Noor Albii Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 36

3K to 6K   out of 107.4K words

fice shima abdullahin tare suka fito taja Masa kofa.
gurin Anty Sa'adah ta nufa Dan karatun dare datake koya Mata na littafan addini.

Acan takai kusan karfe goma na dare suna karatun kafin ta harhadawa anty Sa'adah dakin ta gyara Mata shimfidar gadonta dasuka zauna Baki taje ta dauko Mata ruwan dare datake yawan tashi Sha ta aje Mata kafin ta fito taje ta rufe gidan da koina ta nufi nata dakin tayi Shirin kwanciya tayi addua ta kwanta.


=?G?=?G?=?G?Kuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete =?G?=?G?

Mamuhgee @Arewabooks



*_Rabo sai Mai shi...Bata taba saka ran shigowarsa ko zama jigo a rayuwarta ba sbd kallon datake Masa amatsayin Uba,Abokin mahaifinta,Amininsa Kuma Mariqi.!_*
*_Soyayyace tashiga tsakaninsu Mai girma da qarfi batareda sun ankare da hakanba bayan dukkaninsu sun haramtawa kansu hakan,Shin ta yaya zata kalla mijin yayarta,Yar uwarta wadda ta riqeta tamkar yanda uwa me riqon 'da amatsayin nata mijin?_*
*_Qaddararsu wannan kokuwa itace rabonsa tun farko?_*
*_NOOR ALBI Hasken rayuwata_*
_Littafina dayazo muku da wani salon na dabam Wanda soyayyarsa ta kere sauran labaraina,salonsa ya bambanta da sauran,nishadinsa da shauqinsa na musamman ne_
_Fata dai ku kasance taredamu kuji zafi zafin damuka dawo muku dashi_
*_NoorAlbi#MAMUH_*

Follow me @ArewaBooks
Mamuhgee For my latest updates


*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_

*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_

*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_

*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_

*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya=?G?
*_09032345899_*

*KATIN MTN*

09166221261
[7/10, 9:09 PM] +234 704 076 8969: *_NOOR ALBI_*
_*Mamuhgee*_



2
Ajiyar zuciya anty Sa'adah ta sauke lokacinda taga laylan na aje plate din gefe daya alamar ta koshi
Ta dauki ruwan dake da sanyi sosai
Saikuma ta maida ta aje Dan batashan ruwa Mai sanyi sosai sbd lafiyarta na daya daga cikin abubuwan datake kiyayewa badan kantaba sai Dan kula da Abban da gidan gabaki daya Dan kuwa idan ta kwanta ciwo komai cak yake tsayawa a gidan duk da ba wani babban gida bane ko gidan taro su kadaine agidan Wanda yakeda iya nasa girman na masu rufin asiri.

Miqewa tsaye tayi batareda ta kalli Anty Sa'adah ba ta nufi kofa daukeda plate din da ruwan cikin sanyi tana cewa"

Zanje nafara aikin abincin Rana
Lokaci yafara ja.

Ficewa tayi tabar Anty Sa'adah na bin bayanta da kallon Kamar koyaushe cikin jin qauna irin ta jini dakuma tsantsar burgewa da laylan ke Bata akoda yaushe Dan kuwa Babu abinda Layla ta baro mahaifiyarta tun daga kalar fatar,da jikin,da tafiyar dama sanyi da nutsuwa Wanda hakan kesa Koda mugun kallo Momy Bata kaunar kallon fuskarta sai da dalili Wanda kallo daya take Mata ta dauke Kai,
Ita kanta anty Sa'adah so daya taga fuskar mahaifiyar Laylah
Shine lokacinda sukaje asibiti tareda momyn da aka Kira cewan Abban yasamu hadari aka kaisu har gadon mahaifiyar Laylah alokacinda ta haifeta,
Kallon mintuna masu tsayi Momy tayiwa ZAINAB da jaririyarta kafin suka juya suka fice Bata sake ganin fuskarba har yau saidai Akan fuskar Laylah.

Wayarta ta dauko ta Danna Kiran umma Jamila yayar Momy Wanda ke ji da Sa'adah din itama Kamar itace ta haifeta sbd ita Bata taba haihuwaba.

