Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Aysha Cool Category :  Complete Novels

Chapter   29 / 67

84K to 87K   out of 199.9K words

zan yi mata, Sabir kawai zan gani, a nan za ta wuni, a haWa masa kayansa, da shi zamu tafi, zan kaita gidansu gobe in Allah ya kaimu za su wuni a can, ba ta taSa zuwa gida ba".

Ammi ta ce "Masha Allah, babu laifi"

Rumaisa tana zaune a gaban sabir, da yayi ruf da ciki a kan gado, yake ta bacci, sai shafa sumar kansa take yi tana murmushi. Da hannu Waya ya Waga rumaisa ya juyota tana fuskantar sa.

"Me na yi maka?".

"Ban sani ba, ke wace irin yarinya ce sai ka ce na'ura mai ?wa?walwa, kanki gaba Waya baya gaya miki abun da ya dace, iya abun da aka zuba miki shi ne yake aiki a kanki, ammi fa sirikarki ce, ya dace ki gaya mata wannan maganar?".

Ta kalleshi ta ce "Meye wani sirika kuma, ni ammi babata ce, haka mama ta gaya mini, ka ci sa'a da ba komai na gaya mata ba, har da cewa nonona bai fi girman wake ba, duk wannan rufa maka asirin da na yi ba ka gode ba, ga? gingimen asirin da na daWe ina rufa maka"

Adam ya dafe kai ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ba dai aure ba, zan ?ara aure ba zan zauna da ke ba kamar namiji ba, ba zan iya ba daga nan ki je ki cigaba da faWa"

"Ni ba zan kula ka ba baban sabir, na san haushina ka ke ji saboda na faWi abun da ka ke yi, ni da kai idan na ce zan yi maka nasiha, ba yadda za ka yi ba, amma yanzu na san idan ammi ta yi maka faWa zaka yadda"

Rumaisa ta zubawa sabir ido, Ammi ta shigo, ta ce "Maman sabir, Haryanzu ba ki gama ganin sa ba?".

"Wallahi kuwa ammi, bana gajiya da kallonsa ni ai".

Ammi ta zauna a gefen gado ta ce "Zo ki zauna a kusa da ni mu yi sirri ?ar auta".

Rumaisa ta tashi ta zauna a kusa da Ammi, Ammi ta ce "Kin ga dai ba kya so ya yi miki kishiya ko?" Rumaisa ta ce "Eh".

"Meyasa ba kya so?".

"Kai, ammi duk mata kowa sai na ji ta ce ba ta son kishiya, shiyasa nima na ce ba na so".

"To ki saurareni ki ji, Abun da nake nufi da duk abun da ya yi miki na rashin kyautawa ki gaya mini, ba yana nufin ki din ga faWar sirrin aurenku ba, ya ce mini da wasa yake yi miki, kin ga kin sa ya ji babu daWi".

Ruma ta ce "Ammi, ba dan ya ji haushi na faWa ba, kin ga tsoro nake ji kar na yi wani abu da idan mama ta ji, ba zata ji daWi ba, ta ce na watsar da tarbiyyar da ta yi mini".

"Ba za ta ce haka ba, ai shi mijinki ne, sannan kar ki sake ki faWi irin wannan a gaban wani kin ji?"

"To ammi, in Allah ya yarda".

Ammi ta dafa kafaWarta ta ce "Yauwwa yarinyar kirki, Allah ya sa kin fara makaranta a sa'a, idan aka kwana biyu mai koya miki girki zan Wauko, har gida ta din ga koya miki ".

"Ammi na iya girki fa, ki tambayi iman ki ji, har shi papa ya san na iya"

Ammi ta ce "Waye papa kuma?"

"Baban Sabir "

Ammi ta yi murmushi, ta ce "Masha Allah, Allah Ya albarkaci aurenku"

Rumaisa ta yi gum ba ta amsa ba, dan ita auren nan ya isheta.

Rumaisa ta dage ta bi Iman kitchen, har da ammi a yin girki, sai dai ammin ya jinjinawa basira irin ta rumaisa, da ka ga yadda take gudanar da girkin zaka san, ta horu.

Wuni ta yi tare da ammi, ga iman ga sabir, jin su take tamkar wani Sangare na rayuwarta, da ganinsu kawai ke samar mata da nishaWi.

