Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Aysha Cool Category :  Complete Novels

Chapter   33 / 67

96K to 99K   out of 199.9K words

"Ai ba abun da ki ka gani, family ne mai cike da rikici da ?ulla-?ulla".

"Ai shi ne wannan yayan anty aishan, zai raina mini hankali, ni kuma wallahi yadda mutum ya mu'amalance ni a farko, haka nake tafiya da shi, kin ga rashin mutuncin da suka yi mini ranar da muka je gidan su, da shi, da wannan masifaffiyar mai jan kaya ta Wazu, da wannan jabir Win, shi ma jabir Win da babarsa, wadda ta riga Mummy tafiya Wazu.
Wai takawa ya turo shi ya Wauke ni daga makaranta, na ce ba zan hau motarsa ya kashe ni ba, dan na san haushina yake ji, saboda takawa bai auri ?anwarsa ba, wai ni zai yi wa dabara, a gabana fa ya yi wa papan wula?anci, wai an sace ?anwarsa bai gaya masa ba, shi a wa? Sai ka ce son anty aishar suke yi".

Iman ta ce "Ke dai kawai ki ce, an taSa miki miji kin ji haushi. In dai yaya jamil ne sun saba, faWa da takawa kuma daga baya su zo su shirya. Amma duk da haka na yi mamakin yadda ki ka iya kawo, yaya Mahmud sashen nan, ba ya son ammi da abun da ya shafe ta, balle adam. Lokaci na ?arshe da ya zo, shi ne lokacin da aka fasa aurena, saboda rashin asali, ammi ta ro?e shi ya aureni, har da kukanta, ya ce ba ya so na, ba zai aureni ba". Ta yi maganar hawaye fal idonta.

Rumaisa ta yi shiru, ta ce "Wane irin abu ne wannan kuma? To duk saboda me? Ban gane ba ki da asali ba"

Iman ta share hawayen da ya zubo mata, ta ce "Zan yi miki bayani, yanzu mu cigaba da addu'a papan mimi ya warke" ta yi maganar cikin ?arfin hali tana murmushi.

"Shikenan, ara mini wayarki, na kira gida na gaya musu papa ba lafiya".

Iman ta ce "Amma idan mai sunan baba zaki kira, ki yi masa magana ta what's app, ya hana ni kiransa a waya".

Ruma ta ce "Au kuna waya ne dama?" Ta yi maganar tana dariya.

Da sauri Iman ta ce "A'a, ba waya muke yi ba, ke ce da ki ka kira rannan bai Waga ba".

Ruma ta yi dariya ta ce "BuWe mini data mu yi magana da shi".

Iman ta karSa ta kunna mata data, ta ba ta, yaya umar ta ga iman ta yi saving number.
Ruma ba ta ce komai ba, ta yi masa voice message "Mai sunan baba, ni ce, ka gaya wa mama mijina ba shi da lafiya, mu na gidan ammi, idan ka ga message Win dan Allah ka yi mini magana, rumaisa ce".

Iman ta zare ido ta ce "Ba kya jin kunya, ki ke cewa ace da ammi mijinki babu lafiya"

Rumaisa ta mi?e tsaye ta ce "To me zan ce? Ai maman ma mijina take ce masa, bari na je na gani ko ya tashi, idan mai sunan baba ya yi magana, sai ki kira ni" ta fita daga Wakin, ta tafi na ammi.

Ammi ba ta Wakin, ta tarar da adam a zaune, sai dai ta ga samha a zaune a gefen sa, da flask Win abinci.

Wani abu ne mai nauyi, ya daki zuciyar rumaisa, da ba za ta iya tantance ko menene ba.

Iman kuwa ta cigaba da chatting Win ta, sai ga video call na mai sunan baba.

Gudun kar ta yi laifi, kan ta kai wa ruma wayar ta katse, ya sanya ta Waga, gabanta ya na faWuwa.

Maimakon ya ga rumaisa, ya ga kyakywar fuskar iman, ta bayyana a kan screen Win wayarsa.

Ta Wan sunkuyar da kai ta ce "Barka da yamma yaya umar"

Sunkuyar da kanta da ta yi ne, ya bashi damar ?are mata kallo, ya na jin releif na abun da yake damun ruhinsa.



