Author : Maimoon Category : KDP NOVELS
dan shima yana buƙatar hutu.
Washe gari tun bakwai ya sallami bodyguards ɗin suka koma Abuja, kamar yadda Zannur ya buƙata ,
ƙarfe takwas dai-dai ya fito daga ɗakin, ya shirya tsaf cikin ƙananan kaya, kansa sanye da facing cap sai shade a idanunsa , Snickers ne a ƙafansa na kanfanin Adidas ,a hankali yake tafiya Taufeeƙ na biye dashi bayan yaje ya yi checking out daga hotel ɗin ,har packing space ɗin, "pass the key" ya faɗa a taƙaice"
Taufeeƙ ya miƙa masa key ɗin a zuciyarsa yana faɗin "shi zaiyi driving kenan" mazaunin driver ya shiga ,sai da Taufeeƙ ya gama saka jakansu da kuma jakan kayan cameras da zasu buƙata, a motan,sannan ya buɗe mazaunin mai zaman banza ya zauna ,
warming motar yayi sannan ya tada ya fice a hotel ɗin, map Taufeeƙ ya buɗe ya ajiye a gaban motan ,yana ganin directions ɗin daya kamata subi,
suna fara shiga garin yayi parking motar ya sauƙa , Taufeeƙ ma ya sauƙa , makullin ya wurga masa ya caɓe ,shikuma ya buɗe bayan motan Camera ya ɗauka ya haɗa komai nata sannan ya koma wajen mai zaman banza , Taufeeƙ yayi murmushi yana shiga mazaunin driver ,a zuciyarsa yana tunanin da alama za'a samu abinda a ke so a wannan garin.
Basu wani ƙara tafiya mai yawa ba sukaga hanya ta ƙare mota bazata iya bi ta shiga ba ,sauƙa Taufeeƙ yayi ya dudduba sai kuma ya dawo yana faɗin "Sir i don't think akwai hanya fah da mota zai ƙarasa, sauƙe Camera dake idonsa yayi yace "so!?"
Taufeeƙ ya sosa ƙeya ,yace "I guess da ƙafa zamu ƙara sa ,ina ganin ƙauyen is just a little bit ahead,
murmushi Zannur yayi ganin yayi capturing butterfly ɗin da yake ɗauka ,ba tare da yace komai ba ya sauƙa a motar da sauri Taufeeƙ yace "Sir zan kira faruƙ yana cikin Kaduna sai ya zo ya juya da motar ,gyaɗa masa kai kawai yayi yayi gaba yana sake kallon ɗan hanyan da zasu wuce ɗin.
A firgice ta farka daga baccin daya kwashe ta a zaune ,ta miƙe da sauri tana leƙa tsakar gida ,hasken data gani tarr ne ya sata komawa ɗakin da sauri ta ɗauki jakan makarantar ta ,da roban abincinta tasa goran ruwanta a jaka ,sauri sauri ta fito dan tasan yauma tayi latti,tun asuba ta shirya dan kartayi latti amma gashi sai da tayi latti ,ɗakin Nenne ta leƙa ,taga bata ciki,"to ina Nenne taje da sassafe nan" ganin batada amsa gashi tana sake ɓata lokaci ya saka tai saurin fita a gidan ,
sauri sauri take tafiya ,dan dai makarantar da ɗan tazara,ganin saurin bazai mata ba yasata kwasa da gudu , Allah Allah take ta isa ,saboda yau ne za'a faɗi mutum ɗaya a duk cikin makarantar da ya samu scholarship ɗin zuwa cikin Kaduna karatu , gwamnati zata ɗauki nauyinsa saboda hazaƙarsa ,
Tun da ta shigo taga kowa na aji ,aji ta wuce tana sanɗa a ƙofar ajin ta tsaya ganin akwai Malama a ciki ,sai da taga Malamar ta fara rubutu tukun tayi sauri ta shigo , ta zauna a baya ,sannan ta miƙa ma na kusa da ita jakarta ,a haka sukayi ta passing passing ɗin jakar har kujeran gaba ,wanda shine wajen zamanta ,da dabara ta dinga canza wajen zama har ta iso gaba,tana shirin zama kawai Malaman ta jiyo ,
"Noor!" Malaman ta Kira sunan ta ,da sauri ta juyo " Malaman tace "You Are late again ,right!?" da sauri acikin harshen turanci ,dan kar ta ƙara ma kanta laifi idan tayi venacular tace, "dan Allah Malama kiyi haƙuri ,wallahi makara nayi" ,juyawa Malaman tayi ta cigaba da rubutu tana faɗin "zo ki tsaya a gaban Allo har sai na gama in faɗa miki hukuncinki" tsaya wa tayi tana marairaicewa ,Malama ta sake cewa " kafin na ƙirga uku na ganki a gaban Allo Noor,ɗaya.. ,biyu.." kafin tace uku tayi saurin ƙarasawa gaban Allon ta tsaya, tana kallon duka ƴan ajin,
sai da Malama ta ƙara sa rubutun tukun tace "toh yanzu kafin a fara darasi, ina so in sanar da ku ,mutum ɗaya a cikin makarantar nan da Gwamnati ta ɗauki Nauyin karatunta ,bakowa bace face......."
