Chapter 8 Reading ABNUR Sirrin Hasken Soyayya By maimoon HN Novels

ABNUR Sirrin Hasken Soyayya By maimoon

Author :  Maimoon Category :  KDP NOVELS

Chapter   8 / 8

21K to 24K   out of 24K words

ta juya da sauri ta na kallon Zannur

"and who is she?"ta faɗa a ƙausashe


"Maami pleaaaaase na ce miki za muyi magana idan kin huta please"



Cikin tsawa ta katse shi tana faɗin

"Habibi who is she?,don't you dare lie to me, wayece wannan?,kuma daga ina take?,me takeyi a sama?"



Sunkuyar da kansa yayi dan ya san irin ɓacin ran Maami, idan har bai faɗa mata ba to tabbass ranta ƙara ɓaci zaiyi wanda zai sake ɓata komai.


Cikin inda inda yace
"my w..i..f.e"



"You Are Mad Habibi, ka haukace, how could you?
ta faɗa tana zare ido, da sauri kuma ta juya ga Noor da duk a tsorace take da ita.



Cikin faɗa tace

"me kika yi ma yarona, tell me before I deal with you personally"

Ta faɗa tana tunkaro Noor,

Da sauri Zannur ya sha gabanta yana faɗin


"Maami listen to me,zan faɗa miki komai, pleaaaaase muje ɗakin ki"


"Out of my way Zannur"
ta faɗa tana kallon cikin idonsa.



With suprise Shima yake kallonta, rabonta da ta kira sunansa har ya manta, ya tabbata yau ranta ya kai matuƙa wajen ɓaci.



Cikin sauri yace

"Maami ki saurareni, she is my wife, but I promise bana sonta, ban taɓa sonta ba, kuma bazan taɓa sonta ba, I only helped her, kuma ke kika ce in dinga taimako Maami!"



Wani kallon ka raina min wayo Maami ta ke masa, kafin ta sa hannu ta matsar da shi daga gabanta ta na nufan Noor


Ai da gudu Noor ta juya ta koma sama ta shige ɗakinta ta rufe ƙofar da key, dan wallahi ta tsorata ainun da matar,

amma maganganun sa sun fi mata ciwo fiye da fushin mahaifiyarsa saboda ta san fushin Maami is justified, dole ranta ya ɓaci.



A hankali ta ƙarasa gefen gadonta tana toshe bakinta da tafin hannunta saboda kukan da ke ƙoƙarin cin ƙarfinta



Juyowa Maami ta yi ta kallesa sai kuma ta haura sama, ba tare da ta sake cewa komai ba



Shafa kansa yayi,dan abin ya wuce yanda ya yi tunani, a hankali shima ya haura ya nufi ɗakin Noor, jinsa a rufe yasa ya wuce ɗakin Maami shima a kulle, bai san sanda yayi murmushi ba ya juya ya wuce ɗakinsa ya na kiran layin Abbu



Yasira da ke jin komai, ta yi saurin wucewa ɗakin su ta na jin wani farin ciki,
burinta ya kusa cika, Zannur ya kusa zama nata, ta kusa tashi daga in-charge na kitchen, itama ta zama Mrs Zannur Shuraim,

da sauri ta rufe ƙofar dan tasan su Asabe suna can baya suna wanke kayansu yau,

rawa tayi ta tiƙa tana juyi a ɗakin sai kuma ta faɗa gadon ta na ƙyalƙyalewa da dariya.


*****

"Son, meyasa kayi haka, kaima kasan Hilwa batada wanda take so fiye da kai, da baka ɓoye mata ba tun farko zata fahimceka, but zan mata magana,make sure You apologise"



Cikin sauri yace "i will Abbu,Wallahi i will,but please talk to her she shouldn't be angry,it hurts"


Okay I will talk to her insha Allah, kaje ka samu matarka kuje tare ku bata haƙuri, kasan tayi burin aurenka but ka ɓata mata komai dole tayi fushi"


A hankali yace

"toh Abbu"
duk wannan maganan cikin harshen larabci suke yin sa,


Sai da Abbu ya ƙara yi masa nasiha, da nuna masa kuskurensa kafin sukayi sallama,kasa zuwa ya yi sai kawai ya kwanta a dakin ya na jin a little bit of relieve.