Ayshercool
08081012143
What's app only please, ban da kira please =?O?.
? 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank.
Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please =?O?



Jin shirun ya yi yawa, sai da ta yi zaton, ko wayar ya katse, ta sake Waga kanta, ta ce "Ina wuni yaya umar?".

Wata Soyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke, ya ce "Lafiya ?alau, ya mutan gidan?".

Cikin jin daWi ta ce "Suna nan lafiya, ya mama da su Yaya Aliyu"

"Lafiya ?alau, na ga message Win wannan Yarinyar ne, na mijinta ba shi da lafiya". Yayi maganar yana sake fatan iman ta Wago kanta ya kalleta, ko ya cigaba da jin nutsuwa a zuciyarsa.

Ba tare da ta Wago Win ba ta ce "Eh, ba shi da lafiya, su na gida ita da shi".

"Za su koma gidansu yau ne, ko su na nan?"

"Wallahi yaya ban sani ba, amma dai ba na tunanin su koma yau, bari na kai mata wayar, yanzun nan ta tashi".

"No ?yaleta, idan ta dawo ki ce mu na yi masa sannu, Allah ya bashi lafiya, a gaida sabir".

Murmushi ta yi ta Wan Wago ta ce "To in sha Allah zan gaya musu, mun gode sosai".

"Zan shigo zuwa an jima, sai na duba shi".

"To yaya umar, Allah ya kawo ka lafiya"

Ji yake tamkar kar ya katse wayar, wata irin narkewa zuciyarsa take yi, da jin iya muryarta kawai. Mussman idan ta kira shi da yaya umar, ji yake tamkar ta fi kowa iya faWar sunan.

Kamar wanda aka yi wa dole, haka ya kaste kiran wayar, ya lumshe idonsa ya na haki, ya na gazgata zuciyarsa da babu tantama wannan shi ne so.

Girgiza kansa ya yi ya ce "Ya salam, why? Why? Abun da ban taSa yi ba, ni ko shirin aure ba ni da shi, ina zaman zamana meya aikeni" ya tambayi kansa. Gashi Abubakar ne abokin hirar sa, Abubakar baya nan, kuma duk da haka ma, ya san idan ya gaya masa dariya zai ta yi masa, abun da ba ya so, dan haka yake jin, zai iya jure koma menene.

A ?asan zuciyarsa ya ji kamar dama ce, da zai yi amfani da zuwa duba Adam, ko zai samu ya ga iman.

Rumaisa kuwa, takawa ya ga reaction Win ta, ta ?arasa wurinsa ta ce masa "Wai dama ka tashi, ina ammin?".

"Ta fita ita da Nusaiba" ya bata amsa.

Ta je ta zauna a kusa da shi, ta ce "To meyasa baka ce a kirawo ni ka tashi ba?"

"To yanzu ba ga shi kin zo na tashi ba".

"Ammi zan mutu, ki zuba mini ruwan sanyi, idan mutuwa ce hutu a gareni Allah ya sa na mutu, to ba in da za ka mutu ka tafi, sai na gama makaranta mai lilo" ta yi maganar farko tana kwaikwayon sa.

Murmushi ya yi, da sai da ha?oransa suka bayyana, ya ce "Rashin lafiyar ta wa ce, ta zama abun tsokana kuma".

"Wane irin wula?anci ne, ina magana da Wan uwana zaki zo ki zauna ki na wasu surutan banza?"

Rumaisa ta kalli Samha ta ce "Au dama Wan uwanku ne? To ni kuma ?arewar ?an uwantaka gidansa a kai ni na zauna, ke meyasa ba a kai ki ba? Me Wan uwa?"

"Shut up" yayi maganar yana matse mata baki.

"To ina ruwanta da ni, ba bu kyau wata ta kula mijin wata ba?" Kallonta kawai yake yi.

"To ina ruwana. ka ci abinci ne?"

Ya numfasa ya ce"Ammi ta bani, tun da tafiyarki ki ka yi, ki ka barni".