Dan madaidaicin kicin dinsu ta Isa ta ajiye plate din hannunta tareda Dora ruwan data dawo dasu akan fridge su huce kafin tasha
Ta tattara kayan da akai amfani dasu tafara wankewa cikin Dan sauri sbd lokaci yaja Mata sosai.
Tana gamawa ta goge kayan ta saka a kwando ta dauko tukunya ta kunna lafiyayyan risho dinsu babba ta Dora abincin Rana ta fito ta nufi palon gidan Wanda yake daukeda dakin Momy a gefe saina anty Sa'adah a gefensa sai nata daga can gurin hanyar fitowa palon.

Tsaf tagyare palon ta nufi dakin Momy ta gyaro takoma dakin anty Sa'adah ta gyara kafin ta fito ta nufi palon abbansu Dake dayan gefen tashiga da sallama duk da tasan suna daga kurya Momy na magana dashi Wanda sai babban al'amarine kesa Momy magana dashi Dan haryanxu babu Wanda yasani akan akwai aure tsakaninsu haryanxu kokuwa zaman rufawa Kai asiri suke? itadai abinda tasani a gidan shine zaman alfarma take.

Gyaran palon takeyi cikin nutsuwa saiga momyn ta fito ta fice har lokacin Bata dagoba Saida tagama gyarawa kafin ta nufi dakin Abban da sallama idanuwanta akansa ta qaraso tafara gyaran dakin duk da Babu inda dauda ko rashin tsafta yake a dakin kullum tana gyarawa hakama kullum sai Abdullahi yazo yayiwa Abban wanka da wasu abubuwan tareda wankin kayansa.

Daga zaunen dayake kansa a langabe gefe ya zuba Mata ido cikin yanayin Mai tsananin 'daci da damuwa tareda tausayinta Mai tsanani,
Akan idonsa 'yarsa da zainab ta taso cikin bauta da rashin walwala,
Ta taso cikin kadaici da maraici,
Badan Sa'adah ta tallafi rayuwarta ba da zuciyarsa bazata iya kawo yanzu tana daukan tsananin baqin ciki da damuwarta ba
Shiyasa har abada bazai daina godewa Sa'adah da momyn ba ko Yayane dai sun tallafa rayuwarta alokacinda baya iya tsinana Mata komai amatsayinsa na mahaifinta...

Saidai babbar gagarumar damuwarsa shine shin wane Hali zata shiga idan babusa?
Tayaya zatai rayuwa Kamar kowa tasamu farin ciki?
Ya tabbatarda rashinsa zai qarasa juyarda duniyartane gabaki daya sbd har abada zata qare a bauta da wahalar gidan Dan kuwa kowane lokaci Sa'adah Dake tallafarta zatai aure ta tafi tabarta.

Hawayene suke bin gefen fuskarsa suna gangarowa zuwa kan kafadarsa da kayansa
Zuciyarsa na tsananin quna cikeda damuwa.

Ajikinta taji kukan mahaifin nata
Ta waiwayo ahankali a natse ta kallesa da idanuwanta da ako yaushe suke hasko Masa mahaifiyarta ya rintse ido hawayensa na tsananta gudu alamar kukane Mai tsanani yakeyi na zuciya Dan baida lafiyar fitar sautin kukan ne.

Qarasowa tayi gabansa a natse cikin sanyi ta zauna tareda Dan sauke kanta qasa tsawon mintuna batareda tace komaiba,
Tissue dage gefe ta zaro guda uku ta dago fararen idanuwanta dasukai ja take batareda hawaye sun taru cikinsu ba kokuma suka gangaro ta zubawa Abban takai hannu ahankali tafara share hawayensa Wanda hakan yasa hawayen nasa Suka sake barkewa ba kakkautawa,

Yanajin radadi da zafin Zuciya ba damar furtawa kokuma bayyanawa,
So yake ya bude Baki yasaka Mata albarka tareda Bata hakurin yanda quruciyarta da yarintarta take neman qarewa agurin dawainiya dashi.

