Kuma banajin Dadi bare na dafa abinci shine nakeshan wannan din.

Kallonta yayi da kulawa Kai tsaye yace"

Kinajin wani abun ne?

Girgiza Kai tayi tana qasara shanye cereals dinta tace"

Zazzabine idan nayi bacci sosai Zan warware.

Shiru yayi kawai tareda fidda wayarsa yakira A Abdoul ya sanar masa asiya Masa tickets guda biyu na zuwa New Jersey zuwa gobe.

Tanajinsa Amma batai tunanin da ita zasuyi tafiyarba sai washe garin tanama baccin safe yace ta tashi ta shirya su tafi Dan Haka ba wani shiri ta shirya cikin blue skinny jeans da farar long sleeve kamar yanda shima blue jeans ne jikinsa da farar lv long sleeve,
Sneakers ne a qafarsu farare na Nike
Doguwar Blazer kawai ta Dora akan kayanta blue Suka nufi airport hannunta na cikin nasa dayan hannunta na riqeda handbag dinta tana yiwa Anty Sa'adah txt din cewan"

Zataje New Jersey tadawo kwana biyu.

First class suke Dan Haka ko acikin jirgin tana manne gefensa ba Bata lokaci bacci ya dauketa.

Koda suka Isa New Jersey A Abdoul yariga yayi musu booking suites a _Grand Cascades Lodge_

Motan hotel din ce tazo ta daukesu daga airport Suka Isa,
A matuqar gajiye take Dan Haka wanka tayi da ruwan zafi tayi sallah daqyar taci kadan daga tarin varieties na abincin da yabada order
Tana gamaci ta kwanta sai bacci dama dare yayi.

Washe gari ma bacci ta wuni Yi sai data Gama cire gajiyarta duka cikin kwana biyu kafin ta sake tafara Jin dadin garin sbd Babu inda yake zuwa tunda ta fahimci ba aiki yazo yiba hutawa yake buqata Dan Haka ta sake Masa jiki sosai Suka Gama haukata dukkanin dakin da Palo da koinama..
Kullum idan za'ai gyaran dakin saita tafara harhada dakin sbd yanda suke hargitsa komai.

Tunda tazo garin jikinta baya ganin suturar arzki idan ba sallah zataiba kokuma zasu fita..
Wasu shegun nighties take sakawa da qananun shorts dasuka Gama hautsina hakuri da kawaicinsa ya ringa juyata son ransa suna hutawa..

Kwanansu Tara a garin suka koma LA sbd wata tafiyar data taso Masa Dan Haka suna dawowa tace yabarta a LA din sbd Anty Sa'adah na qasar har yanzu Bata komaba suna buqatan kasancewa da juna.

Ranar daya wuce a asibiti Suka wuni sai dare Suka koma gida tareda Anty Sa'adah da zata kwana gurinta sbd su samu lokacin kasancewa da juna.

Momy tasan duk yanda tayi bazata iya hanasu kasancewa da junaba sbd aka Laylah tasan kafiyar Sa'adah Dan Haka Bata wahalda kantaba hanata zuwa Suka wuce.

Suna dawowa dayake sun Dan gaji tea suka Sha suka kwanta a dakin Laylan,

Washe gari ma dai hakanan ta tashi ba wani qarfi jikinta ta hada musu breakfast Takoma tayi wanka ta Sanya Doguwar Riga Mara nauyi Suka fito sukai breakfast suna gamawa Takoma ta kwanta Dan yanzu Kam zazzabi takeji sosai.

Ahankali zazzabi Mai qarfi ya kwantar da ita kwana biyu Dole yasa anty Sa'adah ta takurata sukai booking appointment da wani likita a asibitin da Abba yake akan washe gari zasu.

Kafin suje asibitin Kuma sai gashi tasamu Dan sauki Dan Haka taso qin zuwa asibitin Dole Anty Sa'adah Tai Mata Suka tafi tashin farko Dr na Gama dubata ya sanar dasu she's 7weeks pregnant...

Wani mummanan tashin hankali da matsananciyar kunyar duniya tashiga gaban Anty Sa'adah har batasan lokacinda hawaye Suka ringa gangarowa Kan fuskarta ba takasa dagowa ta kalli Anty Sa'adah.

Anty Sa'adah ganin hawaye da Kuma halinda Laylan tashiga Kan sakamakon da aka Basu yasa hankalinta mugun tashi gabanta yashiga bugawa da qarfi cikin fargabar me hakan ke nufi?

