Author : Harira Salihu Isahl Category : KDP NOVELS
lalura ba da yanzu haka Kuluwa na babban makaranta
a birni, ko kuwa tana gidan mijinta, dan haka bana son irin abubuwan nan na faruwa,
ki daina barinta haka, kuma ki daina haɗa mini yarinya da aljanu, mu bi ta yacce
take Insha Allah komai zai wuce, za ta samu lafiya kuma."
"Insha Allah ba za'a ƙara ba Kawun Kulu, Allah kuma ya bata lafiya."
"Ameen Hajjona ko ke fa", Kawu ya faɗa tare da yalwata murmushi a fiskansa, dan sai
lokacin ya sake mata fiska, saboda Kawu sosai yake ƙaunar Kulu, shi ne ya
shagwaɓata ya sankaltata ya sangartata, akan Kulu ba irin kuɗin da ba zai iya
kashewa ba, kuma akan Kulu yana iya ɓatawa da kowa ba ruwansa da ya kake a wajansa,
sosai yake ƙaunarta wanda ba dan rashin lafiyarta ba da abin ya fi haka kuma, ya ci
alwashin muddin ta samu lafiya da ransa da lafiyansa, to ko dako sai yayi tayi
karatu, kuma aure ba zai mata na wuri ba sai lokaci yayi, tun ana masa magana akan
hakan har aka gaji aka ƙyalesa.
Sai da Kawu ya gama sannan suka fito da Hajjo, zama yayi a kujeran da Kulu ke
zaune, ya masto da ita jikinsa, cikin soyayya da tausayi ya ce, "Kuluwan Kawu na
kawo miki starabanki kuma kin ƙi kulani tun dawowana."
A hankali ta lumshe idanuwanta tare da mosta laɓɓanta ta ce, "Na go de", da
zazzaƙar muryanta, na ce dole Kulu tayi rowan yin magana.
Hajjo murmushi tayi ta ce, "Shikkenan an gama maganan yau kuma, sai na wani lokaci
idan mai duka ya kai mu, tun da ba mai ɓacuwa bane a ajiye mata."
Kawu ya jinjina kai tare da shafa kan ta ya ce, "Allah ya miki albarka ya kuma baki
lafiya Kuluwan Kawu", ya ƙarishe maganan tare da kwantar da ita a jikinsa, yana
faɗin, "Ga shi ita ta san kan abun kallon bamu sani ba balle a kunna mata ko karatu
ne."
"Sai ka ci abinci ka mata na kan ka dan nasan bacci za ta koma ba jimawa indai Kulu
ce", Hajjo ta faɗa tare da miƙewa ta fice, madafi taje ta ɗauko abincin Kawu ta
kawo masa ta ijiye a gabansa a kan tebur, zuba masa komai tayi, ya wanke hannu da
bismillah ya fara cin tuwon da yaji namomi, loma ɗaya ya kai bakin Kulu amma sai ta
ƙara yin gum da baki taƙi buɗewa, dan dole Kawu ya ƙyaleta ya ci ya cika cikinsa,
ya gama Hajjo ta tattare, sannan ya kwantar da kan Kulu a cinyarsa, yana karanto
mata surorin da ya haddace yana shafa kan ta har ba jimawa bacci yayi gaba da ita,
sannan ya gyara mata kwanciya a kujeran ya miƙe ya fice, dan yin sallah ya kuma yin
sauran shungullolinsa.
Hajjo kuma sallah tayi sannan ta samu waje ta kwanta ita ma, dan huce gajiya tun da
kayan kallon Kulu ce ta iya kunna su, kuma babu abokin hira dole sai dai tayi
baccin.
Su ne basu farka ba sai da lokaci ya ja sosai, Hajjo kama hannun Kulu tayi suka je
banɗaki ta gama suka fito, alwala ta mata suka koma ciki ta saka mata hijabi ta
zaunar da ita, sai da yayi kusan mintuna goma sannan Hajjo ta zo ta ɗaga ta.
Har dare tayi Kulu haka ta wuni kaman mutum-mutumi, komai sai Hajjo ta mata ko
Kawu, dan ko da Kawu ya dawo kama hannunta yayi suka tafi sashin dabbobi, sai nuna
mata yake ya ce wannan nata ne, wannan na jikokinsa da za ta haifa masa ne, shi
kaɗai idan yayi magana sai yayi dariya domin yasan da bakinta na buɗe da yanzu tana
amsawa, har sai da Magrib yayi sannan ya mayarta cikin gida ya wuce masallaci, bai
dawo ba sai da yayi sallahn isha'i.
