Chapter 13 Reading SHAAMEEƘH Alfaharin Basarake by Harira Salihu Isahl HN Novels

SHAAMEEƘH Alfaharin Basarake by Harira Salihu Isahl

Author :  Harira Salihu Isahl Category :  KDP NOVELS

Chapter   13 / 15

36K to 39K   out of 43.9K words

Alhaji baba ba ya masifa, amma muddin abu ya shafi na kawo
rabuwan kan zuri'ansa ne to sai inda karfinsa ya ƙare a kan mutum.
Ummiy inda sabo ta saba, dan haka bata wani jima ba ta miƙe ta fice abin ta, driver
ya ja mota suka yi gidan Daddy, da sallama ta shiga palourn, cikin sa'a kuwa ta
samu Daddy na gida, dan yau ɗin bai je office ba, suna zaune da matarsa suna
hiransu yana aikinsa a gida, duk yara sun tafi school, Jidderh ce daman kawai ta
gama makaranta a yaransa, ita kuma sun tafi gidan small uncle da baby, dan matan
small uncle wacce suke kira da Aunty Zee bata da damuwa sam.

Daddy da Mummy da murmushi suka amsa sallaman Ummiy, Mummy na faɗin, "lale maraba
da mutanen Adamawa."

Ummiy ta samu waje ta zauna tana faɗin, "Yauwa matarmu, yaya sannu da hutawa ashe
yau da sa'a nake tafe, na ɗauka kai ma ka tafi office ai kaman yaya Sulaiman."

Murmushi Daddy yayi ya ce, "sannu da zuwa Fatima, sannunku da hanya, kin yi sa'an
samuna kam dan kwana biyu tun zuwanki bana nan shiyasa ma ba ki ga na leƙa gidan
Baba ba, jiya cikin dare na dawo, kinsan abubuwan ba zama sai a hankali."

"To dai Allah ya taimaka yaya, fatan mun same ku lafiya?"

"Lafiya alhamdulillah sai alkairi Fatima, ya mai gidanki ya labarin Mai sunan Baba,
dan fauziyan kam na gansu tare da Uwar masu gida."

Murmushi Ummiy tayi ta ce, "Baban fauziya yana lafiya, aiki ne ya hanasa samun
daman zuwa dan bai dawo ba, Shaameekh kuma yana can ƙasar mutane yaya."

"Allah ya taimaka ya ba da sa'a, shi kuma mai sunan Baba yaushe zai shigo to? dan
na samu labarin ita Safiya ta kwana biyu da dawowa ma, Kabeer kuma sai ƙarshen
wannan satin za su shigo da sauran ƙannensa."

Ummiy ta ce, "Ameen yaya, Insha Allah shi ma Shaameekh ƙarshen satin nan zai dawo,
ko ranan Juma'a ko Asabar, yanzun ma duba wani mara lafiya ne ya riƙe sa da kuma
wasan da za su yi."

"To Allah taimaka ya basu sa'a, Allah musu albarka ya kawo su gida lafiya duka, ni
bama waya da shi kwana biyu kinsan yaron naki sai a hankali, ga busy kaman
iyayensa, ga kuma kunya kaman mace."

Murmushi Ummiy tayi ta ce, "Shaameekh kam haka yake sai addu'a, ko Baban fauziya fa
sai idan ya ƙirasa, amma haka kawai ba ƙiransa yake ba sai a hankali."

"Allah shirya mana shi ya masa albarka, kinsan wasu mutanen dama haka suke da
kunya, akwai misalansu da yawa, ko cikin sahabban Annabi SAW, ana yaba irin kunyan
sayyadina Uthman RTA", Daddy ya faɗa yana murmushi.

Mummy da daman Ummiy na zama ta tafi kawo mata ruwa, dawowa tayi ɗauke da tire da
abubuwa a kai, ta dire a gaban Ummiy tana faɗin, "Mutan Yola ga ruwa, kada a ce
nabar miji da ishi."