Ita kanta zancen cikin ya firgitata sosai saidai Kuma kukan Laylan yafi Bata tsoro indai cikin bana wanine dabanba Dan kuwa Turakin dabai Gama sanin kamar laylanba bare daukanta matarsa tayaya zaace cikinsane? Dan Haka itama hawayen tafara cikin tsananin tashin hankali da fargabar wannan wane abune yake Shirin faruwa dasu suna zamansu cikin rufin asiri da qaunar mutanannan ace wannan Abu ya bullo.

Gida suka koma Suka zauna Palo jigum jigum kowacce na tsiyayar hawaye musamman anty Sa'adahn datake hango inda wannan tashin hankalin zai kaisu..

Sun Jima ahakan kafin Laylah dataga kukan Anty Sa'adahn yayi yawa Kuma idan ta fahimceta tasan tunanin dayake ranta baifi na inda ta samu cikiba Dan Haka ta share hawayenta tareda kallon anty Sa'adahn ta bude Baki cikin kunya da sanyin jiki tace"

Anty Sa'adah ba abinda kike tunani bane,
Wlh bazan taba aikata zinaba duk inda nasamu kaina da yardan Allah.....

Wani kallo anty Sa'adah Tai Mata tanason magana Amma Tama kasa sbd batasan me zataceba.

Itama shiru tayi takasa fadar yanda cikin yake,
Ba fadawa anty Sa'adahn ba shin tayayama zatai da cikin?
Wannan cikin bayyanarsa masifar Dake lafe ce zata farka Dan a duniya bayan Haj Zinat Aminiyar mum Na'ima itace tafi kowa sanin irin masifar Dake cikin mum din akan Abban Dan kuwa tasha fada agabanta kisa ma zata iyayi akansa...

Wasu sabbin hawaye ne suka gangaro Mata ba masifar mum ba kunyar bayyanar cikin kansa wani tashin hankaline gareta.

Anty Sa'adah da ranta yafara baci da quluwa da Shirun tace"

Bana buqatan wani dogon sharhi ko bayani amsa daya zakiban cikin waye????

Kasa dagowa tayi da fuskarta ahankali ta furta"

Abba.

Tana fadar hakan anty Sa'adah batace komaiba ta miqe jiki a salube tayi daki,
Al'amarin farin ciki mai girma Amma tsoron abinda ke bayansa ya Hana murnar.

Haka suka kwana gidan Babu Mai dogon motsi sbd damuwa sai washe garin bayan sun Gama breakfast jiki amace anty Sa'adah ta saki Bayyanannar ajiyan zuciya tareda cewa"

Jiyan halinda kikaga nashiga Jin ciko ajikinki wlh Bantaba zarginkiba da alfashaba ko makamancinta Laylah,

Samuwar ciki a irin yanayinda aurenki yake ciki yanzu akwai hadari wlh Laylah,
Idan Matar Nan tasan kinada alaqar da Bata uba da 'yaba tsakaninki da Turaki komai zata iya aikatawa Dan Haka Ni wlh duk kinsa hankalina tashi Kuma yanzu,

Ni kaina wlh kunyar sanarda Anne nakeji,
Amma dai duk da hakan karki Bari kowa yasani mubar maganar ahakan tunda kince Nanda wata biyar Zaki samu zuwa Nigeria dogon hutu idan kinje ma fadawa Anne komai
Saidai wlh kiyi kokari Kar Wanda yagane ciki a jikinki.

Kallonta Laylan tayi jiki sanyaye tace"

Anty Sa'adah zai boyu kuwa har wata biyar?

Zaiyi Mana idan kinyi kaffa kaffa tunda ita uwar Taki ba wani zama takeba kullum tana gantalin yawon kasuwanci.

Ajiyar zuciya Laylah ta sauke tareda cewa"

To anty Sa'adah Amma Dan Allah karki fadawa Momy da Anne wlh kunya zanji, bansan ya zanyiba.

Murmushi Sa'adah tasake sai alokacin takejin kaunar cikin sbd tuno farin cikinda Anne zatai da cikin sbd kullum burinta Laylan tagama karatu tadawo ayi gagarumar walimar aurenta da Turakin kowa yasan ita matarsace saita tare da sunan matarsa, Ashe bidirin banza suke can.
##MAMUH#
NOOR ALBI Na kudi ne pay at +234 903 234 5899

Or arewabooks for more pages.
[7/10, 9:36 PM] +234 704 076 8969: *_Mamuhgee 39_*
Daqyar taga asuba tayi ta tashi tayo alwala tazo tayi sallah tana idarwa ta danyi karatun Qur'an tasamu nauyin zuciyarta ya sauka kafin ta miqe takoma gadonta ta Haye Tareda komawa cikin bargo sai alokacin bacci ya iya daukanta mai nauyi.

