Noor Albii Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   12 / 36

33K to 36K   out of 107.4K words

ya haramtawa kansa
Zamanta a matsayin Yar riqo garesa kamar yanda Na'ima tadauka
Da kansa zai aurar da ita Inshallah idan lokacin hakan yayi.

Cikin wata irin sanyin murya da nutsuwar dake bayyanarda rashin sakewarta agurin ta furta"

Ina wuni.

Gyada Kai yayi Kai tsaye Yana cewa"

Seat.

Zaunawa tayi a darare tanajin duk girmansa ya cika gurin Dan Haka sama sama taci abincin Wanda dama Bata iya cinsaba Dan macaroni salad ne sai baked potato da fresh fruits masu sanyi kadan.

Ita tafara gamawa Amma takasa barin gurin Saida yagama ya miqe yabar dining din Yana yimusu Saida safe cikin sautin girma da kulawa.

Yana fita Ms Na'ima tasake zuba Mata abincin Wanda tasata ci Dole ahakan kuwa cikinta ya cika ba laifi kafin suka baro dinning din zuwa Palo Ms Na'ima na janta da zantukan yanayin qasar da rayuwar gidan
Dayake zuwa yanxu tasaba da yanayin Laylan sai rashin tankawarta sosai baya damunta tunda tasan hakan Laylahn take.

Saida bacci yazowa Laylah sosai kafin Ms Na'ima tabarta ta nufi bedroom dinta tayi Shirin bacci ta kwanta
Take bacci ya dauketa sbd koshi da gajiya.

Washe gari da safe data Gama tabbatarda sake kiranta za'ai gurin Cin abincin safe Dan Haka saita lafe taqi nuna ta farka duk yawon kiranta da Cindy taringa Yi Dole aka barta sbd lokacin Turaki ya sauko harya zauna cin abinci
Yana gamawa ya fice.

Sai qarfe goma Sha daya ta nuna ta farka ta tashi tayo wanka tuni akai Mata nata abincin aka Kai dining ta fito Dole sanye da farar chiffon lace blouse da blue palazzo kanta daureda qaramar veil fari fuskarta ba komai bayan glowing na savor beauty moisturizer Babu abinda takeyi
Kai tsaye dining room din Cindy ta nufa da ita agaba tana binta.

Ba laifi abincin da akai ta iya cinsa sbd pancakes ne da Black tea sai soyayyan kwai da potato chips.

Tana gamawa daki Takoma tayi zamanta cikin kadaici da kewa.

Da yamma Dr Noah yasake dawowa yaduba yanayin jikinta ya tabbatarda tasamu lafiya saiya tafiyarsa.
Haka ta wuni ba wani abin Yi ko abokin Hira har dare takuma dojewa fita cin abincin Amma da Rana dayake akwai Dan sani da sabo tsakaninta da Ms Na'ima taje sunci abincin Rana tare a dining din.

Washe gari Bayan fitar Turaki A Abdoul yasakawa Ms Na'ima wasu irin maqudan kudi na siyayyar Laylah da har anshigar da maganar sakata makaranta,
Dadin duniyane yafara cika Kan Ms Na'ima ganin tafara morewa riqon Laylah tun baaje koinaba Dan kudin da aka batan idan siyayyar haukar me zataiwa Laylah bazasu cinyesu Dan Haka Laylah Nagama breakfast Ms Na'ima na jiranta cikin Shirin doguwar Ashape gown ta chiffon Mai tsadar gaske suka fita cikin daya daga cikin manyan motocin gidan.
#MAMUH#

Follow me at Arewabook @mamuhgee Dan samun complete books Dina dama sauran pages na Noor Albi Dake fara sauka acan.