Murmushi Ummiy tayi ta ce, "Daɗina da matar nan neman lada, ko masu aiki ta ƙi bari
na kawo mata, wai komai za ta yi da kanta dan kawai tana storon kishiya", faɗin
Ummiy da take kai abin sha bakinta.

Daddy murmushi yayi ya ce, "kema dai kya ce haka Fatima, sam-sam Maryam bata barin
wani ƙofa ma balle na samu daman ƙaro aure, komai yi take."

Murmushi Mummy tayi ta ce, "Ni bana storon kishiya, idan Allah ya kawo muku ta gari
ku auro."
"A'a faɗa gaskiya fa matarmu", Ummiy ta faɗa cikin zolaya.

Mummy ta ce, "Gaskiyan kenan Maryam bata storon kishiya, nasan na riga na gama
samun tawa fadar ban da damuwa da kishiya."

"Wannan haka yake, kin gama kanainaye mu matarmu", faɗin Ummiy, sannan suka gaisa
cikin fara'a da zolaya, Daddy yana jin su yana aikinsa sai murmushi yake yi abinsa.

Ummiy wuni tayi curr a gidan Mummy bata je ko ina ba, har yaran makaranta suka dawo
suka sameta, duk da sun je gidan Alhaji baba sun mata oyoyo, amma yanzun ma cikin
farinciki suka mata oyoyo suka gaisa, Yusuf mutumin baby yana maƙale da Ummiy.

Mummy ta ƙi barin Ummiy ta ɗaga ko cokali, duk aikinta ita take yi, ko me Ummiy ke
so kamun ta mosta ta miƙo mata, ba ruwanta da Ummiy ƙanwar mijinta ne, saboda Ummiy
ta girmi Mummy a shekaru, ba komai stakaninsu sai girmama juna da wasa da fara'a,
Daddy ma tare da shi suka wuni har ya fita ya dawo, dare nayi Ummiy ta ce za ta
koma gidan Alhaji baba, amma Mummy ta dage sam sai dai su kwana, haka Ummiy ta
haƙura suka kwana, washe-gari da sassafe ta koma gidan Alhaji Baba, saboda sauran
yayyun nata da suke nan, sun riga da sun haɗu da su a gidan Alhaji baba, Daddy da
big Dad ne kawai daman tun zuwanta basu zo ba, shiyasa ta je gidajensu, yanzu sai
anyi meeting, idan sauran yayyun nata sun dawo za ta ƙoƙarta duk ta je musu kamun
su koma ita ma ta koma.

Jidderh ta cancarawa baby kistonta mai ɗan iskan kyau, tun da baby ta zo aiki ya
same su, yau su je nan gobe su je can, su dai su Meelat gaba ta kai su wai gobaran
titi a Jos.


⭐
Ɓangaren Shaameekh mutanen Dubai kuwa, hankali kwance ya samu ya gama duk abin da
ya kamata, ranan Litinin ya haɗu da likitocin da za su yi aiki tare, Dr. Naresh
Trehan daga India, da kuma Dr Fouad M Abbas daga Europe, sai shi oga Shaameekh Dr
Adam M Aliyu.

Sun yi arrangement na komai, kuma cikin ikon Allah ranan Laraba suka yi aiki, wan
da babu ko shakka da yardan Allah sun yi nasara, dan dukkansu ƙwararrun likitoci ne
akan mastalan wannan mutumin, sai dai farkawansa ne kawai za'a jira, daman normally
wannan aikin idan aka yi wa mutum sai ya kai wata kamun ya farfaɗo saboda wasu
condition's, amma su suna stammanin in Allah ya yarda ba zai kai watan ba.

Bayan Shaameekh ya gama da issuen mara lafiya ya samu nistuwa, shikkenan kuma ya
mayar da hankalinsa wajan ci-gaba da tarining na wasan da za su gabatar ranan
juma'a da yardan Allah, daga nan kuma sai tahowa gida Nigeria.