?an shiru samha ta yi, abun da take gani yanzu, ya sha ban-ban da wanda baba uwani take gaya mata, ?arya take yi mata kenan ko kuwa? Ta ce mata ba sa wani jituwa, amma alamu sun nuna mata, kamar sha?uwa a tsakanin su, babban tashin hankalin ta da fatanta, Allah ya sa wani abu bai taSa faruwa tsakanin su ba, ta kuma fuskanci rumaisan tantiriyar fitsararriya ce.

Ruma ta ce "To yanzu ya ka ke ji, da sau?i jikin?"

"Eh, Alhamdilillah"

"To sannu, ka tashi mu tafi gida"

Adam ya ce "Mu je gida ki yi yaya da ni, ba iya jinyata za ki yi ba"

Mi?ewa Samha ta yi, ta fice zuciyarta na zafi, a gabanta adam ya sakarwa wannan shegiyar yarinyar baki, wata banza da ita mara aji, balle mamora.

"Kuma duk mai kula mijin wata, Wan wuta ne, kuma sai ya daina magana" ta yi maganar cikin Waga murya.
Samha ba ta ko juyo ba, ta yi gaba tana ?wafa, ba dan Adam ya auri rumaisa ba, da duk hakan ba ta faru ba, ta Wora zargin komai a kan sa, kuma ya kasa tsawatar mata.

Samha na fita, ya rungumo rumaisa jikinsa, tare da kwantar da kansa a jikin na ta.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meye haka kuma, dan Allah ka cikani"

Bai ce uffan ba, ya ?ara lafewa, yana sauke numfashi.

Shiru ta yi, ba ta kuma ko motsawa ba, ta na jin bugun zuciyarsa a jikinta.

"Ita ma haka ka yi mata ko?"

"Ita wa?"

"Wannan matar da ta fita yanzu".

"Eh, tun da ba kya jin magana, ba zaki saita bakinki ba, idan ta zaneki shikenan" ya sake rungumeta sosai.

Cikin tsoro ta ce "Ba kyau fa"

Yayi ?ar guntuwar dariya, yanzu abubuwanta sun daina bashi haushi, akwai wayo wasu lokutan, wasu lokutan kuwa kanta a kwano yake, gashi dai ta fara girma, amma kamar ba mutum ba, har mamaki take bashi".

Ya kalleta ya ce "Wani al?awarin ki ka yi wa fulani?"

Ta numfasa ta ce "Ba yanzu zan faWa ba. Kuma gaskiya ka Wagani, ka yi mini nauyi, na ji da matsar hannun da ka din ga yi mini Wazu, ?asusuwana sai ciwo suke yi".

Bai Wagata ba, ya kwanta sosai a kan cinyarta, ya lumshe idanunsa.

***
A fusace Jamil yake sosai, ya dubi Jabir ya ce "Jabir, har ni wannan Yarinyar za ta yi wa fitsara, wai ba son fulani muke ba, kenan adam zuwa ya yi yana Sata mu a wurinta, abun da ya wuce ba ya riga ya wuce ba? Shikenan ba ni da zarafin bincike a kan ?ar uwata, ni da a tunanina, na lallaSata na samu wani abun daga bakinta, yadda ka san na harbeta na huta, ka ga iskancin da ta din ga yi mini?"

Jabir ya ce "Wai kai da na gaya maka halinta baka yadda ba? Kai ka ga zaryar da jami'an tsaro suka din ga yi tana asibiti, amma ta ?i magana, sai da aka kai ruwa rana, sannan ta yi".

"Ni anya ba fulanin ce ta gaya mata wani abun ba?"

Jabir ya ce "Ba tabbas, ka san halin Aisha bana tunanin ita ce, bari dai a yi sallar magariba, zan shiga na duba shi"

"Ka dai yi a hankali, ciwon nan nasa ne, ya tashi, ka san kuma sha?e mutane yake yi".

Jabir yayi murmushi bai kuma cewa komai ba.

Tamkar mai comedy, haka rumaisa take ta zuba, tana yi wa Adam shirme samfur -samfur.

Can kuma ta ce "Tashi, in Wauko maka filo, cimyata ta gaji, zan kuma je kitchen in yi girki".

Gyara kwanciyarsa ya yi ya ce "Ina jin releif a haka, ba zan tashi ba"

"Gaskiya cinyata ta gaji, duk jikina ya yi tsami".

