Author : Harira Salihu Isahl Category : KDP NOVELS
KAMMALA KUWA #500 YAKE
INSHA ALLAH.
9161720046
Harira salihu isah
Opay
&
2220553988
Harira salihu isah
Uba
Shedar biya ta wannan layi 07015870735.
Mutanen Nijar ku ma ku yiwa wannan layi magana dan yin payment naku 07015870735.
# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
SHAAMEEKH
B̶̶O̶O̶K1
Officially
𝘽𝙮
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسوللهSAW 🖤🤍
GARGAƊI: masu YouTube channels, masu yin Audion littafi, kada wacce ta ɗaura mini
littafi ba da yawu na ba, domin muddin na ci karo da haka to ko wacece/ wanene zan
ɗau mummunan mataki a kai, hukuma za ta rabani da mutum, A KIYAYE.
̶PAGE NAKU NE
Mom Sani mai gaskiyata
Reemah
Maman Abdalla
PAID #500
Shafi
Na
Biyar.
⭐
Ɓangaren su Big Dad kuwa haka suka kwana akan magana ɗaya dan Hajiya Kubura(Mom),
akwai son mita a ta yanyana magana guda.
Washe-gari big Dad a ƙurarren lokaci ya tashi, dan haka cikin gaggawa ya shige
wanka, yana fitowa kuma ya samu Mom ta farka da magana tun na jiya, da mamaki yake
kallonta na irin halinta na riƙe magana, amma sai ya basar ta hanyar cewa, "Hajiya
ba na ce miki kar ki damu da wannan magana ba, daughter za ta dawo Insha Allah, mu
mata addu'an dawowa lafiya kawai, tun da dai kowa yasan karatu ta tafi bawai wani
abun ba."
Mom cewa tayi, "To shikkenan Alhaji Allah ya dawo da ita lafiya, amma dai kasan
halin Sofiya idan ba da rarrashi ba kam, to ba lallai ta dawo yau ba, kuma ni bana
son surutun su Hajiya Mama, yanzu sai a ta cewa yarinyata tayi kaza tayi kaza."
"Ke kam na ce miki kar ki damu, yanzu dai a taso a taya ni shiryawa na samu na fita
da wuri, banson na kuma yin wani lattin."
"To Alhaji", Mom ta faɗa tare da miƙewa ta fara taya mijin nata shiryawa, suna yi
suna hira har ya gama shiryawa.
Agogon da ke maƙale s hannunsa ya duba, ganin lokaci kawai ɗaukan abin da zai ɗauka
yayi ya ce, "Hajiya ina jin ba zan staya karyawa ba dan na makara, mu je kawai ki
rakani ko."
Mom ta ce, "Haba Alhaji ban da dai ka fita ba ka karya ba kam, ai ko da ruwan zafi
ne ya kamata ka sha", ta faɗa tana ficewa a ɗakanin tare da kwalawa mai aikinta
ƙira.
Mai aikin na zuwa da durƙusa tare da cewa, "Barka da safiya Hajiya."
"Ba ƙiranki nayi ki gaishe ni ba, maza kiyi sauri ki haɗa wa Alhaji tea", faɗin Mom
fiskan nan ba rahama.
"To Hajiya", ƴar aikin ta faɗa tana tashuwa, tayi dinning dan yin abin da aka saka
ta yi.
Alhaji bayan ya fito a ɗakin, tare suka yi dinning area da Mom, ruwan zafin da aka
haɗa masa ta ɗauka ta miƙa masa, shi kuma ya amsa a haka amma sama-sama ya kurɓa
kawai, ya tashi tare da ƙara duba agogonsa yana faɗin, "Mu je ko Hajiya."
Murmushi Mom tayi tare da miƙewa ta bi bayansa dan yayi gaba tuni, har suka isa
wajan motansa driver ya buɗe masa ya shiga, jakansa ta miƙa masa ta ce, "Alhaji
Allah ya tsare hanya a dawo lafiya."
Da Ameen ya amsa, driver ya ja mota suka fice a gidan, ita kuma ta juya ta koma
cikin gidan.
***
A ɓangaren gidan Alhaji Isma'il kuwa mahaifin jidderh, wan da suke ƙira da Daddy,
zaune yake a kan haɗaɗɗen gadonsa da system a gabansa yana aikinsa, Mummy kuma na
zaune daga gefe a gaban dressing mirror tayi wanka ta gyara fiskanta tana ɗaura
ɗankwali, sai da ta kammala ta shafa turaruka sannan ta juyo cikin soyayya da
biyayya ta ce, "Abu Yusuf a ƙyale aikin haka nan mu karya."
