Noor Albii Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   14 / 36

39K to 42K   out of 107.4K words

dasuka sauka Kan fararen cinyoyinta Dake bayyane ya daukesu da Yana dakatawa daga kofar.

Da Dan sauran qarfinta tayi saurin miqewa tsaye har towel din na Dan subucewa daga sama da sauri Takoma cikin toilet tana dafe bango batama Gama ankarewa sbd tsananin rudewa da firgitar datai sai wani Aman Mai karfi yakuma kufce mata tafara kelayawa da qarfin gaske Dan babu komai acikin nata.

Cindy ce data kawo tea din tayi saurin ajewa tana qarasawa cikin toilet din ta nufeta lokacin tuni jikinta yasaki agurin ta zube jikin Cindy gaba daya Bata wani motsi.

Ihu Cindy tasaki tana Kiran sunanta da qarfin gaske cikin rudewa ganin Kamar Laylan Bata numfashi....

Kai tsaye shigowa yayi toilet din ya dauketa gabaki dayanta Yana cewa Cindy ta dauko Mata Kaya ta Sanya Mata.

A gado ya kwantarda ita ya juya ya bar dakin Cindy da duka jikinta ke rawa ta dauko wata doguwar Rigar bacci bataredama tasan abinda takeba ta Sanya Mata tafito ta fada Masa.

Dan shiru yayi Kamar Bai jiba Yana nazarin lafiyarsa idan yakuma hada jikinsa da natan Dan bayan fitowarsa Saida yaje yasha magani ya dawo.

Kallon A Abdoul daya iso Yana jiransa yayi Dan Dr Noah baya gari Dole asibiti za'a kaita.

Dakin yashiga ya daukota da kansa yakaita mota batareda ya lura da kayan da Cindyn tasanya mata Saida Suka Isa asibitin bayan an dauketa anyi ciki da ita A Abdoul ne ya kalli Cindy cikin Dan fada yace"

What was that??

Sauke Kai tayi saboda itama Saida Suka iso asibitin ta lura da abinda tasanyawa Laylan
Cikin damuwa da ban hankuri ta saci kallon inda Turaki ke zaune kamar baisan da tsayuwarsu agurinba murya na rawa tace"

I'm sorry sir I....

Abdoul kaita gida takawo wani kayan.

Daga Haka Bai qaraba ya duba agogon hannunsa Dan koma menene bayason su kwana a asibitin data farfado gida zasu koma.

Kaya kala uku ta dauko sbd gudun wani shirmen suka dawo asibitin lokacin har Laylan ta farko tana bacci Dan Haka drugs kawai suka karbo suka dawo gida.

Yana kwantar da ita ya bar qasan gabaki daya ya Haye sama Bai Kuma saukowaba har washe gari Babu Wanda yaga ya sauko breakfast Haka ya wuni Bai fito ba saidai A Abdoul daya damu sosai yayita kiransa karshe dayake Babu Wanda yake shiga samansa bayan A Abdoul shima tunda su Ms Na'ima Suka dawo qasar Bai qara bin hanyar saman ba Dan Haka hankalinsa ya tashi Sosai yayita Kiran wayar Ms Na'ima Bata dauka ba Dan Haka baida zabi bayan Kiran Anne.

Washe gari har dare ba Turakin ga wayayinsa a kashe Dole yanda Anne tace hakan zaiyi duk da yasan ran Turakin Zai baci Idan aka tura Masa Laylah dakinsa,
daddare yashigo babban palon qasa ya tambaya Cindy jikin Laylah ta tabbatar Masa da taji sauki sosai harma yau ta Dan fita taje makaranta.

Kira Masa ita yace Cindyn tayi
Ba jimawa sai gata tafito sanyeda doguwar jacket data Dora Kan kayan baccinta Dan tuni Tai Shirin bacci harma ta kwanta.

Cikin nutsuwa ya sanar da ita kwana biyu Turaki Bai fito ba wayoyinsa akashe shine Anne tace taje tadubosa tunda masu aikin gidan kaf basa zuwa?? gurin.