Duk ɗalibai suka zuba mata ido ,sai da ta ɗan yi murmushi kafin tace " _NA'IMA_ _RAZAƘ_ _ABDULKARIM_ wacce kuka fi sani da _NOOR_ " .
Duk student ɗin suka hau murna dan dai sun san ,she deserve it ,itakam ta kasa ƙarasawa ma ,sai da Malamar tace mata "congratulations" tukun ta ƙarasa da sauri ta rungume ta kawai ta fashe da kuka,
Malamar ta shafa kanta tace "karki damu You deserve it Noor,ni dama nayi tunanin haka"
a hankali ta ɗago tace" Malama dan Allah ina so zan tafi gida" , "kije badamuwa gobe sai ki dawo congratulations once again" da sauri ta juya ƴan aji na ta mata murna ,tana binsu da murmushi ,
sai da ta fita daga makarantar tukun tayi wani tsalle tana faɗin "Nenne na samo scholarship zan tafi birni ,ita kaɗai take surutunta tana Allah,Allah ta isa wajen Nenne,
"Baiwar Allah" taji an mata magana da sauri ta juya tana kallon wanda yake mata maganan ,saida ta runtse idanunta ta buɗe ganin ɗan birni ,a zuciyarta tana faɗin ,kar dai tun yanzu ne za'a tafi da ita karatun ,ah ah gaskiya ita fah idan ba da Nenne zasu tafi tare ba ,bazata je ba,
"Baiwar Allah" Taufeeƙ ya sake faɗa yana kallonta yadda yaga ta wani rufe idanunta da sauri ta buɗe idanunta ta kallesa ,ta marairaice tafara faɗin ,"dan Allah ba yanzu ba ,ai Ni bansan yau za'a tafi ba ,na ɗauka sai na shirya dan Allah ku bari na fara ɗauko Nenne sai mu tafi tare,
kallonta kawai yakeyi har ta gama tukun yace " baiwar Allah tambaya nakeyi, a garinnan ko akwai wani waje da za'a iya biya a kwana "
shiru tayi sai kuma ta watsa hannunta tace "oho" "kina nufin baki sani ba"
"Eh" ta faɗa tana juyawa ta cigaba da tafiya "keeeee" taji an faɗa da wata Muryar da ta tilasta mata juyowa tagako waye dan ta tabbata ba shi ne wanda ya tambayeta ba.
#maimoon
*ABNUR*
*By* *maimoon* 🤓
*Elegant* *online* *writers* 📚📖
*Free* *book*
*Page* *6*
A hankali ta juyo, tana sauƙe idanunta a kansa,yana tsaye ,tun daga ƙafafuwan sa, take kallonsa, har takai kan fuskarsa,kallonsa kawai takeyi babu kiftawa, bata san yaushe ya ƙaraso kusa da ita ba,sai dai kawai ji tayi yace,"to ko zaki nuna mana gidan mai garin,garinnan?"
Sai da ta saita kanta sannan tace "to nidai yanzu wallahi sauri nakeyi,saboda haka ku nemi wani ya rakaku, inada wani abu mai matuƙar muhimmanci a gaba na yanzu haka"
bata jira abinda zai ce ba, tayi saurin juyawa tana cigaba da tafiya,
Taufeeƙ ya sake baki, yana kallonta,lallai sai yau ya yarda, rashin sani yafi dare duhu,idan ba haka ba,the whole Sir Abubakar shuraim (Zannur)banda,sa kai wanda hausawa suke cewa ,yafi bauta ai ko ganinsa ma wannan bata isa tayi ba wallahi,
Shidai ya na tsaye a wajen kamar wani statue, sai da ya kalli ko ina yaga babu alamar mutum sannan ya juya ya kalli Taufeeƙ,da sauri Taufeeƙ ya ce
"Sir You don't have to worry, I will manage everything" daga haka ya yi saurin juyawa ganin wani matashi ya tsayar da shi, sai da ya tambaye sa ko akwai gurin kwana na kuɗi, matashin yace babu,kafin yace masa ko zai rakasu gidan mai gari, matashin yace babu damuwa,
Sai da saurayin ya rakasu har gidan mai gari, Taufeeƙ ya ce "ɗan saurayi to ko zaka mana sallama da shi mai garin,kafin ya rufe bakinsa mai gari ya fito, yana gyara rawaninsa, matashin yace"gashi nan ma maigarin,
Taufeeƙ ya masa godiya shikuma ya juya ya bar wajen,mai gari ya washe baki ganin Larabawa a ƙofar gidansa yana faɗin "ah ah baƙi mukayi,to to to sannunku da zuwa",cikin gidan ya koma ya fito da tabarma,ya shinfiɗa musu,sai da suka zauna sannan Taufeeƙ ya fara masa bayanin dalilin zuwan nasu.