Daddy dama yana danna system ɗin ne kawai amma rabin hankalinsa, na kan matarsa
sanyin idaniyarsa uwar ƴaƴansa, tun da ta juyo garesa kuma ya bar danna system ɗin,
ya fara sakar mata murmushi har ta gama zancenta, sannan ya numfasa tare da cewa,
"Maman Yusuf anya za ki bari ayi amaryan nan kuwa da irin wannan kwalliya, wa zai
ce ke kika haifa mini manyan budurwaye jidderh da Sadeeya, ga kuma Yusuf."
Murmushi Mummy ta sakar masa tare da cewa, "Idan Allah ya nufa ai yi ya zama dole,
addu'ata dai Allah ya bamu tagari wacce za mu zauna lafiya, idan kuma Allah bai
nufa ba Allah bamu ikon zama cikin haƙuri da juna."
Daddy tasowa yayi tare da ƙarisawa gareta ya rungumeta ya ce, "Ameen idan har
zuciya kike faɗan hakan, dan ku mata akan kishi sai a hankali."
"Kishiya ba daɗi Abu Yusuf, amma tun da Allah ne ya halasta to alhamdulillah Allah
bamu haƙuri, har zuciyata nake maka wannan addu'a, ina son mijina uban ƴaƴana zan
yi haƙuri da shi a ko wani hali Insha Allah."
"Allah ya miki albarka Maryam, Allah kuma ya raba mu da mummunan ƙaddara."
Mummy barin jikinsa tayi tana faɗin, "Ameen Abu Yusuf, muje mu karya ko."
Tare suka fice a ɗakin suna ta zancensu suna dariya, kuma akan maganan kishiya ne
Daddy ke stokananta, har suka ƙarasa dinning ɗin, mummy girgiza kai kawai tayi tare
da ja wa Daddy kujera ya zauna, ta buɗe baki za ta yi magana sai Daddy ya ce, "Wai
ina yaran nan ne suka yi? Babu ko mostinsu."
"Wannan yara sai dai Allah shiryesu ya musu albarka, wai na tashi nayi aikina na
ƙyalesu su huta, amma fitowa su ci ma ya zama aiki, bari na ƙira su", Mummy ta faɗa
tana barin dinning ɗin, ta nufi ɗakin yaran nasu.
Mummy na barin dinning ɗin sai ga Meelat ta iso, ganin Daddy faɗaɗa fara'anta tayi,
kujera ta ja ta zauna sanna ta gaishe da Daddy, cikin girmamawa, ya amsa yana
faɗin, "Sai yanzu kuka fito?"
Ƙasa da kai Meelat tayi tana sosa ƙeya, ta faɗa masa ita ta jima da fitowa tare
suka yi aiki da Mummy, sannan Daddy ya jinjina kai, dan yaran duk sun san shi akwai
wasa da raha da yara, amma kuma akan maganan tarbiyansu ko ayyukan gida, to baya
musu dariya kuma haka Mummy ma, akan horar da su tarbiya to basa ganin haƙoranta.
Mummy da yake tasan Meelat kam dama tare suka yi aikin ta je wasta ruwa ne, shiyasa
bata yi wajanta ba, ta nufi ɗakin Deeyah, tura ƙofan ɗakinnasu Mummy tayi tana
surutu, "Wato ku yaran nan ba ku iya samun waje ba ko, kuna ɗaki kaman munanan
Amare wai nikam yau ba za ku fito ba ne?"
Deeyah da ke kwance akan ƙatoton gadon nasu ne tayi saurin tashuwa, sai da ta duba
gefenta ta ga ba Subby, mostin ruwan da taji a bathroom ne ya tabbatar mata Subby
ta tashi, sunkuyar da kan ta tayi ta ce, "Mummy ki yi haƙuri Allah mun yi sallah,
baccine ya ɗaukemu."
Ƙwafa Mummy tayi ta ce, "Zan yi dai-dai da ku ne, maza ku fito ku karya, ke da
Subeeya kam sai dai gyaran Allah da shiryarsa, kuma wallahi idan kuka ci gaba ba
ku daina ba mazajen ku na tare da aiki, ko kuwa na ce ku kuna tare da aiki ba
ruwana ba ni na muku wannan horarwan ba, dan ba abun da kuka iya", ta faɗa tana ja
musu ƙofan ɗakin ta juya.
Ajiyan zuciya Deeyah tayi, sannan ta sauƙo a gadon, ta wuce bakin ƙofan toilet ɗin
ta staya tana faɗin, "Munafuka ki fito tun da an mini faɗa ni kaɗai hankalinki ya
kwanta kin ji daɗi."
