Chapter 7 Reading ABNUR Sirrin Hasken Soyayya By maimoon HN Novels

ABNUR Sirrin Hasken Soyayya By maimoon

Author :  Maimoon Category :  KDP NOVELS

Chapter   7 / 8

18K to 21K   out of 24K words

wa yace ya bani rigar, mtsww,ta sake hararar rigar.



Miƙewa tayi ta tsaya hankalinta a kwance dan dai ta san ta kulle ƙofar babu mai shigo mata, daga ita sai white clean bra ɗin jikinta da kuma gajeren wando iya gwuiwarta,


a hankali ta ƙara sa cikin toilet ta sako bathtub fari tass ta dawo tayi kwanciyarta tana sake tura baki.



Rufe laptop ɗin yayi yana jingina da gado,a hankali ya furta

"wato ga mai da bathrub kaya"

sai kuma yayi murmushi yana lumshe idanunsa,fararen ƙafafuwan ta zuwa gwuiwarta da kuma fararen cikakkun breast ɗin ta da ke cikin bra kawai idanunsa suke hasko masa,


Da sauri ya buɗe idanunsa da har sun fara canza kala daga farare tass zuwa ja,

hannunsa ya sa ya shafa sumarsa,sannan ya gyara kwanciyarsa a kan gadon yana sauƙe numfashi.


Ƙarar wayar sa yasa ya janyota a hankali yana ɗagawa

"Habibi me ya ke damunka ne,what's keeping you this busy?"

Abinda Maami ta fara faɗi kenan.


Cikin kwantacciyar murya mai nuna akwai abinda ke damunsa yace
"Maami na!"

take Maami ta rikice ta soma jero masa tambayoyi

"son are you alright?,am sure you are not, me ya faru? faɗa ma Maami kaji, ko nazo Nigeria?,"


Cikin son ya kwantar mata da hankali yace

"Maami, babu komai fa, but akwai wani magana da nake so nayi dake, a very serious one"


Ya faɗa yana lumshe idanunsa


"Ina jinka Habibi tell me"


"Ba ta waya ba,zanzo Dubai"


When?


"Next week"


"Allah ya kaimu,but you are sure babu abinda ya sameka koh"


"Maaamiiiii"

Ya faɗa yana jan sunan,

Dariya tayi kafin a hankali tace

"Habibi bazaka gane ba,I won't be able to do without you, you are my life Habibi".

"I know Maami, and you are mine too,Abbu ya dawo daga ukraine?"

Ya tambaya da kulawa,

"Bai dawo ba but Gobe insha Allah Zai dawo"

"Ok Allah ya kaimu"

"Ameen"

"I guess I will hang up now Habibi, we will talk later okay"

"Uhm" ya faɗa ƙasa ƙasa


"Okay bye Maami loves you" Bata jira amsar sa ba ta katse wayar ta.


Ajiye wayar yayi yana miƙewa dan tafiya masallaci.



Yadda suka yi tagumi suka ƙura masa idanu yasa Taufeeƙ ɗan murmushi yana kallon su Amina yace


"kai haba duk kallon na me ne ne haka"


Cire tagumin Asabe tayi tana faɗin "to Sir Taufeeƙ ba dole ba, tun ɗazu ka kasa faɗa mana maganan da ka kiramu a kai, kuma kasan waccar jarababbiyar yanzu zata fara nemanmu a kitchen".


Murmushi yayi sannan ya ce


"okay tom kuna jina"
suka amsa da

"eh" kafin ya cigaba da magana

Sai da ya faɗa musu duk abinda ya sani ga me da auren Sir Zannur kafin ya ɗaura da faɗin


"Kunsan me yasa na faɗa muku"

Girgiza masa kai sukayi mamaki ya ƙi sake su,


"Ok,so nake ku ja ta a jiki, ku nuna mata komai,kunga Ni namiji ne, sannan bana tunanin Sir zai nuna mata komai,dan Allah kar ku bari tayi kaɗaici,

and kamar yadda kuka sani, mu biyar kaɗai muka sani banda ƴan ƙauyensu, please Kar ku faɗa ma kowa matar Sir ce kunji?"