Bata fito breakfast ba sbd baccin datakeyi sai 12 ta farka tayi wanka ta fito taje ta gaida mum tadawo dakinta tayi zamanta anan tasa Cindy ta kawo Mata abincin taci tana gamawa takira Anty Sa'adah suna fira sama sama dan tasamu tasake sakewa.

Anyi Sa'adah data fahimci tana cikin yanayi Mara Dadi ta saki Ajiyar zuciya tareda Kiran sunanta tace"

Laylah kinsa yanayinki dai yanzu ba'a son damuwa ko?
Karki saka damuwar komai a ranki sbd lafiyanki Dana cikinki Dan kuwa qaramin ciki bayason saka damuwa arai zai iya fita,

Kinsamu Allah yasa daga haduwar qaddara so daya da Turaki yayi dake kin samu cikin gwara ki lallaba abinku ki haife kinsamu naki jinin,
Hakama su Anne da Turakin kin saka musu da dukkanin alkhairansu akanmu....

Nidai banason wani Abu ya samu cikin Nan Laylah sbd bakisan yaushe Allah zai Kuma kawo wannan rabonba na yaqara zuwa ya nemeki harki samu wani rabon Dan Haka gwara ki lallaba wannan din tunda kince so dayane Kuma bada saniba.

Kunyar qaryar dataiwa anty Sa'adah tun farko datake maimaita Mata yanzu da damuwar Jin cikinta zai iya zubewa sanadin damuwa yasa taqarajin duk batajin dadin komai.
Haka suka Gama wayar ba wani walwala ta miqe tayo alwala tayi asr prayer ta koma ta miqe a kujera tana chatting da Sofia itama taji ko zata sake.

Wuni tayi a daki Bata fito ko kofar palon ba hakama washe gari wuni tayi a daki taqi fitowa komai a daki Cindy ke kawo Mata.

Kwananta biyar Bata zuwa cin abinci dasu wasan boyo ma takeyi dasu gabaki dayansu sbd ko mum din datake zuwa gaidawa zuciyarta Shiga wani Hali takeyi sbd yanda mum din koyaushe take nuni da wani alamun mijinta Yana Mata yanda takeso,
a tafin hannunta yake,
Kullum biya Mata buqatanta yake, dadai sauran makamantansu duk da ba ita take fadawaba Amma koyaushe alamominta da wayarta da Haj Zinat na nuni da hakan Dan Haka sai kawai ta taqaita zuwa dakin mum din
Qarshema Bayan kwana biyu cewa tayi batada lafiya Dan Haka saita daina fitowama kwata kwata Dan wani radadi takeji cikin zuciyarta bakuma dama ko halin nunawa.

Shi kansa Abban ko txt dinsa dayake Mata ada kullum ya daina Yi itama batai Masa ba saidai kullum dare saitayi kukan data tabbatarda na mugun kishine Dake cinta Amma ba dalilinta na yin hakan shiyasa abun yake cin ranta.

Daqyar taga anyi sati biyu ta koma cigaba da zuwa makaranta sai tazama Bata wani zama gidan dama mum ko anan Atlanta ba wani zama gida takeba kullum tana gurin yawo.

Tunda Suka koma school sofia datasan da sabon cikin data samu koyaushe itace ke kokarin cheering dinta kayan ciye ciye harma da maganinda Aunt siya ta rubuto Mata na masu cikin kullum sofia ke Kai Mata school acan take Sha itakuma ta koma da sauran gidansu Dan bazasu Bari Laylan taje gida da maganinba a samu matsala.

Yau da wuri tadawo daga makarantar sbd gajiya da bacci ma kawai ita takeji Dan Haka ko data shigo harabar gidan tayi parking motarta ta fito rataye da qaramar Gucci quilted shoulder bag dinta ta,
Jikinta Kuma Diva abaya ce ajikinta maroon sai gyalen abayan data daura akanta yayi gefe daya.

Palon tashigo kai tsaye batasan dasuba a palon saidata shigo tayi Ido biyu dashi daidai shigowarta daidai dagowarsa ya kalli kofar sbd qamshinta dayaji hancinsa ya shaqo.

Cikin Ido Suka kalla juna kafin ta dauke Kai ahankali tareda qarasowa tana kallon mum Dake zaune kusa dashi sosai Sosai hakama tana riqeda hannunsa tana zuba Masa soyayya da kudin datakeson yasaka hannu A Abdoul ya Bata.