Subby fitowa tayi tana dariya ta ce, "Wallahi ni ba munafuka ba ce kema kin sani,
zagawa nayi bawai nasan da shigowan Mummy ba ne na zaga, kuma kema da naki da kika
zage kina bacci, bayan kin san nan gidan Mummy ne ba na Mom ba balle muyi bacci
kaman jakuna."
Deeyah matsa mata tayi a hanya ta fito, ita kuma ta shige ta wanko baki da ido ta
fito tana hararan Subby.
"Sai muje mu karya ai mu samu muje wajan yaya jidderh ko", Subby ta faɗa tana
ficewa a ɗakin tare da maste dariyanta, dan Deeyah na bin ta a baya.
Dinning ɗin suka nufa in da suka samu Mummy, Daddy da Meelat, zaune suna jiran
isowan su.
Kujera suka ja suka zauna, sannan Subby ta ce, "Barka da safiya Daddy."
Murmushi Daddy yayi ya ce, "Yauwa yarinyar kirki, sai yanzu ake fitowa ko?"
Ƙasa da kai suka yi dukkansu, tun da sun san halin Daddy ma akan irin haka, shi
kuma bai kuma cewa komai ba ya amsa gaisuwan Deeyah tayi.
Meelat ta buɗe baki za ta ƙira mai aikinsu sai Mummy ta bi ya da harara, ta ce,
"wai meyasa bakwa ji ne ku kam? Za ki ƙirata ta miki me? Ku ba za a more ku ba ko?
Common serving na abinci sai an muku? To daga yau ku zaku dinga serving namu, ke
Sadeeya tashi ki yi serving namu, ke kuma Subeeya ke za ki haɗa kwanukan bayan an
gama ci, Jameela ke kuma ke za ki kai kwanuka kitchen, fatan kun ji ni ai?"
Haɗa baki suka yi wajan cewa, "Eh Mummy."
Gyaɗa kai Mummy tayi ta ce, "To yayi kyau."
Deeyah tashuwa tayi tare da zubawa kowa nasa abin karin, sannan ta koma ta zauna,
dukansu cin abinci suke hankali kwance ba mai magana, sai can Meelat ta ce, "Mummy
nikam ban ji mostin yaya jidderh ba."
Subby da Deeyah kaman su ma jira suke Meelat ta tambaya, suka haɗa baki wajan cewa,
"Yaya jidderh bata cin ɗumame."
Mummy ta ce, "za ku mana shiru ku ci abincin ko kuwa za ku tashi ne ku bita in da
taje ɗin?"
Daddy murmushi yayi ya ce, "Yaran kirki uwata na gidan baba alhaji", ya ƙarishe
faɗa yana ajiye cokalin da ke hanunsa da kuma tea cup, share bakinsa yayi da tissue
yana faɗin, "Alhamdulillahi!"
Dukansu suna gama ci Subby ta tashi ta haɗa kwanukan, Meelat kuma ta ɗauka ta yi
kitchen da su.
Daddy tashuwa yayi ya koma main palour ya zauna, Mummy da Deeyah da Subby su ma
suka koma can, a ƙasa Subby da Deeyah suka zauna kan su a ƙasa, Daddy ne ya kallesu
ya ce, "Ya aka yi yaran Daddy kaman da magana a bakinku?"
Subby ta ce, "Daddy am..dama..uhm."
Kallonta Daddy yayi ya ce, "Ya aka yi ina jin ku."
"Am..daddy dama ba birthdaynmu ya zo, shi ne.."
Kamun ta ƙarishe magana, Mummy ta tari numfashinta ta ce, "Ku shikkenan iya abin da
kuka iya kuma kuka sani kenan, to Alhaji ba abin da yaran nan zasu yi ka barni da
su, shi birthday me amfaninsa me abin farinciki a wajan? Raguwan da kwanakinku ke
yi a duniya shi ne abin murna? Abu ba lada ba ba komai ba.
Daddy ya mayar da idanuwansa kan su ya ce, "Kun ji abin da Mummynku ta ce ko? To
idan kuna son ku yi birthday ku lallaɓata ku yi abin da take so sai ku yi."
"To Daddy mun gode Allah ya ƙara girma", suka haɗa baki wajan faɗan haka, duka suka
tashi suka wuce ɗaki.