Asabe ce ta sauƙe ajiyar zuciya tana faɗin "ai kuwa akwai shidan mu wallahi".

Taufeeƙ yace "waye?"


Waye kuwa banda Yasira itama tasan Matar Sir ce, dan sanda ka faɗa mana,ina kyautata zaton taji.



Shiru yayi sai kuma yace babu damuwa, na san yadda zanyi da lamarinta ku dai kuyi abinda nace .

"Baka da damuwa Sir"suka faɗa a tare.



Miƙewa yayi yace "I know I can count on you both nagode sosai"



Haba haba Sir Taufeeƙ, ya kana haka, ai duk taimakon kai ne ko ba haka ba Asabe?

"Haka take"Asabe ta faɗa tana dariya.


Shi dai bai sake cewa komai ba ya juya ya bar garden ɗin,

suma miƙewa sukayi suka bar garden ɗin suna jinjina maganan.


Yasira dake laɓe ta fito tana murmushi, a fili ta furta,

"Sir Zannur zan tabbatar da na mallakeka, kuma wannan shine mataki na farko da zan mallakeka, tabbass na san yanda zanyi anfani da labarin nan in samu abinda nake so".


daga haka ita ma tabi bayansu Amina dan dama tun fitowarsu ta biyo su dan tace musu su koma bakin aiki amma ganin inda suka nufa yasa ta bisu taga me zasuyi a wajen.



Washegari kamar yadda Zannur yayi umurni haka Taufeeƙ ya ɗauke ta, ya kaita sukayi shopping ɗin duk abinda zata ɓuƙata,


kama daga kayan sakawa,zuwan kayan shafa,da ma duk wasu kayan anfani na mata.


ganin bata san wasu abubuwan ba yasa ya haɗata da ma'aikatan wajen kasancewar babban supermarket ne na manya, yasa matar ta zage ta kwasa mata komai kamar mahaukaciya,

and daɗin daɗawa ce mata da Taufeeƙ yayi she is important to Sir Zannur, kuma shi ya turo su,

ai kuwa sun sha shopping kamar na hauka har yamma tukun suka dawo gida.



Su Amina su suka shirya mata komai,

sannan suka nuna mata yadda ake anfani da komai, duk da yawanci kafin ma su faɗa take karantawa ta gane miye ne sai dai a nuna mata yadda ake anfani da shi.


Haka suka saka ta, ta shirya suka zagaya da ita gaba ɗaya gidan,


a ranar ta sha mamaki ganin irin girman gidan,wani irin mutum ne shi kuwa? tambayar da ta yi ta yi ma kanta kenan.



Zuwa yanzu ta gama sabawa da gidan dan kuwa kwananta shida kenan,amma har ranan bata sake sakasa a ido ba,


Taufeeƙ ma sai jifa jifa take ganinsa,

su Amina sune abokan hirarta, har kitchen take zuwa ta zauna, suna hirarsu,

Yasira kam tsakaninta da ita gaisuwa,idan ta gaisheta ta amsa shikenan babu abinda ke sake haɗata da ita.



What?
Maami ta faɗa ta ƙarfi tana miƙewa, me kike nufi?, You must be out of your senses, do you want to tell me Habibi yayi aure ba tare da nasani ba!?,wannan ma ai maganar banzace,



Shiru tayi tana sauraron mai maganan daga haka ta katse wayanta tana kallon farin balaraben dake gefenta da laptop akan cinyarsa yana operating,
idanunsa sanye da fararen medicated glasses.


Abbu, kanajin wata maganar banza, wallahi i won't take it,I am leaving for Nigeria tomorrow morning.


Ta faɗa zama kusa dashi,ɗagowa yayi ya dubeta sannan cikin kulawa yace


"What happened Hilwa!"