"Mimi"

"Na'am basarake"

"Meyasa ki ka faWi maganar Wazu?"

Ta Wan yi jimm, sannan ta ce "Wacce?".

"A kan Mummy, kar ki sake makamanciyar wannan maganar,Idan maganar ta koma kunnenta fa? Zaki iya haddasa rigima, babu ruwanki da irin wannan abubuwan kin ji ko?".

Ta numfasa ta ce "Waye zai je ya gaya mata, ni fa ba ?arya nake yi ba, wata mata na gani tare da ita, gaba Waya ba kalar mutane ba, kuma da za ta tafi ta tashi ta bita k....."

Ya katseta ta hanyar cewa "Wannan matar tun ina da shekara bakwai a duniya nake ganinta, take azabtar da ni, ko ta Waure ni tamau da sar?a, ko ta din ga dukana da sar?ar, na yi mamaki da ka ce ki na ganinta, ban taSa gaya wa kowa ina ganin ta ba. Rumaisa wannan shi ne ainihin adam, kin ga abun da na din ga yi jiya, kamar mahaukaci, dan ma na daina duka da cizo kamar maye, zaki iya cigaba da zama da ni a haka, abokiyar gaba?"

Ga tausayi ya bata, amma hakan bai hanata yin dariya ba, ta ce "I tuntuni na sani, baba uwani ce ta gaya mini, idan ranka ya Saci ka na komawa kamar mahaukaci, har yaya Abubakar aka gayawa, kan ka aureni, wai kai maye ne. Sanan ban manta ba, kuma ina nan a kan baka na. Ai sai yanzu na gane ka na da Wan kirki kaWan, kar ka mutu sai na gama makaranta mai lilo"

Shiru ya yi jikinsa a sanyaye "Ba ki damu da ni ba sai lilo ko?".

"Kai fa ka gama addu'a ka mutu, kana mutuwa zan koma gida, idan na ?ara girma na auri Yaya Mahmud" ?uri ya yi mata da ido, sai kuma ya tashi daga kan cinyarta ya koma kan gado ya kwanta.

Ita kuwa madigar ko a jikinta ta yi nata wuri, dama ba ta son zaman wuri Waya.

Abun da ya tsaye masa a rai bai wuce, yadda rumaisa ta ce Baba uwani ce ta gaya mata, ya na komawa kamar mahaukaci ba, sai ya ji kimar dattijuwar ta ragu a idonsa, sai kuma abun da rumaisa ta faWa na ?arshe bai yi masa daWi ba.

***
Tamkar ya janyo dare, haka yake ji, ?asan zuciyarsa ya na fatan idan ya je gidan ya ga Iman.
Iman ma sai kaiwa take ta na komowa, ta na fatan Allah ya sa mai sunan baba ya zo.

Ammi kuwa da ta dawo, zuwa ta yi aka yi wa adam tofi, wurin malamin da take sawa ya na yi masa, ta karSo masa, sai dai ta bar shi ya Wan farfaWo har da fara'a ta dawo ta tarar da shi sai a hankali.
Sai ta yi zaton kawai jikin ne.

Haka nan iman ta tsinci kanta da yin kwalliya cikin doguwar riga, har ammi ta na tsokanarta, ko siriki za ta kawo mata.

Ta na nan zaune a falo, ta na danna waya, Sabir sai wasan sa yake yi a tsakar falon, gefe rumaisa ta na cin abinci, dan ba ta kuma komawa wurin takawa ba.

Jabir ne ya yi sallama, duk suka amsa masa, ya shigo cikin fara'a, "Autar Ammi da sirikar Ammi, Barkanmu da wannan lokaci"

Ba yabo ba fallasa, Iman ta amsa masa, rumaisa kuwa ta share shi.

"Ina takawan yake ne?" Iman ta nuna masa sashin Ammi, ya Wan tsaya ya kalli Iman ya ce "Bari in shiga in fito, zamu yi magana dear, kin yi kyau masha Allah"

Iman ta yi masa shiru, rumaisa kuwa ta kwaSe baki.

Ya na shiga ciki, message ya shigo wayar iman "Na zo" message Win mai sunan baba.