Ahankali ta Dan sauke kanta daga kallonsu cikin murya Mai taushi da nutsuwa tace"

Abba Ina wuni?
Mum barka da rana.

Yanda ya amsa Kai tsaye batareda yabar duba wayan dayakeba yasake sakata Jin wani iri ta wucewarta Dan dama ba wani tsayawa tayi ba.

Mum dakeson kudi gurin Turakin ta kalli Laylan cikin kulawan kissa tace"

Baby yau kifito kici abinci damu anjima kadan sbd munyi kewan cin abinci as happy family dukanmu.

Dagowa yayi ya zuba Mata idanuwansa da tanajinsu akanta suke
Sai Bata waiwayoba ta gyada Kai kawai Dan batada dalilin cewa aa.

Tana shiga daki wanka tafara Yi tayi sallar la'asar da akai ta Kira Cindy a waya tace takawo Mata fruits masu sanyi.

Tana Gama cin fruits dinta waya dasu Anne tayita Yi suna debe Mata kewansu data qaru tasa Jin qasar ta isheta.
A daki tayi wuninta sai dare Bayan tagama sallar isha tayi wanka kamar bazata fitoba sbd zamanta dakin yafi Mata nutsuwa yanzu Amma sbd batada dalilin qin fitar yasata zuro slippers ta fito ta nufi dining room din.

Tun a kofar shiga ciki ta tabbatarda Yana cikin sbd hancinta daya Bata tabbacin,

Numfashi ta sauke ahankali tareda Dan rufe ido ta bude tana hadawa da Ajiyar zuciya zuciyarta na neman narkewa Amma ta daure ta qaraso ciki.

Dagowa yayi ya zuba Mata idanuwansa Dake kokarin bada kamewarsa..

Doguwar fitted pencil gown ce a jikinta red Mai zib a gaba daga sama har Wasa,
Yanda rigar ta lafe a jikinta ta kwanta ne ya fidda asalin shape Dinta Sosai
Abin dabata lura dashiba cikinta ya Dan kumbura kadan ajikin rigar yafita saidai ba a ganewa ko kadan...
Ga wani irin Hasken gaske data qara har wani glowing takeyi.

Jin idonsa akanta yasa zuciyarta takasa hakuri ta dago ta kallesa itama
Idanuwansu suka shiga cikin na juna take taji kamar zata sakar Masa kukan tsananin kewarsa datai agurin saidai ba wannan damar Dan Haka ta dauke idonta tareda zaunawa gefen mum da taketa fama zuba Masa abinci tana Masa wasu salo salon daukan hankali duk Dan samun biyan buqatarta dataketa bi ayau din na kudin.

Murmushin yaqe tasake tana kallon mum da har lokacin Bata zaunaba tana serving dinsa da kasalalliyar murya tace"

Sannu da aiki mum.

Batareda ta waiwayo ba muryarta duk a washe tace"

Thank you baby.

Har Lokacin Bai dauke idonsa daga kantaba duk sai takasa komai ta aje cup din madarar data dauka batareda Tasha ba ta dago ta kallesa yanayi na Rasa abin Yi dakuma rashin mafita ta zuba Masa idonta Dake neman cikowa da hawaye.

Wani irin rufe ido yayi ya bude ahankali cikin Jin cin abincin ya fita kansa gabaki daya ganin hawayen idon nata,

Miqewa tsaye yayi ya juya yabar dining room din
Mum tabisa da kallo da gudu ta aje serving spoon din hannunta tabisa tana Kiran sunansa cikin firgicin karta Rasa damarta na abinda takeso.

Suna fita itama ta miqe batareda taci komaiba tabar dining room din tana share hawayenta da bayan hannunta.

Har bedroom dinsa Ms Na'ima tabisa jiki na rawa hankali tashe Dan kuwa zuwa gobe da safe idan Bata turawa Zinat kudinba akwai matsala,
Shagunan kasuwancinsu da boutiques dinsu komai na neman lalacewa kudi suke nema sosai Ido rufe Dan kila sai ta danganta da zuwa Nigeria din da kanta.

Baya buqatan hayaniya ko wace irice a yanzun Dan Haka tana shigowa tun kafin tafara Masa hayaniyar ya janyo takardarda tun safe takawo Masa take bibiyarsa ya zari pen ya saka Mata hannu akai ya miqa Mata.

