Author : Maimoon Category : KDP NOVELS
been trying to reach you but baka picking calls ɗinka, I hope everything is fine there? " shiru yayi kafin ya samu ƙarfin halin haɗa kalmomin bakinsa "maami ya Dubai?" "lfy ƙalau habibi ina Noor" shiru yayi ya kasa cewa komai ,shirun da taji yayi yawa ya sata sake faɗin "Habibi are you there? "Umm...Maami" "are you okay my boy? mai yake faruwa me kake ɓoyemin? I hope you are not trying to hide anything!"
"maami babu komai fah don't you believe me"
"na yadda da kai mana my boy, to yanzu ina Noor? it has been long tunda mukayi magana da ita, kai mata wayan "
A ɗan daburce yace "umm wai Noor ..in kai mata wayan? to ai tayi bacci,batajin daɗine shine sai ta kwanta"
"ok shikenan maybe next time Allah ya sauwaƙe ka kira abbun ka, yace yakiraka baka picking " "a hankali yace "insha Allah Maami" daga haka yayi hanging Kiran yana sauƙe ajiyar zuciya.
Da sauri kamal ya shigo gidan, hannunsa riƙeda jarida wanda hotonta ke jiki ɓaro ɓaro ,ita kaɗai ya samu a tsakar gidan tana wanke kwanukan da suka ɓata da safe ,yanayin da taga ya shigo ya sata saurin ɗauraye hannunta,
tana ƙarasowa tsakar gidan dai dai umma ma ta fito daga ɗakin ta, tana faɗin "Noor Nikam Ina kikaga na ajiye goron da ke cikin ledannan ne?
tsayawa tayi tana kallonsu yadda sukayi cirko cirko a tsakar gidan. "Lafiya?" Ta tambaya tana kallon Noor "umma nima wallahi bansani ba, haka naga ya shigo kamar ba lafiya ,umma ta karkata akalar tambayan nata ga kamal da ke tsaye yana kallonsu,
miƙa mata jaridar yayi yana faɗin, Abdul ne ya shiga cikin gari ɗazu, shine nace masa ya siyomin jarida dan na karanta, shine fah kawai naga hoton Noor ajiki ,Umma ta karɓa tana dubawa, sai kuma tace to me aka rubuta ajiki? ko yan uwanta suke nemanta? ai dama dole su nemeta!! "
Kamal kallonta kawai yake ganin tana ƙoƙarin wucewa ɗaki ya sa yace"Noor!" Ta juyo Amma Bata dawo ba, a hankali yace "bakya tunanin 'yan uwanki suna cikin wani hali na rashin ganinki? kuma haryanzu baki ga buƙatar ki sanar damu komai ba!?"
shiru tayi ba tare da tace komai ba, a hankali umma ta ƙaraso inda take ta dafata tace"Noor bana miki kallon ƙasa da abinda na haifa, bakya tunanin idan ke 'ya tace kika bar gida irin haka, hankalin dole ya tashi to bare mahaifiyar ki, Yakamata ki faɗa mana abinda ya rabo ki da gida Noor, ko kina tunanin bamu kai musan damuwarki bane ?
da sauri ta girgiza mata kai tana faɗin"umma dan Allah karkice haka, wallahi kun kai kuma har kunfi haka a gurina"ta share hawayen da ya zubo mata tace "insha Allah na muku alƙawari yau zaku san komai game dani, amma ina neman alfarmarku, ku bari zuwa baba ya dawo zuwa dare, ina so na baku labarina a gaban sa "umma ta yi murmushi tana faɗin Allah ya kaimu Allah ya muku albarka "suka amsa da ameen
Maimoon#
*💖*ABNUR**💖
*By* *maimoon* 🤓
*Elegant* *online* *writers* 📚📖
*Free* *book*
*Page* *4*
Kamar yadda ta faɗa kuwa, hakan ce ta kasance, bayan sallar isha duk suka taru a ɗakin Baba ,kasancewar Umma ta sanar masa komai ,
Kamal na shigowa ,Umma ta aikasa ya kira Noor,tunda ya zo ya kirata take jin faɗuwar gaba,shi kuwa dama bai tsayaba, yana kiranta yayi juyawarsa ya koma ɗakin,but zuciyarsa na cike da ɗokin jin labarin nata.
