Chapter 6 Reading ABNUR Sirrin Hasken Soyayya By maimoon HN Novels

ABNUR Sirrin Hasken Soyayya By maimoon

Author :  Maimoon Category :  KDP NOVELS

Chapter   6 / 8

15K to 18K   out of 24K words

gaishe shi, a taƙaice ya amsa musu yayi shigewar sa ciki,



Ganin basu lura da ita ba yasa Taufeeƙ ƙarasawa ya buɗe mata ƙofan yana murmushi dan yadda yaganta duk a tsorace.



Ƙafafuwan ta zuro a hankali,waɗanda suke cikin flat shoes Wanda ya kawo mata tare da kayan jikinta,a hankali ta ƙarasa fitowa tana kallon ƙatoton mansion ɗin da aka kawota, a hankali take bin bayan Taufeeƙ ɗin har cikin main parlour na gidan,inda bodyguards suka riga suka shigo musu da kayayyakin su.




Da gudu Asabe da Amina suka fito a kitchen ɗin suna rige rigen ƙarasowa wajen Taufeeƙ,kallonsu yayi yana murmushi yace

" kukuma Fah "

da sauri Amina tace

" Sir Taufeeƙ yanaga kun dawo da wuri, Ni wallahi ban ma san ran dawowan ku nan da wata uku Bama wallahi"

ta faɗa tana kallon Noor ta ke tsaye kawai tana kallonsu"

"Sai kuma kika ganmu koh"
Taufeeƙ ya faɗa yana hawa da kayan Sir Zannur steps ɗin.

sai da ya kai ya dawo ya ɗau sauran sannan ya kalli Asabe da Amina yace

"ga baƙuwa,ku gyara mata ɗaki a sama, anan zata zauna and ku kula da ita sosai fah, idan ba haka ba ku da Sir Ni dai babu ruwana"

ya faɗa da sigar tsokana yana haurawa saman,

Har rige rigen ƙarasowa wajenta sukeyi, Asabe tace "sannunki da zuwa baƙuwar Sir" ta faɗa tana murmushi.

*💖ABNUR💖*

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

*Page* *10*


Ita dai kallon su kawai takeyi,ba tare da tace uffan ba,
kallon juna suka yi sannan suka maida kallonsu gareta, Amina tace "Ni sunana Amina,wannan kuma......"



"Asabe". Asabe ta faɗa tana tarar numfashin Amina.

Murmushi kawai tayi musu ba tace komai ba.


Taufeeƙ da ke sauƙowa ya kallesu yace

"wai kun san waye ce ita kuwa kuka ajiyeta a tsaye, nace ku kaita ɗakin sama, baku Kaita ba kun tsaya kuna cika ta da surutu koh"

ya faɗa yana ƙarasa sauƙowa



"Sir Taufeeƙ dan Allah a ina kuka samu wannan kyakkyawar yarinyar son kowa ƙin wanda ya rasa,wallahi har ta shiga raina"

cewar Amina tana murmushi.



"Matar Sir Zannur ce"


ya faɗa a taƙaice yana nufan ƙofan falon dan dai baya son tambayoyi,
dan ya riga ya san halin su Asabe.

a ranshi yana ayyana irin zaman da za'a yi a cikin gidan tsakanin Sir da kuma Madam ɗin sa.


"Matar Sir ce", maganar daya doki ƙwaƙwalwar Yasira kenan wacce ke fitowa daga kitchen,dan yiwa su Amina magana suje su cigaba da aikinsu,

kasa ƙarasowa falon tayi daga bakin kitchen ɗin ta ƙura ma Noor idanu, wacce ke tsaye duk tsayuwar ma ta isheta.


Bata gama tantance
abinda kunnuwanta suka jiyo mata ba taji Muryar su Asabe dake ta murna kamar waɗanda aka ma bushara da aikin hajji



Asabe na faɗin "Sannu da zuwa Madam, wai da gaske ke matar Sir ce,ya ilahi,ina zansa kaina"

ta faɗa tana sake
kwashewa da dariya kamar taɓaɓɓiya,


Duk yadda take jin zuciyarta sai da ta ɗan murmusa ba tare da ta shirya Ba.