****

"Hilwa!!" Shiru tayi daga masifan da take ta yi tana mayar masa abinda ya faru,


"Hilwa!" ya sake maimaitawa

"Abbu bazaka gane ba..."
bai barta ta ƙarasa ba yace

"na gane i understand you wifey, kawai ina so ne kiji other side of the story, ki tsaya kiji dalilin sa please for me"
ya faɗa yana marairaicewa


"Why are you blackmailing me emotionally" ta faɗa tana murmushi


Shima murmushin yayi dan da alama ta ɗan sauƙo, a hankali yace

"cause I know exactly the type of wife I am married to"

dariya tayi tana zama akan gadon ba tare da tace komai ba

A hankali yace

"i missed you hilwa!"


"Tun yanzu ai kuwa bazan dawo ba sai nan da 2 month"


"You are joking" ya faɗa da ƙoƙarin sata ta manta da duk ɓacin ran ta.


"Am serious...." shiru tayi jin ana knocking sai kuma taja tsaki tana faɗin


"Ɗan ka da ka turo gashi nan har ya iso"


Cikin harshen larabci shima ya mayar mata,

"ɗanki dai, Habibi ne Fah kin manta"


Batace komai ba ta miƙe ta buɗe ƙofan ta dawo bakin gado ta zauna tana ɓata fuska ,


A hankali kamar wani Maraya ya ƙaraso ɗakin yana kallonta da fuskar tausayi, har abin ya kusa bata dariya,
amma ta gimtse ta ƙi kulawa.


Zama ya yi kusa da ita ya kwantar da kansa a kan Cinyarta, har ta ƙarasa wayan ta kashe ta ajiye ba tare da ta kula shi ba, a hankali ya soma magana

"Maamiii" bata kula ba

Ya cigaba da magana

"Maami pleaaaaase an so sorry, please Maami listen to Habibi"

Juyar da kanta tayi tace ina sauraron ka

Da sauri ya miƙe ya zauna daman he trust Abbu shi kaɗai yasan yanda ya ke sauƙo da Maami duk tsananin fushin da tayi kuwa.


A hankali ya soma bata labarin abinda ya faru tun zuwansa Baulawa har kawo yanzu.

With shock ta juyo tana kallonsa, sai kuma ta sake haɗe rai tana faɗin "none of my business,
Yanzu abinda nake so da kai, kaje ka kira min waccar da kake ikirarin matar kace, kuzo nan yanzunnan"


A sanyaye ya buɗe baki zai yi magana ta ɗaga masa hannu tana nuna masa ƙofa,


Miƙewa yayi ya fice a ɗakin yana jin kamar ya kurma ihu, ya zaiyi ya mata bayani ne wai.



A ƙofar ɗakin ya tsaya, sai da ya ɗan yi jim sai kuma ya soma knocking a hankali,
sai da yayi sau huɗu kafin ta buɗe ƙofan


Kallonta yayi tayi ganin Yadda idanunta suka yi jajir suka kumbura,


Tana haɗa ido dashi tayi saurin juyawa ta koma ɗakin shima shigowa yayi ya jingina da ƙofa ya harɗe hannuwansa yana kallonta, sai kuma yace

"kukan me kike yi?"


Bata kula shi ba, ta share hawayen da ya zubo mata,

ƙwafa yayi a hankali yace
"taso ki biyoni"

Da sauri ta kallesa,


Bai sake kallonta ba ya juya har yakai bakin ƙofa ya juyo yace

"zo ki wuce"

A hankali ta miƙe ta biyo bayansa, har ɗakin Maami.


Maami na ganinsu ta haɗe girar sama da ƙasa tana karkaɗa ƙafanta,


Noor kam ta gama tsurewa, ƙirjinta sai dukan uku uku yake.


Da sauri ta ƙaraso ta durƙusa, tana faɗin

"Maami dan Allah kiyi haƙuri wallahi bazan sake ba"


Dariya ce ta kusa kufce wa Maami sai ta
miƙe kawai tana faɗin

"keee tashi ki tsaya"


A hankali ta miƙe ta tsaya tana share hawayenta,


Sai da Maami ta ƙara taku biyu zuwa gabanta kafin ta jawota ta rungume gabaki ɗaya tana murmushi,


Buɗe idonsa yayi a hankali dan yayi zaton marinta Maami zatayi, da kuwa bazai iya jure gani ba.


Da mamaki yake kallon Maami, sai kuma ya sauke wani wawan ajiyar zuciya a ransa yana faɗin

"You Are the best Maami na"


"Me ya saka ki kuka daughter,is this how to welcome your mother in law?"