Hijab ta sanya, tana karanto addu'a a ƙasan ranta ,tasan yanayin da take ciki yana da nasaba da tuno labarinta da zatayi.
a hankali ta ƙarasa ɗakin kanta a ƙasa ,sallama tayi duk suka amsa suna kallon ƙofar ,a hankali ta ɗaga labulen ɗakin ta shiga ,can nesa kaɗan da su ta zauna tana fuskantarsu gabaki ɗaya, a hankali ta gaishe da Baba,ya amsa da fara'a yana tambayar lafiyanta ,ta amsa da ladabi ,kana Baba ya ƙara da cewa
"Noor naji komai a bakin Aisha, tacemin yau Zaki faɗamana daga inda kika fito, da kuma dalilin fitowar taki ,naji daɗi matuƙa da kikayi wannan tunanin dan yana da kyau musan hakan ,saboda haka muna sauraranki kuma inaso ki faɗamana iya gaskiyarki".
A hankali Kamal ya gyara zamansa yana kallonta ,Umma ma kallonta kawai takeyi,sai da ta share guntun hawayen idanunta, kafin ta fara da faɗin......
WAIWAYE (mafarin labarin)
_Garin_ _BAULAWA_ _dake_ _ƙarƙashin_ _jihar_ __Kaduna_Nigeria_
Yarinya ce yar kimanin Shekaru 16 ,doguwa ce sosai ,fara tass kamar balarabiya, fararen ƙafafuwan ta da babu takalmi take tsalle dasu, tana caɓalasu a cikin ruwan daya kwanta a ƙasan saboda ruwan saman da ake kan yi a garin,
Gaba ɗaya ta gama jiƙa jikinta,har gashin kanta da yake tare waje guda ta cureshi ,wani irin farin ciki take wanda fuskarta ya kasa ɓoyewa ,
Yara ne sun kai su shida a zagaye da ita,suna jiƙa jikinsu suna wasa ,ta biye musu kamar wata sa'ar su ,
duk wanda yake garin ya kwana da sanin wannan hali nata,tana matuƙar son ruwan sama, hakan yasa ko a ina take idan har ana ruwa to akanta yake ƙarewa, kuma abin mamakin shine ko irin zazzaɓin nan na mura batayi idan ta shiga ruwan.
Malaman makarantarsu kuwa sunsha dukanta, akan ana aji tana shiga ruwa, amma inaaa gobe ma zata koma har sun haƙora sun ƙyaleta .
Ɗaga kanta tayi sama ganin ruwan na shirin ɗaukewa ,ta ɓata fuska sauran yayyafin da ke sauƙa yana sauƙa mata a samar kyakkyawar fuskarta ,a hankali ta kama ƙasan rigarta tana matse ruwan, sannan ta nufi ƙasan bishiyan neem ɗin dake kusa da su ta zaro takalmanta ,ta sanya su ba tare da ta kula yaran da suke cigaba da wasansu,da ruwan caɓalin da ya kwanta ba kawai tayi hanyar gida.
A daidai zauren ɗan ƙaramin gidan ta tsaya tana sake matse kayan jikinta ,sai kuma tayi sallama tana ƙarasawa tsakar gidan ,babu kowa hakan ya bata daman saurin faɗawa ɗakinta ta kwaɓe jiƙaƙƙun kayanta,ta canza wasu ,ta buɗe jakarta ta ciro littafan makarantarta ta zauna ta naɗe ƙafafu ta ajiyeshi a gefe,
Jin alamar mutum na zuwa kusa da ɗakinnata ya sata saurin buɗewa ta fara karantawa ,ɗaga labulen Nenne tayi tana kallonta,sai kawai tayi murmushi tana faɗin
"Noor!"
Da sauri ta amsa "na'am Nenne" Nenne ta ƙaraso cikin ɗakin tace "ina jiƙaƙƙun kayan da kika jiƙa" shiru tayi tana kallon Nenne ta ƙasan ido ,a ranta tana addu'ar Allah yasa kar tayi mata faɗa,
Ai kuwa kamar Nenne tasan miye a ranta ta soma faɗin "wai Noor meyasa baki san ciwon kanki bane sam,mutum bayi da aiki sai shiga ruwan sama, bakya tsoron sanyi ya kamaki?"