Abincin dare suka ci dukkansu, amma Kulu kam Kawu ne ya haɗa shayi mai kauri da
kansa ya dinga bata, da ƙyar ta yarda ta buɗe baki tana amsa, a hakan ma wani na
zuba a jikinta, kaɗan ke shigewa maƙoshinta, ko Hajjo tayi magana sai Kawu ya ce
gwanda hakan, da a barta ba komai a cikinta gwanda ko kaɗan ne ta taɓa, sai da suka
gama sannan ya koma ɓarin dabbobinsa, Hajjo kuma ta wasta mata ruwa a nan cikin
gida da yake waje yayi duhu, suka gama ta saka mata kayanta mara nauyi riga da
wando mai kyau, wan da yayi matuƙar amsan jikinta, don kuwa Kulu ba dai kayaki ba,
Kawu jimeta yake shiga ya sayo mata kayakin ƴan gayu, da wuya ka ganta da riga da
zani, balle kuma a kai ga ta saka ɗinkin ƙauyen nasu.
Sai da Kawu ya kai ta ɗakinta ya mata addu'a, sannan ya ja mata ƙofa ya fito ya
koma ɗakinsu, kaman kullum sai da yayi sallahn nafila sannan ya kwanta gefen
matarsa cikin damuwa, Hajjo ita ta dinga rarrashinsa tana basa haƙuri, faɗi take,
"Kawun Kulu yanzu idan baka cire wannan damuwa a ran ka ba mai kake so ya sameka?
Idan fa wani abun ya sameka Kulu ka sanya cikin mastalan rayuwa, abu guda shekara
da shekaru, yanzu shekara goma sha biyu ake nema kullum abu guda, dan Allah ka
lallaɓa lafiyanka ko dan yarinyarmu."
Kawu ajiyan zuciya ya sauƙe tare da cewa, "Hajjo dole abin ya dameni, ina haƙuri
ina kawar da kai kuma na ɗau ƙaddara, amma jama'a basa gajiya da ka-ce-na-ce, amma
ba komai Insha Allah watarana sai labari, Allah ya bai wa Kuluwa lafiya ya kuma
bata miji nagari."
"Ameen Kawun Kulu", Hajjo ta faɗa tana murmushi, daganan suka kwanta bacci.
Kulu a ɓangarenta bacci ta kasa yi, domin haka abin yake mata idan dare yayi to
bata iya runstawa, shiyasa daga gari ya waye to duk ƙarancin mintunan da ta kwanta
sai tayi bacci, dan biyan bashin na daren da bata yi ba, haka idanuwanta biyu har
sai da asuba ya kawo kai sannan bacci yayi gaba da ita, ba jimawa kuma ana ƙiran
sallah Kawu ya shigo ya tayar da ita, Hajjo ta kai ta banɗaki da alwala da komai,
gari na haske kowa ya kama ayyukansa, Kawu ya shirya ya tafi kasuwa bayan ya karya
ya kuma duba dabbobinsa, Kulu kuma bacci ta dinga yi hankalinta kwance.
Kwana biyu masu kyau aka kwashe a irin wannan yanayi, tun magana da tayi rannan sau
ɗaya ta ce ta gode, to bata kuma cewa komai ba, kuma daman ƙa'ida ne idan tayi
magana ɗaya shikkenan, kuma komai sai Hajjo sun yi wa Kulu, yan da aka ajiyeta haka
za'a same ta a zaune a wajan, kuma Kawu alƙawari ne kullum ya je kasuwa zai kawo
mata staraba, haka za'a ta ajiyewa wai ba mai ɓacuwa ba ne, dan bata cin komai, ko
shayin ma wataran bata buɗe baki sai anci sa'a yake karɓa, rabi da kwata na zuba
bai wuce kwata ke shiga maƙoshinta ba.
A kwana na uku kuwa tun cikin wannan dare Kulu ta sha baccinta lumui har da juyi,
kaman wacce ke shirin faɗowa daga ƙaramin gadon nata, asuba nayi kuma akan kunnenta
dan ana ƙiran farko ta wara dara-daran idanuwanta a hankali, tare da sakin wani
irin murmushi mai ƙayatarwa, duk da akwai duhun asuba amma hakan ba zai hanaka
hango kyawawan fararen haƙoranta ba, wan da ke dandashe da haɗaɗɗen wushiryanta, ga
dimple nata mai shegen kyau, wanda a duk tsawon kwanki ukun nan ko alamansu baka
gani, amma da mamaki ga Kulu da murmushi yau ko me dalili sai Allah.