=?G?=?G?
Eznah
Tarayya
Deen Marshal
Ubayd maleek
Min qalb
Buri daya
Kaunarmu
Noor Albi
Dacewa
Dawood
Zucuyarmu daya
Auren raba gardama
Taura biyu
[7/10, 9:25 PM] +234 704 076 8969: *_Mamuhgee 17_*
Duk yanda Ms Na'ima taso Kar tayi kishin Sa'adah kasawa takeyi saidai kamar yanda Haj Zinat ta fada Mata dannewa kawai takeyi Bata wani nunawa saidai ko inda Sa'adah take Bata kalla sbd duk iya qanqantawa tagama daukan Sa'adahn a qasqance ganin harda ilimin boko Mai qarfi sosai Bata dashi Dan Haka sai sukafi maida hankali akan Laylah wadda cikin kwanaki kadan Ms Na'ima din tagama fahimtar irin kaunar da Anne ke yiwa Laylah ga laylan nada wuyar sakin jiki da mutane Dan Haka tuni ba itaba ba Haj Zinat ba suka maida hankali sosai Kan nunawa Laylah kulawa Sosai,
Musamman Ms Na'ima ke janta ajikinta tana Mata siyayyar kayan Yan gayun 'yan Mata 'yayan manyan duk da Anne Babu abinda Bata siya musu na duk Wani abun buqata Amma dayake Ms Na'ima wayayyar Yar gayun gaske ce sai siyayyar datakewa laylan yana sake wanke Laylan
Anne said kawai takawo ido tasake sakawa Na'ima Dan tagama gane manufarta ta son abata Laylan Dan samun damar data fi wadda take da ita yanzu Alan dukiyar Turaki,
Murmushi kawai takeyi na ganin wautar Na'ima so da dama idan taga yanda suka taqarqare akan Dole qaunar Laylah sukeyi ba
Kuma ganin rashin sanin zaisa bazata taba cutatar da Laylahn ba ayanzu Dan Haka saita bar komai ahakan yanzu saima tabada fuskan da Ms Na'ima din ke daukan Laylah tana fita da ita.

Laylah Bata sakewa da Ms Na'ima Sam ko kadan sbd sanin matsayinta na kishiyar Sa'adah batason jawowa Sa'adah matsala sai Anty Sa'adah din ta nuna Mata bakomai ai hakan shizaisa azauna lfy kowa da kowa,
Da Haka Ms Na'ima taja Laylah sosai jikinta har Dan Dole Laylah tafara sakewa da ita Dan har cikin ranta so take ta cusa qaunarta Mai qarfi a zuciyar Layla ta yanda zata dauketa tamkar uwa tako Ina yanda Turaki zai sake musu komai yanda yakamata tunda ta rungumi 'yar Kamar ita ta Haifa.



Sa'adah tafara zuwa makaranta tuni a one hundred level takuma farawa tana karantar Biology
Kuma ba laifi tafara sabo da makarantar da 'yan friends din data fara tsirarru ga uwa uba surutu da manyan designers Kaya data duka
Ga hankalinta tuni yagama kwanciya Dan Laylah tasamu lafiyarta cikakkiya itama karatun zata fara Amma Ms Na'ima ta dage akan ita baza'a sakata anan Abuja ba da ita zata tafi USA acan zata sakata karatun kafin su tashi dawowa Laylan tagama Inshallah idanma harta tashi dawowan Laylah Bata kammala karatun ba zata jirata ta kammala kokuma tabarta acan tadawo tunda Turaki na can ga maids a gidan Kuma.

Da wanna ba musu Anne ta Amincewa tafiya da Laylan wadda da farko ta daga hankalinta Amma Sa'adah ta lallasheta tareda sanar da ita Anne tace acan kusa suke da gurinsa Abba zaa ringa kaita tana dubo Abba da Momy tarea Bata qwarin gwiwar karatun shine zai tallafi rayuwarsu data iyayensu Inshallah Dan Haka badan tasoba Haka ta amince musamman da Anne ta zaunar da ita ta rarrasheta Akan Turaki nacan Dan Haka kartaji tunda yasan matsayinta akansa na dolenta.
Hakama dai maganar ganin abbanta shine yafi komai Bata nutsuwa da tafiyar wadda takasa gane dalilin dayasa Ms Na'ima ke sonta Haka Bayan ita din qanwar kishiyarta ce Amma idan ta tuna wasu daga nasihun Anne sai tana yadda da akwai sauyin da Allah ke kawo maka na rayuwa da basai ka tsaya wani tunaninba Bayan gode Masa.


