Author : Sumayya Abdulkadir Category : Taskar Novels
Mijin-Sakinah,
matukar sabo kuwa. Ya shiga raina fiye da tunani, yau kwana bakwai da tafiyarsa amma har
yau kewarshi ba ta sake ni ba, walwalata ta ragu, farin cikina ya taqaita.
A makaranta ba na tsinana komai, sai tunanin Mijin-Sakinah da al’amuranshi, tareda tuna
abubuwanda suke gudana a tsakanin mu, masu kara min kaunarsa.
Mutum ne mai kyakkyawar zuciya, da kirki na gasken-gaske, tareda biyewa kuruciyata, da
karbar rayuwa a duk yadda ta zo masa. Na samu kaina cikin wani sabon al’amari akan
Abdulhakim. Na soma tambayar kaina shin me ke damuna ne? Ni ‘yar gidan Limamai?
‘Note’ ya taru ban yi ba, sai Nadiya nake kaiwa ajinsu idan ‘yan ajinmu sunyi ta yi min. Don
haka da aka zo jarabawa na kwaso na talatin.
Yau da dare Daddy ya shigo, bayan mun gaisa na nufi kicin na kawo mishi ruwa da lemu, na
zuba mishi a tambulan ya sha.
Ya dube ni sosai ya ce, “Wannan ramar ta mece ce Sakinah?”
Na sunkuyar da kaina ina murmushi, na ce, “Mun yi jarabawa ne Daddy”. Ya ce, “Ina
sakamakon?”
Cike da tsoro na ce, “Yana daki”. Ya ce, “To kawon in gani”.
Jiki babu kwari na shiga daki na fiddo mishi result din.
Ya duba ya dago da sauri ya kalleni, “Na talatin Sakinah?” Na sunkuyar da kai cikin rashin jin
dadi. Kamar ince da kasar ta tsage in shige sabida kunya.
“Sanda kina gida na nawa kike dauka?”
Muryata na rawa na ce, “Na goma ko takwas ko bakwai”.
Ya ce, “Hakan na nufin kina da damuwa a yanzu, wadda ban sani ba? Fada min ko ta mece
ce.....”
Na ce, “Wallahi Daddy babu”. Ya ce, “To me yasa sakamakon ki bai yi kyau ba? Idan
Abdulhakim ya ga wannan zai ji dadi ne?” Na girgiza kai ban yi magana ba.
Ya ce, “To ki dage next term kada inga sakamako irin wannan”. Na ce, “Insha Allahu zan dage”.
“Abdulhakim ya ce in tambaye ki, mene ne amfanin wayar da ya baki don ku dinga gaisawa kika
rufe ba kya budewa?”
Na ce, “Na manta da ita ne Daddy saboda exam, amma yanzu zan bude”.
Ya ce, “Ki bude ki sata a caji, kada ki kara rufewa sai in za ki kwanta barci. Duk wata damuwarki
ki sanar dani kin ji ‘yata Sakinah? Ki dauka ni da M.T duk daya ne, babu banbanci.
Na samu malamin Islamiyya wanda zai dinga zuwa har gida asabar da lahadi ya dinga koyar
dake karatun Alkur’ani da sauran litattafan addini, kina so?”
“Ina so Daddy, na gode sosai”.
“To Allah ya yi muku albarkar biyayyar da kuka yi mana, kuma ya baku masu yi muku
kwatankwacinta, ko fiye da ita. Ni zan wuce, ba kya son komai?”
Na ce, “Akwai komai, kuma akwai kudi, sai dai John ne ya ce yana tunin albashinsa”. Ya ce,
“Babu damuwa, zan ganshi”.
“A gai da Hajiya”.
Ya ce, “Za ta ji”.
Yana fita na yi daki na soma laluben lokas inda na san na ajiye wayata, na fiddota na hada na
jona caji. Kafin a jima ta cika.
Tun ina tunanin Mijin-Sakinah zai kira yau, gobe ko jibi har na hakura, na ci gaba da mai da
hankali a kan karatuna na Islamiyya da boko.
Watanni biyar ke nan da tafiyar Mijin-Sakinah, na dawo daga makaranta ko uniform ban cire ba,
na shiga gidan Hajiyar Abdulhakim don na gaishe ta, kasancewar na kwana biyu ban shiga.