Amina tace"mun shiga uku, matar gida muka bari a tsaye, Asabe bazaki nuna mata ɗakin ba" ta faɗa cikin rashin sanin abinyi itama murnar ta kasa barinta.


A hankali tace"Sunana Noor, kuma ina so in yi sallah, a ina zanyi"

ta faɗa tana murmushi


Da sauri Dukansu suka fara rige rigen yi mata jagora zuwa ɗakinta,

tsaf ɗakin yake, hakan yasa suka barta tayi sallah,suka sauƙo suna cigaba da hirar abin,


Asabe tace"anya Sir Taufeeƙ ba wasa yake mana ba kuwa, ya za'a yi Sir yayi aure babu sanarwa babu komai"


Amina tace wallahi kamar kin shiga zuciyata,ko Maami ma bazata yarda da wannan auren ba".


"Nima haka nake gani" cewar Asabe suna ƙara sa sauƙo wa daga matakalan.


Hango Yasira da sukayi yasa suka canza hirar


Asabe ta ɗaga murya tana faɗin"wallahi Fah matar Sir kyakkyawa, daga gani zatayi hankali"

Amina ta karɓe "kuma wallahi ba ƙaramin dacewa sukayi ba, Allah dai ya barsu tare ya tsole idon maƙiya"

ta faɗa tana kallon gefe.

Har suka wuce ta bata ce musu komai ba, zuciyarta banda tafasa babu abinda takeyi.

"ya za'a kayi min haka?, ya za'a yi ka auri wata ba Ni ba?, kai kaɗai na tanadawa kaina, kai nawa ne Ni kaɗai,
dan Ni kaɗai aka halicceka Sir Zannur, bazan taɓa yarda ka zauna da kowace mace idan ba Ni ba,sai dai bayan raina" ta ƙara sa faɗa kamar mai shirin zarewa.


Juyawa tayi a fusace ta wuce su Amina a kitchen ta bi ta ƙofar baya ta tafi ɓangaren su, tana tunanin yadda zata ɓullo ma lamarin idan har ya kasance gaskiya ne.



Asabe da Amina suka bita da kallo sannan suka ƙyalƙyale da dariya ƙasa ƙasa suna faɗin "a sauƙa lafiya".



Tunda suka fita suka barta, ta tsaya tana ƙarema ɗakin kallo,
nan ɗin ɗakin ta ne kenan?, ita ce yau zatayi rayuwa a nan ba tare da Nennen ta ba, tabbas mutuwa bata barin wani dan wani yaji daɗi,idan ba haka ba da Nenne bazata mutu ta barta ba,

hawayen idonta ta share sannan ta juya ta nufi ƙofan da ta gani wanda tafi tunanin shine banɗaki, shiga tayi ta tsaya tana kallon toilet ɗin.
yafi na hotel ɗin da suka sauƙa a Kaduna kyau da girma da tsaruwa nesa ba kusa ba,
bata wani sha wahalan yin amfani da toilet ɗinba kasancewar ta gane tun na hotel ɗin hotel ɗin, sai da ta yi wanka ta wanke tsefeffen gashin kanta da shampoos ɗin da ta gani a toilet ɗin,sannan ta ɗauro alwala, sai kuma ta tsaya tana tunanin kayan da zata saka,

bathtub ta gani kala kala a banɗakin,haka kawai taji a jikinta shi ake sakawa idan anyi wanka, murmushi tayi ta jawo guda ɗaya mai kalar sky blue tana kallo,

sai da ta saka sannan ta sake jiƙaƙƙen gashin kanta a bayanta, ya sauƙa har kusan ƙugunta duk da a jiƙe yake.



