Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Aysha Cool Category :  Complete Novels

Chapter   25 / 67

72K to 75K   out of 199.9K words

yadda rumaisa ta iya girki.

Rumaisa ta ce "Hmm, tun ba a barina na yi a gida, in yi in jagwalgwala har na iya, yaya Abdallah tare muke girki, har a YouTube yake ganin girki mu gwada, daga baya na gane girkin wahala ce, na daina".

Iman har bayan la'asar tana nan, baba uwani na yi tana hawa benen, wai ko suna bu?atar wani abun.

Direba har ya zo Waukar iman, takawa bai dawo ba, haka ita ma iman ta tafi, gidan yayi mata shiru da yawa.

Sai yanzu take jin haushin tafiyar su mai sunan baba, ko a waya basu kira mata mama ba.

Baba uwani ta shigo falon da sallama da kayan abinci, ta ce "Uwar Wakina, ga abincin mai gida, da naki na dare".

Rumaisa ta ce "A'a ai mun yi girki da iman, mun rage masa".

"To wannan Win a koma da shi kenan?"

Rumaisa ta ce "Eh, abincin ma a daina kawowa kawai".

"Amma saboda me?".

Ruma ta ce "Saboda na daina wahalar da ku, na iya girkin nima"

'Amma ai giwa ba ta ce mana haka ba".

Ruma ta ce "Da gaske nake na iya, kar ki damu"

Baba uwani ta fara jin haushin, rashin yaddar da rumaisa take nuna wa yadda ta?i sakin jikinta da ita.

Rumaisa ba ta damu da sanin dawowa ko fitar Adam ba, idan ba wani abu take bu?ata ba, dan haka har ta yi bacci ba ta san ya dawo ko be dawo ba.

A cikin bacci yake jin kuka sama-sama, ya buWe idonsa ya ji ana taSa shi ana kuka.

Ya tashi sosai ya ce "Waye wannan?"

?ar siriryar muryarta ya ji tana cewa "Ka tashi zan mutu, dan Allah ka tashi!"

A burkice ya tashi, ya kunna fitilar wayarsa ya haskata, rumaisa ce a tsaye ri?e da hannunsa, tana kuka.


Ayshercool
08081012143

*Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*


https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please =?O?

A gigice ya tashi zaune yana tambayar rumaisa ko lafiya.
Idanuwanta duk sun yo waje, sai sauke numfashi take yi, hannunta Waya ri?e da cikin ta, tana kuka.

"Ki yi mini bayani, menene meya same ki?".

"Cikina ciwo, zan mutu dan Allah ka taimakeni, wayyo mama" a gigice ya sauka daga kan gadon, ya kunna fitila hakse ya gauraye Wakin.

Tana dur?ushe ta ri?e cikinta, hankali tashe ya buWe wardrobe Win sa, ya saka jallabiya, ya Wauki mukullin motarsa, ya tafi Wakinta da sauri, ya Wauko mata hijjabi, ya saka mata, ya ri?o hannunta.

Da ?yar take iya takawa, sai yarfe hannu take yi tana kuka, suka saukko ?asan benen.

Baba uwani na jin motsi but kamar fitar tusa ta fito, "Ranka ya daWe lafiya? Meya samu ?ar ta wa?".

"Ba ta jin daWi ne, zamu je asibiti".

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meya sameki haka?"

Rumaisa ba ta amsa mata ba, ta cigaba da kuka.

"YallaSai ko biyoku zan yi, ko za a bu?aci wani abu, ba ka tafi asibiti kai kaWai ba, daga kai sai ita".

Adam ya ce "A'a baba uwani, ki yi zamanki dan Allah, ba sai mun wahalar da ke ba, zan iya kula da ita".

Ya saka rumaisa a mota, ya kunna ya fita.

A cikin motar ma, she was very restless, ta rasa in da za ta sanya kanta, ta juya nan ta juya can, sai kuka take yi.

"Ko dai wani abun ki ka ci ya Sata miki ciki? Ko kuma abincin da suka yi ne ya saki ciwon ciki, na ji da yaji abincin".

"Nima ban sani ba, cikina zai haWe da ?afata duk ciwo fa suke yi mini, na shiga uku".

"Meye wani kin shiga uku kuma, ki yi addu'a, sannu".