⭐
Kuluwa na sakin wannan ƙayataccen murmushin, a hankali ta mosta laɓɓanta, cikin
sansanyar daddaɗan muryanta ta ce, "ALHAMDULILLAHIL LAZI AHYANA BA'ADA MA AMATANA
WA ILAIN-NUSHUR...." Ta karanto da duk sauran adduo'in tashuwa a bacci, sannan ta
miƙe tsaye tare da yin miƙa, Uhmn Masha Allah santaleliyar haɗaɗɗiyar budurwa.

Cikin nistuwa take tafiya kaman wacce ke tambayan ƙasa kamun ta taka, har ta fito a
ɗakin nata, jin ba alaman mostin iyayenta hakan ya tabbatar mata basu tashi ba,
tura ƙaramin bakinta tayi tare da zuwa bakin ƙofan ɗakin tayi sallama.

Kawu cikin baccinsa da bai yi nauyi ba ya jiyo mostin buɗe kofa, tashuwa yayi ya
zauna yana sakin murmushi dan yasan ba ko shakka zai yiwu Kulu ce, tana yin sallama
kuwa ko gama rufe baki bata yi ba ya amsa, da sauri ya tashi Hajjo yana faɗin,
"Hajjo tashi Kulu na sallama."

Hajjo a ɗan firkice ta tashi, kusan rige-rigen isa bakin ƙofan suka yi, haka suke a
duk lokacin da maganan Kulu ya dawo, to farinciki suke ji kaman ranan ta fara
magana a duniya, fitowa suka yi Kawu ne ya fara mata magana cikin ƙauna, da
fillanci ya tambayi ya aka yi me take buƙata?

Kuluwa cikin shagwaɓa ta ce, "Banɗaki Hajjo za ta raka ni."

Ba musu Hajjo ta yi gaba ta bi bayanta suka fice, rakata tayi har cikin banɗakin
dan ko ta tsaya a waje to ba za ta yarda ta shiga ita kaɗai ba wai storo take, sai
da ta gama buƙatar ta sannan suka fito, Kawu ma ya shiga ya kama ruwa ya fito, duk
su ukun tare suka yi alwala, Kawu ya ja su suka yi nafila a tare, har sai da aka
ƙira sallah sannan ya tafi masallaci, Kulu da Hajjo suka yi nasu sallahn su ma.

Suna idar da addu'a da komai, Kawu na shigowa Kulu ta durƙusa ta gaishe shi ya amsa
da fara'a yana saka mata albarka, yana mai ƙara hamdala a zuciyansa, yana addu'an
Allah ya raba Kulu da wannan cuta da aka rasa gane masa, Allah ya bata lafiya na
har abada.

Hajjo ma amsa gaisuwan Kulu tayi, sannan Kulu ta miƙe Hajjo ta raka ta banɗaki,
Kulu yau da kan ta tayi wanka sannan suka fito, ta wuce ɗakinta, sharp-sharp ta
shirya cikin riga da wandonta masu taushi, sannan ta fito ta wuce kitchen, ta hura
wuta ta ɗaura ɗumame, ta fito ta share stakar gida, kamun ta shigo ciki kuma Hajjo
ta gyara palourn da ɗakunan nasu, amma Kulu sai da ta ƙara gyarawa ta cika ko ina
da ƙamshi, tuni gida yayi fes-fes sai ƙyalli kawai yake yi da ƙamshi.

Kuluwa aiki ta sha kaman wata mai aiki da inji, kuma sam-sam babu sanyin jiki a
ayyukanta, sai dai in tafiya take to ka rantse ƙwai ne ya fashe mata a ciki.

Ita ta haɗa komai na karyawa, suka karya da iyayenta, sannan Kawu ya miƙe zai fice,
ta tashi ta rakasa tana faɗin ya kawo mata staraba.