Ta faɗa tana ɗago ta daga jikinta, kasa cewa komai Noor tayi


A hankali Maami ta miƙa masa hannu tana faɗin "come my boy"


Ƙara sawa ya yi ya shige jikinta, ta haɗa su duka ta rungume ta na shafa sumar kansa

Da ƙyar ya buɗe bakinsa da yayi masa nauyi yace

"thank you Maami naa"


Ɗago kansa tayi tana kallonsa tace

"You know I love you Habibi,so dole ne naso duk abinda ka ke so!,
but gaskiya You both have to apologise to me Dan kun rage min burina akan aurennan"


Da sauri suka haɗa baki wajen faɗin

"We are so sorry Maami"


Dariya Maami tayi tana faɗin
"You Are pardoned "

Sake rungumeta yayi yana ƙara jin tsantsan ƙaunar ta .

Ita dai Noor Satan kallonsa kawai takeyi









Maimoon🤓#
*💖ABNUR💖*

*By* *maimoon*

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

*Page* *14*



Ɗagowa yayi karaf suka haɗa ido da ita, da sauri ta sunkuyar da kanta, sakamakon hararar da ya watsa mata,
miƙewa yayi yana faɗin,

"Maami, You really scared me"ya faɗa yana ɓata fuska, dariya Maami tayi tana faɗin,

"You know Bai kamata na sauƙo yanzu bama, but I have no choise, tunda kun haɗani da Abbu"

Dariya yayi sosai yana faɗin, "i trust Abbu shiyasa right away na faɗa masa, gashi komai ya wuce cikin sauƙi"

Ita dai Noor ta kasa ɗauke idanunta akansa, yadda ya ke dariyan sai ya sa ta shagala sosai da kallon sa, dan bata taɓa ganin ya na farinciki haka ba.


Sake haɗa ido sukayi dashi, ganin ta na kallonsa ya sa shi jan kumatun ta ya na faɗin,

"kallon Fah baby!"


Sai da ta kusa ƙwarewa, saboda yadda abin ya zo mata a bazata, Maami tayi murmushi tana faɗin,


"Wayene ɗazu ya ke cewa 'bana sonta kuma bazan sota ba nikam"

sosa kai ya yi yana murmushi,

"so you take me as a fool, ta ya ma za'ayi ba zaka so wannan kyakkyawar yarinyar ba, she is more like Arab don't you see?

Itadai ta kasa cewa komai, sai kallon sa take da zallar mamaki.

Miƙewa ya yi ya na faɗin,
"Maami, seriously am starving"
ya faɗa ya marairaicewa, Maami ta kalli Noor da ke jikinta har sannan,tace

"daughter your husband is starving" a hankali ta ɗago ta kalleshi, sai ya kashe mata ido, ya shafa cikinsa.

Miƙewa kawai ta yi ta ce"Maami i will arrange the table sai mu ci abinci, kema bakici komai ba"


tana faɗin haka ta juya ta fice a ɗakin, da ido ya bita sai kuma ya shafa kansa ya yi murmushi.

Maami ta ce, "zauna Ina son magana da kai"

Zama ya yi a ƙasa dai dai ƙafafuwan ta, ya kwantar da kansa akan cinyar ta, a hankali ya furta
"ina jinki Maami na"

Hannunta ta sa a kansa ta na masa head massage a hankali,lumshe idonsa ya yi saboda yadda yakejin ɗaɗin yadda takeyi ɗin

A hankali ta ce

"what about her family Habibi,ya zamuyi kenan"

Shiru ya yi sai kuma yace

"Maami i don't know much, but ita zata faɗa mana ai koh?,
Ki bari idan kin huta sai muyi maganan da ita"

Jinjina kai tayi ta na faɗin "Ok I think it will be better"

Sallama tayi ta shigo ɗakin, Maami tace

"daughter sannu fah"

Girgiza kai kawai ta yi tana faɗin "the table is ready Maami."

Bai so ya kalleta ba, but Sam zuciyarsa ta kasa bashi haɗin kai, ɗagowa yayi ya na kallonta suna haɗa ido ya sake galla mata harara da yasa tayi saurin juyawa zata bar ɗakin

Maami ma miƙewa tayi tabi bayanta kafin shima yabi bayansu zuwa dining hall ɗin.