Da yamma, rumaisa ta silale ta fita harabar gidan, ba tare da sun sani ba, ta din ga zagaya fulawoyin gidan, da manyan bishiyu.
Wani zomo ta gani, fari tas da shi, yana tsalle-tsallen sa, ga sauran tsuntsye da suke kaiwa suna komowa.
Da sauri ta bi zomon, tana son ta kama shi, sai dai ta ga ta Sullo wani wuri.

Yana zaune a kan fararen kujeru, gabansa da litatafai, da system, ya tattara nutsuwarsa sosai a kan abun da yake yi.

Bayansa ta gano ta ce "Papa" a hankali ya waiwayo ya kalleta, ta Wan tsura masa ido, sai kuma ta ce "Laa ashe ba papa ba ne kai ne, na gane ka, da ka taSa sawa na shigo gidan nan" ta yi maganar tana ?arasawa in da yake.

Ya ce "Wow, ashe zamu sake haWuwa, sannunki, ya ki ke?"

"Lafiya ?alau" ta ?arasa maganar tana zama a kujerar da ke facing Win sa.

"Yau ya aka yi aka bari ki ka shigo, har ki ka zo nan?"

Da Wan mamaki ta ce "Wa zai hanani shigowa, to shi ya kawoni"

Mahmud ya ce "Shi wa?"

"Baban Sabir, ba ka san yanzu mijina ne ba?"

Ya Wan yi turus, sai yanzu ya gane zancen da Mummy suke yi ita da su Samha Wazu, amma bai gane ba, kasancewar tun da ya dawo sai yau ma ya fito.

"Da gaske ke adam ya aura?".

Rumaisa ta ce "Hmmm, ya aka yi baka sani ba? Ba a gidan nan kake ba, ba ka zo bikinmu ba kenan?".

"Ina ?asar waje ai, can makaranta, labarin bikin kawai na ji".

Cikin mamaki rumaisa ta ce "To ta yaya kuna gida Waya, amma ba ka sani ba, wai ku ba ?an uwa ba ne?".

"Eh, kowa babarsa daban".

"To, ku ?a?an kishiyoyi ne?".

Yayi dariya, tambayarta ta yi yawa amma ya ce "Eh".

"TaS to ni wallahi ba za ayi mini kishiya ba, amma to dai meyasa ba ka zuwa wurin su, baka san yayi aure ba?".

"Ni ma ba ya zuwa wurinmu"

Ruma ta ce "Ai papa sai fatan Allah ya shirya shi".

"Ke ma yana yi miki halin na sa kenan, na rashin kirki?"

"Hmm, ai ba dan Sabir ba ko, ba zan aure shi ba, amma dai ya sakani a makaranta mai kyau na ji daWi".

Mahmud ya tattara nutsuwarsa a kan ta ya ce "Da gaske dai, ke ki ka dawo da jaririn nan?"

"Wai meyasa ?an dagin nan naku, suka damu da lamarin nan ne? Wato an rainani ko? To anty aisha da kanta ta bar mini jaririn nan, kuma har da zobunanta da Wankwalinta, ta bani, ni fa bana damuwa da kowa sai ya yadda da ni a duniyar nan, malaminmu ya ce idan Allah ya yarda da kai, ka huta, shiyasa ni ban damu da kome za a ce a kaina ba".

Mahmud ya yi dariya ya ce "Wow, i like your confidence "

"Wai kai ya sunaka ne?".

"Mahmud" ya bata amsa, Wan turus ta yi tana kallon sa, "Dan Allah da gaske?"

Ya ce "Eh"

Ta ce "Innalillahi, sunan babana, sunan Wa na"

ya ce "Shikenan na yi ?a, na zama daddynki"

Ta yi dariya ta ce "yauwwa to ka taSa zuwa ka ga Wa na? Ranar nan na ce ka je wurin ammi ka ganshi".

"Zan je wataran".

Rumaisa ta ce "A'a, yanzu dai mu je in ga mamanku, ita ce ban taSa gani ba, kai ma sai mu je ka ga Wa na, mai sunan ka".

Mahmud ya ce "mijinki ya huta kallon Tv, ke kaWai kin isa ba shi dariya".

Ta ce "TaS, sai ka ce wata cartoon, mu je ka nuna mini ita" ya tashi tsaye, yayi gaba, ya jagoranci rumaisa har tsakiyar falon Mummy.