***
Ummiy tana shiga ɗakinta ta kwanta dan ta huta, sai dai abin da tayi tunanin shi ya
faru, dan ƙiran Daddy ne ya shigo wayannata, sai da ya kusa stinkewa ta ɗauka tare
da yin sallama da tattausar muryanta.
Daddy ajiyan zuciya ya sauƙe a ɓangarensa tare da cewa, "Allah ya ja kwanan Uwar
gidan Shu'aibu, Ummiyn Shaameekh da baby."
Ummiy a taƙaice ta ce, "Tare da kai", sannan ta gaishesa ya amsa.
"Lafiya kuwa naji muryan Ummiyn Shaameekh cikin fushi, wani laifi nayi na bada
haƙuri", Daddy ya faɗa cikin zolaya.
Ummiy shiru ta masa bata ce komai ba, sai da ya dage da tambaya sannan ta ce, "Ba
ka kyautawa Daddyn Shaameekh, kai fa kasan da maganan meeting ɗin nan duk bayan
wata uku, amma kullum sai hanya-hanya kake baka son zuwa, kuma hakan ba daɗi yake
yiwa Baba Alhaji ba sam, tun da dai kasan anriga da an zama ɗaya, su Yaya Sulaiman
suna magana har sun gaji sun yi shiru."
Daddy da yake yasan ba shi da gaskiya a wannan magana, haƙuri ya dinga bai wa
Ummiy, yana mai tabbatar mata yanzu ma wani shungulla ne ya riƙe sa, idan ba haka
ba ya so musu ba zata, sai dai kawai su gansa a gida, da ƙyar da lallami ya shawo
kan Ummiy ta haƙura, amma da tabbacin Insha Allah wani jiƙon da shi za'a yi, in dai
da rai da kuma lafiya, sannan Ummiy ta saki ranta, yana murmushi ya ce, "To yanzu
goben ne za ku tafi ko kuwa jibi?"
"Insha Allah jibi za mu wuce, ga baby ma da rigimarta wai ita ba za'a je a mota ba,
kuma naga duk abin ɗaya ne, inma ba'a je a motan ba, dole jirgin a Maiduguri zai
ajiye mu, sannan mu bi mota zuwa Yobe", faɗin Ummiy cikin jajanta nacin baby da son
jirgi.
Dariya Daddy yayi nasu na manya sannan ya ce, "Ayi haƙuri ayi wa uwata yacce take
so, inaga dole mu nemi private jet ko dan baby."
"Amman kam da ya kamata."
"To Allah ya tsare hanya ya kai ku lafiya, sai kun isa za ki haɗa ni da su Baba da
Mama na basu haƙuri da bakina, kamun yarona ya isa shi ma ya taya ni basu haƙuri",
Daddy ya faɗa yana murmushi.
Ummiy ma murmushi tayi ta ce, "Insha Allah zan haɗa ku, shi Shaameekh ɗin ma ai
aiki ya same sa a can Dubai ɗin, zai duba wani mara lafiya kuma wannan aikin nasu
na wasa da rai ɗin za su yi shi."
Dariya Daddy yayi sosai jin Ummiy ta ce wai dambe wasa da rai ne, sai da ya
stagaita sannan ya ce, "To Allah taimaka ya basu sa'a, da duba mara lafiyan da
wasan da yake da shi ɗin duka Allah sa yayi a sa'a."
"Ameen dan isar Annabi SAW", Ummiy ta faɗa, sannan suka ci-gaba da hiransu na mata
da miji, Daddy sai zolayanta yake yayi kewanta, Ummiy kuwa ta ce ai zance yake so
wai an ce da gauro ya iyali, da yayi kewanta ai da ya dawo, a haka dai har suka yi
sallama da fara'a, kuma cike da shauƙin juna, musamman Daddy da yake matuƙar kewan
matar tasa da ƴar sa gudan jininsa.
