Author : Harira Salihu Isahl Category : KDP NOVELS
tun da aka sauƙeta a mashine suka yi sallama da Kawu, sai ga wani irin
nistuwa da kwarjini sun mata ƙawanya, kan ta a ƙasa take tafiya a hankali cikin
nastuwa kaman bata son taka ƙasa, har ta shige ajin nasu, Allah ya taimaketa
tukunna Malami bai shigo ba, dan haka kujeran da take zama ta nufa ta zauna.
Ƴan ajin nasu tun shigowanta suke ta washe baki, dan kuwa sun san tun da suka
kalleta ita kaɗai to bakin a buɗe, da bakinta a kulle to tare da mahaifinta za ta
shigo ko Malama, Kulu ba ta wani yin wasan banza a makaranta ko neman reni, amma
kuma tana da daɗin sha'ani da kowa, tana fahimtan karatu sosai ba kamar ta a ajin
nasu wajan ƙoƙari.
Wata mai suna Fadila ce ta shigo ajin, direct a wajan zaman Kuluwa ta kai
idanuwanta, ganin Kuluwa sai ta washe baki, domin taji daɗin ganinta, rashin
zuwanta kwana biyu ba ƙaramin kewanta tayi ba, ƙarasowa tayi ta zauna a gefenta
tare da cewa, "Hauwa'u Ibrahim sai yau?"
Murmushi mai kyau Kuluwa ta sakar mata, tare da cewa, "Ummmn", tana gyaɗa kai
alaman eh.
Fadila ta ce, "Sannu da dawowa to, ga abubuwan da aka yi kwana biyu da baki zo ba,
sannan darasin ranan na malam lissafi ina so ki ƙara mini haske a kai."
Kuluwa cikin nistuwa ta karɓa ta shiga copynsa, tana gamawa malami ya shigo musu, a
taƙaice sai da aka fita tara sannan suka zauna tan yi wa Fadila bayanin darasin su
na ƙarshe akan lissafi, haka suka wuni a makarantan Kulu ita ce nan ita ce can, ba
kowa take yi wa magana ba, amma idan wanda take yi wa magana take tare da shi to fa
an shiga uku da surutu, dan in a aji ne sai an sa sunanta sau ba adadi a noise
marker, ba ruwanta ko malami na aji surutunta take yi, don idan bakin Kuluwa ya
buɗe to fa ba shi da full stop wato mastaya, sauƙin abun ma abin da aya shafi
karatu take yi wa surutun, dan idan ta tashi sai ta iya fara kawo abin da aka musu
daga farkon term har ƙarshensa, wai bayani take a haka Kuluwa mai craming za'a ce
mata ko screenshot.😂
⭐
A ɓangaren mutanen Arab emirates (Dubai), Shaameekh tun da suka yi wannan aiki ya
baro asibiti ko leƙa wa bai sake yi ba, kawai ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya kan
training nasa ne, wanda hakan ya sa Shaameekh ya ƙara wani ƙwanji, damastansa suka
ƙara fitowa da Six-packs nasa ma Masha Allah, idan ka kallesa ba riga ba za ka so
ɗauke idonka daga kallon surarsa ba.
Yau da take juma'a ranan da za su yi wasan ne, amma da yake sai zuwa dare za su yi
to tun da asuba Shaameekh ya shige wajan mosta jikinsa, sanye da short-nicker
kyakkyawan ƙirjinsa a waje, Punching bag ya ɓata lokaci sosai wajan bugunsa, sannan
ya koma kan kan sauran, sai haɗa zufa kawai yake yi, domin lokaci ya ɗauka mai
stayin gaske yana aiki guda, har sai azahar sannan ya sararawa kansa ya fice a
wajan cikin takunsa na ƙasaita, kai ka ce ba gama wahalar da kansa yayi ba, haka ya
wuce ya kwankwaɗa ruwa mai sanyi a fridge nasa sannan ya shige ɗakinsa.
Toilet ya shige a haka, tare da sakar wa kan sa ruwan sanyi yana lumshe ido, bai da
damuwan da ya wuce anjima tayi su yi su gama su huta, ya gama packaging na kayansa
da komai, yau ɗin nan yake son barin Dubai idan Allah ya amince.
Sai da ya ɓata lokaci mai stayin gaske wajan wanka, ya haɗa da na juma'a da alwala
duka, sannan ya sanya rigan wankansa ya fito, hannunsa riƙe da ƙaramin towel yana
goge jikinsa, haka ya wuce gaban Haɗaɗɗen walldrop nasa ya nemo 3quater da t-shirt
bodyhug ya saka(Shaameekh zuwa juma'a da guntun wando 🤣), ya kuma feshe jikinsa da
turare sannan ya ɗau key na motansa da wayoyinsa ya fice a gidan, ya nufi
masallaci.