Mai gari yayi gyaran murya yana faɗin"dan dai wannan babu wata matsala,dan gurin da zaku zauna kam,amma sai dai fa zaku biya haya".
Taufeeƙ yace babu "damuwa,zamu biya ko nawane", mai gari yace "to madalla sai ku tashi in nuna muku wajen".
Sai da ya nuna musu inda zasu zauna, Taufeeƙ ya biya,sannan mai gari ya koma gida yana ta murna, ya samu kuɗi.
Sai da Taufeeƙ ya gyara yadda zaima Sir Zannur daɗi sannan ya shigo musu da kayayyakin su, shidai bai ce komai ba, dan dai ya je wuraren da suka fi wannan complications, idan dai har zai samu abinda ya ke so, bare nan.
A gajiye yake, hakan yasa wanka kawai yayi, ya kwanta, yanajin nishaɗi, daga gobe yakeso ya zaga garin ya gani idan har zai samu abinda yakeso duk da yaga alamar hakan tun daga shigowar sa garin.
A take bacci ya ɗauke shi, Taufeeƙ da ya shigo ɗakin bayan shima yaje nasa ɗakin ya shirya, ya buɗe jakan kayansu ya ɗauko bargo,mai matuƙar kyau da taushi, ya lulluɓa masa, ya tsaya ya na kallonsa,
"Sir is such a rare gem, samun kamarsa sai an tona gaskiya,yana fata da kuma addu'ar Allah ya bashi mata, wacce zata bashi farin ciki, wacce zata kula da shi,dan he really deserve that, Amma bai san meyasa sam batun aure baya cikin ajenda ɗin rayuwarsa.
Fita yayi daga ɗakin, ya ja masa ƙofa ya fito waje, tafiya kawai yakeyi yana kallon garin mai cike da ni'imomi iri-iri,sai yamma ya dawo,a shirye ya gansa tsaf da alama fita zaiyi yace
"Sir zakaga garin ne" "eh" kawai yace ya sa kai ya fice, shima ya bisa a baya, sai da suka zaga garin sosai, sai da sukayi sallar isha, sannan suka dawo gida,a gaskiya garin yayi masa ba kaɗan ba,yasan zai samu abinda yakeso a nan.
Daga gidan mai gari aka kawo musu lafiyayyen abinci,har da su kaza, Taufeeƙ ne kaɗai yaci, shi kam kwanciya kawai yayi, daga haka bacci ya ɗauke shi
Ita kam Noor tunda ta koma gida,tundaga tsakar gida take ƙwala kiran "Nenne,Nenne,burina ya cika,rayuwarmu ta kusa canzawa Nenne,ganin Nenne bata fito ba ya sata ƙarasawa ɗakin,da sauri Nenne dake kwance tana fitar da numfashi da ƙyar, ta juya mata baya,dan bataso ta fahimci halin datake ciki,amma inaa ta makara,
Da sauri ta ƙara so ta tsuguna tana kallon Nenne,hankali tashe ta soma faɗin "Nenne baki da lafiya ne, me ya sameki Nenne na", cikin ƙarfin hali Nenne ta riƙe hannunta sannan ta shafa kanta tana faɗin,ki kwantar da hankalinki,babu komai fah kawai zazzaɓi ne yake damuna tun safe,kuma naji sauƙi sosai",Noor ta sauƙe ajiyar zuciya,tana faɗin Alhamdulillah, ai nazata ciwonki ya tashi",
Gyara zama tayi ta riƙe hannuwan Nenne duka biyu tana faɗin "Nenne na samu scholarship,gwamnati zata ɗau nauyin karatuna a cikin gari",
Nenne ta faɗaɗa
murmushinta tana faɗin "masha Allah, Allah yayi miki albarka Noor,ya haɗaki da alkhairi ko bayan raina", Noor bata wani kula da batun Nenne ba ta miƙe tana faɗin,
"Gobe ranar bikin shekara,dole ma na je na binciko abinda zan ci ado gobe dashi", ta faɗa tana miƙewa tabar ɗakin,
Ai kuwa ranar batayi bacci da wuri ba,sai kai komo take tsakanin dakinta,da ɗakin Nenne, sai wajen ƙarfe sha biyu tukun tasamu bacci ya ɗauke ta a ɗakin Nenne,
kallonta kawai Nenne takeyi yadda take baccinta,a nutse,tana fata da addu'ar Allah ya bawa ƴar ta kyakkyawar rayuwa,mai ƴanci ba irin nasu ba,shafa kanta tayi,sannan ta mata addu'ar bacci ta shafa mata,itama ta lumshe ido,take bacci ya ɗauke ta.