Wani private hospital suka je da yake kusa da su, aka buWewa rumaisa file ya shiga da ita.

Suka gaisa da likitan, ya tambayi abun da yake damun rumaisa.

Ta ce masa "Cikina ne da ?afafuwana, da bayana na farka na ji suna ciwo, na kasa bacci ciwo suke sosai".

Cikin tausayawa likitan ya ce "Wajen ina ne yake yi miki ciwon?"

Ta nuna masa mararta, ya ce "Kin fara al'ada ne?".

Cikin kuka, ta ce "Meye ma al'ada?".

"Period, ko in ce jinin al'ada" Adam ya bata amsa.

"Ban sani ba ko na fara, amma lokacin da ka watsa mini ruwan kwata, na yi rashin lafiya, na yi fitsari da jini, yaya Aliyu ya ce wai Al'ada ne".

Takawa ya ce "To kuma ruwan kwatar ne ya saka ki ka fara?"

Ta ce "Eh, tun da ai ni da ban taSa yi ba"

Likitan yayi murmushi ya ce "Za a kai wata nawa da farawar? Kuma tun daga wancan lokacin kina yi ne, har zuwa yanzu duk wata?".

"Ni fa na manta, cikina ne kawai yake ciwo" tayi maganar tana rimtse idonta.

Adam ya ce "Za ayi watanni takwas".

Likitan ya sake tambayarta, ko da ta yi fitsari ta kuma ganin jinin, ta ce masa a'a.

Yayi counseling Win ta a kan personal hygiene, amma ba ta san ma me yake cewa ba.

Ya rubuta mata magunguna da allurai, Adam ya karSa ya ja hannunta suka fita.

Ta bashi tausayi ba kaWan ba, lokacin yana tare da aisha, tana gaya masa irin azaba da wahalar ciwon, ita da ta san ciwon kanta ma kenan, balle rumais da hankali bai gama isarta ba.

A dur?ushe haka take tafiya, ya zauanr da ita, ya sayo magungunan, suka je ayi mata.

Sai dai ta ce Allah karta ba za a buWe mata jiki a ganta a gaban Adam ba.

Ga ciwo na cinta, ga zunzurutun wauta, in da Allah ya taimaka, nurse Win da take on duty mace ce.

?arshe ta tsaya ayi allurar nan, ba ta tsaya ba, dai da adam ya fita, daga waje yana jiyo kukanta, sai ka ce ?ar shekara biyar, saboda an yi mata allura.

Sai dai ana gama yi mata allurar ta hau amai, kasancewar tun rana rabonta da abinci.

Aikuwa Adam ya din ga yi mata faWa, na rashin cin abincin da ba ta yi ba, sai dai gaba Waya hankalinta ba ya tare da ita, ?arshe sai da suka dangana da saka mata ruwa.

Haka Adam ya zauna da ita, har asuba a asibitin, aka gama yi mata abun da za ayi mata, na ?arin ruwa da allaurai ya Wauke ta zuwa gida.
Suna tafe a hanya ta samu barci, dama tun suna asibiti yayi sallar asuba.

Da ?yar ya kaisu gida, saboda barccin da yake ji.

Sai da suka isa gida ya tasheta, ta fita daga motar tana takawa a hankali.

Baba uwani na jin tsayuwar motar, ta fito tana yi musu maraba, tana tambayar jikin rumaisa, Adam ya ce mata da sau?i.

Suka nufi step Win bene, baba uwani ta sake cewa "Takawa ko zan zo na taimaka da wani abun ne?"

Ya ce "A'a ta warware, ciwon ciki ne dama, yanzu bacci za ta yi"

Ta ce "To shikenan babu laifi, Allah ya ?ara lafiya".

Ya amsa mata da Amin.

Sai da ya raka rumaisa har Wakinta, sannan ya juya ya fita, sai dai yana fita ya ji kukanta ta na faWin "Na shiga uku, zan mutu".

Da sauri ya koma yana tambayarta menene?.

Ta Wage doguwar rigar jikinta, Jini na bin ?afarta.

"Dan Allah ki yi wa mutane shiru da wannan koke-koken, maganin me zai yi miki?"

"Jinina ne zai ?are, idan ya ?are mutuwa zan yi".