Nafilansa yayi raka'a biyu kamun aka shiga salla, sannan da aka idar ma yayi raka'a
huɗu, domin sallahn juma'a duk da ita ma nafilance, amma ana haɗa ta da nafilfulun
da ake yi wa sallahn azahar, sannan an fi son mutum yayi biyu a farko huɗu bayan
sallahn juma'an, saboda yin biyu bayan sallahn juma'a kan saka wasu tunanin ko ka
cike juma'a ta koma huɗu ne(wato azahar kenan ba juma'a ba), idan huɗu kayi farko
ya fi kyautuwa biyun ka bar su ka yi a gida maimakon a masallacin.
Shaameeƙh ya ɗau tsawon lokaci yana addu'oinsa na neman alkairi da sa'a, game da
wasan da za su yi anjima, saɓanin wasunmu da ko exam's za su yi sai an haɗa da
tsafi, ƙwallo tsafi, dambe stafi, aure tsafi, kasuwanci stafi etc, Allah kyauta
mana wannan zamani.
Ganin har la'asar ta kusa, bai wani bar haraban masallacin ba, kawai ya zauna ya
ci-gaba da addu'oinsa, har lokacin sallahn la'asar ɗin tayi, sannan yayi sallahn ya
fito ya yi wa motansa key.
Wajan shaƙwata hakan nan mai kyau Shaameeƙh ya nufa, yana parking motansa ya fito
tare da zura hannunsa a aljihu yana taku mai kyau, ta nufi wajan zaman nasu fiskan
nan sam ba fara'a.
Su biyu ya samu zaune a haɗaɗɗen table nasu, Manseer na hango sa ya fara dariya
kaman ba lau ba, ɗaya gayen da ke zaune a gefensa ne ya ɗan ja guntun staki ya ce,
"Mai zaman banza kana da buƙatar a duba maka lafiyan kan ka akan wannan dariyan."
Manseer sai da ya stagaita dariyan sannan ya ce, "Muhseen ba za ka fahimci me nake
yi wa dariya ba, dubi fa wannan ƙaton gardin gauron sai ya wani ce ba ya buƙatan
aure yanzu, bayan a yanzu haka da ba'a kan gajimare yake ba ma Batman nasa a murɗe
yake stam, kai amma na tausayawa matayenku, ai duk mai auran ɗan dambe aiki ya
ganta, dan wannan mosta jikin naku, ba iya damastanku ke ƙaruwa ba har da Batman
naku, wayyo kukam kyawunta ku samu mata masu halittan zurfi da ɗan buɗaɗɗen Garage,
kuka haɗu da mai matsatstsan Garage kam gaskiya spanner's nata za su ji a jikinsu,
dan engine's na ƴan dambe daban ne", Manseer ya ƙarisa maganan dai-dai shaameeƙh ya
iso wajan nasu.
Shaameeƙh ciki-ciki ya musu sallama, sannan ya samu waje ya zauna, da yake ya ji
ƙarishen maganan Manseer, hararansa yayi tare da cewa, "Ɗan iska dai bai ji daɗi ba
a rayuwansa, a ce mutum bai da magana sai ta banza, ɗan iskan ma'aikacin asibiti
kawai."
Manseer yana dariya ya ce, "Ƴan iskan fa suna da yawa, tun da kai ɗin ma aikin
asibitin kana yin sa."
Muhseen hannu ya miƙa wa Shaameekh suka gaisa, sannan ya ce, "Man ka ƙyale wannan
mai zaman banzan bai da aikin yi ne, mu da muke da wasa zuwa jimawa ai munsan da
abu a gabanmu."
Kamun Shaameeƙh ya buɗe baki tuni Manseer ya ce, "Ni kuma na gaban nawa kai ka sace
su? Ko ka fara shafi-mulera ne bamu sani ba?(masu kwashewa mutane al'auransu).
Shaameeƙh dafe kai yayi ya ce, "Allah ya shiryaka."
"Ko wani ɗan kutuma-nege na buƙatan shiriya, musamman dai kai wanda wai baya son
zancen aure", faɗin Manseer yana kai abin sha bakinsa.
Muhseen murmushi yayi ya ce, "Mai zaman banza ka je mun sallameka."
"Ƙafata ƙafarku, sai za ku shiga da'ira(filin wasa), sannan nayi gefe dan ba ta
wajan na biyo ba, Allah rufa mini asiri da yin dambe, na je wataran a bugar da ni a
bar matata da heartbreak babu harkan hawa gajimare, dan na tabbata bugu guda aka
mini a da'irar wasanku sai lahira ko dogon suma, abin da bakwa zama haka kawai,
daga masu stafi sai asiri, sai dodonni ƙulle-ƙullenku."
Muhseen murmushi yayi ya ce, "Mastalan masu zaman banza kenan, ka ga mu za mu iya
jaa da masu stafin dan Allah muka kama kuma ya isar mana."
Manseer da Muhseen sai surutunsu suke Shaameekh na jin su bai ce komai ba, sai ma
ordern abu dai-dai buƙatansa da yayi, abinci da zai ƙara masa energy a jiki ba zai
damesa zuwa anjima ba.