Kulu na dawowa ta gyara wajan, ta yi wanke-wanke da komai, ta je wajan dabbobin
Kawu ta duba su tana murmushi har mai kiwonsu ya zo ya fice da su, sannan ta gyara
wajan ta koma cikin gida, sai da Hajjo ta kuma rakata banɗaki tayi wanka, amma
yanzu a waje Hajjo ta staya da yake gari yayi haske storon nata ya ragu, sannan
suka koma ciki ta kuma saka wani dogon riganta mai kyau ta kanti, ta zo ta kunna
musu kallo, Hajjo da ita ma tayi wanka ta shirya zama tayi tana faɗin, "Kulu yau ba
za ki makarantan ba ne?"

"Hajjo sai gobe zan je yau kisto za ki mini", ta faɗa da ƴar muryanta cikin
shagwaɓa.

Hajjo bata ce komai ba kuma, tun da tasan idan Kulu bata yi niyan yin abu ba babu
mai saka ta dole musamman makaranta, idan kuma tayi niya to ba sai an saka ta tayi
ba, watarana tana son bokon watarana kuma bata so haka take, hakan kuma baya hanata
ƙoƙari a makaranta dan a ta Allo har ta sauƙe, littatafai take yi da hadda.

Kulu zama tayi a ƙasan palourn akan pillow, Hajjo kuma na kan kujera suna fiskantan
TV, Hajjo ta fara taje kan Kulu ta fara raki tana faɗin, "Wayyoo kai na Hajjo,
Wayyoo zafi, nikam na fasa."

Hajjo ta ce, "Ai nasan halinki Kulu, ina sake wa za ki ce a miki, abu mai sauƙi ne
ma ki saka kuka, dan haka sai mun yi, ni halina da ke kenan idan bakinki ya buɗe
Shikkenan duka duniya sai sun sani, ki addabi mutane da abu kaɗan ihu kaman jare."

Tura baki Kuluwa tayi ta ce, "Yauwa Hajjo kinsan me?"
"Uhmn ko banyi niyan yin hira ba sai kin mini ai Kulu, shiyasa idan bakin ya kullu
duk sai ki sa gidan yayi ba daɗi, ni bar damuna da surutu muyi kallon."

Hajjo na kitso Kulu na raki, tana kuma kan surutu kaman cakwai-kwai-wa, ga murya
zaƙi kaman sikari, dan dole Hajjo ke amsawa bata yi niya ba, idan kuma abin ya ishe
ta sai ta yi shiru ta ƙyaleta, gaba-daya surutun Kulu ya hana Hajjo fahimtan mai ma
ake a TV, Allah Allah kawai take Kawun Kulu ya dawo ko za ta huta, dan wannan
suturun sai shi, daman shi ke biye mata.


***
FAN'S WAI HAKA DAMAN KULUWA KE DA SUTURUN STIYA AMMA KWANA BIYU TA ZAMA KURMA🤣
MENENE DAMUWAN DA KE DAMUN KULUWA?
MENENE ASALIN LABARIN KULUWA?

SU WAYE WAƊANNAN FAMILY?

ALHAJI BABA YA CE SABODA SU SHAAMEEKH ZA'A YI WANNAN FAMILY MEETING ƊIN, ME ZA SU
ZANTA KUKE TUNANI?

SHAAMEEKH YA CE BA YA SON AURE, TA YA ZAI ƁULLEWA MAGANAN AUREN KO KUWA DAI ZA'A
ƘYALE SA NE?

ME KUKE TUNANI GAME DA SOFFY ZA TA SAMU SHAAMEEKH KO KUWA?

JIDDERH BAIWAR ALLAH YA NATA LAMARIN ZAI KASANCE, SAFWAN NE KO KUWA SHAAMEEKH?

WAI MENENE MA ASALIN LABARIN WANNAN FAMILY? ME YA KAWO RASHIN JITUWA TSAKANIN UMMIY
DA MATAN YAYYUNTA MUSAMMAN BIG MOM?