Ya ce "Mummy, ga amaryarku fa ta ce na kawota ta gaida babata"

Gaba Waya suka juya suna kallon rumaisa da ke bin su da kallo.

Samha ta fara ganewa a cikin su, ta kalli Fauziyya da ru?ayya, sai dai suna haWa ido da Mummy, jikinta ya yi sanyi, gaban Mummy kuma ya yi mummunar faWuwa.

Mummy ta ce "Wace wannan?"

Samha ta yi tsaki ta ce "Matar Adam ce, saboda asara, kalli abun da ya kwaso saboda ba ya gudun abun kunya".

Mahmud ya kalli Samha ya ce "Ba ruwanki, ba wurinki na kawota ba" ya kalli rumaisa ya ce "Daughter, ga mamana nan"

"To ya na ga ba ka kama da ita, kana kama da ammi?" Ji yayi wani irin gumi ya tsatstsafo masa ta kafar gashin jikinsa.

Mummy cikin jarumta da iya duniyanci ta ce "Ikon Allah, da ba a kawo mini ita mun gaisa ba, kai ka kawo mini ita, takawan ne ya ce ka kawo ta mu gaisa?"

Mahmoud ya ce "A'a, cewa ta yi zata zo ta gaida babata".

Fauziyya ta ce "Tir?ashi, ashe da muka ganta a wurin dinner ta fi cika ido, ni Wallahi ban gane ta ba ma"

Samha cikin ?uluwa ta ce "Mummy wai meyasa ki ke wani sakar mata fuska, meye ala?arta da ke, tun da ba Wanki take aure ba, kuma ba ayi niyyar kawota ta gaishe ki ba?"

A fusace rumaisa ta ce "Baiwar Allah wai me na yi miki ne? Kullum ki ka ganni sai kin zageni, ba ruwanki da ni, ni ba wurinki na zo ba".

Mahmud ya ce "Samha ba ruwanki da ita please, ki ja girmanki, daughter ga mamana".

Rumaisa ta kalli mummy, ta risuna kamar yadda ta ga ana yi ta ce "Barka da wannan lokaci "

Mummy ta ce "Barkanmu dai, kuna lafiya?".

"Lafiya ?alau"

"Ya mijin naki, ya Sabir? Ko da yake fushi nake yi da mijinki, ba ya zuwa in da nake, kuma ba ya kawo mini Wan naki, Allah sarki fulani, ashe tare aka yi garkuwa da ku?".

Rumaisa ta yi shiru, ba ta ce komai ba.

Mummy ta ce "Ru?ayya, ki saka a kawo mata abinci".

"A'a na ?oshi, yanzu muka gama cin abinci da ammi".

Cikin ?arfin hali Mummy ke magana, domin wani irin bugu ?irjinta yake yi, har hakan na neman bayyana a fuskarta.

"Ni ma ai babar takawa ce, ki zauna mu yi hira mana, da takawa, da aisha, duk ?a?anmu ne, haka muka ji rasuwar ta, mun shiga tashin hankali da ruWani, babban abun takaicin yadda ta haihu a hannun 'yan bindiga, abun bai yi mana daWi ba".

Maimaita rumaisa ta amsa mata, sai ta tashi ta ce wa Mahmud "Daddy mu tafi mu je ka cika mini naka al?awarin" kallon rumaisa suke yi, da tunanin anya ma ba ta da taSin hankali kuwa? Abun da ake tambayarta daban, abun da take yi daban.

Yayi murmushi ya ce "To mu tafi, tun da kin ga mamana, kin gaisheta".

Rumaisa ta ce "Eh, Mummy sai anjima "
"To amarya, sai mun zo gidan naki kuma"

Allah ya kawo ku.

Mahmud ya nuna mata Fauziyya da ru?ayya ya ce "Wannan ?annena, ga Fauziyya ga ru?aiyya"

Kan ya ce wani abu a kan Samha ta ce "Ita kuma wannan na santa, mai zagina ta na ce mini ?ar aba, na santa a gidan baba farin rawani, mai girma turaki, baban anty aisha, shikaWai ya yi mini mutunci a gidansu".

Yayi murmushi ya ce "To shikenan mu je" suka fita.
Samha ta tashi zaune ta ce "Na shiga uku, na rasa me ma zan yi? Kaina ya gama kullewa".