Sai da ya cika cikinsa sannan ya duba agogo, ganin lokaci ya ja ya miƙe tare da
cewa, "Muhseen za mu yi maganan a can, yanzu lokaci ya ƙarato akwai abin da zan
ɗauka, after isha'i sai mu haɗe."
Manseer ya ce, "Ɗan ƙwaya tun yanzun za ka sha ƙwayar taka dan ta jiƙa, a dai dinga
jin storon Allah za'a mutu."
Shaameeƙh ko kallon Manseer bai yi ba ya bar wajan.
Muhseen murmushi yayi ya ce, "Kai fa ba ka da dama Manseer, dan kasan kai kuran
ƙarfen Man ne shiyasa kake masa haka, anyway tare na gan ku, nima ka ga tafiya
akwai abin da ban ƙarisa ba."
"Ku dai dinga jin storon Allah wallahi, ban da shan ƙwaya ko tsaface-tsaface saboda
abin duniya, abin da ma hanya ce mai sauƙi da za'a muku 1 blow 7 die sai dai ku ji
walakiri na faɗin Man rabbuka?"
Dariya sosai Muhseen yayi ya ce, "To wa ya ce maka duka an taru an zama ɗaya ne?
Dan wasu nayi dole wasu na yi ne, a komai a ko ina akwai na gari akwai na banza, mu
Allah muka kama, kuma kai ma ka dinga faɗa wa kanka gaskiya ka rage harkan mata."
Manseer ya ce, "Mu da mata ai mutu ka raba, Batman ba haƙuri dole sai an kai engine
zuwa ga Garage."
"Allah ya shiryeka mai zaman banza", faɗin Muhseen yana murmushi.
Manseer yana dariya ya ce, "Ameen masu duka ɗaya mutuwa."
Muhseen tare da Manseer suka miƙe, Manseer ne ya biya kuɗin komai har da abinda
Shaameeƙh ya ci, sannan shi da Muhseen kowa ya shige motansa ya kama hanyarsa.
Shaameeƙh yana barin wajansu ya wuce gidansa direct, ya jawo system nasa yana
ayyukansa, sai Magrib ya tashi yayi sallah, bai tashi a wajan ba sai isha'i, ya
jima yana addu'a sosai, sannan ya miƙe ya shige wanka, yana fitowa cikin isa ya
shirya hankali kwance, yanzun ma 3quater ya saka da armless dan sai ya je wajan
wasan nasu, zai sanja kaya zuwa na shiga filin wasa.
Shaameeƙh sai wajan ƙarfe goma ya bar gidan, amma Manseer ne ya zo ya ɗauke sa dan
ya haɗa kayansa na tafiya Nigeria, daga can Manseer zai kai sa airport ba zai komo
gidan ba, ya gama sallama da mai gadinsa kmda mai aikinsa.
Manseer na driving yana faɗin, "Gaskiya Man kana son wahalar da kan ka sosai, daga
ka gama wannan banzan wasan sai airport ba za ka bari ko hutawa ka yi zuwa gobe ba,
sai ka ce abin barin duniya, ko a maste kake ayi maganan auren a kawo maka matar
ce?"
Shaameeƙh guntun murmushi yayi wanda yayi matuƙar fito da kyawunsa, cikin muryansa
mai daɗin sauraro ya ce, "A mugun hannu ma nake, kai ƙarshenta ma a ƙafa nake, kai
baka ganin idan ba wasa za muyi ba bana son yawan mosta jiki sosai-sosai, saboda
saka Manhood na yake ya dinga harbawa neman taimakon gaggawa."
Wani irin dariya Manseer ya saka tare da dukan stairy, kaman zai yasar da su a
hanya ya ce, "Haba Man ai ni nasan duk karya ce kake, ɗazu yanda na ganka nasan ai
jiki ya mostu da kyau, to wallahi kamun ka fara tafiya kana ƙoƙarin danne abu a
stakiyan ƙafa gwanda tun wuri ka yi aure."
Guntun staki Shaameekh ya ja ya ce, "ban shirya aure ba yanzu, ban da lokacin
mace", dai-dai sun iso filin da za'a yi taron.
Manseer yana parking ya ce, "Ka kusa daina fita kenan, domin idan ka ƙuresa ya
harba ba komawa sai ya ji sa a sararin gajimare."
Shaameeƙh tattara komai da zai buƙata yayi ya fice a motan yana faɗin...
***
Wannan SHAFI na kuɗi ne, na ba da shi bonus ne saboda murnan zagayowan ranan auren
Uwar Batoorl da Abou Batoorl, masu daraja habibtiees a mana addu'a da bakunanku
masu albarka.
Kuɗin littafi ₦500 a sa a wannan account da ke a ƙasa👇
9161720046
Harira salihu isah
Opay
&
2220553988
Harira salihu isah
Uba
Shedar biya ta wannan layi 07015870735.
Mutanen Nijar ku ma ku yiwa wannan layi magana dan yin payment naku 500f.
+227 88 73 81 26
Sai kuma a turo shedar biya ta wannan layi
07015870735.
# Hareeyh
# 09161720046
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