Da wannan aka hau Shirin tafiyarsu USA, Ms Na'ima farin cikin tafiyar takeji sosai musamman ta kalli Haj Zinat tana zare siririyar sarqar white gold din Dake wuyanta dasuka dawo daga Gama harhada bayanan komai na manyan stores data barwa babban 'dan Haj Zinat ragamar cigaba da kulawa da komai tace"

Zinat kisake yiwa siddika sabuwar huduba sbd tana min hauka acan ko kudin ticket din dawowa bazan siya Mata ba Zan korota
Dan kuwa banason duk wani abun damuwa ko ciwon Rai acan
Hutawa najeyi da mijina.

Murmushi Haj Zinat tayi tana aje wayarta data Gama amsawa tace"

Idan hankalinki Bai kwantaba da haukarta ki barta Mana a samo wata kije da ita.

No zuwa da itan zaifi sbd Laylah da ita tasani zatafi Jin dadi idan akaje da Mai Mata hidimar data sani tun anan sbd Kinga turancin ba wani jinsa takeba Dan Haka masu aikin can zasuyi Mata wuyar muamala shiyasa sbd ita kawai zanje da siddikar.
Dan Haka idan tamun abinda zai sakamun ciwon zuciya ratayeta zanyi kowama ya huta" taqarasa fada da Dan takaicin halayen siddikar duk da sune suka sakata ta gwane a munurfin da gulmar Dan kawai dauko musu kowane irin zance.

Dan gyara zama Haj Zinat tayi cikin Isa tana cewa"

Laylahn ma sai anyiwa Siddikar fadan kiyaye abinda takeso da Wanda bataso Dan zata iya kwafsawa tunda munafurci kawai tafi gwanewa akai.

Wani lafiyayyan murmushi Ms Na'ima tayi tana daukar face wipes taqara da Neutrogena makeup remover akai tafara goge fuskarta tana cewa"

Duk halinta zatai tabari ne Dan kuwa amfanin dagewa da tafiya da Laylah shine Zan fake da karatun nata naqi dawowa Dole yanzu zamu zauna Kamar kowanne ma'aurata gani gashi a gida daya qari ga 'yar riqo duk ihun Anne da damuwarta Akan rashin haihuwa dai yanzu Zan huta tunda burinta yacika ta aura Masa gagari
Dan kuwa ko ganinsa ita Annen bazataiba bare juyayyar Matar da aka aura masan saidai taqaraci karatun bokonta tagama tayi gaba tasamu bokon koshi taqaru dashi taje tasamu wani mijin Turaki Kam bana yara bane
Ita kanta dataji komai ta Isa Bata Gama saninsaba bare wadda ya Isa haihuwa.

Dama duk tsanani Kam karkiyi sake yadawo Baki Gama sakashi a kwana ba da kisisina da komai
Tunda gaki da 'yar Mahmoud a hannu kowa yasan irin Aminci da qaunar Dake tsakaninsu Dan Haka kinsan tunda suka dauko yarsa duk Wanda ya sota shine nasu
Tunda gashi yanzu Anne Tadawo tana sake Miki sosai sbd Laylan Dan Haka Turakin ma karkiyi sake
Gwara ki nuna Masa da gaske kike kece uwarta yanzu.

Wani murmushin tayi kawai batareda tace komaiba Dan kuwa kamar anyi komai angama ne.


Bayan dogon shiri da tsare tsare dai jirginsu ya daga zuwa USA inda Laylah take zazzabi da mutuwar jiki suka sameta na yanayin data samu kanta a jirgi doguwar tafiya duk da wannan shine karonta na biyu Hawa jirgi Bayan Wanda suka shiga zuwansu Abuja tareda Anne.