Wai Habibi yayi aure,ake faɗamin, zancen banza, zancen hofi,Ni nasan hakan bazata taɓa faruwa ba da amincewata ba, saboda haka zan tafi Nigeria,dama ina so inga Habibi, jikina Yana bani Yana cikin wata damuwa.


Janyota yayi yana manna mata kiss a forehead kafin yace

"ok but ki kwantar da hankalinki,Zannur yana lafiya,and bazai yi aure bada yardar ki ba, so now smile"


Murmushi ne ya suɓuce mata,ya shafa kanta yana murmushin shima,shigewa jikinsa tayi tana faɗin

"Abbu what if da gaske yayi auren?,kasan Habibi Yana da Zurfin ciki.



"Ki kwantar da hankalinki everything that happens is for the best okay,zan sa ayi miki booking flight ɗin don't worry".


Ta gyaɗa masa kai tana sake kwantar da kanta a ƙirjinsa, tana tunanin Allah yasa ba da gaske bane dan kuwa bazata taɓa yadda da hakan ba.



*💖ABNUR💖*

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

*Page* *12*


_Washegari_


Tun safe Zannur yake jinsa wani iri,ya kasa fita,ko nan da can.


ganin ya kasa nutsuwa
ya sa ya jawo laptop ɗinsa,yana kallon ta,
yadda ta shige cikin bargo ta rufe har kanta.

sai kuma ya ja tsaki yana faɗin,

"mutum yayi ta bacci tun safe".



Yana ƙoƙarin rufe laptop ɗin yaga tayi miƙa tana yaye bargon daga jikinta,
sai ya fasa rufewa, ya cigaba da kallon ta,

miƙewa tayi zaune a kan gadon tana mutsuka idanunta,sai kuma ta zuro ƙafafuwan ta ƙasa, slippers ɗinta ta sanya kafin ta miƙe,

har ta shige banɗaki,kafin ya sauƙe ajiyar zuciya yana shafa sumar kansa a fili ya furta



"Ke amana tace, saboda haka dole ne in sa ido akanki"


sai kuma yayi murmushi yana rufe laptop ɗin, dan har yaji mood ɗinsa ya canja, yana jin sa cikin nishaɗi,
duk da wani sashi na zuciyar sa na fargaba wanda bai san fargabar miye ba.



Agogo ya kalla, ganin ƙarfe goma saura minti goma, ya sashi miƙewa shima ya wuce toilet.


sai da yayi daɗe a banɗakin kafin ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa,
cikin abinda bai fi 30 minutes ya shirya tsaf cikin riga da wando na *_Louis Vuitton_* Agogo ya sanya da pcap a kansa duka na *_Louis Vuitton_* sannan ya feshe jikinsa da mayen turarensa na *_shumukh_* slippers ya sa a ƙafan sa shima na *_Louis Vuitton_* sannan ya koma gefen gadon ya zauna,ya jawo laptop ɗinsa Yana dubawa, dan baya tunanin zai fita ko ina.


Iska da fara sauƙan yayyafi ya shashi miƙewa yana leƙa waje,
ai kuwa sai ruwa ya tsuge kamar da bakin ƙwarya, saurin matsawa yayi daga jikin window,aransa yana tunani yadda za'a yi wasu da basu san ciwon kansu ba har su bari ruwa ya jiƙasu idan ba tsautsayi ba.



Komawa yayi ya zauna ya sake jawo laptop ɗin,kai tsaye ɗakinta ya duba ganin bata ciki yasa yayi ƙwafa yana kashe laptop din gabaki ɗaya, ya miƙe ya fice a daƙin,



Ɗakin hoto ya shiga yana ƙarasawa ya ɗauki Camera,saboda yana son yin capturing ruwan yanda yake sauƙa,


a hankali ya yaye labulen balcony ɗin yana saka Camera ɗin a idanunsa,iskan ruwan na kaɗawa yana sa rigar jikinsa haɗewa da jikinsa .