Shiru tayi tareda sauke kallonta daga kansa zuciyarta na harbawa da fargaban haduwarta dashi sbd abinda ya faru kwana biyu Wanda haramun ne gareta faruwar hakan,
Mijin yayarta Abokin mahaifinta duk da tsautsayine na ciwo da zuwan Abu Amma hakan ya tsaya Mata arai harta fara Jin kamar zamanta anan Bai kyautu ba duk da riqontane ake Amma sai tanajin tsoron zamanta nan Yana shigarta.

Kiran Anne ne yashigo wayarta tana dauka Kai tsaye Annen tace"

Laylah kije kidubo Mana Turakin ko lafiya hankalinmu duk ya tashi ga ba Wanda zai dubaso maza jeki kidubo Mana tun kafin Abu yayi nisa.

Jin hakan yasa gabanta faduwa ta dago ta kalli A Abdoul da duk yayi wani iri lokaci daya na rashin sanin halinda uban gidansa yake ciki Jin yake kamar yayi tsalle yagano lafiyar Turakin.

Da sauri ta juya ta nufi hanyar saman ta Haye gabanta na tsananta faduwa da sauri,
Bata taba ko kallon hanyar Master bedroom dinsaba sbd iyakacinta palon shima sai babban dalili idan ankirata kokuma taje Kai wani abin Dan Haka Bata taba kallon hanyar bedroom din nasa ba...

Tsayawa Tai bakin kofar tana Dan knocking kofar hannuwanta na Dan rawa,
Sake knocking takeyi tafara tsorata da Shirun itama Dan Haka taci gaba da bugawa tana jiran Jin motsi Amma shiru.

Rasa sanin abin Yi tayi ta daga wayarta da sauri ta saka Kiran Anne tana dauka Bata jira me Annen zatace ba tace"

Ba'a bude ba..

Laylah kishiga ki duba
Bari kawai nakira Abdoul ya hawo ya duba..

Komawa gefe tayi tana jiran tahowar Abdoul din sai gashi ya hayo da sauri ya qarasa dakin tareda knocking so daya ya Murda kofar yashige.

Sosai hankalinsa ya tashi da ganin yanayinda turakin yake Dake nuni da rashin lafiya sosai ataredashi saidai Kuma qarfin halinsa yasa Yana zaune Kan sofa tarin magungunansa birjik agabansa wainda yaketa faman Sha Amma erection dinsa yaqi sauka shiyasa ya nesanta kansa da fita ko Ina sbd kallo daya zakai Masa ka iya gano wani abin.

Ahankali ya dago idanuwansa dasukai wani iri yayiwa A Abdoul din daya shigo kallo daya ya dauke Kai yana bude Baki cikin dauriya yace"

Akwai damuwa ne?

Cikin tsananin kulawa da damuwa A Abdoul yace"

Hankalinmu ya tashi da rashin fitowarta Anne tabada izinin nashigo na duba,
Wayarsa yafara laluba Yana cewa"

Zankira Dr Allen yanzu na sanar dashi halinda kake ciki.
Juyawa yayi da sauri yafice Yana Nemo Numbern DR Allen.

Qasa ya sauko Laylah na biye dashi cikin sauri yace"

Ahada Black tea Mai zafi akai Masa Kar asanya sugar likita zaizo ya dubawa yanzu ba jimawa.

Gyada Kai kawai tayi jiki a Sanyaye
Ta nufi kitchen din da kanta ta Dora Masa tea din tana cewa siddika ta gasa Mata bread uku da kwai.

Tana gamawa ta hada a tray ta fito dasu ta nufi saman da tuni har A Abdoul yaje da gudun masifa yazo da Dr Noah duk da bashine likitansa na asalin lalurarsa ba Amma zai iya taimakawa.