WAYE WANNAN BAWAN ALLAH DA SHAAMEEKH SUKA MASA AIKI, DA AKE FAƊIN MUTUM MAI MASTAYI
NE A NIGERIA!

Kada dai ku manta labarin fa ko fara sa bamu yi ba, free page's kaman ƙullewan kai
kawai ke ƙunshe cikinsa, asalin amsoshinmu da kuma asalin labari na paid page's,
book 1 book 2 wataƙila har book 3.

A yanzu littafin SHAAMEEKH ₦500/ 500f yake, kada ku bari rashin sharhinku ya ja
book 3 ya zama payment nasa daban ne, kun tabbata Uwar batoorl na yin littafi free
muddin ta samu SHARHI yanda ya kamata ko da kuwa a paid tayi niyan yin sa misali
ƳAR KARUWA, sannan littafi na komawa paid ko kyauta tayi niyan yin sa misali
JAHILCI KO AL'ADA.

Kada ku bari a baku labarin wannan littafi namu mai ɗauke da abubuwa da yawa, wanda
ba za su misaltu ba, abin sai wan da ya biya ya karanta.

Anan na kawo ƙarshen free page's, Sai mun haɗu a PAID PAGE'S INSHA ALLAH alƙalamin
Uwar batoorl zai nishaɗantar da ku kaman ko da yaushe.


9161720046
Harira salihu isah
Opay
&
2220553988
Harira salihu isah
Uba
Shedar biya ta wannan layi 07015870735.

Mutanen Nijar ku ma ku yiwa wannan layi magana dan yin payment naku 500f.
+227 88 73 81 26
Sai kuma a turo shedar biya ta wannan layi
07015870735.


# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
SHAAMEEƘH
B̶̶O̶O̶K1

Officially


𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


‫ اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله‬SAW 🖤🤍


GARGAƊI: masu YouTube channels, masu yin Audion littafi, kada wacce ta ɗaura mini
littafi ba da yawu na ba, domin muddin na ci karo da haka to ko wacece/ wanene zan
ɗau mummunan mataki a kai, hukuma za ta rabani da mutum, A KIYAYE.


WANNAN SHAFI gaba ɗayansa sadaukarwa ne a gare ni da kuma Mijina, Alhamdulillah ala
kulli halin, ina tayamu murnan zagayowan ranan aurenmu, Allah Ubangiji ya karo mana
zaman lafiya, Allah ya azurtamu da zuri'a masu albarka.


PAID PAGE
Shafi
Na
Goma.


⭐
Hajjo kisto mai kyau ta yiwa Kuluwa, kiston su na fulani, cikin hannu babba sai
bayan hannu ƙanana biyu, haka ta mata haɗaɗɗen cukunta, da kuma guda bibbiyu a ko
wani ɓangare na goshinta dama da hagu, ba ƙaramin kyau kiston ya yi wa Kuluwa ba,
dama mai kyau idan ya ƙara da wanka to ba'a magana.

Kuluwa surutu ta dinga yi, hira dai mara kai balle wajan zama, faɗi take, "Hajjo ai
ni da Kawu za mu je Makka da Madina, kuma zan sayo miki baby staraba fa, ni kuma
Kawu zai sayo mini miji na dinga masa abinci, ina masa wanka na lallashesa yayi
bacci na goye sa, kin ga zan shiga aljanna tun da ina masa biyayya."

Hajjo girgiza kai tayi ta ce, "Daɗina da ke watarana idan kika yi magana kaman a
baki kyauta, watarana kuma kaman a rufe ki da duka, Kulu kin fa girma, sa'anninki
kin sani duk yawanci sun yi aure, wasu har da yara, amma ke shirirtanki ba kaɗan ba
musamman idan surutunki ya mosta."