_AMB & Alt perm rep AB TURAKI north Buckhead Atlanta Georgia_

Cikin wata black Audi A8 aka daukosu daga airport zuwa gidan Wanda Laylah Bata wani damu da yanayin tsananin tsaruwarsa da sabuwar duniyar dasuzoba sbd yanayinta batajin Dadi zazzabi sosai ne ajikinta dukda tana daurewa
Dan Haka suna shigowa gidan aka nufi lafiyayyan dakinta da Ms Na'ima tasa aka gyara Mata shi daga shigowar tasu aka ja luggages dinta zuwa can tace saddika ta kula da ita itama zata huta tana Jin gajiya
Tadaga wayarta da tun a mota tasaka layinta na qasar takira numbern A Abdul dasuke tareda Turaki a office Yana Masa bayanin wasu takardu ya sati kallon Turaki Dake zaune yayi crossing dogayen qafafunsa cikin wasu irin Ash Alexander amosu vanquish ii suit fuskarsa da fararen idanuwansa na kallon screen na Apple iPad Air Dake gabansa na bayanin da A Abdoul ke Masa.

Wani Kiran ne yakuma shigowa yakuma kallon Turaki da tun Kiran farko Bai dagoba bare na biyun
A natse A Abdoul din ya dakata da fadin"

Ms Na'imah ne take Kiran shud I take the call ko naci gaba??

Agogon _jaguar executive_ dake daure a hannunsa yafara kalla yaga lokaci yasan ta isa isowane a yanda Anne ta fada Masa Na'ima din Hanya
Kafin ya dago ya kalli A Abdoul din dake Kiran umarninsa yace ya amsa Kiran.

Juyawa yayi ya fice daga office din tareda daukar wayar cikin Bata nata girman yace"

Barka da isowa.

Kai tsaye ko gaisuwarsa Bata amsaba tace yaturo Mata likita tazo da yarinya ba lafiya.

Tana Gama fadar hakan ta kashe wayarta.

Saida yafara Kiran Dr Noah ya sanar Masa kafin ya kashe Yana mamakin inda tasamu yarinyar zuwa da ita
Ya koma gurin Turaki Yana barin tunanin zancen.
##MAMUH#



pay 300 @+234 903 234 5899

Mamuhgee's complete books

Deen Marshal
Ubayd maleek
Min qalb
Kaunarmu
Buri daya
Tarayya
Eznah
Dawood
Zucuyarmu daya
Daiman
Auren raba gardama
Dacewa

Duka completes dinsu suna AREWABOOKS @Mamuhgee
[7/10, 9:29 PM] +234 704 076 8969: _*Mamuhgee 19*_
Siyayya sosai Ms Na'ima tayiwa Laylan ta kayan Yan Mata 'yayan gata,
Komai da aka siyo Mata designers na yayan gayu tun daga kan handbags da shoes da kayan sawar dasu agago,da perfumes da undies ma da aka siyo Mata Kaya guda harma da nightwears.
Harda sabuwar waya Mai tsada sosai ta aka siya Mata tun acan aka saka Mata komai tasaka Mata Numbern Anne wadda takejin buqatar su dawo gida takira ta gaisa dasu musamman anty Sa'adah datakejinta tamkar uwa.

Sai yamma suka dawo gida sbd Saida suka biya spa.
Suna dawowa sallah kawai Laylah tayi ta saka Kiran Anne wadda Kamar tasan Laylah ce Bata qi daga Kiran ba kamar yanda take wasu lokutan na qin daga baquwar numbern Amma ganin international number saita daga.

Cikin sanyi da nutsuwa Kamar koyaushe Laylah tace"

Assalamualaikum Anne Ina wuni.

Da mamaki Mai tattareda farin ciki Anne ta amsa sallamar tana cewa"

Masha Allah Laylah tasamu Kira kenan.

Ahankali Laylan tasaki murmushi Mai qaramin sauti tana cewa"

Dazu ne aka bani wayar,
Ya gida Anne?
Inasu halima duk suna lafiya?