Abinda ya gani ta cikin Cameran ya sashi saurin janyewa daga idanunsa yana ƙura mata idanu,

tabbass ba gizo idanunsa ke masa ba, ita ɗince a cikin ruwan sama, baki a sake yake kallonta, yanda take juyi tana nishadi a cikin ruwan,


shagala yayi da kallonta, tundaga sama har ƙasa yake yake kallonta,


riga da wando ne a jikinta masu laushi na *_Dior_* kanta ta saka band Wanda ya Bama gashinta daman sauƙa ta bayanta, *_Stuart weitzman Cinderella slippers_* ne a fararen ƙafafuwan ta,

yanda take dariya ya sa shi mayarda Cameran idanunsa ba tare da ya sani ba.


hotuna yayi ta mata ba tare da tasan ma yana gun ba,Dan kuwa babu wanda yake zuwa ta bayan balcony ɗin,shiyasa ma ta je can dan bazata iya ƙin shiga ruwa ba.


Ajiye Camera ɗin yayi a hankali ya fice a ɗakin.


Hannuwanta ta tara a ruwan ya cika ta watsa a fuskarta,ta sake tara hannun tana shirin watsawa taji an riƙe hannuwan nata,

a tsorace ta ɗago, idanunta suka shige cikin nasa,fuskarsa babu alamar wasa,gaba ɗaya ya gama jiƙe jikinsa,ƙirarsa na ƙarfafa ta sake bayyana saboda yadda ruwan yasa kayan ya manne da ƙirjinsa,



Kallonta kawai yakeyi ba tare da ya ce komai ba, da sauri ta ƙwace hannunta tana shirin barin wajen dan batasan sam zaizo wajenba,

ita bata mayi zaton yana gidan ba,dan rabon ta da shi tun ranan da ya kawota,


da sauri ya sake riƙe hannunta, yana jawota gabaki ɗayanta zuwa jikinsa,kasa koda ƙwaƙƙwaran motsi tayi,cikin Muryar da shi kansa bai san yana da ita ba ya soma faɗin


"me yasa kike shiga ruwa,bakya tsoron mura ya kamaki?"


Ɗagowa tayi ta kalleshi,sai kuma ta sunkuyar da kanta,ta kasa cewa komai,


"Tambayar ki nake"ya faɗa a hankali yana dubanta.


"To ai Ni ina so,kuma ko a Baulawa ma ina shiga"
ta faɗa tana turo baki.


"To nan ba Baulawa bane, nan ba'a shiga ruwan sama, idan dai baso kike ki ƙarar min da kuɗina a asibiti ba".


"Ni ruwa baya sani rashin lafiya" ta faɗa a shagwaɓe,


"I see"ya faɗa ya na sake ta

Ai kaman jira takeyi da gudu ta bar wajen,ya bita da kallo yana shafa jiƙaƙƙen sumarsa,


su Amina da Asabe da ke leƙe ta kitchen sai tafawa sukeyi duk da basa jin me suke faɗa,

Asabe ta ɗaga hannu sama tana faɗin"Allah ka aurar da mu"Amina ta amsa da

"Ameen ya Allah muma dai muji me ake ji"

suka sake ƙyalƙyalewa da dariya,

Yasira da ke tsaye itama ta ɗayan ɓangaren ta ja tsaki, sai kuma tayi murmushi a zuciyarta tana faɗin

"komai ya kusa zuwa ƙarshe".


kallon jikinsa yayi, yaga yadda yayi sharkaf da ruwa,a hankali ya furta


"Yuk"
Yana ɓata fuska,sai kuma ya ja tsaki, sam ba abinda yake son ce mata ba kenan,
so yayi ya mata faɗa, amma bai san ya akayi harshen sa ya kasa bashi haɗin kai ba,shima juyawa yayi ya bar wajen yana sakin attishawa.