"To ai Hajjo shiyasa na ce nima Kawu zai sayo mini miji, kyakkyawa fari bana son
baƙi kaman mijin bibalon baffa", Kuluwa ta faɗa tana tura baki kaman za ta yi kuka.

Hajjo ta ce, "To Allah ya baki lafiya ya kuma baki miji nagari, ya nuna mana
lokacin da rai da lafiya."

"Ai lafiyata lau Hajjo, kuma kin ga idan Kawu ya sayo mini miji to nima har da gaɗa
da wasanni (event's na Fulani) sai anyi a aurena."

"Allah ya nuna mana to."

"Ummmmmmn na ma fasa ai Hajjo, sai nayi karatu na zama babba, har da kuɗi zan yi in
dinga bawa kowa shayi irin nawa da safe a garin nan, in sayawa kowa kayan ƴan gayu
irin wanda Kawu ke saya mini, kuma kullum idan na fita nima sai na kawo wa kowa
staraba a garin nan, ai nayi kirki ko Hajjo?" Faɗin Kuluwa tana washe baki irin ta
faɗi abin arziƙin nan.

Hajjo shiru ta yi wa Kuluwa bata kuma ce mata komai ba, har ta mayar mata da ɗan-
kwalinta, amma sai Kulu ta zame wai ai zafi take ji a kanta idan ta saka ɗan-kwali,
a bar kiston ma ya sha iska ya huce kada ya lalace ya ɓaci da zafin da ake yi,
Hajjo idanuwanta ta mayar kan TV kawai, bata kuma tankawa shirmen Kulu ba, dan idan
ba shirme ba kisto abinci ne da za'a ce zafi zai ɓata sa, a haka har bacci yayi
gaba da Hajjo a kan kujeran.

Kuluwa ajiyan zuciya ta sauƙe tare da lumshe kyawawan idanuwanta, ta kuma buɗe su a
hankali, sannan ta miƙe tana mai ambaton Allah, tsakar gidansu tayi ta shiga ayyuka
cikin nistuwa, dan kamun ka ce me tuni ta ɗaura abinci ta gyara gida tsaf, sai dai
duk abin nan da take yi fistari take ji, amma ta kasa shiga banɗaki sai kai kawo
take kaman mai safa da Marwa, tana ta faman maste ƙafafuwanta, a haka har ta gama
aikin amma Hajjo bata tashi ba, tana gama haɗa komai ta je ta zauna a gaban Hajjo
kawai ta saka kuka.

Hajjo cikin bacci take jin muryan Kuluwa na sheshsheƙan kukanta, tuni ta buɗe ido a
razane tana faɗin, "Me ya faru Kulu?", Da muryan bacci.

Kuluwa kam kuka take bilhaƙƙi stakaninta da Allah, tana kan haɗe ƙafafuwanta, wan
da lura da hakan da Hajjo tayi shi ya sanya ta gane abin da Kuluwan ke yi wa kuka,
miƙewa tayi kawai ta rakata, basu komo ciki ba kuma sai da Kuluwa tayi wanka, suka
yi alwala sannan ta wuce ɗakinta, Hajjo ma ta wuce nata ɗakin, tana addu'an shiriya
wa Kulu, a ce fistari idan ta kamaka sai ka zama kaman wani ɗan goye.

Hajjo na yin sallah ta fito duba aiki, amma ta tarar Kuluwa ta gama komai, murmushi
tayi tare da sanya mata albarka, da mata fatan samun lafiya, domin tana da tabbacin
ko aurar da Kulu suka yi yanzu idan ta samu lafiya, to ba dai miji yayi kuka da ita
akan aikin gida ba, sai dai wani abun daban.

Kuluwa tana idar da sallah ta shirya abinta, ta fito wai za ta anguwa amma Hajjo ta
hanata, akan ta bari sai Kawunta ya dawo, haka Kulu ta zauna zaman jiran dawowan
Kawunta har bacci

13 / 15