Chapter 8 Reading SHAAMEEƘH Alfaharin Basarake by Harira Salihu Isahl HN Novels

SHAAMEEƘH Alfaharin Basarake by Harira Salihu Isahl

Author :  Harira Salihu Isahl Category :  KDP NOVELS

Chapter   8 / 15

21K to 24K   out of 43.9K words

ganku zan barku taren shikkenan."

"Baby am sorry kin ji dan Allah ki daina fushi da ni, kema kina gani ai ba komi
tsakaninmu tun kamun ma ki zo, ba yacce na iya da rashin mutuncinta ne kawai."

Leesha ta buɗe baki za ta yi magana sai Angelina ta haɗe bakinsu( wa iya zubillah).

Leesha da Angelina kenan, ƙawayen Soffy na ƙut da ƙut, kuma abokanan faɗanta,
dukkansu a nan Delhi suke karatu, course ɗaya class ɗaya komai ɗaya haka suke,
Angelina ƴar India ce a nan suka haɗu da Soffy, sai Leesha da take ƴar Nigeria a
babban birnin Abuja, mahaifinta babban hamshaƙin mai kuɗi ne, to daman ita already
idanuwanta a buɗe suke saboda an sangarta ta da kuɗi, tana zuwa India ta haɗe da
Angelina wacce daman ta jima tana bin Soffy da maganan lesbian ta ƙi, to Leesha na
zuwa suka jone sai dai addu'an Allah ya shirya.




***
Jirgin su Soffy yayi landing a babban filin jirgi dake cikin garin Yobe, da misalin
ƙarfe 11pm da mintuna a agogon Nigeria.
Ganin dare yayi kuma daman ba tayi waya da gida ba, hakan ya sa ta nemi taxi
kawai, kwatance ta masa yace ya gane anguwan, shiga tayi suka kama hanya.


Big Dad da big Mom zaune suke a palourn nasu, kallo suke suna hira su biyunsu.
"Assalamualaikum", Sabeer ne yayi sallama yana mai shigowa palourn, bayan iyayen
nasa sun amsa masa sallaman.

Ƙarasowa palourn yayi, ɗaya daga kujerun dake palourn ya samu ya zauna, cikin
girmamawa ya ce, "Barka da dare Dad."

"Yauwa barkanmu son, sannunka da shigowa ko."

Amsawa Sabeer yayi tare da gaishe da iyayen nasa duka, suka amsa sannan big Dad ya
ce, "Sabeer ya labarin ƙanwarka ne kam, shiru fa har yanzu bata dawo ba kuma
layukanta ba sa shiga, both na Nigeria da na Indian, mutum tun jiya yana hanya."

Sabeer ya ce, "Dad inajin bata taso da wuri ba ne, but am sure yau za ta shigo
komin dare."

big Mom ta ce, "To Allah ya sa, Allah ya kawota lafiya, ni damuwana ma yanzu
layukanta duka a kashe ba sa shiga, idan ta iso ya za'a yi ta sanar balle driver ya
je ɗaukanta."

"Mom ba ga taxi's ba, tun da ta rufe wayoyin ta ai sai ta hau motorn haya kuma,
driver ma ya huta fita da daren nan."

Big Mom Hararan Sabeer tayi ta ce, "Lallai ma Sabeer ashe ba ka da imanin ƴar
uwanka, ƙanwar ka ta biyo motan haya da daren nan, kana faɗa ko damuwa baka yi ba."

"Mom ya za'a mata to? ra'ayinta ne fashigowa da daren a hakan ma wai dan an mata
magana ne, dan haka ita ta jiyo ko ba haka ba Dad?"

Murmushi big Dad yayi ya ce, "Allah ya shirya ka son."

Da "Ameen", Sabeer ya amsa.

Big Mom ta ce, "Wai Alhaji har kana murmushi kana biye masa, ƙanwarsa na can hanya
ga dare, ai wallahi da ace ta ƙira to Sabeer zai sha mamaki, dan shi zai je ya
ɗauko ta."

Murmusawa yayi dan yasan rikicin mahaifiyar tasa, da kuma son da take wa Soffy,
kaman ita kaɗai ta haifa mace, cewa yayi, "Allah ya huci zuciyan Mom tamu, da ta
ƙira kam Insha Allah zan je ɗaukota, ur wish is my command Hajiyar mu."

Big Dad ya ce, "So kin ji ai ɗan ki mai jin magananki ne."

"Allah ya muku albarka dukanku", faɗin big Mom.