Ummiy tana kashe waya ta jawo ayyukanta ta hau yi, sai da aka yi sallahn Magrib
sannan ta tashi tayi sallah, bata bar kan darduma ba sai da tayi isha'i, tana
idarwa ta fito palourn, suka ci tuwon dare da baby sannan ta koma ɗakinta dan bacci
take son yi da wuri yau, sakamakon washe-gari juma'a kuma yana da kyau ga dukkan
ɗan Adam, ko da kuwa a sauran darare baya samun tashuwa yayi nafila, to wannan dare
ta alhamis wacce washe-garinta juma'a ne, ana son mutum ya tashi ko raka'a biyu ne
yayi, yana mai yawaita salati ga Annabi SAW, sannan ya kai buƙatunsa wajan
mahaliccinsa, musamman yanzu da duniya sai dai mu ce Allah ya sa mu cika da Imani,
to mutum ya yawaita lazumtar YA RABBI INNAKA AFUWWU TU HIBBUL AFWA FA AFU'ANNA,
domin ruwaya ce ta hadisi guda daga Nana A'isha AS, ta tambayi Manzon Allah SAW
idan Allah ya ƙaddara mata ganin lailatul-ƙadr, wani abu za ta yawaita faɗa, sai
Annabi stira da amincin Allah su tabbata a gare sa ya faɗa mata wannan addu'a,
wanda kuma ba ana nufin iya daran lailatul-ƙadr ba, a stawon rayuwanmu ake so mu
yawaita lazumtar wannan addu'a, Allah Ubangiji ya yafe mu ya mana afuwa, Allah sa
mu gama da duniya lafiya, wadanda suka riganye mu tafiya kuma Allah kai musu rahama
da haske makwancinsu.
Wannan dare haka Ummiy ta raya sa yacce addini ya so, ana ƙiran farko ta je ta
tayar da baby, ita ma tayi nata nafilan, ko da suka yi sallahn asuba duk ba wan da
ya tashi sai da ya karanta Suratul-Kahfi da kuma salatin Annabi SAW.
Baby taya mai aikinsu Talatu tayi suka staftace gidan saƙo da lungu, wanda daman
duk ranan juma'a hakan suke yi, ba su suka kammala ayyukan ba sai wajan ƙarfe goma,
kuma lokacin Ummiy ta tashi bacci, sannnan suka karya, baby ta wuce ta wasta ruwa
ta shirya tafiya ƙunshi dan basu da class sai yamma, a yau za ta yi ƙunshi da
gyaran kai, dan kisto kam sai sun je Yobe jidderh za ta mata.
Ummiy shirin tafiya asibiti tayi, ta fito suka fice tare da baby, tana mai jaddada
mata kada ta yarda bata je makaranta ba, baby ta amsa suka sauƙeta a inda za ta yi
abubuwan, driver ya wuce da Ummiy asibiti.
Baby ƙiran ƙawarta Deejerh tayi ta zo ta ɗauke ta suka tafi gidan ƙunshi, ba su
wani jima a can ba aka gama mata mai shegen kyau, sannan suka wuce saloon aka wanke
mata kai, sai da ta ƙira Ummiy ta sanar mata ta amince, sannan suka wuce gidan su
batoorl, a can suka baje kolin hiransu, baby kam har da bacci tayi, sai da yamma
tayi lokacin class sannan suka tashe ta, duk suka shirya suka yi school, class ɗin
bai wani jima ba aka tashi, dai-dai lokacin Ummiy ma za ta koma gida, suka biyo da
driver suka ɗauki baby, Deejerh da Batoorl suka gaishe da Ummiy ta amsa tana
fara'a, tare da musu sannu da karatu.
Deejerh ta ce, "Ummiy a kawo mana tsaraban Yobe."
Murmushi Ummiy tayi ta ce, "Insha Allah khadija, ku gaishe da gida ko, Allah muku
albarka."
Suka haɗa baki wajan amsawa da Ameen, da kuma yi wa su Ummiy addu'an a dawo lafiya,
sannan driver ya ja mota suka tafi, Deejerh ta aje Batoorl a gidansu, ita ma ta
wuce nasu gidan..
Kada ku manta daga wannan sai last free page, garaɓasa ta ƙare daga wannan page
ɗin, kina son a cigaba da tafiya da ke to maza hanzarta ki biya.
***
MASU DARAJA HABIBTIEES NA UWAR BATOORL AKWAI GARAƁASA GUDA, A YANZU KAMUN MU
KAMMALA FREE PAGE'S TO KUƊIN LITTAFI DAI ₦300/250f NE, IDAN MUN KAMMALA KUWA
₦500/500f YAKE INSHA ALLAH.
9161720046
Harira salihu isah
Opay
&
2220553988
Harira salihu isah
Uba
Shedar biya ta wannan layi 07015870735.
Mutanen Nijar ku ma ku yiwa wannan layi magana dan yin payment naku 500f.
+227 88 73 81 26
Sai kuma a turo shedar biya ta wannan layi
07015870735.
# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚, SHAAMEEKH ,
B̶̶O̶O̶K1
Officially
𝘽𝙮
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسوللهSAW 🖤🤍
GARGAƊI: masu YouTube channels, masu yin Audion littafi, kada wacce ta ɗaura mini
littafi ba da yawu na ba, domin muddin na ci karo da haka to ko wacece/ wanene zan
ɗau mummunan mataki a kai, hukuma za ta rabani da mutum, A KIYAYE.