Ita dai bata ce komai ba, sai ma wasa da ta shiga yi da takaddar hannunta ,idanunta na cika da hawaye ,dan Allah na gani batason faɗa sam ,tsorata ta yakeyi ,
Tsagaita wa Nenne tayi da faɗan,sanin halin ƴartata ta ƙarasa kusa da ida tana jawota jikinta,ai kuwa kamar jira take ta rungume ta ta soma kuka, shiru Nenne tayi sai kuma tace "Noor,bawai Ina miki faɗa bane dan bana sonki Ah ah ina miki faɗane saboda babu wanda ya kaini sonki, a yanzu ina tare dake ,watarana ba na nan Noor,banaso ki sha wahalan rayuwa ko bayan raina ,shiyasa nakeso ki san ciwon kanki tun yanzu,Noor ko babu komai watarana aure zakiyi ki tafi gidanki ,koh haka zaki je ki masa idan kunyi auren ?" ta tambaya tana murmushi jin bata amsa ba sai ajiyar zuciya da take sauƙewa ,yasa Nenne cigaba da magananta dan tasan ba amsawar zatayi ba ,
"Kina jina Noor"Nenne ta faɗa tana shafa kanta ,girgiza mata kai tayi ,Nenne tace"Noor ko babu aure Akwai mutuwa ,banaso na rigaki mutuwa ki shiga wani haali,da sauri ta ɗago tana rufe mata baki take wasu hawayen suka sauko mata ,ta sake rungume Nenne tana faɗin "Nenne bazaki barni ba, idan har kika mutu nidai binki zanyi,kuma Ni bazan yi aureba har abada".
Murmushi kawai Nenne tayi tace "to shikenan naji ,yanzu ki cigaba da karatunki bari naje wani unguwa yanzu na dawo" ,da sauri tace Nenne zan biki ,nan take Nenne ta haɗe rai tace bazaki bini ba kuma idan kika kuskura kika fita a gidannan kafin na dawo zan saɓa miki" ,a hankali ta gyaɗa kai tana faɗin "insha Allahu Nenne "
Nenne ta fice a ɗakin ,ita kuma ta cigaba da karatun ta tana tunanin," ina Nenne take zuwa kwana biyunnan da bataso ta sani?"
Sai da ta tabbatar Nenne ta bar gidan sannan ta rufe littafin, ta mayar jakanta, ta ɗauko jiƙaƙƙen kayan taje ta shanya ,sannan ta dawo tayi kwanciyar ta a ɗan ƙaramin gadonta ,tana sake tunanin maganganun Nenne,
Ita bazata yi aureba har abada, saboda bazata taɓa yadda ,wani yayi mata abinda mahaifinta yayi ma Nenne ba,kowa yasan mahaifinsa amma banda ita,ko kamanninsa bata saniba, sai sunansa da take anfani dashi ,alhalin yana raye ,yana birni yana cigaba da rayuwarsa ,kamar bai san da su ba.
_ABUJA_ _NIGERIA_
Murza steery kawai yake, hankalinsa gabaki ɗaya yana kan tuƙin da yakeyi ,a hankali yayi horn a gaban wani babban Duplex house,mai gadi ya wangale masa gate ɗin yana ɗaga masa hannu,bai bi ta kanshi ba, sai ma cusa motar da yayi cikin gidan Yana driving a hankali ,fuskarsa ɗauke da wata ƙasaitacciyar murmushi,tafiya kamar na minti takwas a cikin gidan, ya kaisa parking space ɗin da aka adana dan motocinsa .
A hankali ya ƙarasa ciki yayi parking, sannan ta fito daga motar, wani remote ya danna, nan take motar ta ɗagu sama ta jeru a cikin ƴan uwanta da suke hawa hawa ,anan take wata motar daban tayi replacing ɗin waccar,
body guards ɗinsa su shida ya kalla yadda suka tsaya suna jiran umurni,bai ce musu komai ba, ya nufi main entrance ɗin gidan, yana taɓa bluetooth ɗin kunnensa ,a hankali cikin murya mai amo ya fara faɗin "then they are all fired" ɗan shiru yayi yana cigaba da tafiyarsa, alamar yana sauraron mai maganan sai kuma yayi ɗan murmushi yana faɗin,"then I will meet you in 3 hours time"
daga nan ya kashe wayarsa ,daidai ya iso ƙofar da zai sada shi da main hall na gidan ,security ɗin ƙofar ya sanya sannan ya ƙara sa cikin parlorn yana zama a kan kujera , turarensa na _SHUMUKH_ shi ya kaima su Amina da ke kitchen saƙon dawowarsa, dan tuni ya karaɗe ko ina ,
da sauri Yasira ta fice daga kitchen ɗin ,kasancewar ita ce in charge na kitchen ɗin ,ɗan nesa dashi ta tsuguna tace " Sir lunch is ready , should I serve you!?" bai ɗago daga danna wayar da yakeyi ba, ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa Yana faɗin "maybe later" da kallo kawai ta bisa .