Batace komaiba sai share hawayensa datakeyi ahankali tana kallonsa
Yasan bazatai maganaba sbd Yana iya hango tsananin dacin da zuciyarta ke cikk a ganinsa hakan
Dan Haka yafara kokarin danne kukansa Yana Dan sauke kansa daqyar sbd wani lokacin kasa kallonta yakeyi sbd nauyi duk da Yana matsayi na uba.

Ahankali ahankali take qarasa goge hawayensa har zuwa Kan rigarsa Sama sama cikin nutsuwa.

Damqe tissue din tayi a tafin hannunta bayan ta Gama goge Masa ta sake dagowa ahankali cikin sanyi da nutsuwa ta kallesa tsananin qaunarsa na bayyanuwa akan fuskarta ta bude Baki a natse tace"

Har abada bazan daina sake fada maka ba laifinka bane,
Qaddararmu ce mu duka ahaka,
Allah Bai dauki ran mahaifiyataba sbd wannan al'amarin
Ya karba ranta ne sbd lokacinta yayi,
Kadaina kallon kanka a matsayin uba daya Gaza,
Kallonka ko ahaka Yana bani nutsuwa da qarin qarfin tawakkali ga ubangiji.
Ka cire damuwar yanayin zamana da rayuwata sbd ban taba ganin laifin kowaba agame da hakan,
Idan Dole anason ganin laifin wani
Nice Mai laifin,
Sbd rabon haihuwata ne,
Rabon zuwana duniyane yaxo ta hanyar tarwatsa rayuwarku ku duka,
Ahakan har abada bazan taba daina yiwa Momy addu'a ba sbd koma yayane Bata barni nayi rayuwar titi ba ta barni Ina rayuwa a qarqashin inuwarta data 'yarta
Hakan ma ya isa ka godewa Allah.

Rintse idanuwa yayi Yana Dan daga Mata hannu kadan akan ta Kama.

Kama hannun nasa tayi ta damqe Suka sauke ajiyar zuciya atare kowanne Yana kallon Dan uwansa.

Saidataga yadan kawar da damuwar kafin ta saki hannunsa ta qarasa gyara dakin tadawo gabansa ta dauki ruwa ta zuba a cup takai bakinsa tana basa
Wasu na shigewa wasu na zubowa tana gogewa da tissue.

Tana Gama basa ruwan tasake goge Masa jiki kafin ta fice daga dakin ta koma kicin gurin aikin abincin data Dora.

Qarfe daya da rabi tagama komai tasake gyara koina kafin ta nufi dakinta Dake da Dan qaramin toilet aciki tayi wanka tareda alwalar sallar azahar ta fito tafara yin sallah kafin ta shirya cikin doguwar rigar atampa Wanda anty Sa'adah ta Bata Dan kuwa kaf suturarta kayan anty Sa'adah ne,
Bata taba saka sabon Kaya a rayuwartaba sai kayanda anty Sa'adah tasaka tacire tabata
Duk da bayan kusan shekaru takwas zuwa Tara da anty Sa'adah ta Bata akwai banbancin jiki Dan anty Sa'adah ba ramammiya bace hakama bawani qibane da itaba saidai batada tsayi
Sabanin itakuma datake da Dan tsayi daidai
Hakama batada jiki Amma tafi anty Sa'adah nonuwa sbd anty Sa'adah jikinne kawai da ita batada nono ko kadan,
Wasu kayan idan anty Sa'adah din ta Bata tana kaita gurin wata tela Dake anguwar a rage Mata wasu Kuma hakanan take yawo cikinsu harta tsufa.

Fitowa tayi ta nufi kicin ta dauko abincinsu Momy da anty Sa'adah tafara kawo palo Dan Nan sukecin abincin.
Kicin Takoma acan taci nata sama sama tana gamawa ta nufi palon abbansu sbd ganin lokacin Shan maganinsa yayi.

Da sallama tashiga palon Kai tsaye
Saitaga baqi
Bakuma kowa bane face Dr Abbakar wanda yake babban Orthopedic likitane yasan Abban ne shiyasa har lokacin shine yake riqe da ragamar kula da Abban dakyau hakama da kansa yake Dan duddubasa ata bangaren paralyze dinsa daya saka gefen jikinsa baya Aiki sosai duk da dayan gefen ba laifi Yana aiki
Kuma ahakan danma ya tsaya tsayin dakane akan nemawa Abban lafiya shiyasa ba wani sosaineba rashin aikin gefen dan wani zubin ba'a ganewama.