"Ai gara ki mutun in huta, ki yi mini shiru ni, bari na yi wa baba uwani magana, ta zo ko da abun da zata taimaka miki da shi".

Da sauri ta girgiza kai ta ce "Dan Allah kar ka kirata, ka kirawo mini su Yaya usman a waya, dan Allah"

Kallonta yake, cike da mamakin wauta da rashin hankalinta.

"Ke wai ya ki ke so na yi ne?, shikenan ba zan huta ba saboda na aureki? Tun da ba za a kirata ba, sai ki wuce toilet ki gyara jikinki".

"Ban san ya zan yi ba, jinina kar ya ?are ka mayar da ni asibitin".

Guntun tsaki ya ja, ya wuce banWakinta, ruwa ya haWa mata, ya fito ya ce "Shiga" ba musu ta taka a hankali ta wuce banWakin.

Ya nuna mata yadda za ta yi, ta wanke jikinta, ya fita daga banWakin, ya janyo akwatin lefenta, ya Wauko mata pad, kasancewar lokacin da aka haWa lefen har da ita a ciki.
Ya Wauke bedsheet Win daga kan gadon.

Ta fito sanye da doguwar rigar da ta shiga da ita banWakin, tana ta raSe-raSe.

Ya kalleta ya ce "?azamar ina ce ke? Ba ta Saci da jini ba ki ka kuma sakawa?".

"To ba kaya zan fito?" Ta yi maganar tana kawar da kanta gefe.

Ajiye mata pad Win yayi, ya Wauki bedsheet Win ya fice.

Ya je ya dawo, ya tarar da ita ta canza kaya, amma pad Win na? in da ya ajiyeta.

"Ba zaki saka bane?".

"Ban iya sakawa ba, waccan ma su yaya ne suka saka suka bani"

Kallonta yayi, kuma da gaske take maganar, ba wai wasa take ba.

Ya nuna mata yadda za ta yi amfani da ita, ya sanar da ita, duk awa biyar zuwa takwas, ta yi wanka, ta cire pad Win ta Waure a leda, ta canza phant ta canza wata.
Ta jinjina masa kai, ya fita ya bar mata Wakin.

Ba tare da ya rintsa ba, haka ya shirya fita aiki, ko karyawa bai yi ba ya sauka domin tafiya, ya cewa baba uwani, idan rumaisa ta tashi a tabattar ta ci abinci, sannan akwai bedsheet a washing machine, a wanke a shanya, a haWa da kayanta da ta cire suna banWakinta.

Ta amsa masa da za ayi, sannan ya fice.

Ko da baba uwani ta ciro bedsheet Win, ta shanya, kallonsa ta din ga yi, da in da jini ya shata, ta yi shiru da ta tuna a yadda ya tafi Ruma asibiti jiya.

"Anya ba wani abun ne ya faru a tsakanin su ba, babu ko tantama ya haikewa yarinyar nan, amma dai wannan akwai jarababbe wannan ?ar tatsitsiyar ?ar? Wannan ba labarin da zan gaya wa Samha ba ne, ko Hajiya Jamila ?arshenta ma na sha zagi".

Babban abun da ya yi wa rumaisa daWi, bai wuce da ta tashi ta tarar da iman ba, ta ce "Anty Iman, meyasa baki tasheni ba?"

Iman ta ce "Ni na isa? Yaya ne ya ce lallai in zo, in tayaki zama ba kya jin daWi, karatu nake yi an kusa yi mana screening na sauka".

Rumaisa ta ce "Ni dama ki dawo gidan da zama, ina jin daWin ganinki a gidan nan, tun da aka kawoni fa, ban ga mama ba, ranar da ki ka zo, su mai sunan baba su ka zo, ko zama ba su yi ba, suka tafi"

"Eyya, kar ki yi kuka, baba uwani ta ce baki karya ba, ki karya sai na baki wayata, ki kira maman".

Haka kuwa aka yi, rumaisa ta karya, ta karSi wayar Iman dan kiran mama a waya, amma ba ta shiga, sai ta saka lambar mai sunan baba ta kira shi a waya.