Tun daga bakin kofar shiga falon Hajiya na soma jiyo muryar Mami, gabana ya fadi na juya zan
koma sai gasu sun fito ita da Hajiya, ga dukkan alamu tafiya za ta yi.
Daidai sanda na juya zan tafi Mami ta ce,
“Sakinah, saboda na zo wajenki za ki juya?”
Na juyo na tsuguna a kasa ina gaishe ta. Ta kama hannuna ta dago ni ta ce, “Ki yafeni Sakinah,
kan duk abin da ya faru a baya. Na zo ne in ga dakinki, in kuma baki hakuri”.
Na ce, “Ni baki yi min komai ba Mami”.
Ta ce, “A’a, na yi miki, sai dai ki ce kin yafe ni”.
Na ce, “To na yafe ki, muje kiga dakin nawa”.
Har Hajiya muka je, Mami ta shiga ko’ina ta yaba, dakin Abdulhakim ne kadai a kulle. Na debo
kayan shafa na (Neutrogena) cikin leda na ba ta.
Da kyar ta karba, ta ce, “Ni ya kamata in kawo miki, ga shi ban kawo komi ba sai in amshe
naki?”
Na ce, “Na neman albarka ne Mami”.
Ta ce, “To, Allah ya yi miki albarka”.
Bayan fitar Mami da Hajiya na cire uniform na yi wanka na zuba riga da siket cikin kayan
Mijin-Sakinah, na kunnawa gidan burner da turaren touch me. Na tadda Sabuwa a kicin tana
kwashe abinci.
Na ce, “Sannu da aiki”. Ita ma ta yi murmushi ta ce, “Sannu da dawowa”.
“Yau kin yi lattin gama abincin”.
Ta ce, “Gas ne ya kare, amma akwai electric da shi na yi, kin san kuma ba shi da sauri”.
Muna haka Sadi ya soma shigo da jakunkuna manya-manya. Fitowar nan da zan yi na yi ido
hudu da Abdulhakim a falon yana zaune yana amsa waya, ya mike dogayen kafafunshi
sumul-sumul dasu a kan kilishi ya jingina da throw pillow.
Fitowata ina murmushi bai sa shi ya daina wayar da yake yi ba. Na muttsike idona na tabbatar
shi ne ba gizo idanuwana ke min ba.
Ya kara wani irin kyau mai sanyin gani a ido, fatar jikinshi da sajenshi sunyi sumul sun kwanta
sunyi lumm sai sheki suke, wani lallausar qamshi na tashi a falon wanda ban taba jin qamshi
mai dadinsa ba.
Da gudu na karasa gabanshi na zube daidai kafafunshi ina dariya. Ni kaina na rasa dalilin da
yasa yau ban fada jikin shi ba kamar yadda na saba. Ya rufe wayar ya cillata kan kujera yana
murmushi, “….This is not the kind of welcome I like....”
Ya bude min dukkan hannuwanshi, na fada ciki a hankali, ya rungume ni yana rada min cikin
kunnuwana cewa, “….Sakinah na yi kewarki!”
Yinin ranar zungur, Abdulhakim ko masallaci bai je ba, duk inda ya yi ina naniqe da shi don
tsoron, kada ya sake gudu ya barni.
Yana tambaya ta abubuwan da suka faru a bayanshi. Ya ce in dauko result ya gani. Jiki babu
kwari na dauko na kawo mishi.
Ya karba ya duba, ya qura min ido cike da fushi ya ce,
“Alqawarin mu dake ke nan Sakinah?”
Na girgiza kai na sunkuyar da kaina. Ya ce, “Tunda haka ne tsarabar da na kawo miki na fasa
baki su Nadiya zan aikawa, sannan kawo hannun ki maza mu kwance abotar tamu, daga yau
bana yi da ke”.
Na soma sharar hawaye ina cewa, “Ka yi hakuri ABDULHAKIM ba zan kuma ba”.
Ya yi mamakin kiran sunanshi da na yi a yau, don ban taba yi ba. Ya ce, “To gaya min dalilin da
ya sa ba kya mai da hankali a karatu”.
Na sunkuyar da kaina naki amsawa, ya cigaba da nacin tambaya da kyar na iya na ce,
“Tunaninka nake yi”.
Ba karamin mamaki ya yi ba. Ya ce, “Kuma don kina tunanin mijinki sai ki ki yin karatu? Ba kya
tunanin nima karatun nake yi? Nima ai ina tunaninki, amma bana bari ya hanani ci gaba, ya
hana min yin karatun da zai amfane ni.