Da sauri ta tashi ta yi waje, a harabar gidan ta tarar da mai sunan baba, a cikin ?anan kaya yake, amma yayi kyau sosai da sosai.

Sai da ta furta Masha Allah, a hankali.

Unexpectedly ya Waga kai ya ga Iman, cikin zazza?ar muryarta ta ce "Sannu da zuwa yaya umar".

"Yauwwa sannunki" daga nan ta yi masa jagora, har ciki.

Ruma na ganinsa, ta tashi ta din ga tsalle ta na murna, amma ya basar da ita ya Wauki Sabir, da ya rarrafo wurinsa da gudu.

"Mai sunan baba, ba ka yi murna da ka ganni ba?" Kawai yayi mata murmushi, ya na sake rungume Sabir.

Ko da suka shiga sashin Ammi, Jabir na ganin mai sunan baba ya haWe rai, ya yin da takawa mamaki ne ya kama shi da ya ga mai sunan baba.

Suka gaisa da Ammi, yake gaya mata rumaisa ce ta ce masa magidanta ba lafiya, ya zo ya duba shi kan ya sanar da mama, dan za ta iya tayar da hankalinta.

Ammi ta ce "Ruma ce ita ma da abun ta, ai ya warware, dan Allah kar ka gaya mata hankalinta ya tashi, ya ji sau?i.

Mutumin da ya zo dubiya, bai fi mintuna goma ya yi ba, kuma daga takawan har jabir bayan sallama da ya yi musu, babu wanda ya sake kulawa, ya yi wa ammi sallama.

Kayan ciye-ciyen ya ba wa sabir, sai dai sabir ya ?i yarda ya ajiye shi ya ma?al?ale shi.

Ya fita da shi a kafaWarsa ya na murmushi, murmushin ba ?aramin kyau ya yi masa ba.

Jabir ne ya biyo bayan sa, ganin Iman ma ta bi bayan mai sunan baba.

Ya Wan kalleta sannan ya ce wa Sabir "Ka je wurin antynka, ko da kai zan tafi babana?"

Iman ta yi murmushi ta ce "Baban mai sunan baba"

Murmushi ya yi, ya mi?a mata sabir da yake ta ihu, ya na sake mi?awa umar hannu.

"Ke iman zo ki wuce, ina son magana da ke, na gaya miki tun Wazu amma kin yi banza da ni, ki ka bi wani" Jabir ya yi maganar cikin umarnin da iman ta ji ya yarfata.

"Amma uncle J, ai gani na yi ka na wurin takawa ne, shiyasa".

"Shut up malama" yayi maganar cikin fushi da kishi.

"Meye haka? Yayana ne fa, me ta yi maka?" rumaisa ta yi maganar tana harar Jabir.

Magana yake son sake yi, amma mai sunan baba ya ?ura masa ido. Sai kuma ya yi shiru, ya ji ya kasa sake magana.

Rai a Sace ta wuce, ba ?aramin haushi? ta ji ba, dan tuni ta fara kuka.

Ruma ta ce "Mai sunan baba, bari na raka ka"

"No, ki je ki kula da mijinki, zan ce ki na gaishe su" ya juya ya fice, wani irin takaici ne ya kama mai sunan baba, ba ?aramin haushi ya ji ba, abun da jabir ya yi wa Iman, kuma ya lura da yadda yake shishshige mata tun lokacin bikin rumaisa, tabbas ba dan a gidansu yake ba, zai nuna wa jabir, ba a shiga shirgin sa"

A harabar gidan mai sunan baba suka haWu da Mahmud, Mahmud ya yi masa magana, mai sunan baba ya tsaya suka yi musabaha, sai dai ya yi ta kallonsa, ya na tunanin yanzu ya baro Adam a ciki, kuma dai ya san ba shiga sabgar juna suke yi ba.

Mahmud ya ce "Ba Adam ba ne, mahmud ne, amma ka na da ala?a da rumaisa ko?".

Mai sunan baba ya jinjina masa kai ya ce "Eh ?anwata ce".

"Kamannin na gani ai, sunana Mahmud"

Mai sunan baba ya ce "Babban suna, ni kuma umar"

Mahmud ya ce

33 / 67