Tun a lokacin da ta yi masa kira na farko, tana neman rumaisa, ya gane lambar, kuma lambar take cikin kansa, ko da bai Waga ba ya san lambar iman ce, yana kallon wayar ta ?araci ringing Win ta, ta kaste ya?i Wagawa.

Lambar Usman ta yi trying, shi ma sai da ta kusa katsewa, sannan ya Waga yayi sallama.

"Saboda tsabar kun tsaneni, kun kawo ni, kun ajiye ni, ba wanda yake nemana mama ma ta?i zuwa ta gannu, kuma bani da lafiya ma"

"Iyee, ko amsa sallamar ma ba zaki yi ba, sai wassafo mini ?orafi?".

"Mama ta?i ta zo ta ganni, ni na gaji da zaman gidan nan, dan Allah ku zo ku tafi da ni, gida nake so, kuma bani da lafiya".

Usman ya ce "Ke ban son shirme, a hakan zamu zo gidan naki, ki na yi wa mutane kuka?? Meya sameki?".

"Fitsarin jinin da nake ne na kuma yi, a asibiti fa na kwana, cikina ya din ga ciwo, jini sai zuba yake mutuwa zan yi idan baku zo ba".

Maimakon usman ya tausaya mata, sai ya ?ya?yace da dariya, ya ce "Kin ci kai, Allah sarki girma ya zo".

Cikin kuka ta ce "Yaya usy da gaske nake, a asibiti na kwana wallahi"

Sai kuma ya daina dariyar ya ce "Ahha haba dai?".

"Tun da baka yadda ba, bani mama mu gaisa".

Usman ya ce "Maganar gaskiya mama ta tafi cikin gari, yi wa mutane bangajiya, amma idan ta dawo sai a kiraki".

???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?"To ai ba wayata ba ce ba".

"Aliyu yana da lambar mijinki, zamu zo ma in sha Allah, Allah ya ?ara lafiya uwar gida sarautar mata" yayi maganar cikin zolaya. Ganin ba shi da niyyar Waukar maganar ta ta serious ya sanya ta katse wayar.

***
"Ya ake ciki da maganar yaron nan ne, kwana biyu na jika shiru, babu wani update a kan moves Win sa ne?".

"Ranka ya daWe, ai babu wani sabon abu, ka san yayi aure kwanan nan, kuma kamar ma hankalinsa ba ya kan aikin a kanka yanzu, ko cikin Abujanma, ya fi watanni rabonsa da zuwa".

"A'a fa, ka san yaron nan da wayon tsiya, kar in je lumbu-lumbu yake yi mini, yana wani binciken ta ?ar?ashin ?asa, ko shirya wani abu da ban sani ba".

"Babu abun da yake aiwatarwa, ba tare da na san motsinsa ba, a yanzu dai haka babu ranka ya dade".

Ya juya ya kalli wakili ya ce "Khalifa, kai wurinka babu wani update Win".

Khalifa ya Wan sauke numfashi ya ce "Babu Daddy, sai dai ina nan ina ta bin diddigin sa fiye da yadda ka ke tsammani, babu wani abu da yake yi s kanmu, sai dai wani ?ishin-?ishin da nake ji, wai yarinyar da ya aura, ita ta tserato da Wan sa daga wurin masu garkuwa da mutane, amma bani da tabbas, an ce in jira a samu tabbacin hakan".
Senator wakili ya jinjina kai ya ce "Duk yadda ake ciki ka sanar mini, idan har ita Win ce, ka samo mini tabbacin hakan, a kan lokaci".

"To shikenan, In sha Allah daddy"

***
A duk lokacin da rumaisa ta je canza pad, cikin ?yan?yami take yi, kuma a tsorace take da tunanin jininta zai ?are, har sai da iman ta fuskanci wani abu, amms ba ta takura mata da son sanin menene ba, tun da ba ta gaya mata ba.
Mai sunan baba kuwa wuni yayi yana kallon missed call Win, iman a wayarsa, yana tunanin me za ta ce masa haka, da har ta yi masa 3missed calls, ko tana nufin ta ce Haryanzu ba ta san wayarsa ba ce ba?.
Gashi dai yana sane yayi ignoring kiran, amma yana son sanin dalilin kiran.