Deeyah kaman mai shirin kuka ta ce, "Wallahi Mummy tana ɓata mana show, amma
bakomai yanzu bari nayi wanka, idan na fito kema sai ki shiga, mu wuce wajan yaya
Jidderh a gidan baba alhaji, in yaso sai ta taya mu yi wa Daddy magana, nasan Mummy
ba za ta ce komai ba indai yaya Jidderh ce tayi magana."
Subby ta ce, "Ki shiga ki watsa ruwan kamun ni kuma na gyara mana ɗakin, kin ga
daganan mun fara yin abinda Mummy ke so."
Tashuwa Deeyah tayi ta shiga wanka, ita kuma Subby ta gyara ɗakin tsab, Deeyah na
fitowa ita ma ta shiga wankan, bayan mintuna ta fito.
Shiryawa suka yi dukkansu cikin Black Abaya wan da yayi mugun amsan su( gaskiya
wannan family ba dai kyau ba kam Masha Allah.)
Sun fito palourn suka samu Meelat ma ta fito ita ma a shirye staf, cewa tayi,
"Yaya Subby zan bi ku mu bata haƙuri tare."
"To muje meelatyna."
Ɗakin mummy suka je suka ce mata za su wuce gidan Baba a Alhaji, a dawo lafiya ta
musu suka fice a cikin gidan, za su fita suka haɗu da Uncle Sale, stugunnawa suka
yi duka suka gaishesa, ya amsa masu da fara'a yana faɗin, "Yaran Uncle sai ina da
safen nan tun rana bai yi ba, kun ci kwalliya haka kaman masu yin gasan kyau."
Duk murmushi suka yi, Meelat ta ce, "Uncle za mu gidan baba Alhaji ne."
"Ah to kun kyauta, ku ce za ku je kwacewa uwarmu miji, to ku dawo lafiya, nima bari
na shiga wajan yayana", faɗin Uncle Sale Yana murmushi.
Tashuwa suka yi suka wuce, shi kuma yayi cikin gidan.
Gaishe da baba mai gadi suka yi suka buɗe ƙofan, suka fice suka nufi gidan baba
Alhaji a ƙafa suna tafiya suna hira.
Uncle Sale da sallama ya shiga palourn, amsawa Mummy tayi tana faɗin, "Maraba da
mijin Hajiya."
Murmushi Uncle Sale yayi ya ce, "a'a fa mummyn yara, matar Alhaji dai ba mijin
Hajiya ba."
Zolayan juna suka yi kaman ko yaushe, sannan suka gaisa cikin mutuntawa, Uncle Sale
ya ce, "Yayana na nan kuwa?"
Dai-dai lokacin da yayi tambayan a lokacin Daddy ya fito a ɗaku, ganin ƙanin nasa
sai ya faɗaɗa fara'ar fiskansa.
Mummy ta ce, "To ƙanin Yaya ga yayan naka."
Murmushi Uncle Sale yayi ya ce, "Barka da fitowa yaya, yau nayi sa'an samunka a
gida, bansan ka dawo daga ƙasar da ka je ba, kawai na zo gwada sa'ata ne."
Daddy waje ya samu ya zauna suka gaisa sannan ya ce, "To ya aka yi ina labari?"
"Yaya babu labari fa yanzu ma takardun can na zo amsa, idan suna kusa a taimake ni
da su."
"Okay ba mastala, amma dai suna office kuma yanzu daman zan fita ne, in yaso sai mu
wuce tare ka amsa ko."
Uncle Sale amsawa yayi, suka miƙe a tare za su fita, Mummy ta ce, "Mijin Hajiya ba
za a ci abincin Hajiya ba ne?"
Da murmushi Uncle Sale ya ce, "Kar Hajiya ta damu zan dawo na ci da rana."
"Allah ya dawo da ku lafiya", ta faɗa tare da bin bayansu, ta raka su har bakin
ƙofan palourn, san da suka ja mota suka fice a gidan, kamun ta koma cikin palourn
nata, tana jin gidan ya mata girma shiru, sauran yara sun tafi makaranta ga su
Jamila sun yi gidan baba alhaji.
Sai da Mummy tayi duk abin da za ta yi sannan ta wuce ta kwanta, dan ta hutawa
rayuwanta.
Jidderh na zaune a ɗaya daga cikin kujerun palourn hajiya Mama tana kallon,
hankalinta rabi na kan waya rabi na kan TV.
Sallaman su Subby da taji ne ta amsa tana ɗagowa, su kuma suna shigowa carab suka
ga yaya Jidderh, kuma ita ta amsa musu sallaman, da sauri Meelat ta ƙariso wajanta
ta rungumeta, tana faɗin, "Babbar Yaya na yi kewanki."