A hankali ta buɗe ƙofan banɗakin ta fito tana rarraba idanu,
da sauri ta ƙara sa wajen ƙofa ta murza key tana sauƙe ajiyar zuciya,a fili ta furta


"hmm kawai sai wani ya shigo ya ganni a haka ai da kunya ta kasheni"

sake kallon jikinta tayi sai ta rufe fuskarta da hannunta tana ɗan dariya,



Duk abinda takeyi yana zaune yana kallonta, a cikin laptop ɗin sa, da yayi connecting da duka cctv cameras na gidan,murmushi kawai yayi ganin yadda ta rufe fuskarta a fili ya furta

"silly girl"

Amma a cikin ransa yana mamakin kyaun yarinyar ga ta da gashi abinda yake matuƙar so a wajen mace,
sai dai shi baya ganin har gaban abada zai taɓa iya zaman aure da ita.


rufe laptop ɗin yayi ya miƙe yana kai komo a ɗakin, babban damuwar sa a yanzu bai wuce yadda zai sanar da Maami da Abbu zancennan ba,

waya ya ɗauka yayi dialling Numbern Taufeeƙ Yana ɗagawa yace

" ina so zuwa gobe ka kai yarinyar can ka yi mata siyayyan kayan anfaninta and banaso ta nemi komai ta rasa i hope you understand"


daga ɗayan ɓangaren Taufeeƙ ya amsa da

"Yes Sir"

katse wayan yayi sannan yayi cilli dashi a kan gado yana kai hannunsa ya ya mutsa lallausan yalwataccen sumarsa, a hankali ya furta

"everything will be alright soon".

juyawa yayi ya fice a ɗakin gaba ɗaya ba tare da ya ɗau wayan ba.


Knocking ɗin da taji a ƙofar ɗakin ya sata saurin mayar da kayan da ta cire, ta ƙara sa bakin ƙofan tana faɗin

"waye ne?"

jin shiru ya sa ta ƙara sawa, ta murda ƙofan ta buɗe tana kallon wanda ke bakin ƙofar,

kallon kallo suka shigayi kafin tayi murmushi tana faɗin

"bismilla"

daga haka ta koma ciki

Sai da Yasira ta haɗiye wani mugun yawu kafin ta yi ƙarfin halin ƙarasawa ciki tana ƙoƙarin yin abin da ya kawota ba tare da ta kwafsa ba.


Da murmushi ta dube ta tana faɗin

"sannunki da zuwa, Sunana Yasira ni ce in charge na kitchen ɗin gidan nan gaba ɗaya"

ta ƙarasa tana ƙura ma Noor ɗin ido


A hankali tace

"nagode".

ɗan shiru Yasira tayi sai kuma tace ko zan iya sanin ke kuma wacece ta faɗa tana sake kallonta.


"Bakida hurumin sannin wace ce ita!"

da sauri dukkansu suka juya suna kallon mai magana,
da mamakin Noor ke kallonsa yayinda Yasira cikin sauri ta shiga faɗin

"Sorry Sir i just came to welcome her,am sorry Sir"

ta faɗa tana raba idanu
Bai ce mata komai ba yaƙarasa cikin ɗakin,


zuwa lokacin ƙamshin turarensa na SHUMUKH ya gama cika ɗakin,

fuskarsa babu yabo babu fallasa yace


"ina so ki haɗa min duka staff ɗin da ke cikin gidannan by 6 o'clock",

"Okay Sir" ta faɗa da sauri.

"You may leave" ya faɗa ba tare ta ya sake kallon inda take ba.


Da sauri ta fice a ɗakin tana waiwayensa.



Sunkuyar da kanta Noor tayi tana wasa da yatsunta, zuciyar ta na wani irin bugu,
dan gaba ɗaya ya canza mata daga wanda ta sani a da.



Taku biyu ya ƙara yana kallonta yace

" ƙarfe 6 yayi miki a falon ƙasa, i hope you understand!?.