Ƙarfe 3:00 ya fito daga ɗakinsa ya sake shiryawa cikin wasu ƙananan kayan,but ya ƙara rigar sanyi akai,


sauƙowa yayi falon ƙasa ya zauna yana danna wayarsa.


a hankali itama take sauƙowa ta canza kayanta zuwa doguwar rigar abaya ƙafafuwan ta san ye cikin flat shoes na *_Miu Miu_* kitchen ta nufa batare da ta lura da shi ba, a hankali yace

"tea"

Cak ta tsaya,sai kuma ta juya ta kallesa,ganin idanunsa a lumshe yasa kawai ta juya ta nufi kitchen ɗin,



Amina da Asabe na ganinta suka soma gulma ƙasa ƙasa suna dariya,


"Ku kuma fa"
ta faɗa tana murmushi itama,

"Ina kwana Madam"

suka haɗa baki wajen faɗa,murmushi kawai tayi.

"Ina kwana"
Yasira ta gaisheta a daƙile, itama ƙasa ƙasa ta amsa, tana faɗin

"Yasira ki haɗa tea, ki saka kayan ƙamshin a ciki, da citta, yanzu ina jiranki ki kawomin parlour".


Yasira ji tayi kamar ta fashe ƙasa ƙasa tace"ok ma"


Daga haka ta juya ta bar kitchen ɗin.


Asabe da Amina suka tafa suna faɗin

"wannan irin shiga ruwa na masoya ai dole su sha shayi saboda sanyi"

Amina tace "haka abin yake"
suka sake kwashe wa da dariya.



Ita dai Yasira ko takan su bata bi ba,ta haɗa shayin,ta jera a kan tray mai matuƙar kyau sannan tace

"Amina kikai mata"


"In kai mata ina?,Ni rufa min asiri, matar gida tace ki kai mata kice in kai mata, ah ah wallhi"


Yasira tayi ƙwafa ta suri tray ɗin ta fito,

ganin Sir Zannur a falon ya sa ta saita kanta da fuskarta ta gyara tafiyarta, a yangance ta ajiye a kan Centre table ɗin tana kallon sashin da Noor take zaune,

itama kallonta takeyi,kawar da kanta tayi tana kallon Zannur tace

" Sir should I serve you tea"


Itadai Noor kallonta kawai takeyi

"don't worry,ki barshi, ki je ki cigaba da aikin ki"


ya faɗa ba tare da ya dube ta ba,

"ok sir"

ta faɗa badan ran ta ya so ba, ta miƙe ta bar wajen, da ido Noor ta bita kawai,


Ɗago wa yayi daga danna wayar yace

"Are You waiting for me to ask you to serve the tea"


Da sauri ta sauƙo daga kujeran tana ɗaukan cup ɗin ta shiga tsiyaya masa shayin.


Satan kallonta kawai yake yi yadda take yin komai a nitse,har ta gama ta miƙa masa, yana shirin karɓa wayarsa tayi ƙara,


Ganin Maami haka kawai yaji gabansa ya faɗi, ɗagawa yayi tare da yin sallama,

"Habibi come and pick me up at the airport"


Da sauri ya ajiye cup ɗin daya karɓa yana faɗin
"what!!, Maami, wani airport ɗin"

"Nnamdi Azikwe International Airport"

ta faɗa a taƙaice tana katse wayar ta.


Wayar hannun sa ya bi da kallo, sai kuma ya juya ya kalli Noor, ba tare da yace komai ba kawai ya juya ya nufi ƙofa,

kallo ta bishi da shi,a ranta tana tunanin anya lafiya kuwa, shayin da ya bari ta ɗauka,sannan ta kira landline na kitchen, tace suzo su maida tea ɗin.



daga haka ta haura da nashin a hannunta tana tunanin abinda ya ɗaga masa hankali haka.







Maimoon#

💖ABNUR💖



By maimoon🤓



Elegant online writers📚📖



Free book📚



Page 13



Har ya isa Airport ɗin, bai dai na tunanin mai ya ka wo Maami Nigeria all of a sudden ba.