Tareda Abdullahi babban Yaron Abban Wanda har lokacin halacci yasa yake tareda dashi Yana taimakawa gurin hidamar kulawa dashi,
Kusan duk wasu hidimar asibiti madai shine yake jagoran saidai Laylah tabisa abaya.

Ganinsu kowanne fuska ba wani walwala yasata juyawa Takoma ahankali bayan tagaida Dr Abbakar din cikin nustuwa.

Bayanta dukkaninsu sukabi da kallo har Dr Abbakar din Wanda yariga yasan damuwar Abba ba akan rashin kyawun results dinsa dasuka fito na asibiti akan yarsa ne wadda yakejin ko yayane idan Yana Raye tana abun kallo da dogaro Koda Baida wata moriya agareta dagashi har ita suna debewa juna kewa da baqin ciki.

Ajiyar zuciya Dr Abbakar yayi shima cikeda tausayin Abban dama laylan
Ya dago ya kalli abdullahi ya miqa Masa wasu takardu yace"

Malam Abdullahi karba wannan Dan Allah kaimun mota Ina fitowa.

Karba yayi cikin girmamawa jiki a sanyaye ya fice.

Bayan fitar Abdullahi sake sauke numfashi Dr Abbakar yayi tareda kallon Abba da yayi nisa cikin tunani fuskarsa Babu wani alama dayake bayyanarda yanayin da zuciyarsa take ciki,
Zuwa yanzu zuciyarsa tafara riqewa da tawakkalin tabbas komai kaddarowar ubangijine,
Duk kaunar dayakewa 'yarsa yasan idan lokacinsa yayi Allah bazai barsaba,
Hakama Babu wata qaddarar da Allah ya sauko Mata dazai iya sauya Mata,

Results dinsa sun nuna infection daya shiga qashinsa tun farko farkon hadarin da ba'a yanke qafafunba sunyi yawanda harsun fara shiga jininsa,
Tabbas yasan yanda yakeji ajikinsa lokacinsa yakusa zuwa
Saidai duk ya kalli Layla da rayuwarda zai barta aciki hankalinsa tashi yakeyi yabar jikinsa,
Tsoro da fargaba tareda kukane suke lullubesa aduk lokacinda yayi tunanin hakan.

Alhaji MAHMOUD tabbas rikicewar lafiyarka a Yan lokutan Nan sunada babbar nasaba da damuwa da kuncin dakake Tarawa aranka,
Da zaga sassauta damuwa da tunani kasamu hutun zuciya Dana qwaqwalwa ko yayane za'a ringa samun sauki ko yayane.

Sunkuyar da Kai Abban yayi ahankali cikin irin yanayinsa na masu ciwo irin nasa batareda ya iya ko dago idanuwansa ya kalli Dr Abbakar din ba.

Shiru sukai tsawon mintuna kafin Dr Abbakar din ya miqe tsaye Yana kallon abban cikin kulawa yace"

Zan tafi gobe zandawo zamu sake dibar sample ajikinka Inshallah saimu gwada wani awon mugani,
Allah yaqaro lfy.

Juyawa yayi ya fice daga dakin har lokacin Abban Bai motsaba Yana yanda yake.
Ahankali idanuwansa suka sauya zuwa ja jikinsa na daukan zafi na wani irin zazzabi Mai qarfi daya saukar Masa atake saidai zuciyarsa ta riqe yakasa tunanin komai saina Mutum daya daya fado Masa a Rai wato babban Amininsa Wanda shikadaine zai iya magance babban abunda yazo ya tokare ransa tsawon shekaru wato damuwar Laylah.
#MAMUH#




=?G?=?G?=?G?Ku??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????yi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete =?G?=?G?