Girgiza kai kawai tayi batare da tace komai ba.


Buɗe ƙofar da akayi ya sa duk suka juya suna kallon Asabe da ke ƙoƙarin shigowa, tana turo ƙaramin table ɗin da aka jera abubuwa daban daban akai,
wani burki taci tana riƙe handle ɗin, tayan jikin table ɗin suka tsaya cak akan tiles ɗin da sauri ta juya tana dariya ƙasa ƙasa tare da faɗin
"Sorry Sir",ai bansan kana tare da Madam ba".



daga haka ta juya da sauri ta bar ɗakin, kallo yabi ƙofar da shi sai kuma yayi ƙwafa yana juya wa shima ya fice a ɗakin, ya barta a tsaye tana binsu duka da kallo


Da gudu Asabe ta nufi kitchen tana dariya,Amina dake goge plates tace

"kee Asabe lafiyarki "

"Bari kawai Amina Nikam ai yau naga yadda ake love"

ta faɗa tana satan kallon Yasira da ke duba time table ɗin girkin satin.


Amina ta ajiye plate ɗin hannunta tana faɗin

"fisabilillahi fah, a Ina kika gani"


"Hmm ke dai bari wallahi, dana je kaima Madam abinci bansaniba ashe Sir yana ɗakin kekam dai abin ba'a magana "


Ta faɗa tana ƙoƙarin ƙular da Yasira ai kuwa haƙar ta, ta cimma ruwa, dan kuwa dangwarar da schedules ɗin girkin tayi, ta bar kicin ɗin tana danne kukan da ke shirin zuwa mata.


Amina tace tana ƙoƙarin kwaikwayon Muryar Yasira
"Wallahi Sir bazai yi aure yanzu ba"

duk suka tuntsire da dariya.



Ƙarfe 5:00 dai dai ya shigo ɗakin nata,
ganin bai ganta a ciki ba yayi tunanin tana banɗaki,

a jiye ledar hannunsa yayi sannan ya zaro takadda a aljihunsa ya ɗaura akan ledan ya juya ya fice a ɗakin.



Tunda ta fito take kallon babbar ledan dake kan gadon,


ƙarasowa tayi ta na kallon farar takaddar da aka linke ta tsaf, a hankali ta ɗau takaddar tana warwarewa,


"Don't make the mistake Of making me wait,make sure 6 ta miki a ƙasa"


Ƙara maimaita karantawa tayi sai kuma ta jawo babban ledan tana kallo kayan dake ciki.



Dress ɗin take kallo babu ko ƙiftawa, a hankali ta kalli agogon ɗakin ƙarfe 5:31

Da sauri ta warware kayan tana ƙoƙarin sanya su,doguwar rigace irin ta princesses ɗin nan blue colour,
sai da ta saka kayan sannan ta warware gashinta da ya riga ya bushe, ta sake naɗeshi kamar yadda ta saba, sannan ta ɗau gyalen kayan mai ɗan girma amma ba sosai ba ta sanya,

kallon kanta ta tsaya yi ganin bata da maraba da princess ɗin da take gani a littafan makarantar ta murmushi tayi, nan take hawaye ya kawo idanunta, tayi iya ƙoƙarin ta na ganin ta mayar da su,


a hankali ta zura flat shoes ɗinta tana fitowa ɗakin da sauri, ganin six ɗin ya kusa,

a hankali take sauƙowa daga kan steps ɗin idanunta nakan inda take sanya ƙafafuwan ta, dress ɗin ta ne ya harɗe ta da sauri tayi baya tana rutse idanunta,

jinta a jikin mutum yasa tayi saurin buɗe idanunta tana kallonsa, yayinda ƙamshin turarensa na _SHUMUKH_ ya ke mata maraba a duk ƙofofin hancinta.