Allurar da Dr Allen ya rubuto musu yanzu yanzun itace Dr Noah yayiwa Turakin tareda kallonsa cikin kulawa da nutsuwa yace"

Baka buqatan riqe kanka Haka sosai you have to let it out sbd zakaiwa kanka illa sosai tunda desire din tafara zuwane gadan gadan control nata zai fara wuya saidai Kuma saika lura sosai gurin having first sex din zai iya zuwa da tangarda.,
Amma dai for now Dole zaka daina kokarin dannewa lokacine yazo Dole zaka Bari abinda kakeji ya fita.

Dr Noah na fitowa tareda A Abdoul Dake Palo Yana jiransa Dan Bai shigaba tana shigowa daukeda tray din harma da fresh milk Mai sanyi kadan ta hado duk ta kawo.

Kallonta A Abdoul yayi Yana cewa"

Ki Kai Masa bedroom...

Ficewa sukai ganin dakin bude Kuma ganin Suma duk ciki Suka fito ya sanyata nufar dakin Kai tsaye tareda sallama Mai sauti Bata dagoba ta kutsa Kai dakin qamshin Bois elite na tashi tako Ina Yana rikita kanta da qafafunta Dake Dan rawa ta nufi table Dake dakin tafara kokarin ajiyewa.

Tunda tashigo Yana zaune a sofa Bai motsa ba bayan idanuwansa dasukai taushi Babu abinda ya zuba Mata Yana kallon yanda qafafuwanta ke hardewa
Tana dososhi ya dauke kallonsa daga gefenta gaba daya musamman qamshinta na Creed Dake tashi daga jikinta ahankali ahankali.

Tana ajewa cikin nutsuwa tace"

ALLAH yasauwaka yakawo afuwa.

Juyawa tayi ta fice tabar dakin da qamshinta dabaiyi qarfi da yawan nasa ba Amma hancinsa na Jin natan na shigarsa.

Da sanyin jiki tayi bacci hakama da safen da sanyin jiki ta tashi batareda tasan meya kawo Mata hakan ba Haka ta shirya ta tafi makaranta tagamo wuninta tadawo har lokacin batajin dadin ranta Sam.

Ms Na'ima lokacinda saqon Turaki na ticket da akai Mata booking na dowowarta yashigo wayarta tayi mamaki sosai saidai koda Laylah takirata ta sanar da ita bayada lafiya kwana biyu saita fasa dawowa Dan Bata Gama abinda takeba tunda ba wani abin zatai Masa idan tadawoba.

Kwana biyun sosai ciwonsa ya damu Laylah dake daukan hakan amatsayin kaga Wanda ya kyautata rayuwarta data mahaifinta dama ta Yar uwarta tagansa cikin Hali na ciwo.

Sam baya saukowa cin abinci yanzu saidai Cindy da A Abdoul yace anbawa damar Hawa Kai Masa abinci acan sbd har lokacin Ms Na'ima Bata dawoba.

Da wannan gidan yakoma kamar rayuwar kadaici takeyi sbd yanzu kowa Bata gani daga ita sai masu aiki take rayuwar gidan,
Kwata kwata ta daina ganin Turakin sbd ya yankewa kansa nesantarta sbd yanayin lafiyarsa ga Na'ima Bata dawoba Dan Haka yasaka kansa zama busy Sosai Sosai ko gidan Baya dawowa sai dare daya shigo Babu Mai sake ganinsa a qasa sai zai fita Kuma.

Ganin Haka ta maida hankalinta Kan karatunta itama ta rage zama gida sosai koyaushe tana makaranta ko gidansu Sofia.

Ahaka Ms Na'ima ta shanye kusan sati hudu kafin tadawo lokacin Turakin baya gari yayi tafiya Dan Haka sai gidan yadan dawo Mata daidai Amma hakanan takejin kewar su Anty Sa'adah.

Washe gari tana dawowa daga makaranta tana shigowa gida sai ganin Anne tayi A Palo zaune batasan lokacinda tasaki wata dariyar farin ciki ba tana qarasawa da sauri ta rungume Annen tana cewa"

Anty Sa'adah fa???