Mamuhgee @Arewabooks




*_Rabo sai Mai shi...Bata taba saka ran shigowarsa ko zama jigo a rayuwarta ba sbd kallon datake Masa amatsayin Uba,Abokin mahaifinta,Amininsa Kuma Mariqi.!_*
*_Soyayyace tashiga tsakaninsu Mai girma da qarfi batareda sun ankare da hakanba bayan dukkaninsu sun haramtawa kansu hakan,Shin ta yaya zata kalla mijin yayarta,Yar uwarta wadda ta riqeta tamkar yanda uwa me riqon 'da amatsayin nata mijin?_*
*_Qaddararsu wannan kokuwa itace rabonsa tun farko?_*
*_NOOR ALBI Hasken rayuwata_*
_Littafina dayazo muku da wani salon na dabam Wanda soyayyarsa ta kere sauran labaraina,salonsa ya bambanta da sauran,nishadinsa da shauqinsa na musamman ne_
_Fata dai ku kasance taredamu kuji zafi zafin damuka dawo muku dashi_
*_NoorAlbi#MAMUH_*


Follow me @ArewaBooks
Mamuhgee For my latest updates



*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_

*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_

*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_

*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_

*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya=?G?
*_09032345899_*

*KATIN MTN*

09166221261
[7/10, 9:12 PM] +234 704 076 8969: https://arewabooks.com/book?id=628264fab77ff582983da456





*_NOOR ALBI_*
_*Mamuhgee*_

4
Washe gari tunda safe da hadari Mai qarfi aka tashi da iska
Da sauri ta fito palon ta nufa windunan dake palon guda biyu ta rufe ta nufi dakin momyn da sauri ta bude ahankali sbd karta dameta da motsinta
bakinta daukesa sallama ta shiga
Momyn na kwance kan gadon ta nufa windon dakin ta rufe ahankali ta fito ta nufa dakin anty Sa'adah itama ta rufe Mata nata windon kafin ta fito tsakar gidan lokacin iskan yaqara qarfi da gudu ta qarasa dakin abbanta ta rufe Masa koina duk da idonsa biyu bata tsayaba sbd aikin gabanta ta fito da hanzari tafara kwashe shanyar wankin momyn datai jiyan duk wasu har zun fado sunyi qura tahau kwashewa zuwa lokacin tuni ruwa masu qarfi suka sauko ta shiga ciki da sauri ta aje kayan palon Kan kujera duk da tasanma saita Kuma wanke wasu
Ta fito tsakar gidan ruwan na dukanta tahau tattara kayan dake tsakar gidan takai na kaiwa cikin takai na kaiwa Palo tasake fitowa ta taje ta bude gida sbd Kar suna ciki Abdullahi yazo basuji bugun gidansaba.

Kofar kicin ta tsaya ta kakkama gefen? kayan jikinta ta Dan matsesu tarage musu ruwan dake tsayaya ta zame Dan kwalin kanta shima ta matse daga waje ta shanyasa Kan kofar kicin din sbd Kan yasha iska Dan kuwa ta barsa da dankwalin sanyin Kan Dana dankwalin suka hadu sanyi zai shigeta ya kwantar da ita
Babu ciwon Dake tsananin azabtar da ita kamar sanyi idan yashigeta
Gashi kwantawarta ciwo ba kyau
Wuya takeci Mai tsanani Dan duk rintsi saitayi aikin dake kanta ga abbanta idan ta kwanta batada Mai kulawa dashi Dan hakan nema take dannewa duk girman ciwo sai idan yafi qarfinta Dan Haka takeda kiyayewa akan lafiyarta.

Risho ta kunna ta Dora ruwan zafi ta hada qullun kunun alkamar dazatawa Abban Takoma ta zauna Kan kujera tana jiran su tafada wani irin sanyin ruwan da ake Yana ratsata tanaji.

Ba jimawa ruwan suka tafasa ta hada kunun ta zuba Masa a flask dinsa ta rufe ta juyewa Anty Sa'adah sauran a flask itama sbd tanashan kunu sosai itama musamman nata dayake da Madara take shansa sbd lafiyar fata Inji momy.

Cikin ruwan takuma fitowa takaiwa bbanta ta basa Tasha tabasa magani ta goggoge Masa jiki ta fito Yana binta da kallo yanda take jiqe sharkaf sai Kama jiki take karta jiqa Masa daki Takoma kicin tahau aikin abincin karin kumallonsu momy.

Dakin Sa'adah taje cikin rashin son takurata daga baccin datake tace"

Anty Sa'adah me za'a dafa na Karin?