"Jikina ya na bani akwai wani abu Soyayye a game da yarinyar nan, dole zan ganta a karo na biyu, kuma ya zama dole baba uwani ta sanya mini ido sosai a kan su"

Fauziyya ta ce "Ji munafuka kai, wai Mahmud ba ya kama da ke, kin ga idonta a tsaitsaye"

Mummy ta ce "Na gani" nan suka cigaba da tattaunawa a kan abun da yakamata su yi a kan rumaisa.

Ammi kuwa sai neman rumaisa suke yi, basu ma san in da ta yi ba, ammi har hankalinta ya Wan fara Wagawa.

Rumaisa kuwa da suka fito harabar gidan, sai surutu take yi wa Mahmud, kamar dama can sun saba, ya fi takawa sau?in kai da sakin fuska, a wajejen harabar sashin ammi ya tsaya ya ce "To shikenan, ki gaishe mini da takwarana". Ta kalleshi ta ce "Haka muka yi da kai, ba na gaida mamanka ba, ni ma ka zo mu je ka gaida tawa"

Ya Wan yi jimm yana kallon rumaisa, "Dan Allah haba daddy, ni fa a gidanmu ban san babana ba, sai yayyena su bakwai, komai nake so suna yi mini, dan Allah mu je ka ga Sabir".

"Ki shiga ki Wauko shi, ki kawo shi na ganshi".

Ta no?e kafaWa, kawai ya tsinci kansa da bin rumaisa.

Ba Ammi ba, har iman sai da ta razana, ganin Mahmud a filin falonta, shi kansa tsayawa ya yi yana bin su da kallo, rabonsa da falon nan, kusan shekara da wani abu, da Ammi ta neme shi, ta nemi alfarmasa kai tsaye ya ce ba zai yi ba.

Ammi ta ?ure shi da ido, kamar yau ta fara ganinsa.

Kallo Waya ya yi wa ammin, ya sunkuyar da kansa, ?asan zuciyarsa yana tuna abun da ya yi mata na ?arshe da ya kasa mantawa.

"Ashe ka dawo, ya makarantar?"

Ba tare da ya Wago kai ba ya ce "Lafiya lau"

Ruma ta ce "Ka zauna mana" ta nufi in da Sabir yake wasa da kayan wasansa, yana ta rarrafe yana Sarna, ta Waukko shi ta kawo masa shi.

Ya karSi sabir, ya zauna da shi a jikinsa, ta kalli sabir ta ce "Waye wannan?"

Sabir ya ?ura masa ido, Mahmud wani murmushi ya saki, ya shafa kan Sabir, wata irin ?aunar yaron ta shiga ransa, da yake jin tamkar daga jikinsa ya fito. Har aka yi dambarwar nan aka gama, bai taSa ganin Sabir ba.

Cikin murmushi ya ce "Na yi kama da babanka ko, nima babanka ne"

Su Nusaiba kamar tv, haka suke kallon Mahmud da rumaisa.

Ruma ta ce "Ba papa ba ne, uncle ne wannan"

Mahmud ya ce "A'a Daddy dai" ya mi?e da Sabir a hannunsa ya nufi hanyar waje yana faWin "Allah ya bani? Wa ba mata"

Ruma ta bi bayansa tana cewa "Ai wallahi gara in bar maka takawa da in bar maka Sabir"

Ammi ta ce "Kun ga ikon Allah, me rumaisa ta gaya wa yaron nan ya yarda ya zo in da nake?"

Nusaiba ta ce "Wallahi ammi ni ma mamaki abun ya bani, wancan karon fa, kalli yadda aka kai ruwa rana, kan ya zo kiran da ki ka yi masa, bai kuma zuwa ba, kin ga ikon Allah yau shi ne har cikin falonki, kai lamarin baiwar Allah nan yana Waure mini kai"

Kasa jurewa Ammi ta yi, ta fashe da kuka, nan da idonta ya yi ja.

Iman ta ce "Ammi dan Allah ki yi ha?uri, ki cigaba da jurewa, jikina ya na bani komai ya kusa zuwa ?arshe"

"Allah ya sa, ina fatan hakan".

Yauwwa share hawayen, iman ta yi maganar tana gogewa Ammi hawayen fuskarta.

Mahmud kuwa ba abun da yake sai dariyar shirmen rumaisa.