Da sauri ta miƙe daga jikinsa tana kallon dukkan ma'aikatan gidan da suka zubo musu idanu suna kallonsu,

wani kunya taji ya rufe ta, shikam ƙara tsumewa yayi, ba tare da ya sake kallonta ba ya ƙara sa sauƙa a matakalan, itama binsa tayi a baya tana tattare dress ɗinta,


Ma'aikatan ne suka shiga gaishesa cikin matuƙar girmamawa,


Asabe da Amina da gulma ya kusa kashe su kasa jurewa sukayi sai da suka yi ƙus ƙus ɗinsu,suna dariya ƙasa ƙasa.


Yasira kam fashe wa ne kaɗai batayi ba amma ta kumbura tayi suntum, sai ƙwafa takeyi.



A hankali ta ƙara so ta tsaya a gefensa tana kallonsa,

"have a seat"


ya faɗa ba tare da ya kalleta ba, a hankali ta zauna a kujeran dake kusa da nashi tana wasa da hannunta,


da sauri duk ma'aikatan suka shiga gaisheta, murmushi kawai takeyi amma ta kasa amsawa,



Sai da yayi gyaran murya kafin ya soma magana.............




Maimoon🤓#


Maimoon🤓#

*💖ABNUR💖*

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

*Page* *11*


Do anyone of you have any problem?

tambayan da ya fara yi kenan,

cikin girmamawa duka suka amsa da

"No Sir"

"Good"
sai da ya ɗan kalle gefen da take, kafin ya mayar da kallonsa a kan dukkan ma'aikatan gidan dake gabansa,


"Let me go straight to the point, wannan da kuke gani"
ya juya ya kalleta, suma duk juya wa sukayi suka kalleta, kafin suka mayar da kallonsu gareshi.



"Amana ta ce!,so ina so ku bata dukkan wani respect she deserves,I hope you understand?"


"Yes Sir" suka haɗa baki wajen faɗa.


"You may introduce yourselves to her"

ya faɗa yana komawa ya jingina da kujera yana latsa wayarsa.


Ɗaya bayan ɗaya suka shiga gabatar da kawunansu, tun daga bodyguards ɗin gidan, zuwa masu kula da flowers, masu gadi,masu kula da motoci,masu kula da tsaftace gidan, sannan su Asabe waɗanda sune suke da ragamar komai da ya shafi kitchen ɗin gidan.


a dai dai nan Taufeeƙ ya shigo falon, da sauri ya ƙarasa yana faɗin

"Sorry Sir, I was late,wallahi..."


Ɗaga masa hannu yayi bai ce komai ba, yana cigaba da abinda yake yi a wayarsa,


ganin abinda akeyi yasa Taufeeƙ yin shiru,har last person ya gama introducing kansa kafin Taufeeƙ ya karɓa da faɗin


"And I am Taufeeƙ Muntasir, his personal assistant,
Ni nake kula da duk wani abu na Sir Zannur,kama daga kayan sakawarsa,inda zaije, waɗanda zai haɗu dasu, da sauransu".


Ya kai ƙarshen maganan yana murmushi,kallonsu tayi tayi,ba tare da tace komai ba, can kuma ta nisa tace,


"Nagode sosai da gabatar da kanku da kuka yi a gareni, Ni sunana Noor, kuma Ni ma...."


"What the hell are you trying to say",


ya faɗa da sauri har yana ƙoƙarin ƙwarewa yana zare mata ido.


Da sauri tayi baya, tana kallonshi itama,ta kasa cewa komai,to miyene a ciki idan ta faɗa musu cewa ita matarsa ce.



Taufeeƙ ma da mamaki ya ke kallonsa, da sauri ya juyo ya kalli staffs ɗin sa yace


"You may all leave"


juyawa sukayi suka fara ficewa a cikin falon suna tunanin to wacece wannan ɗin a wajensa,


Taufeeƙ ya bisu da ido har suka gama ficewa, kafin ya juya ya kalli su Amina ya musu alama da ido,

da sauri suma suka tashi suka nufi kitchen,Amma harga Allah sunason sanin me ke faruwa.