Washegari tun safe ta shirya acikin uniform ɗin ta na boko,sai lokacin waɗannan mutanen jiyan suka faɗo mata,to me ya kawosu ƙauyen su,more especially ɗayan ma,yayi mata kwarjini da yawa,ko me zasu je yi a gidan mai gari,
da wannan tunane tunanen ta gama shirinta tsaf ta yi ma Nenne sallama, ta fice a gidan,dan dai yau batayi latti ba,
Tun safe Sir Zannur yake zaga garin, Taufeeƙ dai binsa kawai yakeyi,idan yaga abinda ya birgesa sai ya ɗauka a hoto,mutanen ƙauyen sai kallonsa sukeyi,
wasu samari yaga sun zuba masa ido,ganin irin kallon da suke masa ya sa shi ƙara sa wa inda suke yace
"sannunku"
, da sauri ɗaya yace sannu bawan Allah,kafinma ya sake magana duk suka taso suka zo kusa dashi,suna masa sannu,
murmushi yayi yace "in ɗauke ku hoto!? Ya tambaya yana ƙoƙarin sakewa da su,da sauri suka ce "eh" ai kuwa suka hau jeruwa, ya ɗauke su yana nuna musu,
ai kuwa sai yaga mutane sunata ƙaruwa, wai suma a ɗauke su.
abin har ya bashi dariya, harda tsofaffi gyarawa yayi yana ta ɗaukansu a hoto,yana ɗan yin baya,don ya samu capturing abinda yake so,
buge mutum ɗin dayayi garin komawa bayanne ya sashi saurin juyowa yaga waya buge, bai sani ba, ita kam da har ta kai ƙasa, kasa ɗagowa tayi,
a hankali ya ƙarasa wajenta ya miƙa mata hannu,ɗaga kai tayi ta kalleshi,tabi hannunsa da yake miƙa mata da kallo,
miƙewa tayi ba tare da ta kama hannun nasa ba, tana karkaɗe jikinta,
A hankali yace "meyasa kina tafiya bakya kallon gaban ki"
Da batayi niyyan kulasaba, amma jin abinda yace ya saka juyowa ta kallesa da kyau sannan ta maimaita abinda ya faɗa sai kuma tace"malam sai kuma aka ce maka, kai ka dinga tafiya da baya da baya akan layin da ba siya kayi ba ko"
Kallonta ya tsaya yi,sai yanzu ma ya gane ta da sauri Taufeeƙ ya ƙaraso,yana kallonsu,
Bata sake cewa komai ba, kawai ta juya tayi wucewarta,baki sake suka bita da kallo, kafin yayi ƙwafa yana juyawa ya bar wajen,
Tun da aka tashi school ta dawo gida take shirin bikin shekara da ƙyar ta samu ta gama shirya wa, duk da bata yi kwalliya irin na yan ƙauye ba, sai dai ɗigon kwalli da ta yi guda uku a ƙasan haɓarta,sai fararen lumsassun idanunta da ta sanya wa kwalli,
ta fito rass da ita,sai da ta shiga tayi ma Nenne sallama, sannan ta fita a gidan ta nufi wajen bikin shekara wanda ake yinsa duk shekara a ƙauyen,duk wani al'adu nasu za'a yi a wajen.