Sai da ta yi serving Maami, sannan ta saka nata ta ja kujera ta zauna, dan tana tsoron ta saka masa, ya gwaleta a gaban Maami

Har ta saka spoon, zata fara ci, ta ji ya ce

"Baby kin manta da Ni ne,I told you am starving"

Da sauri ta ajiye spoon ɗin tana kallonsa,

Maami dai abincinta kawai take ci, bata kula su ba,
Plate ta ɗauka zatayi serving ɗin sa ya yi saurin riƙe hannuwan ta, ya ce "barshi kawai I will eat with you"

Ya faɗa ya na matso da kujerar sa kusa da nata, baki a sake take kallonsa ita iya saninta ko a guri ɗaya basu taɓa cin abinci ba bare plate ɗaya.

Ba tace komai ba ta koma ta zauna, tana tsakuran abincin, shima kaɗan yaci ya ajiye spoon ɗin, itama ajiye nata spoon ɗin tayi, ta tsiyaya masa ruwa, ƙarba yayi ba tare da yace komai ba, sai da yasha kaɗan ya ajiye cup ɗin sannan ya miƙe

"Habibi har ka gama kenan"
Maami ta tambaya itama ta na zarar tissue

"Yeap Ina so zan ɗan fita but I won't be long"

"Okay take care"

Bai ce komai ba ya juya ya fice, ita dai Noor da ido take binsa, ta gagara gane shi wani irin mutum ne, sai ta yi ƙoƙarin gane halinsa sai ya sake canzawa completely.

Landline ɗin kitchen ta Kira akan suzo suyi clearing ɗin table ɗin kafin tabi bayan Maami da ta wuce sama.

ɗakinta ta wuce dan yin sallah, sannan ta bar Maami ta huta, a hankali ta zauna a gefen gado bayan ta idar da sallah, tana tunanin abubuwan da yayi ta yi ɗazu, sai kawai tayi murmushi,

miƙewa tayi taje gaban madubi ta na kallon kanta, wasu hawaye taji sun cicciko idanunta, cikin kukan ta shiga furta

"Abba ina ka tafi ka barmu Ni da Nenne, gashi Nenne ta rasu ta barni Ni kaɗai, Nenne ta rasu ba tare da ka nemi gafarar ta ba, me ya hanaka dawowa garemu Abbana."

Sai kuma ta share hawayenta ta na sake faɗin,

"bana buƙatarka har abada, dan dama bansan soyayyarka ba ban taso naji ɗumin kaba, sannan bansan koda kamannin ka ba,"
Kuka ne ya sarƙe ta ta zube a wajen tana cigaba da kukan gwanin tausayi.


Yasira jin shiru shiru, bata sake jin wani hayaniya ba ya sata fitowa falo, a lokacin taga Sir Zannur yana fita a gidan, da sauri ta ƙara sa ƙofar dining hall ɗin tana leƙawa, ganin Noor da Maami suna cin abinci tare, ba tare da wani alama na tashin hankali ba, ya sata ja da baya, a hankali take ja da baya kafin ta ruga da gudu ta koma ɗakinsu, durƙushewa tayi a wajen tana sakin kuka mai sauti, sai kuma ta shiga sumbatu cikin kukan tana faɗin,
" wallahi tallahi ina sonka, kuma bazan taɓa yarda na rasa ka ba, kai ne rayuwata, Allah ne ya ɗaura min sonka, kuma bazan taɓa haƙura da kai ba, kamar yadda bazan zauna da kai tare da ko wace mace ba, zan iya aikata koma miye ne dan na mallake ka, koda kuwa ta kama da wani ya bar duniyan nan ne"

sai kuma ta share hawayenta tana murmushi ta cigaba da sumbatu kamar zautacciya
"ai nayi zaton zai zo min da sauƙi ne shiyasa na kira Maami na faɗa mata, amma yanzu naga alama babban shiri kake buƙata Sir Zannur wallahi, wallahi, wallahi, duk wanda ya shiga tsakanina da farin cikina kwanan shine ya ƙare ta faɗa tana miƙewa a zabure kamar mahaukaciya.


Su dai su Asabe basu san me ake ciki ba, suna can baya suna wanki, suna hirar su, gabaɗaya basu ma san da zuwan Maami ba bare haukar Yasira.