Sabeer ya amsa da Ameen, sannan ya ce, "kuma kasan me Dad? Allah ko ɗazu da na je
gidan Baba Alhaji, sai da ya tambayeni ko ta iso, Hajiya mama tai ta surutu."

Big Dad jinjina kai yayi ya ce, "Allah ya shiryaku ya iso da ita lafiya, ku na saka
mini iyaye surutu da girmansu."

"Dad na faɗa misu za ta dawo, za ta dawo, amma stofin nan sai surutu suke yi...",
Sabeer bai ida gama rufe baki ba sai ganin mutum suka yi ya shigo palourn kaman an
jeho sa daga sama.

"Ayoyoo Mom, Ayoyoo Dad", da haka ta shigo palourn ba sallama.

Sabeer ne ya kalle ta, sannan ya ce, "Sis ina sallaman?"

Tura baki Soffy tayi tare da haɗe fiska ta wuce wajan Mom, tana faɗin, "Mom i miss
you soo much wallahi, Dad sannunku da gida."

Sabeer rai a ɓace ya ce, "Ba da ke nake magana ba?"

Mom ce tayi caraff ta amshe tare da cewa, "Haba Sabeer wani irin rashin imani ne
haka? Yarinyarka ta dawo ko hutawa ba tayi ba kana mata tsawa haka, ni fa bana son
takura."

"Mom sallama ne fa bata yi ba, kuma gaskiyan ne masifa? To Allah ya baki haƙuri
Hajiyarmu, amma dai dawowan ma ba don Shaameekh ya mata magana ba, to ba dawowa za
ta yi ba."

Big Dad ne ya ce, "Soffy bana son shirme daga yau kada na kuma ganin kin shiga waje
ba sallama, Sabeer kai kuma bana son surutu daga dawowan ta ka rufe ta da faɗa,
sannan mamanka na faɗa kana faɗa."

Ƙwafa big Mom tayi ta ce, "A'a Alhaji ka ƙyale sa dai yayi surutun tun da shi ya
haife ni ko ya haifa mini ita, a ce ba za'a bar yarinya ta huta ba daga dawowanta
sai masifa, Sabeer kada ka fita a idona inma uban wa ya saka ta dawowa ba dai ta
dawo ba, to bana son dogon magana."

Soffy miƙewa tayi tana faɗin, "Mom and Dad nikam na shiga daga ciki dan na gaji",
ta faɗa tana nufan hanyan da zai sada ta da ɗakinta, ba tare da ta cewa yayan nata
komai ba.

Big Mom ta ce, "Okay doter a huta lafiya."

Ajiyan zuciya Sabeer ya sauƙe tare da miƙewa yana faɗin, "Hajiyanmu da Alhajinmj
nima na gudu safiyar alkairi."

Iyayen nasa haɗa baki suka yi wajan cewa, "To Allah ya tashe mu lafiya."

Da Ameen ya amsa ya fice a palourn yayi part ɗin da yake nasu yaran mazan gidan.



⭐⭐
Ɓangaren Shaameekh da ya shige wanka, sai da ya ɗau lokaci sosai kaman ko yaushe
sannan ya fito, sanye da rigan wankansa mai kalan bula(blue).
Gaban dressing mirrornsa yaje yana drying gashin kan sa, yana gamawa ya shafa
man sa mai stadan gaske, sannan ya ƙara tajewa, ya shafawa gashin nasa turaren kai,
sannan ya taje gemun sa ɗan dai-dai gwanin sha'awa, lokaci ya duba ganin lokacin
sallahn magrib ya ƙarato kuma daman yana da alwalansa, dan haka sama-sama ya shafa
mai ya sanya jallabiya da short, ya fesa turarukansa masu daɗin ƙamshi na gaske, ya
ɗau keynsa motansa ya fice a ɗakin.

Ruwa ya ɗauka a fridge ya sha kamun ya fice a palourn, Motor ya shige ya mata key
sai masallaci.

Ko da suka idar da sallahn bai tafi ba, har sai da yayi isha'i, bayan ya idar
da azkar nasa da komai fita yayi a masallacin ya shiga motor yayi gaba.
Sai da yayi tafiya sosai, wanda da alama ya bar anguwan da yake ma gaba ɗaya.

A Gaban wani babban gida yayi parking bai shiga da motorn ba ya sauƙa, yayi
knocking ƙofan jin shiru ya sanya shi turawa ya shiga cikin gidan.