Yasira da ta kasa nutsuwa, ta maƙale dan taji abinda yake faruwa, ganin bata shigo ba yasa Asabe leƙowa tana ɗaga murya tare da Faɗin,


"Wallahi Laɓe dai ba kyau ne dashi ba fisabilillahi"


da sauri Yasira ta ƙarasa kitchen ɗin, tana tsinewa Asabe a zuciyarta dan tasan Sir ya ji abinda Asaben ta faɗa.



Duk da yaji amma bai damu ba, mai da kallonsa yayi ga Noor dake tsaye tana kallonsa a tsorace,


"WHO do you think you are?

ya tambaya yana matsowa kusa da ita

Ɗan matsawa bawa tayi itama ba tare da tace komai ba.


Cikin kakkausar murya ya sake faɗin "ki bani amsata, ke wayece a cikin gidannan".


Cikin matuƙar shakka da tsoronsa da taji ya shigeta tace "Ni matar....."


"Darn it!" ya faɗa yana buga kujerar gefensa, sannan ya ɗago jajayen idanunsa yace


"don't ever make that mistake,a duk rayuwarki kar ki kuskura ki taɓa furta ke matata ce, ke amana tace da Nenne ta barmin bayan haka baki da wata matsayi a zuciya ko kuma rayuwata,ina fatan kin fahimta?"



da sauri ta gyaɗa masa kai idanunta na kawo ruwa,
ta ɗaga kai ta dubi Taufeeƙ da ya sunkuyar da kansa yana jin ba daɗi, he is sure Sir will regret this one day.


"Ke me ce ce a wajena?" ya sake jefo mata tambayan yana kafe ta da ido,

da sauri tace "Ni amanar kace da Nenne ta baka, bayan haka bani da gurbi a rayuwarka"



"Good, from now on, duk abinda kike buƙata ki tambayi Taufeeƙ,I don't think I have anything to do with you".



Daga haka ya juya yayi wucewarsa sama ya barta a nan a tsaye.



Ƙarasowa Taufeeƙ yayi yana kallonta kafin cikin matuƙar girmamawa yace,



"Madam kiyi haƙuri, komai zai wuce, i am sure shi kansa bai san me ya ke so ba,but Ni na san ko shi waye,ba zai taɓa wofintar da rayuwar ki ba.



A hankali ta ɗaga idanunta da suka ɗan yi ja kaɗan tana kallonsa sai kuma tayi murmushin ƙarfin hali tana faɗin,


"babu komai,Ni kaina bana so na zama komai a rayuwar sa,iya amanan da ya riƙe ma Nenne na ya ishe Ni, kuma bazan daina gode masa ba, bisa taimakon sa a gareni"


Daga haka ta juya da sauri tana tattare rigarta ta haura saman ta barshi anan tsaye yana tunani,shima juya wa kawai yayi ya nufi main kitchen na gidan.



Karo yaci da Amina dake fitowa daga kitchen ɗin da manya manyan warmers zata kai dining hall,



Da sauri ta ja baya tana faɗin"Sir Taufeeƙ kana buƙatar wani abu ne".


Murmushi yayi yace


"jeki shirya table ɗin sai ki kiramin Asabe, ku sameni a garden akwai maganar da zamuyi Ni da ku".



"Ok Sir Taufeeƙ angama, Allah dai yasa da ɗumi ɗumin ta zaka bamu"


"Idan kunzo zakuji ai" ya faɗa yana juyawa ya bar wajen.




Tunda ta shiga ɗakin ta saka key tafaɗa gadonta tana jin kuka na taho mata amma bata so tayi,
dan bata ga dalilin yin su ba,

ita kanta sai yanzu take ganin wautar ta da har take ƙoƙarin nuna kanta a matsayin matarsa.


Miƙewa tayi ta zare rigar jikinta tana yin cilli da ita



"Bazan sake saka rigar Bama,to ma

6 / 8