Yau sai da takawa ya dawo, sannan iman ta fara shirin tafiya gida, rumaisa ta din ga yi mata magiya a kan ta kwana, amma ta ce ba ta gaya wa ammi ba, direba ya zo ya Wauketa ya mayar da ita.

Takawa ya dubi ruma da ta haWe rai saboda Iman ta tafi ya ce "Ya jikin naki?".

"Da sau?i"

"Kin sha magungunan ko kuwa?".

"Na sha" ta amsa masa a ta?aice, bai sake kulata ba ya ?yaleta, dan yanayin fuskarta ya nuna masa a fusace take, idan ya biye mata rashin kunya za ta yi masa.

Mai sunan baba kuwa, missed calls Win nan a ransa ya wani, zuciyarsa na ta raya masa ya bi kiran nan, ko ya manta ya cigaba da sabgoginsa, sai ya tuna, yayi iya ?o?arinsa ya manta, amma ya kasa, yana ta tunanin menene haka mai muhimmanci da ya sanya ta yi masa missed calls har uku.

Babban abun da ya Satawa iman rai, bai wuce yadda ta koma gida ta tarar da Jabir ba, ya kasa ya tsare a falo, suna hira da Ammi, yana ganinta ya hau rawa jiki, ya fara yi mata hira.
Iya ?o?arin ta take yi, kar ammi ta fuskanci wani abu, dan haka ta ke amsa masa hirar.

Ammi ta tashi ta bar musu falon, ta tafi Wakinta, iman na shirin tashi ita ma, wayarta ta fara ringing, ba ta duba ba ta Waga ta saka a kunnenta, tare da yin sallama.
Shiru yayi bai amsa ba, sai wani numfashi da yake saukewa a hankali, yana jin yadda murayar ta ta, ta daki zuciyarsa.

"Hello, ba a jina ne, Assalamu alaikum" ta yi maganar cikin Wabi'arta ta iyayi.

"Missed calls na gani" yayi maganar cikin dakakkiyar muryarsa da take razanata.

Sai da ta Wan ruWe, amma ta yi iya yin ta, ta haWa nutsuwar ta wuri guda ta ce "Yaya Umar ina wuni?".

"Lafiya ?alau".

"Dama Anty Rumaisa ce ta karSi aron wayata ta kiraka, kuma ba ka Waga ba, ba intentionally na kira ka ba, ai ka gaya mini na daina kiran wayar ba tata ba ce, ka yi ha?uri dan Allah" ta ?arasa maganar kamar za ta saka masa kuka.

Ji yayi jikinsa har wani rawa yake yi, dan shi a rayuwarsa, idan ba mama da rumaisa ba, babu wata ?a da yake keSewa yayi wata doguwar magana da ita, ko ita rumaisan ba shiga shirgin ta yake yi ba, amma ya tsinci kansa da jin daWin sauran muryarta.

Amma da yake namiji namiji ne, cikin basarwa ya ce "Ina rumaisan take?".

"?azu ne na je gidanta, ba ta jin daWi shi ne ta karSi wayata, ta kira ka, amma ta ji sau?i".

"Shikenan" ya katse wayar.

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, duk da muryarsa na razanata, amma ta tsinci kanta da jin daWin kasancewa da shi ta waya. Wani guntun murmushi ta yi, tana Waga kai ta ga Jabir da Nusaiba duk ita suke kallo.

"Iman da wa ki ke waya?" Jabir yayi maganar a hasale.

"Kamar yaya? Yayan Anty rumaisa ne".

"To meye ala?arki da shi" ya sake yin maganar yana tsareta da ido.

Tashi ta yi tsaye ta ce "Yayan matar wa na ce, kuma ni babu wani abu tsakani na da shi, ta ari wayata ta kira shi ne kawai".

"Ina fa lura da yadda ya din ga bin ki da kallo lokacin bikin nan, idan ya ganni tare da ke ya din ga hararata".

Ta girgiza kai ta ce "Gaskiya kai ne ka ga haka, amma ba hakan bane" ta wuce ta nufi Wakinta.

Jabir zai kuma magana, Nusaiba ta ce "Uncle J, ka bi ta a hankali, fushi da tashin hankali ba naka bane ba, ba abun da yake tsakaninta da mutumin nan, na riga na baka shawara, ka je wurin ammi

25 / 67