Wannan shi ne kashedi na karshe, idan kika kara dauko sama da goma idan na tafi ba zan sake
zuwa ganinki ba sai na gama duka. Ki yi ta tunanin nawa in kinga tunanin shi ya fi dacewa
dake”.
Ya cillar da report din ya mike ya nufi shower.
Ganin yau Mijin-Sakinah ya yi fushi dani, duk sai na ji babu dadi, hankalina ya tashi. Yana fitowa
na kama kafafunshi hawayena na diga akan tafukansa, na ce,
“Don Allah ka yi hakuri bazan sake ba”.
Muryarshi tayi sanyi. Ya ce, “Ni kam me kika yi min da za ki bani hakuri? Iyakaci in kin ki yin
karatu in auro mai karatu wadda za ta koyar da ‘ya’yana karatu, ba wadda za ta koya musu
tunanin miji ba.....”
Na kara tsananta kukana na ce, “Don Allah kada ka auro kowa wallahi ba zan sake ba”.
Ya juya baya yana dariya amma ya gintse, “Saboda me ba kya son a auro wata? Bayan hudu
Allah ya ce in yi?”
Na ce, “Ni dai bana so, don Allah ka bari”.
Ya ce, “Ai ba zan bari ba, idan ba za ki yi karatu ba ni kuma ba zan fasa aure ba”.
Don haka wannan zangon bayan komawar Abdulhakim na nade hannun riga da kafar wando na
durfafi karatu ba ji ba gani, na bokon ne ko na Islamiyyar.
Kuma kwalliya ta biya kudin sabulu na dauko na bakwai a ajinmu. Da Abdulhakim ya zo goyona
ne kawai bai yi ba, don ya nuna min farin cikinshi.Har Daddy ma ya yi murna ya kuma sa min
albarka.
***
Shekara kwana ga mai yawan rai, a yau muka samu hutu wanda daga shi in mun dawo zamu
shiga aji daya na babbar sakandire.
Abdulhakim ya gama course din shi a Beirut ya kuma samu qarin girma a ‘Julius Berger’. Yana
daga cikin ma’aikatansu da suke ji dasu saboda fasahar da Allah ya ba shi.
Idan ya tsara gini, ko bature albarka. Sai dai kokarin da yake na samun ‘transfer’ zuwa nan
Abuja har yanzu bai samu ba.
Shekaru biyu ke nan da aurenmu, wadanda suka yi daidai da cikata shekaru goma sha hudu a
duniya. Zuwa lokacin na fara sanin kaina, na kuma fara sanin wane ne mijina Abdulhakim Khalil
Ribadu?
Dogo ne, ba shi da kauri sosai, kuma ba ya da rama. Wankan tarwada mai mikaqqen hanci, mai
yawan sumar kai, ma’abocin yalwar fararen idanu masu sheki (oily eyes).
Duk inda ake neman mutum ma’abocin kwarjini da kamala za a sanya Mijin-Sakinah a ciki.
Babban abin da ke burge mutane dashi shi ne halayensa masu nagarta.
Mijin-Sakina yana da saukin kai, sannan abin hannunshi bai rufe mai ido ba, kullum bayarwa
yake, kuma kullum kara samu yake.Kin san dai ma’aikatan ‘Julius Berger’. Cikin shekaru biyu
kacal da aurenmu Abdulhakim ya ce ya ga alhairori da budi kala-kala wanda yake da tabbacin
falalar biyayya ga iyaye ne. Don haka yake kara rike ni Sakinah da amana da soyayya ta gaskiya, wadda bai taba tunanin
zai yiwa wata diya mace ba.
Har kuma inda yau ke motsi, bai taba daura min lalurar aure ba. Duk da hakuri yake yi, yana
kuma tunanin Sakinah is too young....... har gobe ya dora mata bukatar auratayya.
Rainona kawai yake tare da koya min soyayyarsa, don haka yake yawan yin azumin tadauwa’i,
wanda ni ban san dalilinsa ba. Illa duk ranar da ya ce yana azumi, in ce azumin me kake? Ya ce
na neman lada man Sakinah!”.
Zan numfasa, muje ga littafi na 2, wanda tare yake da dan uwansa, maman Safah da Marwah
ce……