*******
*_*_
AL RAJWA VILLA'S, AJMAN, DUBAI_*_*


Zaune yake a katafaren falon, ya jingina da kujera, da alama yayi matuƙar zurfi a tunani.

dafa shi da yaji anyi yasa ya ɗago idanunsa da har sun kaɗa sunyi jaa, farin Balarabe ne kyakkyawan gaske mai cikar kamala sosai.


Ammi, cikin harshen larabci, ta soma faɗin,

"me yasa bazaka daina uzura ma kanka ba mijina." kallon farar balarabiyar yayi ba tare da ya ce komai ba ya miƙe tsam ya bar mata falon, wani ɗaki ya shiga inda kana gani kasan na zane zane ne,

ƙara sawa yayi gaban board ɗin zanen, ya ɗau brush ɗaya ya saka a paint, a hankali ya lumshe idanunsa sai kuma ya buɗe ya shiga zane, wasu siraran hawaye na sauƙa a kan fuskarsa,

Ammi ce ta sake shigowa ta tsaya ranta a ɓace ta ke faɗin

"yanzu a tunaninka wannan shine abinda ya dace ka dinga yi koh?, ka zana hoto ɗaya a iya lissafina yafi ɗari, kullum sai ka zana, meyasa bazaka sauwaƙema kanka, nima ka dube Ni ba?"


Ɗagowa yayi, ya kalleta sai kuma yace

"Please nadiya, I need a break"

Daga haka ya fice ya koma ɗakinsa yana rufewa da makulli

Ƙwafa tayi,tana jin zuciyarta na suya, a fusace ta ƙarasa gaban allon ta yi wurgi dashi, tana faɗin,
"na tsaneki, ya zan yi da ke?, kin zame min annoba, kin kasa barina in ji daɗin rayuwata."

sai kuma ta juya a fusace ta bar ɗakin tana huci.

Falonta ta wuce, inda ƴan mata biyu da namiji ɗaya ke zaune suna video game, babbar cikinsu bazata fi 15 ba sai mai bi mata wacce ita ma bazata fi 10 ba namijin kuwa bazai fi 7 ba,

A fusace tace, "farhaana, ku wuce falonku, ku barmin falona bana son hayaniya yanzu"

Da sauri farhaana tace, "Ammi Are You ok, ke da papi ko?"

Bata kulata ba, sai zama da tayi ta riƙe kanta da duka hannuwanta, da sauri farhaana ta kora ƙannen nata suka wuce part ɗin su, tana tunanin sai yaushe papi zai koma kamar kowa?, sai yaushe zai zauna tare da su kamar yadda ko wani uba yake zama da ƴaƴansu?


************

Tunda Maami ta zo, Zannur ya canza mata,

gabaɗaya Noor ta rasa gane ina ya dosa, a gaban Maami kulawa yake bata da har take jin dama har zuciyansa yake mata hakan, amma inaa, bayan idon Maami banda harara babu abinda ke haɗashi da ita, a rashin sanin ta kuwa duk wani shiga da fitanta akan idanunsa takeyi, dan kuwa yana iya yini yana kallon ta a laptop ɗin sa, Taufeeƙ ya tafi Bangaladash saboda wakiltar Zannur akan wasu ayyukansa,hakan yasa bata ganinsa, Asabe da Amina kuwa, kullum cikin ɗebe mata kewa da sakata dariya suke, Yasira ta sake kamar babu komai a zuciyarta, but ita kaɗai ta san gagarumin abinda take shiryawa wanda zai ruguza farin cikin duka ƴan gidan.


Satin Maami biyu ta koma Dubai, da kewan Habibi da kuma Noor, dan kuwa shaƙuwa sosai ya shiga tsakaninsu, ta sake wayar mata da kai akan abubuwa da dama, sannan kafin ta tafi ta sa an nemo mata malamai har biyu na islamiyya da boko tana cigaba da karatunta, a halin yanzu Noor Bata da wata damuwa da ya shige ta Zannur, amma shiɗinma sam bata saka shi a rai ba bare ya hanata walwala.


12 ga watan August dai dai da cikar Noor shekara ɗaya da wata huɗu a gidan, shine ranar da abubuwa suka fara canzawa, ƙaddarar da bazata taɓa mantawa ba, da duk wani wanda yake gidan ya faru wanda yayi sanadiyar ruguza duk wani hasashen farincikin Noor.................



Kuyi haƙuri page ɗin yau yayi kaɗan, bana ɗan jin daɗi ne shiyasa, Amin uzuri


Maimoon#



8 / 8