Dariyar manya Annen tayi tana cewa"

Duk lafiya kalau Sa'adah ma da kike Jin nauyin fara tambayarta kafin kowa lafiyarta kalau
Tana daki tareda baqi datai dangin mahaifiyartane sukazo Zan Bata numbrnki saita kiraki,
Yaya kike?
Ya qasar kina Jin Dadi kuwa?
Zaki iya zama kokuwa nasa Turaki ya dawo Dake Nan?

Murmushi kawai ta iya saki ahankali tana cewa"

Lafiyarta kalau.

Kin tabbata Zaki iya zama dasu anan din dai ko?

Kasa cewa komai tayi sbd itakam duk yanda sukai da ita Yi zatai Dan Haka batajin tanada zabin inda zata zauna acikinsu koina zata iya zama ayanzu tunda Bata tareda mahaifinta.

Ga dangin Momy da Annen tace sunzo kilama tafiya zasuyi da ita kamar yanda dama sukace bazata zauna dindindin hannun Sa'adah ba zasu dauketa Takoma gida,
Yanzu da Momy Bata Nan idan Suka dauketa tasan gidan umma Jamila za'a tafi da ita direct Dan Haka ita batada zabi aduk inda za'a kaita
Me gata ne yakeda zabin gurin dazai iya zama.

Sosai Anne ta tambayeta lafiyarta dakuma tambayoyi akan idan batada matsala da komai na gidan
Hardai suka gangaro akan karatu da Laylan zata fara ta Bata qwarin gwiwa da tabbacin zata iya sosai idan tabada himma kafin suka aje wayar tanajin nutsuwa da kwanciyar hankali akan maganar datai da Annen Dan kuwa magana da Anne na Bata nutsuwa shine abinda tasabu dashi a zamansu.

Wanka tayi kafin ta fito komai na dakinta da siyayyar da akayo Mata angama tsarasu ako Ina take dakin yazama na cikakkiyar budurwa
Tana fitowa Cindy data Gama aikin tana ficewa tabar siddika datake qarasa kunna Mata humidifier itama tana gamawa ta fice.

Zama tayi gaban mirror tana kallon fuskarta akaro na farko data zauna tana qurewa kanta kallo tareda Shiga tunanin wannan wace irin rayuwace tasamu kanta aciki kuma wadda take ga Kamar Jin dadin yayiwa marainiyar kamarta yawa.

Mai tashafa da body mist ta miqe ta duba closet dinta da aka gama gyarawa shaqe da Kaya saidai abin sanyin jikin shine yawanci ba kayan mutunci bane Dan mafi yawansu wanduna ne da skirt na Yan gayu da batasan yazatai sabo da sakawa
Dogayen rigunan ciki qalilan ne Suma duk ba masu mayafai bane saidai idan ka saka ka daura qaramin scarf akai.

Batada zabi Bayan saka wando da Riga Takoma bakin gado ta zauna tana daukar sabuwar wayarta da har cikin ranta tayi farin cikin samun wayar sbd waya dasu anty Sa'adah duk da tanajin tanason kira taji abbanta Amma tasan Momy bazata taba iya magana da itaba Dan Haka ta hakura da hakan tunda anty Sa'adah na waya da ita tanajin komai tana fada Mata hakanma yayi zataci gaba da Masa addua ta jira hukuncin ubangiji akan ranar haduwarta da Mahaifinta.

Da daddare ba dalilin rashin fitowarta cin abinci Dan Haka Dole ta fito sanye cikin Riga da wando masu Fadi kalar Ash kanta daure cikin qaramin scarf saidai gashinta ya fito kadan
Tana shigowa dining room din taga ba kowa aciki tasaki boyayyar Ajiyar zuciya tana Shirin juyawa saiga Turakin ya doso dining room din sanye cikin Ash Armani's da slippers baqaqe da Suka bayyanarda Hasken qafafuwansa
Kyakkyawar fuskarsa a sake saidai bakuma Wai Yana murmushi bane ko dariya
Tana ganin hakan ta dawo tana matsawa daga hanya Yana kawowa ya dago fararen idanuwansa yayi Mata kallo daya ya dauke Yana amsa siririyar gaisuwarta datai Masa itama bayan ta sauke idanuwanta daga kallonsa.