"Ka ga daga nan, ba zan Wara ko ina ba, sai ka bani Wa na, daga gani sai ka ce zaka tafi da shi, to in gaya maka yau gidanmu zamu tafi da shi, sai ranar Litinin za a dawo da shi".

"Ta yaya zaki kula da shi? Kema baki wuce a kula da ke ba ai"

"Zan iya, wanka ne dai, sai in saka ko baba uwani, ko su barira su yi masa wanka".

Ya ce "Baba uwani kuma?"
Ta taSe baki ta ce "Na fasa ba ta, ni matar nan ba ta yi mini ba, dan dai kawai ammi ta ce ta zo ta zauna da ni ne, ta yi saka ido, kamar mara gaskiya".

"Daughter, ki kula sosai da lamarin gidan nan kin ji ko? Sannan kar ki yadda wani ya din ga sanin abun da yake faruwa a gidanki, mussaman baba uwanin".

"Kai ma ka lura ta na da saka ido ko?"

Mahmud ya ce "Eh to kusan haka, sannan ki kula da takwarana sosai, da sosai"

"TaS, ka manta ni na kula da shi ranar da aka haife shi ranar majaifiyarsa ta bar duniya, kwananmu uku muna bulayi a daji, bamu samu hanya ba, na zaci ma mutuwa zai yi " ya Wan ware ido ya ce "Haba dai"

Ta yi ?asa da muryarta ta ce "Wallahi da gaske nake, ka san yadda ake garkuwa da mutane kuwa, to in gaya maka har sunan wasu na ji, Anty Aisha fa wasu ne suka saka a saceta, saboda papa" kallon ruma yake cikin mamaki. Ta cigaba da c???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ewa "Kuma wai ?an gari ba su san meyafaru ba, suka ce shi ya kasheta yayi tsafi da ita, na san abubuwa da yawa, na ?i gaya masa, ya fiye fushi da zafin zuciya, shiyasa ma?iyansa suke nasara a kansa. Ai ni na fi shi wayo fa, in gaya maka ranar da muka tafi katsina a kan bullet da bindigogi na zauna, jakunkunkunan, duk an yi musu lamba, duk na haddace lambobin. Har da wani gari da na je, an ?ona garin, na ga wani tsoho, muka yi hira da shi".

"Amma Meyasa ba zaki gaya masa abubuwa da ki ka sani ba?"

"Sai abu biyu ya faru, ya daina saurin fushi da zuciya, na biyun kuma ba wanda zan gaya wa"

Murmushi yake yana kallon rumaisa, ta fiye surutu, but she's very talented akwai hikima, da kaifin basira a maganganunta.

"Me ki ke yi a nan wurin?" Ta ji muryar takawa a kausashe.

"Daddy na kawo wa Sabir, ya ga takwaransa".

"Uban waye ya ce ki bashi Wa na?"

Ya tunkari Mahmud, zai karSi Sabir, amma Mahmud ya ri?e Sabir, by force Adam ya hankaWe shi, ya karSi Wan sa, har ya yi gaba ya dawo, ya fizgi hannunta ya nufin sashin Ammi da ita.

Ya balbleta da bala'i "Kin san hatsarin da yake cikin abun da ki ka aikata? Kin san me gayen nan zai iya yi, da ki ka Wauki Wa na ki ka bashi, What if yayi amfani da hakan against me? Wani irin gargadi ne ban yi miki a kan yadda za ki zauna da mutane a gidan nan ba?"

Rintse idonta ta yi, saboda yadda yake ta zazzaga mata masifa.

Ammi ta taso, ganin yadda jikin Adam yake rawa, ta karSi Sabir, ta ja Adam ta zaunar da shi, ta ce "Wannan ha?ilon na meye haka? Ka kwantar da hankalinka ba abun da zai faru".

"Ammi yarinyar nan ba ta jin magana, duk abun da zan gaya mata ba ta ji".

"Ni dai na san ba da kunnen wani nake ji ba, kuma na san abun da na aikata dai-dai ne, ko ba komai na saka uwa ta ga Wan ta, tun da har ammi ta ji daWin abun da na yi, ta ga Wan ta, na ji daWi, Kuma ni yana yi mini kirki ina ruwana da faWanku, ni duk wanda yake son sabir ina son sa, na

29 / 67