Direct palourn gidan ya shiga da sallama ba kowa a palourn nan ma shiru, sai
sautin TV da ke aiki.
Bedroom ya wuce kai staye, "Assalamualaikum", shiru ba'a amsa masa ba nan ma, sai
dai ya ji alaman mostin ruwa a banɗakin, hakan ya sanya shi gane cewa mai gidan
yana banɗaki ne.

Wucewa yayi wajan makeken haɗaɗɗen gadon da ke cikin ɗakin, ya yiwa kan sa masauƙi
a bakin gadon ya zauna, tare da fiddo wayansa yana danna.

Can ba jimawa Manseer da ke banɗakin ya fito ɗaure da towel mai ɗan girma a
ƙugunsa, ganin mutum zaune a kan gadonsa ya sanya shi buɗe baki zai tsala ihu, shi
kuwa Shaameekh da kan sa ke kan waya, to daman ya ji fitowansa dan haka cewa yayi,
"Ka ga malam kar ka kashe mini dodon kunne da ƙaton muryanki."

Ajiyan zuciya Manseer ya sauƙe ya ce, "Innalillahi ɗan air kai ne dama? Za ka sa na
sume", ya faɗa yana ƙarasawa gaban closet nasa tare da cigaba da magana, "Wallahi
Man ka storitani mutum sai ka ce wani aljani."

"Ka sani ko ni aljanin ne, ƙaramin ɗan iskan gauro kawai a ce wai duka wannan ƙaton
gida, ba mata sai dai mutum yai ta bin matan banza", faɗin Shaameekh.

"Man ba gauro za ka ce ba, gauro da yayan sa ƙaton gardin gauro mara lafiya, dan
tabbas baka da lafiya."

"Mtsww! wai mutum ace a zo gida ba mai gadi balle mai aiki, taklless of matan gida
tsabar rashin gaskiya, Allah dai ya yaye maka, bari naje Nigeria tabbas sai na zuga
Abba an maka aure."

Dariya Manseer ya saka ya ce, "Au wai Man an faɗa maka hakan damuna zai yi? Kai
dai da ba kada ishashshen lafiya ne zai dame ka, ni ai ka ga alaman ko mata huɗu
zan zauna da su kuma na yiwa ko wacce ciki, ka ga abin da zan ce maka shi ne kawai
Allah ya stare hanya, dama dai auren nake so je ka zuga Abban kawai."

"Ɗan iska kai ne dai ba ka da lafiya ni garau nake, matan ba su gabana ne kuma ban
shirya aure yanzu ba", Shaameekh ya faɗa yana taɓe baki.

"Matsalarka Man ni dai auren ma kuwa shi ne a rai na, sannan in ban yi wannan
shekaran ba to Insha Allah wani shekara zan shiga daga ciki."

Shaameekh barin danna wayan yayi yana kallon Manseer ya ce, "Man wai ina za ka je
kake kwalliya haka?"

"Yawon nemo chika(beb) zan je, ai abin da kake son ji kenan dama", Manseer ya faɗa
yana fesa turare.

Taɓe baki Shaameekh yayi ya ce, "Ka gama muyi magana please ni shi ne abin da ya
kawo ni, ba shirme ba."

Bayan manseer ya gama shiryawa, palourn suka fito suka zauna, Manseer ya ɗauko
musu abin sha a fridge da snack's ya ajiye, sannan ya ce, "Man ko zaka ci abinci?"

"Allah ya sauwaƙa naci girkin namiji, kai fa bayan iskanci har da daudanci kake yi,
idan ba haka ba me ya haɗa ka da dafa abinci? Girki ai sai mace kai kuma ka ƙi
ɗaukan Maid staban maƙon kuɗi."

Manseer ya ce "Ba ruwanka da kuɗi na tun da na iya", ya faɗa yana wucewa kitchen.

Da plate ya fito cike da jolof na taliya da manja, wan da ya ji kifi da su green
beans, sannan ya zauna yana cin abincin sa, yana faɗin, "kai dai tun da ba zaka ci
girkin namiji ba sai mace ya rage maka, nikam ba na cika cikina daman ni na girka
abu na ba wani ya girka mini ba."
Shaameekh Yoghurt kawai ya ɗauka shi ma kurɓan yayi ya ajiye, sannan ya ci gaba da
danna wayansa.

Manseer yana gama cin abinci ruwa ya kora, sannan ya tattara wajan ya kai kwanukan
kitchen, ba jimawa ya dawo ya zauna gefen abokin nasa.