Tana isa wajen ta tarar har an fara, can nesa ta samu ta tsaya tana kalle kalle,
Tun shigowar ta wajen ya lura da ita, ya tsaya da ɗaukan hoton da yakeyi yana kallonta,shi kansa bai san dalilin da yasa yake kallonta ba,samun kansa yayi da ɗaukan ta hoto ba tare da ta sani ba,
yayi mata yakai kala uku, kafin ta juyo, karaf idanunta ya shiga nashi,kallonsa tayi taga yana ɗaukan ta hoto ai kuwa ta wani murguɗa baki ya ɗauka a haka,
sai da ya kalli cikin
camera ɗin sai ya samu kansa da yin murmushi kawai,bai sake kallonta ba ya cigaba da ɗaukan abinda ake yi,
A ƙarshe aka kira ƴanmata,aikuwa ita da ƙawayenta suka shiga,waƙa aka saka musu na mutan ƙauye,suka hau yin rawar a nutse, a hankali, baya ya koma yana kallonsu, yadda suke rawar a tare suna juyawa, ba ƙaramin burgesa abin yayi ba, hoto ya shiga ɗaukan su,wanda duk nata ya fi yawa a ciki,
Ba a tashi taron ba har kusan magrib, duk aka fara watsewa, Taufeeƙ ya ƙara so inda yake a tsaye ya jingina da wata bishiya, yana kallon hotunan, a kan nata ya tsaya yana kallo, yanda ta murguɗa baki da taga yana ɗaukan ta murmushi yasake yi, a zuciyarsa yana faɗin"she is just Soo naive".
Taufeeƙ yace "Sir Are we leaving now,Yakamata ka huta fah,". Ɗagowa yayi yakallesa yana jin nishaɗi wanda ya daɗe baiji irinsa ba,ko dan bai taɓa ganin al'adu namu na ƙasar Hausa bane,shi kansa bai sani ba,
Batare da ya kalle shi ba yace "kaje zan dawo anjima, ina son na yi wani abu first".
Taufeeƙ ya buɗe baki zai yi magana ya ɗaga masa hannu kawai, bai sake cewa komai ba ya juya ya bar wajen.
Tsayawa yayi yana tunanin to me ya hanashi komawa gida,what is he waiting for,shi kansa bai sani ba,
kamar ance ya ɗaga kansa ya hangeta tana nufo inda yake,ita kaɗaice sai ɗan ƙaramin sanda,da ta riƙe a hannunta tana wasa da shi,
tsayawa tayi tana magana da su lantana, sai dariya takeyi, Camera ya ɗauka ya cigaba da ɗaukan ta hoto, yadda take dariyan ya sa ya kasa ɗauke idanunsa a kanta,
kamar ance ta juyo kuwa taga, yana ɗaukan ta, a fusace ta taho inda yake, tana kallonsa ta fara faɗin,
"malam wai lafiya", sai da ya kalleta kamar bazai yi magana ba sai kuma ya gyara tsayuwa yace, "me kika gani,na Sanki ne da zaki tambayeni lafiya".
Da mamaki take kallonsa sai kuma tace "baka Sanni ba, Ni ma ai ba saninka nayi ba, to meyasa kake ɗaukana hoto?,
Wani kallo yayi mata sannan yace"sai kuma wa ya ce miki ke nake ɗauka?, saboda ke kaɗai ce, sai ke zan ɗauka?,ga kyawawan ƴanmata nan in rasa wa zan ɗauka sai ke".
Sake baki tayi tana kallonsa sai kuma ta juya a fusace zata bar wajen ba tare da ta ce masa komai ba,
riƙe hannunta taji anyi, da sauri ta juyo tana kallonsa da mamaki, da sauri ya sake hannun nata yana kallonta da idanunsa da suke sakata jin ta kasa nutsuwa,
A hankali cikin lallaɓi yace, "ƙanwata me yake haɗa mu ne kam naga tunda nazo garinnan muke samun matsala da ke", jin a yadda yayi maganan ya sata faɗin"to waya sanine,"
murmushi yayi sai kuma yace to shikenan tunda baki sani ba, can we be friends? Da sauri ta kallesa sannan ta ce ƙasa ƙasa"Ni bana abota da maza"
Kallonta ya ƙarayi,shi dariya ma take basa wallahi, sai kuma yace "kinga Ni baƙo ne a garinnan, ko a garinku bakwa son baƙi ne?
Girgiza kai kawai tayi, yace yauwa ƙawata, to yanzu miye sunan ƙawar tawa a hankali ta ce "Noor"
"Ni kuma Zannur" ya faɗa yana kallonta,murmushi kawai tayi,sai kuma yace to,yanzu kinga tunda mun zama friends shikenan nima sai ki nuna min garinku koh!?, Gobe insha Allahu zan jira ki sai ki zaga dani in ga garinku, ko bazaki nuna min ba? Ya tambaya yana kallonta,
"Zan nuna maka " tafaɗa tana kallonsa, kawai mamaki takeyi daman