Da ido Annen ta nuna Mata bedroom dinta tana cewa"

Tana jiranki a dakinki hutawa takeyi.

Sakin Anne tayi ta nufi dakin ta tadda anty Sa'adah kwance kan gadonta tana bacci tayi wanka da alama Dan rigar jikinta bamai nauyi bace.

Kasa tada ita tayi ta aje handbag dinta tareda wayarta tana fadawa toilet da sauri tayo alwala tazo tayi sallah har lokacin anty Sa'adah Bata farka ba Dan Haka ta fito Takoma gurin Anne tana sake bayyanarda farin cikin zuwansu dayake Ms Na'ima Bata Nan tafita Koda suka iso.
#MAMUH#
[7/10, 9:29 PM] +234 704 076 8969: *_Mamuhgee 24_*
Jikinta amatuqar mace yake Yana rawa ta janyo rigarsa Dake gefenta ta rufawa jikinta ta sauko gadon tareda nufar kofa ta fice dakin ta nufi Wanda take ciki tashige.
Tana Shiga daki toilet ta nufa da sauri itama ta sakarwa kanta ruwa tana Jero Ajiyar zuciya ba kakkautawa sbd ba qaramin yamutsa kwanyarta da birkita tayiba da abinda yafaru mintinan dasuka wuce a bedroom dinsa.

Saidataji tana neman shidewa ta fito ruwan tadauro towel ta fito ko kanta daya jiqe da ruwan data sakarwa kanta Bata busarba ta saka wasu kayan baccin ta kwanata tareda duqunqunewa cikin bargo.

Asubar fari ta tashi sbd dama Bata samu damar bacci ba ko kadan
Dukkanin abinda yafaru ya tsaya Mata cikin Kai koina ta juya hannuwansa takeji suna yawo jikinta,
Bakinta kuwa harda safen datai brush tanajin sauran qamshin Lebon mint mouth wash aciki.

Wayarta tahau dubawa Bata ganiba Dan Haka tayi amfani da iPad dinta tayiwa kanta booking ticket na komawa Atlanta
Ta tashi tayo wanka ta shirya cikin dogon pencil skirt da Riga ta Dora kimono har qasa akai ta fito janyeda akwatinta cikin sa'a kuwa batagansa ba bare motsinsa ta fito ta tari taxi sai airport.

Kodata Isa Atlanta Sofia takira tazo ta dauketa takawota gida lokacin mum Na'ima na babban palon gidan tareda Haj Zinat suna fira hankali kwance suna jiran agama hada dining suje cin abincin Rana.

Tare suka kalleta dukkaninsu cikin kulawa da farin ciki Haj Zinat tace"

Masha Allah Laylah tadawo
Ashe da rabon zamu hadu kafin natafi.

Janyo hannunta ms Na'ima tayi tana cewa"

Happy to see back baby,.so ku gaisa da Zinat tanata son ganinki kafin ta tafi kuwa..

Wani irin nauyin mum din takeji Mai tsanani da kunyar kanta Dan sai tanajin Kamar wani zaisan abunda yafaru tsakaninta da Turakin acan
Ta qaraso a darare gabansu tana Dan sakin murmushin Dole da sanyin murya tace"

Sannu da suwa Momy Zinat,
Ya hanya?
Yaya su Anty farida?

Lafiya kalau Laylah
Ya karatu?
Da rayuwan Atlanta?
Kinata kokari ko?
Allah ya taimaka kinji?

Amin Momy Zinat nagode.

Kallon Ms Na'ima tayi a sanyaye tace"

Mum ya gida?
Bakizoba nadawo sbd school Sofia nata kirana.

Da kulawa tace"

Barin nayi har Zinat ta tashi tafiya saimuje LA din tareda ita itama ta duba Abban naki dama daga can ta wuce.

Murmushin yake kawai tayi tareda nufar hanyar dazata kaita bedroom dinta tana cewa"

Ok Bari na shiga ciki da ciwon Kai na dawo sbd mura.