Maganar dataso fada na nuna damuwar barowar da yayi baici abincinba Yana miqa Mata takardar ta shanye maganar da cewa"

Thank you my love.." ta juya da tsananin farin ciki ta tafiyarta tareda mantawa da maganar rashin cin abincinsa Dan dama kusan Dan hakan ne tazo tayi kisisinar.

Tsabar tsananin buqatan kudin da yanda take matse dasu yasa tana zuwa daki takira A Abdoul ta sanar Masa zai Bata kudi masu yawa Turaki ya saka Mata hannu,
Tanason rabi cash rabin a account Dan Haka yazo yanzu ya kawo Mata cash din.

Hakuri yabata tareda sanar da ita Yana office din turaki haryanzu wasu ayyukan masu mahimmanci yake bazai samu fitowaba ko gobe idan Bai gamasuba bazai iya zuwa koinaba gskia.

Tsoki ta sake a fili tace"

Ganinan zuwa yanzu office din na amsa tunda dama a office dinsane sbd Ina buqatan su kwana hannuna gobe tun 6 akwai inda zanbi flight din Athens.

Ok" kawai yace Mata kafin ya aje wayar.

dayake Bata Saba tambaya fitaba ko sanar Masa saidai tafiya Mai nisa Haka Dan Haka Kai tsaye ta sauya Kaya ta nufi dakin Laylah ta karbi key din motarta sbd ita Bata Jan mota da kanta Dan Haka duka motocin gidan ba wadda ba'a fita cikinta da ita Kuma sunyi Mata girma data dauka yanzu ta fita tunda itace zata tuqa shiyasa ta karba ta Laylan datake ta Yan Mata Mara girma sosai sai shegiyar tsada.

Bayan fitar mum din sbd karta dawo kawo Mata key din motar batanan yasata barin kofar dakinta bude batareda ta Sanya key ba dama Bata wani saka key a dakin sai jifa jifa sbd Cindy dake shigowa tunda safe gyaran dakin idan tana bacci kokuma wani aikin.

Tashi tayi daga kwantawar datai da rigar jikinta Dan bazata iya bacci da itaba ta nufi closet dinta ta zuge zip din rigar daga sama har qasa tana kokarin janyo Ciro pyjamas dinta ta Sanya aka bude dakin tareda shigowa Kai tsaye tanajin anrufe ta dakata daga abinda takeyi batareda ta juyoba Dan kuwa atmosphere din dakin daya sauya da sanyayyan qamshin Bois elite ya tabbatar Mata da ko waye
Dan haka sai jikinta yayi Sanyi ta kasa juyowa sai Ajiyar zuciya data sake a boye.

Qarasowa yayi Ahankali bayanta Yana tsayuwa akai knocking kofar dakin.

Ta juyo tareda kallonsa kafin ta juya ta kalli kofar
Kafin tayi wani motsi ya bude Baki Kai tsaye yace"

come in.

Bude kofar Cindy tayi tashigo daukeda qaton ceramic tray jere da noodles Mai zafi daya saka ta dafo Mata da Madara Mai sanyi sai green tea dinsa.

Aje komai taye ta juya ta fice da tray din tareda Jan kofar dakin Takoma kitchen ta dasa aikin zaman gadin dawowar Ms Na'ima duk da tasan idan tayi fitar dare irin Haka zata dauki time Bata dawoba.

Bayan fitar Cindy kallon abincin tayi zuciyarta na narkewa ta maida kallonta kansa da Ido ya nuna Mata abincin Yana kamo hannunta ya sakata jikinsa ya rungume tareda sauke boyayyan Ajiyar zuciya,

Duk kamewarsa da basarwarsa tareda riqe kansa dayayita Yi kwanakin akan rashinta sai dayayi azabtuwan zuciya Mai tsanani da har ya kame kansa a sama ya daina fita aiki sosai.

Itama tsananin kewarsa yasata sakin hawayen shagwaba tana lafewa jikinsa har sai dasuka Jima ahakan kafin ya saketa ya Kama hannunta Suka Isa qasa Suka zauna K??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????an center carpet Dake dakin.

Jikinsa ta zauna yaringa Bata noodles din ahankali tanaci har sai data koshi ya kalleta Yana goge Mata baki da tissue ahankali yace"

Are you sure ya Isa Haka?

Yes Abbah"" tafada tana daukan tea dinsa shima ta miqa Masa ya karba Yana Sha ahankali Yana kallon yanda take kallonsa harya shanye.

Miqewa sukai yakaita toilet tayo brush suka fito ya zauna bakin gado tareda zaunar da ita Kan qafafunsa suna fuskantar juna yace"

Fushin buya a daki

23 / 36