Ms Na'ima Dake gefensa ta miqa Mata hannu ta Kama suka qarasa dining din tana cewa"

You look fresh my girl.

Sunkuyar da Kai kawai Laylan tayi suna zaunawa.

Bayan sun Gama cin abincin Kai tsaye kallon Laylah yayi bayan ya miqe yace ta samesa Palo idan tagama.

Kasa hadiye ruwan dake bakinta Tai sbd wata irin fargaba data sameta ta dago ahankali ta kalli Ms Na'ima Dake Mata murmushi tace"

Take it easy Girl ba komai bane zaiji abubuwan dakike buqata ne da Kuma raayinki Akan abinda kikeson karanta.

Kallon Ms Na'ima din tayi tareda bude Baki cikin sanyi da nutsuwa tace"

Me zance?

Wata dariyar Jin Dadi Ms Na'ima tayi ta Jin dadin Laylah tafara zama tafin hannunta akan sai abinda tace.

Ta Kama hannunta suka miqe zuwa gurin Turakin tana cewa"

Daddynki ne kibar Masa zabi da kansa ya zaba miki kawai dai ki dage kiyi karatu sbd akwai yiyuwar rayuwa Mai kyau agaba idan kikai karatu zamuji Dadi Sosai agaba.

Gyada Kai kawai tayi batareda tana fahimtar komai da Ms Na'ima din ke fada ba Dan duk Bata nutsuwarta.


Zaune yake gabaki daya yagama sauya iskar palon da qamshin jikinsa Wanda Babu Wanda zaiyi haduwa biyu zuwa uku dashi batareda ya Gama sanin wannan qamshin nasane na musamman.

Saida suka kawo tsakiyar palon kafin ya dago daga wayar daya keyi ya zuba musu idanuwansa take Laylah ta Dan rage takunta ta danyi bayan Ms Na'ima itama kanta Ms Na'ima din idanuwan Turaki kasheta sukeyi Dan Haka ita qafafuwanta sauri suka qara Kamar ansaka musu batir ta qaraso gefensa ta zauna tanajin a duniya batajin akwai ranar dazata iya barin Turakin ya iya kallon wata macen da sunan so ko makamancin hakanba Dan kila Aron hauka zatai ta halaka koma wace da danginta gabaki daya.

Dauke kallonsa yayi daga kan Laylan wadda duk tabi ta rikice Tama Rasa gurin zama saitayo gurin Ms Na'ima din tana kokarin zama a qasa.

Muryarsa dake sake rudar da ita sbd kamewa da Rabin Wasa ko kadan acikinta ya furta"

Gobe za'a fara fita Dake zuwa harkar makaranta Dan Haka ki ringa kula Nan ba Nigeria bane karkiyi qawayen banza ok??

Bata Gama gane meyace ba kawai dai ta gyada kanta cikin biyayya tareda furta "nagoge" ahankali.

Daga Haka Ms Na'ima ce ta ringa tsarowa Laylan zance da nasiha akan ta dage tayi karatu.
Ita dai Kai kawai take gyadawa Bata iya bude Baki.

Sai kusan goman dare tadawo bedroom dinta ta sauke numfashi tareda Ajiyar zuciya tana zare kayan jikinta ta nufi toilet tayo alwala ta fito ta Sanya kayan bacci Kamar yanda Ms Na'ima ta Gama Bata tsari da yanda zata ringa gudanar da komai.

Face cleanser ta Gama goge fuskarta kafin ta kwanta Wanda shikuma a spa din dasukaje aka karbo Mata shi akace ta ringa shafawa kullum kafin kwanciya shima duk aikin Ms Na'ima ne.

Washe gari qarfe goma A Abdoul yazo ya dauketa a motar Turakin yakaita Emory inda dama tun zuwanta washe gari aka

12 / 36