wani ɗaki ya shiga ya jingina da bangon ɗakin yana bin ɗakin da kallo ,cameras ne kala kala ,da kuma hotuna iri iri na nature da na mutane iri iri ,murmushi kawai yayi ya nufi Camera ɗaya ya ɗauka, sannan ya ƙarasa balcony ɗin ya kai Camera ɗin idonsa, sannan ya ɗauki entire area ɗin a hoto ,yana jin matuƙar farinciki,
ɗaukan hoto is his passion,he is very proud to be an explorer ,tunanin inda zai je next domin ɗaukan hotunansa yakeyi ,yana buƙatar zuwa guri that is full of nature, but still local,
Yana son capturing al'adu da kuma sabbin abubuwa that's why yake neman inda zaije a cikin Nigeria ya gaji da capturing ƙasashe ,so yake ya fito da beauty na ƙasarsa ,ya kamata yayi research yaga ina zaije tourism this time a cikin Nigeria,
fita yayi a ɗakin ya nufi ɗakinsa, ya zauna gefen gado yana dialling Numbern Maami, ringing biyu taɗaga tana faɗin "Habibi" a hankali kuma a shagwaɓe yace "Maaami " yadda yayi maganar yasa ta faɗin "and now ,me kake so kuma this time!?",wani murmushi yayi dan yasan Maami ta gama ganesa ,ya shafa yalwataccen sumarsa, da bayida maraba da ta asalin larabawan Dubai, a hankali yace"not much Maami ,kawai suggestion ɗinki nake nema akan wani abu"
tace "ok am all ears Habibi, hope dai bawani abu bane ya dameka ko" murmushin ya kuma yi yana lumshe idanunsa sannan yace "not at all ,kawai dai so nake nayi exploring a ƙasata ,Ina so naje tourism somewhere very local but full of nature ,shine nace bana tambayi suggestion ɗin ki ,i know, no one will know better than you do"
wani murmushi Maami tayi da har yana iya jiwowa tace " ok then why not Kaduna state well the state is full of nature just the way you like it" shiru yayi sai kuma yace " amma kin manta nace miki local ,Kaduna ai is too polished for what I want"
dariya Maami tayi tana faɗin "and what about villages ɗin dake under Kaduna" ɗan shiru yayi sai kuma yace "kamar wanne kenan?"
"Wannan kuma you have to research to find out " "okay Maami ,Abbu fah ?" "Abbu yaje finalizing deals da wasu companies a ukraine " "okay then I guess we will talk later" "okay Habibi take care" a hankali yace "sure" sannan ya katse wayar ,ajiyeta yayi ya jawo laptop ɗinsa ya shiga yin research akan Kaduna state ,
_BAULAWA_ ya sake maimaita sunan ,a hankali yayi murmushi yace "i guess I already got it!"
Wayansa ya ɗauka yayi dialing Numbern personal assistant ɗinsa , Yana ɗagawa yace masa "we are going to Kaduna by Wednesday ,so prepare the needful " "yes Sir " taufeeƙ ya amsa ,kashe wayar yayi yana faɗawa kan gadon a hankali ya furta"its going to explore, Allah yasa na samu abinda nakeso a wannan ƙauyen" ,sai kuma ya ƙara murmushi yanajin kamar wani al'amari mai girma na tunkarosa
Is it really going to explore!?me zai faru a ƙauyen BAULAWA ,zai samu abinda yake so kuwa !?🤓the story has just begun🤝
*ABNUR*
*By* *maimoon* 🤓
*Elegant* *online* *writers* 📚📖
*Free* *book*
*Page* *5*
*Wednesday*
*Abuja Nigeria*
Ƙarfe 7:30 dai dai, ya fito daga Gym ɗin dake cikin gidan ,gaba ɗaya ya gama haɗa zufa,Gym wears ne a jikinsa na kamfanin Nike,Wanda ya karɓesa matuƙa kamar dan kwalliya ya sanyasu, a tsanake yake haura steps ɗin duk da kuwa sauri ya keyi ,dan yau zai wuce Kaduna,
Amina,Asabe,da kuma,Yasira da suka ɗan buɗe ƙofar kitchen ɗin ,suka bisa da kallon, ajiyar zuciya suka sauƙe a tare,ganin ya gama haurawa,
Amina tace"wato kuɗi yayi ne Wallahi, shidai Sir a rayuwar sa ba shida matsalar komai,na farko ga kyau,ga kuɗi, ga iya shiga mai kyau,ke Ni komai yasa gani nake kawai dan kwalliya ya sa su" Asabe ta karɓe tana faɗin "hmm! kawai mata ta rage masa Wallahi shi ke nan ya cika cif-cif" Yasira tace"taɓ Sir kam ko zaiyi aure ba yanzu ba wallahi" Amina ta amshe "to sannu Maami!, kika sani?,wataƙila ma munkusa shan biki ko ba haka ba Asabe?" ta faɗa tana tafawa da Asabe , "aikuwa wallahi idan zaiyi ma ba sani zamuyi ba sai dai muji guɗar ƴan kawo amarya" Asabe ta faɗa tana ƙarasa wanke kwanukan dake cikin sink ɗin ,
Yasira dai bata sake cewa komai ba ta fice a kitchen ɗin tana wani ɓata rai ,Asabe ta sake tuntsirewa da dariya tana faɗin"kai kaji wahalalliya,wallahi wahala ce Bata isheta ba" Amina tayi ƙwafa tana faɗin "atoh ai ita taga zata iya" suka cigaba da wanke wanke suna taɓa hira.