Tana shigewa dakinta Cindy dake gyara Mata dakin tun shigowarta ta Isa dakin tafara gyara Mata kafin tashigo ta kalli Laylan tana cewa"

Welcome Ms Laylah.

Kai kawai ta gyada tareda aje kayan hannunta tayi hanyar toilet tashige.
Kodata fito Cindy tagama komai ta fice Dan Haka sallah kawai tayi ta Haye gado ta kwanta ko abinci Bata fito taciba taredasu mum Na'iman Dan wani irin mutuwar jiki yake tareda ita.

Sai dare ta daure ta fito sbd mum Na'iman datake ta tambayar lafiyarta kalau kuwa
Dole ta sake tafito sukaci abincin dare tare harma ta zauna Palo tana Amfani da iPad dinta kusan karfe goma kafin ta tashi tashige.

Washe gari tanada zuwa school Dan Haka tana tashi wanka tayi sama sama Tai breakfast sbd tayi latti ta wuce makaranta.

Kwana biyu Bata zama Sosai sbd makaranta kafin tasamu kanta har tana hutawa gida sosai
Daga bayama dasuka samu break koyaushe tana kicin taredasu Cindy matuqar tana gida Dan mum Na'iman kam tayi busy Sosai Bata zama sunata hidimar business dinsu dasuke na kayan da Haj Zinat zata tafi dasu.

Ranar data cika kwana Tara da dawowa ranar Turaki ya dawo gidan tana fitowa daga dakinta da safe ya nufa dining room sanyeda fararen Riga da wando kanta sanyeda hular sanyi fara itama ta shiga Kai tsaye
Sai ganinsa tayi zaune Kan kujerarsa sanyeda milk Balenciaga polo shirt da milk Wandon Alexander yayi wani irin fresh haske gabaki daya yacika dakin da qamshinsa fuskarsa na Kan abincin dayake ci Bai dagoba.

Rudewa take nemanyi sbd faduwar da gabanta yayi na rashin tsammanin ganinsa ta saci kallon Ms Na'ima Dake zaune tana cin abincin tana Masa Dan surutu ta daidaita kanta da murya Mai Dan sanyi tace"

Ina kwana Abba.

Dagowa yayi a zuba Mata fararen idanuwansa dasuka qarasa rudar da ita Amma ta Dan Dake tana kallon Ms Na'ima tace"

Good morning mum.

Morning Laylah
Qaraso Mana,
Abbanki ma gashi yadawo
Zo muyi family breakfast.

A sulale ta qaraso tana zaunawa batareda takuma dagowaba.

Gurin yayi tsit suna cin abinci sai Ms Na'ima Dake zuba zancenta na kisisinar son bin Haj Zinat dazatai Dubai su qarasa siyayyar kayan manyan shagunansu Dake Nigeria din Dan Haka kudi takeso sosai yabata dakuma qarin kamar yanason daukar tsarin zamanta a gida a Yan kwanakin ta lura saidai tunda yariga ya Saba Mata da baya takurata sai hakan yazo Mata wani iri bakuma tanajin zata iya zama guri daya.

Suna gamawa ita tafara tashi ta bar gurin Dan tanajin takurar zaman dama
Daki Takoma ta kunna wayarta da Cindy tabata tana fitowa tace A Abdoul ne yace tabata.
Cajin wayar tasaka tareda Shiga ciki tana duba abubuwa.

Wunin ranar ms Na'ima Bata zaunaba sbd gobe da qarfe shidan asuba jirginsu zai tashi Dan tana lurada Turaki zai hanata tafiyar saita nuna Masa jikin qanwar mahaifiyarta uwar riqonta ya tashi dama ba lafiyayya bace Dole yabarta tayi tafiyar da sharadin sati biyu cif zatai tadawo.

Bayan tafiyar mum Na'ima sai itama Bata wani cika zama ba Dan Haka Yan aikin gidan ne sukadai koyaushe.