A hankali ya ƙaraso in da ta ke tsaye,ta na sanye da abaya, fuskar ta da glass mai kyau,ta fito a Mrs shuraim ɗinta.


Rungume ta ya yi ba tare da yace komai ba, sai lokacin ta lura da shi,da sauri ta ɗago kansa ta na kallon sa


"Habibi are you Ok?" murmushi ya yi ya ce

"babu kawai am happy saboda zuwanki ne"
ya faɗa ya na murmushi.


Cikin matuƙar farinciki,ta manna masa kiss a both chicks ɗinsa da forehead ta na faɗin

"I missed you so much Habibi,mu je gida".



Bai ce komai ba ya ɗago daga jikinta,ya na Jan trolley ɗinta,kasancewar bai fito da bodyguards ba.



Sai da ya sa a mota, kafin ya zagayo ya buɗe mata ƙofan motan,



"my Queen,shall we?"

ya faɗa yana nuna mata motar



Dariya tayi sosai tana kallon shi, kafin ta shiga ta zauna, shima ya zagaya ya shiga motar, amma gabaɗaya tunaninsa na ga abinda zai faru idan Maami ta haɗu da Noor.


Ganin he is carried away ya sa Maami shafa furkarsa ta na faɗin

"Habibi are you hiding anything?"



Da sauri ya girgiza mata kai,yana faɗin



"Maami kin san na ce miki ina son muyi magana idan nazo Dubai!, so tunda kinzo, I will explain everything to you Amma sai kin huta"



Ƙura masa ido tayi tana kallonsa,sai kuma ta ce,


"nima kai na akwai abinda nake so in tambayeka that is very important, Dan kusan ma shi ya kawo Ni Nigeria, duk da nasan ba zaka taɓa yin hakan ba da amincewa ta ba".


shiru yayi yana sauraranta, dan bai kawo ko a ransa ta san da aurenshi ba, to wa ma zai faɗa mata idan ba shi ɗin ba.



Motar ce ta kusa kufce masa saboda tambayar da ya jita a bazata

"Habibi wai kayi aure ba mu sani ba?"


Da sauri ya ja burki da ƙarfi yana duban ta

"Who told you this Maami?"


"Kar ka damu nasan ba gaskiya bane, wata ce kawai ta kira ni wai ka yi aure but I didn't believe her" ta faɗa tana murmushi


"Maami zan faɗa miki komai idan mun je gida"

Shine kaɗai abin da ya iya furtawa, zuciyarsa na tafasa, tabbass da ya san waye ya faɗa ma Maami zancennan, sai ya sashi yayi regretting, but yasan yanda zai ɓullo wa Maami,

fatan shi kawai Allah ya sa kar Maami ta ɗauka da zafi, dan ya san ta, tana sonshi sosai, amma tana da matuƙar kafiya akan abinda ba ta so.



Har suka iso gidan ba wanda ya sake cewa komai,

da sauri bodyguards suka buɗe musu ƙofa suna yi ma Maami sannu da zuwa cikin matuƙar girmamawa,

hannu kawai ta ɗaga musu, ta wuce, shima ya bi bayanta jiki a sanyaye,


A falo ya sameta tana tsaye ta na ƙarema ko ina kallo,


"Ƙarasowa yayi yace Maami ki huta sai muyi maganan kinji!"


Bata ce masa komai ba ta nufi bene,
tsayawa tayi cak,ganin wata kyakkyawar matashiyar budurwa tana sauƙowa,ja baya tayi tana kallon Noor,sai kuma ta juya da sauri tana kallon Zannur


Har ta ƙarasa sauƙowa kafin ta lura da waɗanda ke falon, kasa wucewa tayi,sai ta tsaya kawai tana kallonsu,



"Ina wuni"ta faɗa cikin in-ina dan dai daga ganin matar kasan itace mahaifiyar Zannur duk da ba wani kama yake da ita sosai ba.



Kallonta kawai Maami keyi,tama kasa amsawa,sai kuma

7 / 8