Shaameekh ya ce, "Yanzu dan Allah bayan girki har da wanke plate's or me suke ƙiran
sa da hausa duk kai kake yi Man?"

"Capital Yes ma kuwa ɗan renin wayo, wai wanke-wanken ne mai ake ƙiransa da hausa,
kana nufin baka san sunan wanke-wanke ba, to har da shara da goge goge ni nake yi,
ai dai kaga gidan clean.

Ikon Allah fan's, abin mamaki gani Shaameekh da dariya, har da riƙe ciki dan
dariya, sai da ya stagaita sannan ya ce, "Kai ɗan daudu, kai ɗan iska, kai ɗan aiki
and the most funny thing about all this is that kai ne kuma mai gadin gidanka", ya
faɗa yana dariya har da riƙe ciki.

Manseer ya ce, "Shege mugu kayi ta dariya kaman mahaukaci, ai dai wallahi a cewa
mace ga ni ga kai ta zaɓa ɗaya, to am telling you ba mai zaɓan ka, dan ba abinda
za ka mata idan ba ka tara mata gajiya ba, sannan ka bar ta da ayyukan gida duka
ita ɗaya."

Shaameekh guntun ya ja ya ce, "Daman da kake maganan nan what is she there for? Ai
in ni zan yi wa mace aikin gidanta, to ta mutu ba'a mata aiki ba wallahi, tayi
aikinta staff sannan ta zo na ƙara mata da nawa aikin."

Manseer ɗaga hannu sama yayi, ya ce Allah kar ka kashe ni ka nuna mini ran da zan
ga Shaameekh, yana yi wa mace aiki, ai kuwa ranan duniya duka sai ta ɗauka, har
media sai sun ganka sun sheda sun tabbatar mace ta saka ka aiki."

Taɓe baki Shaameekh yayi ya ce, "Mu magantu akan abin da ya kawo ni."

Manseer hankulansa duka ya tattara ya miƙa wa Shaameekh yana sauraransa, ya ce,
"Ina sauraranka aboki."

Sai da Shaameekh ya numfasa, sannan ya ce, "Akwai mastala babba Manseer."

Cikin yanayin kulawa Manseer ya ce, "Mastalan me haka Man?"

Shaameekh cewa yayi...



***

MASU DARAJA HABIBTIEES NA UWAR BATOORL AKWAI GARAƁASA GUDA, A YANZU KAMUN MU
KAMMALA FREE PAGE'S TO KUƊIN LITTAFI DAI ₦300/250f NE, IDAN MUN KAMMALA KUWA
₦500/500f YAKE INSHA ALLAH.

9161720046
Harira salihu isah
Opay
&
2220553988
Harira salihu isah
Uba
Shedar biya ta wannan layi 07015870735.

Mutanen Nijar ku ma ku yiwa wannan layi magana dan yin payment naku 500f.
+227 88 73 81 26
Sai kuma a turo shedar biya ta wannan layi
07015870735.


# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
SHAAMEEKH
B̶̶O̶O̶K1

Officially


𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


‫ اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله‬SAW 🖤🤍


GARGAƊI: masu YouTube channels, masu yin Audion littafi, kada wacce ta ɗaura mini
littafi ba da yawu na ba, domin muddin na ci karo da haka to ko wacece/ wanene zan
ɗau mummunan mataki a kai, hukuma za ta rabani da mutum, A KIYAYE.


PAGE NAKU NE
Heartbeat
Masoyiya bealkysu
Ƙanwa ecleema

PAID ₦500
500f
Shafi
Na
Shida



⭐
Subby bayan sun ɗan yi hira da baba Alhaji, fitowa suka yi palourn wajan
jidderh.

Zaune take a inda suka bar ta sai dai yanzun call take yi, duk zaunawa suka yi a
gefenta suka zagayeta, kaman masu neman gafara ko ɗaukan karatu.

Meelat ɗaukan remote tayi ta sanja tasha suna kallo, kamun ta gama wayan.
Sai da Jidderh ta gama call ɗin, ta ajiye wayan sannan ta ce, "To sarakunan
surutu sai yanzu kuke dawowa kun je kun dami stoho koh?"
Subby ta ce, "A'a fa yaya Jidderh, shi ya riƙe mu da hira, Hajiya mama ma ta zo ta
jona mu, sai da muka gudo yanzun ma, mun ce masa wajan yayarmu muka zo ba wajansa
ba."