Cikin bacci Sa'adah ta juya tana sake shigewa Dan madaidaicin bargonta tace"

Laylah duk abinda kikai Amma dai karki manta da kunu na.

Anty Sa'adah jiya Momy bataci abincin dareba sosai Naga abincin yayi saura ko ulcer dinta ya tashine saina dafa Mata ruwan tea da faten dankali kawai.

Kimata duk yanda kikai kaina na ciwo bacci nakeji sosai.

Juyawa tayi Takoma kicin din tahau aiki.
Wani maganin ulcer din momyn tafara dafawa Mai wuyar dahuwa Haka taita jira har yayi kafin ta dafa taliya Mara yaji ko kadan sbd momyn ta juye a kula ta zuba Mata maganin a babban kofi ta saka Mata a fridge duk da Babu wuta zaiyi sanyi sbd ruwan sanyin Dake ciki.

Tana gamawa anan kicin din taci abincin sama sama tagama tai wanke wanke ta sharesa tsaf ta fito lokacin ruwan sun Dan rage sosai sai Dan yayyafi ta nufi dakinta tacire kayan jikinta ta watsa ruwa ta sauya zuwa wata atampar tafara gyara nata dakin fes ta fito tafara aikin gyaran palon tana gamawa tashiga na mum tayi Takoma na anty Sa'adah tayo tafito tsakar gidan shima Tai Masa tas kafin ta fita tasamo garwashi maqota tazo tayi turaren wutarda momyn qaidane sai anmata shi Dan tanason qamshi.

Gurin abbanta ta nufa ta gyare Masa koina taje ta dauko Dan sauran burbushin hayaqin turaren daga palon Momy takawo Nan dakinsa shima yasamu Dan qamshin ko yayane,
sai alokacin ta zauna gabansa bayan ta aje kaskon turaren cikin kulawa a natse Tai Masa Ina kwana tana kallon idanuwansa dasuka qanqance Suka sauya launi da alama Bai samu bacci ba ta dauko ruwa tasake bashi yasa cikin kulawa a natse tabude Baki tace"

Abba?
Akwai wani matsala da kakeji ne?

Saida ya Dan hadiye yawun dayake hadiyewa da dabara daqyar shiyasa shi nasa ciwon baya zubarda yawu ta gefen Baki Allah ya taimakesa saboda saukin dayake samun Yana iya hadiye yawu.

Dan rintse idanuwansa dasukai laushi yayi ahankali alamar yanada damuwa.

Faduwa gabanta yayi da qarfi saidai fuskar Bata nuna hakan
Ta zuba Masa fararen idanuwanta batareda ta iya cewa komaiba.

Hannunsa Dake rawa da gyangyadi yadan daga yayi Mana alamar karta damu bayajin ciwon komai.

Shiru kawai tayi Dan batasan Mai zataceba bayan jurewa ta boye damuwarta sbd ko nacewa tayi tasan abinda yake damun nasa Babu abinda zata iya Masa bayan tashiga qunci da damuwa sai addu'a da take Masa.

Shiru sukai daga ita harshi Dan ko Dan zancen datake Masa wasu lokutan takasa sbd mutuwa da jikinta yayi dakuma damuwar datashiga yanzu din akan yanayin nasa tasan Dole Kam akwai abinda yake damunsa tsakanin jiya zuwa yau din.

Ganin gwara ya kwanta kozai samu baccin yazo Masa yasa ta tashi ta tura kujerarsa har bakin gadonsa da kanta ta mirginasa zuwa Kan gadon ta gyara Masa kansa akan pillow ta rufe Masa Rabin jikinsa sbd akwai sauran sanyi sosai na ruwan saman da aka gama ta bude Masa windows Dan iska da Sanyi na shigo Masa ta fice Takoma dakinta itama ta zauna jigum sbd Haka tata rayuwar take.

Sai qarfe kusan goma Sha daya saura momy da anty Sa'adah suka fito dayake komai takawo musu palon na Kari suka zauna karyawa
Ita Momy tuni tayi wanka kafin ta fito.

Motsinsu yasata aje littafin datake karatu na koyan

2 / 36