Wannan PAGE naku ne masoya alƙalamin Uwar batoorl gaba ɗaya, alkairin Allah ya kai
muku a duk inda kuke a faɗin duniya, Uwar batoorl na ƙamnarku Masu daraja
habibtiees.
PAID #500
500f
Shafi
Na
Tara.
⭐
A hankali drivern ke tuƙa su Ummiy, sakamakon Ummiy bata son ana gudu a kan hanya,
baby da ke zaune a gidan baya a gefen Ummiy, dubanta ta ta kai kan Ummiy tana
murmushi ta ce, "Ummiy gobe ai ba da wuri za mu tafi ba tun da flight za mu bi ko?"
Ummiy ta ce, "Idan kika tsaya baccinkin nan za ki tashi a ce miki na jima da isa
Yobe, dan haka idan za ki gama komai da wuri ki gama."
Baby shiru kawai tayi tare da kwanciya a jikin Ummiy har suka isa, driver na
parking Ummiy ta fito, ita kuma baby ta ɗauka wa Ummiy jakanta da labcoat suka
shige cikin gidan a tare, Ummiy tayi ɗakinta ita ma baby tana zuwa ta ajiye wa
Ummiy labcoat nata ta wuce nata ɗakin, sai da ta wasta ruwa sannan ta shiga haɗa
kayan da za ta tafi da su, a daren ranan duk suka gama kimstawa, kuma da wuri suka
kwanta.
Washe-gari asabar da safe bayan sun karya sun yi komai da komai, zuwa ƙarfe takwas
suka fito, sai da suka yi waya da Shaameekh da kuma Daddy sannan suka fice a gidan,
baby sai washe baki take kaman wacce bata taɓa hawa jirgi ba, ko kuma bata taɓa
zuwa Yoben ba.
Driver ne ya kai su airport, jirginsu ya ɗaga ƙarfe tara na safe sai Maiduguri, a
can suka sauƙa, da yake Ummiy tayi magana da Daddy (yayanta baban Jidderh), to sun
samu an turo musu driver daga gida, tun da wuri ma yake jiran isowan su, suna sauƙa
ya saka kayakinsu a mota suka ɗauki hanyan Yobe.
Sun baro Yola ƙarfe tara sun iso Maiduguri ƙarfe goma sha ɗaya saura na safe, sun
ɗau hanyan Yobe a cikin a wanni huɗu suka isa, da yake drivern gida ne to a sannu
suke tafiya, zuwa ƙarfe huɗu na yamma da yardan Allah Ummiy suna cikin gidan alhaji
baba.
Driver na gama parking baby ta ɓalle murfin mota ta fito, da gudunta tayi cikin
gidan tana washe baki tana faɗin, "Yaya jidderh oyoyo ina kike ga babynki."
Hajiya Mama da ke zaune a palourn ita da Alhaji baba, haɗe fiska tayi tana faɗin,
"Fauziya sallaman da aka koya miki kenan?"
Tura baki baby tayi ya ce, "Stohuwa ina yaya Jidderh."
"Ta tafi koyan sallama dan ƙaniyarki", Ummiy da shigowarta kenan ta faɗa haka, tare
da yin sallama.
Amsa sallaman Ummiy su Hajiya Mama suka yi, Alhaji baba na faɗin, "ƙyalesu amaryata
ƴar Fulani, zo abinki na faɗa miki ina Hauwa'u take", ya faɗa yana sakar wa baby
murmushi.
Hajiya Mama taɓe baki tayi ta ce, "Da ka barta ai rashin sallaman nata ya kulata,
Faɗimatu sannunku da hanya ko, sannu da gajiya."
Ummiy na murmushi ta amsa tare da samun waje ta zauna tana faɗin, "Barka da hutawa
Mama da Baba fatan mun same ku lafiya?"
"Lafiya alhamdulillah Faɗimatu, ki bari ku huta tukunna za mu gaisa ai, ga amaryata
daga zuwa ta shiga sumbatun neman Hauwa'un da bata jima da barin gidan nan ba",
faɗin Alhaji baba yana murmushi.
Hajiya Mama ta ce, "Sai ta bi takwaran gidan ubanta ai tana can ita ma da rashin
jin ta, halan Faɗimatu ke ce baki koya wa ƴar ki sallama ba."
Ummiy tana murmushi ta ce, "Haram Mama, rashin ji ne kawai."
"Ko kuma ɗaukin son ganin ƴan uwanta ba, ni ai nafi