Murmushi Jidderh tayi ta ce, "Shikkenan yayi kyau sannun ku da fitowa."

"Yaya Jidderh wai da Ya Safwan kuke waya ne?" faɗin Deeyah.

Taɓe baki Jidderh tayi ta ce, "Eh Deeyah, shine fa uban ƴan naci da jaraba, mutum
ba zai gane ba a son sa ba."

"Uhmn yaya Jidderh tun da bai gane ba shikkenan ai, nikam dan Allah ki yarda ma
gobe ya fitar da ke ɗin, sai ki kawo mana chocolate", Deeyah ta faɗa tana murmushi
dan tasan stokanan Jidderh tayi.

Jidderh hararan Deeyah tayi ta ce, "Za ku fara ko? To ku fita a idona ba inda za
je, ku rufamini asiri na mutu a gida maza su binne ni, kar garin biye muku na kashe
aurena."

Subby caraff tayi ta ce, "Ai kuwa yaya Jidderh gwanda kam kar ki je ko ina, yacce
kowa ke hanyan dawowan nan kar a samu akasi, Ya Shaameekh yayi diran mikiya."

"Yauwa Subby ke kam kin gane", faɗin Jidderh tana murmushi.

Murmushi Subby ma tayi ta ce, "Yauwa yaya Jidderhta, kinsan birthdayn mu ya zo?"

"Au ku ce mun kusa shan shagali, daman kwaɗayin birthday cake nake yi."

"Eh yaya Jidderh ya zo, cake kam har sai kin ture ma Insha Allah."

Jidderh ta ce, "Amma ina birthdayn naku sai bayan family meeting da 1 week?"

Deeyah ta ce, "Ƙwarai haka ne yayarmu, kamun lokacin nasan Ya Shaameekh ya koma
ƙasar da ya fito, kada ya mana cikas ya hana mu, tun da bai cika jimawa ba idan ya
zo, nasan zai iya komawa kamun ranan, idan ba haka ba kunsan akwai case yin
birthday ɗin nan, Ya Shaameekh kaman ba wan da ke zama a ƙasar waje ba, sam baya
son irin abubuwan nan."

Subby ta ce, "yaya Jidderh in ma bai koma ba, ai sai mu je gidan Small Uncle ayi a
can, da sauran abubuwan duka ma yi a can hankali kwance ko?"

"Caɓ amma dai Subby an gaishe ki, kin dai san bayan gidan Daddy ba inda yake son
zuwa sosai sai gidan Small uncle, tun da suna shiri da aunty Zee sosai, ke dai mu
yi addu'an Allah ya sa zuwa wannan lokacin ya koma akan time kawai", faɗin Meelat
da ke sanya haƙarƙarinta akan kujeran da take zaune.

Jidderh shiru tayi tana sauraransu duka, sai da Meelat ta gama magana sannan ta ce,
"To duk ya ishe ku nasan yaya za a yi komai ya tafi dai-dai Insha Allah, amma bana
son yayana ya koma da wuri, dan haka ku bar ma addu'an komawansa da wuri, ko yana
nan zan yi ƙoƙari komai ya tafi yan da kuke so, kar ku damu ƙannen Jidderh."

"Ai yaya Jidderh tun da muna da ke mun san komai normal ne, Allah dai ya bar mana
ke."

Da Ameen Jidderh ta amsa tana murmushi, sannan suka ci-gaba da zantawa da ƙannen
nata, shikkenan komai ya wuce ta haƙura ta kuma mance, Jidderh na ƙaunar ƙannenta
sosai, shiyasa ma ko sun mata reni bata dogon fushi da su take haƙura, halin
Jidderh yayi ko ta ina fan's.
⭐
Shaameekh zaune yake a arniyar palourn nasa tare da wani Balarabe, fiskansan nan a
haɗe gam kaman hadari ya haɗu ta gabas, wan da yanayin fiskansa ke nuni da maganan
da suke yi ba sonsa yake ba, dan idan ka ga fiskansa za ka ɗauka jira yake a ce
firit ya shaƙe Balaraben.

Balaraben ke magana cikin harshen turanci ya ce, "Sir ka taimaka mana, majinyacin
na cikin mummunan hali, mawuyacin hali na gaske yana jin jiki, wan da idan baka
taimaka ka masa wannan aikin ba to zai iya rasa rayuwarsa gaba-daya a ƙanƙanin
lokaci, ka taimaka mana Sir dan Allah", duk da turanci Balaraben yayi

8 / 15