Kwanan mum biyar da tafiya tadawo school a gajiye taci abinci kawai tayi wanka ta kwanta da wuri Dan Haka ko dining bataje cin abinciba sbd ko Turakin Ms Na'ima na tafiya ya daina zuwa cin abinci dining itama daina fitowa tayi a daki ko kitchen takecin abincin ta shige.

Kwana biyu saita lurada kamar bayanan ta daina ganin A Abdoul a gida Dan Haka itama hutu take kwana biyun na fashin zuwa makaranta.

Sanyeda Riga da skirt marasa nauyi ta fito daga kicin bayan sungama barnarsu a kitchen itadasu siddika saiga Sofia Nan Suka dunguma zuwa dakinta suna Hayaniya
Sai dare Sofia ta fito zata tafi tasaka driver yakaita tadawo ciki Kai tsaye wanka tashiga.

Tana fitowa ta tadda siddika dakinta tana jiran fitowarta.

Kallo daya Tai Mata tana nufar gaban mirror tace"

Akwai wani abin ne?

A Abdoul yau duka Bai shigoba ga abincin sir Turaki is ready
Munkira A Abdoul din yace afada Miki kikai Masa sama.

Shiru tayi tsawon mintuna tareda tuno abin daya faru dasu a LA tanason Jin fargabar zuwan Amma ganin Nan gidane hakan bazai taba faruwaba
Bare tasan abindaya faru a LA wani tsautsayine da dukkaninsu yakamata su manta Dan kilama shi bazai iya tuna abinda ya farun ba.
Ta cire tunanin komai tace to
Siddika na fita ta shirya cikin kayan baccinta Riga da wando ta saka doguwar kimono Mai zip har qasa ta fito kanta rufe da hular kayan baccinta taje ta dauka abincin ta nufi saman tana cire tunanin komai aranta.

Bakowa a palon bayan tv Dake aiki ba murya ko kadan ga sanyin AC da yayi yawa da qamshinsa daya Gama kame palon duk da humidifier Dake aiki tana sakar da nata qamshin Amma nasa ya fita daban.
Kayan tea tagani ajiye Kan table na kujerar dayafi zama alamar yariga yasha tea Dan Haka ta ajiye abincin Kan table tana kokarin juyawa sai Kuma ta juyo ta kalli kofar master bedroom dinsa ta qarasa tayi knocking ahankali Dan sanar dashi takawo abincin.

Shiru ba'a budeba
Takuma bugawa ahankali saitaji shiru
Dan Haka sai ciwonsa na wancan Karon ya Fado Mata arai ta janye daga jikin kofar ta daga wayarta Dake hannunta ta saka Kiran A Abdoul Yana dauka ta sanar Masa takawo abincin tayita buga kofar Abban Amma ba motsinsa.

A Abdoul Baya gari Amma cikin daren zai dawo Dan Haka yace"

Nakira wayarsa akashe suke tun yamma karki tafi kishiga ki duba ko lafiya.

Kashe wayarsa yayi sbd Yana airport sunfara shiga jirgi dama dan Haka ya kashe wayar gabaki dayanta Yana sakawa aljihu harda Kuma qarin rashin baiwa Laylahn zabi bayan na shiga duba Turakin da kanta tunda Ms Na'ima Bata Nan.


Kallon kofar tayi tareda komawa jikin kofar takuma bugawa kadan taji still ba motsi Dan Haka cikin fargaba ta Murda kofar tashiga tana kallon koina ganin dakin da haske kadan sai sanyi da qamshin ke tashi.

Wani yawu ta hadiye sbd qamshinsa da y???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?anayin duhun dakin da tsit din da taji duniya ta dauka ya tuno Mata da tarayyarsu a LA ta rufe idanuwanta ahankali tana kokarin dakatawa daga inda take tsayen batareda ta qara gaba ba sai gashi ya fito toilet dinsa daureda towel da rashin Hasken sosai yasa batasan wace kalar bace illa farar lafiyayyar fatarsa datake bayyane Yana zuba qamshin shower gel dinsa masu tsada ya zuba Mata idanuwansa alokacinda

14 / 36