Wanka ya fito ,a gaggauce ya shirya cikin riga da wando na kamfanin _LOUIS_ _VUITTON_ sai da ya gyara sumarsa yanda ya keso,sannan ya gyara gemu da sajensa wanda duk wanda yasan larabawan Dubai yasan yadda Gemu da sajansu yake,sai da ya gama ɓata lokaci a gyaran sannan ya ɗau perfume ɗinsa na _SHUMUKH_ ya feshe jikinsa da shi ,wani button ya danna ,wani drawer ya buɗe wanda takalmansa suke jere ,na different companies _,WHITE ADRIAN ITALIAN SHOES_ ya zaro ya sanya a ƙafafunsa ,ya ƙara danna wani button ɗin wani mini drawer ya buɗe ,Agogo ya cire guda ɗaya ya sanya sannan ya kwashi wayoyinsa da jakan laptop ɗinsa ya fice a ɗakin,
Da sauri bodyguard ɗinsa guda ɗaya ya ƙaraso ya karɓi kayan hannunsa yana gaishesa, Taufeeƙ dake tsaye ya ƙaraso shima tare da faɗin"morning Sir". "morning "ya amsa a taƙaice ,buɗe masa mota yayi ya shiga baya ,shikuma ya shiga gaba,ɗaya daga cikin bodyguard ɗin ya shiga mazaunin driver ,sauran kuma suka shiga wata mota daban ,suka fice a gidan,
Amina,da Asabe dake leƙen window suka sauƙe Amina tana faɗin ,"to sai kuma sanda muka ganshi, Aljanun sun motsa " Asabe ta ce"kee bari a jiki babu ruwana wallahi" Amina tace "ke ma ai kinsani irin wannan fitar da yayi tunda kika ga Sir Taufeeƙ ,to zasu je yawon ɗauke ɗauke ne ,ai dama tunda naga Sir Taufeeƙ ya zo jiya ya haɗa abubuwan ɗaukan hoto da akwati da komai Na Sir ,nasan to sai kuma mun gansu"
Asabe tace "to ai hutareren mu " Amina tace "wallahi Fah " suka koma kitchen, dan dama tun sauƙowar sa sukaji shine yana fita suka fito su leƙa .
Kasancewar tsakanin Abuja da Kaduna ,ba wani nisa bane ya sa su tafiyan da mota, ƙarfe biyu saura suna cikin Kaduna, hotel suka wuce, wanda dama Taufeeƙ ya gama shirya komai ,sai da suka tsaya sukayi sallah ,sannan suka ƙarasa , a hankali ya juyo ya kalli Taufeeƙ yace"tomorrow by 8 "zamu tafi ,make sure by 7 waɗancan sun koma Abuja ,"
a ladabce Taufeeƙ yace "Sir your security matters, da dai anje da su for security purposes".
"just do as are told mr" ya faɗa ba tare da ya juyoba ,
"pardon Sir ,your wish is always my command , za'a yi kamar yadda kace"
bai sake cewa komai ba har suka iso ƙofar ɗakin nasa ,da sauri Taufeeƙ ya sa katin ,ƙofan ta buɗe ,sai da ya tabbatar ya gama masa duk wani abun da zai buƙata ,kafin ya bar ɗakin ,ya nufi nashi ɗakin