Jidderh ta ce, "kuna mini rashin kunya kam ba dole na tafi na bar muku gidanku ba."
"Yaya Jidderh ki yi haƙuri, Allah nikam ban yi magana dan a ɓata miki rai ba, kiyi
haƙuri ba zan sake ba", faɗin Meelat tana kama kunnenta.
Subby da Deeyah ma zuwa suka yi suka rungumeta suna faɗin, "Yaya jidderh tamu ba za
mu sake ba ki yi haƙuriiiiii."
Murmushi jidderh tayi, dan yacce suka ja kalman haƙurin ya ba ta dariya, cewa
tayi, "Na yafe muku ai ya wuce kar ku sake, shi ɗan uwanmune kuma yayanmu, bai
kamata mu muna ƙannensa kuma muna zaginsa ba."
Haɗa baki suka yi suka wajan faɗin sun daina, jidderh kuma ta murmusa ta tare da
faɗin, "Yayi kyau to Allah ya muku albarka, sai ku zauna mu sha hira tun da kun zo,
daman nima zama shirun ya ishe ni, duk sa'oin nawa maza ne kuma nasan basa nan."
Miƙewa suka yi duka suna faɗin, bari su je su gaishe da stoho da stohuwa tukunna,
suna dawowa.
Palourn Baba Alhaji suka nufa da sallama suka shiga, ba su wani staya ba suka
wuce ɗakinsa direct suna ƙwala masa ƙira kaman ya ci bashin su.
Baba Alhaji yana kwance yana jan carbinss, jiyo muryan fitinannun jikokinsa sai ya
miƙe tare da jawo madubin idonsa ya maƙal, tare da amsa musu sallaman da suka yi.
"Ɗan stoho barka da hutawa", faɗin Deeyah.
Shi kuma ya ce, "Yauwa stohuwa Halimatu-Sadiya, kun samu shigo kenan."
"Eh mun shigo angonmu", suka faɗa tare da gaisar da shi, ya amsa musu dukansu da
wasan jika da kaka suka sha hiran su.
Baba Alhaji ya ce, "Yauwa Subiya yayar taki tana dawowa yau ɗin ne?"
Subby ta ce, "Ɗan stoho nikam a gidan Daddy na kwana ba a gidanmu ba, banma san ko
tana dawowa ba."
"To Masha Allah, Allah ya muku albarka duka ya ƙara haɗa kawunanku, Allah ya dawo
da ita lafiya, ku so junanku ku ci gaba da haɗa kanku iyayen nan naku ne duka Allah
raya ku ya baku mazaje nagari jikokina", faɗin Baba Alhaji cikin tsananin ƙaunar
jikokin nasa.
Meelat ta ce, "Kaka Alhaji nikam ina da kai ai ina da miji nagari."
dariyan manya baba Alhaji yayi, tare da cewa, "To amaryata amma dai duk da haka,
kun ga nikam na tsofe karbna tafi na barku, gwanda kumun abokanayen takara tun da
wuri."
Dariya suka saka dukansu wai wato kaka Alhaji abokanayen takara za'a maka, ya amsa
musu da "eh mana."
Hajiya Mama ce ta shigo tana faɗin, "Su wanne munanan ƴammatayen ne suke damar mini
miji da surutu?"
Baba Alhaji ya ce, "A ƙyaleni nayi hira da Amarena ke kam kin stufa yanzu, su ake
yayi."
"Yauwa angon faɗa mata dai mu kake yayi, mu ne na zamani ita kam ta tsufa", faɗin
Subby, sannan suka ci-gaba da hiransu har da Hajiya Mama cikin nishaɗi.
⭐
Shameekh tun da ya koma ya kwanta, yake sharar baccinsa hankali kwance, shi ne bai
farka ba sai da agogo ta buga ƙarfe sha ɗaya na safe, sannan ya wara idanuwansa ya
wara a hankali, yana mai karanto addu'oinsa, sannan yayi miƙa da salati.
Yaye bargon da ya lulluɓa da shi yayi, ya miƙa hanunsa ya jawo wayansa da ke kan
bedside drawer, ( Uwar batoorl na faɗin yau kam ba call ne?) Sai ga Shaameekh ya ja
guntun tsaki, ganin misscalls ɗin da aka tara masa.
Duba ƙiraye-ƙirayen yayi amma babu na Ummiynsa a ciki, dan haka numbernta ya laluɓo
wan da yayi saving da FAVORITE SOUL, har zai yi dialing sai ya duba time, ganin
11am a Dubai wan da yayi dai-dai da