Zuciyar Mutum Book Complete By Sumayya Abdulkadir Takori .pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Taskar Novels

Chapter   6 / 7

15K to 18K   out of 19.8K words

da kika ga Abba kike kuka?”
Na ce, “Saboda ban taba rungume shi bane a rayuwata sai yau”.

Ya kwanta sosai cikin kilishi ya ce, “Bani labarinki Sakinah, kin ce Mamanki tana Libya, ga
Abbanki kuma a nan, basa tare ne?”
Na ce, “Basa tare, nima ban santa ba, Abba ya ce tun sanda ta yayeni ta tafi”.
Ya ce, “To wace ce ta rike ki?”
Na ce, “Mami matarsa”.
Ya ce, “Hajiya Lami ke nan qawar Hajiyata?”
Na ce, “Eh”.
Ya ce, “Bana son matar nan ban san me ya sa ba. Bana son tarayyarta da Hajiyata, tun daga
lokacin da Hajiya ta sani na kaisu wani qungurmin jeji tare a Bidda”.
Na yi shiru ban ce komi ba, don ba zan iya zagin Mami a idon kowa ba. Na riga na yafewa
Mami duk abin da ta yi mini, tunda dai ta rike ni da dadi ba dadi har na kawo munzalin da nake
a halin yanzu.
Na soma hamma, yana magana bana jin shi sosai saboda barci da ya ci karfina. Ya mike ya
miko min hannunshi na kama, har dakin barcina.
Na kwanta a gado, ya ja bargo mai laushi da taushi ya rufe ni, sannan ya dauki ‘remote’ ya rage
karfin A.C
“Sleep well matar Abdulhakim……!”. Na ji shi yana fadi sama-sama. Sabida tuni barci ya ci
karfina. Ya fita ya ja min kofar.
***

Washegari ma tare muka hada kalaci, sannan na shirya cikin ‘uniform’ dina. Na juya na dubi
kaina a mudubi. Ni kaina na firgita da irin kyawun da na ga na yi cikin dan lokaci qalilan.
Ya fito shi ma cikin shiri na dakakkiyar baqar shadda galila, sai maiqo take. Na ce, “Mijin
Sakinah ka yi kyau”.
Ya ce, “Allah Sakinah? Don baki ga naki kyan cikin uniform din nan bane”.
“Ina uniform ya ga kyau Mijin-Sakinah?”
“Yana yin kyau a jikin special people (mutane na musamman) irin Sakinah Abdulhakim”.
“A’a, Sakinah M.T Liman nake, kowa haka yake kirana a makaranta”.
Yace “tuni kika tashi daga Sakinah M.T Liman, kin dawo Sakinah Abdulhakim Khalil Ribadu”.
Sai na yi murmushi ban ce komi ba.

Muna tafe a hanya kira’ar Abdurrahman Sudais na tashi cikin (Suratul A’araf), har muka iso
makarantarmu. Ya yi parking a inda aka tanada don adana motoci muka karasa ofishin
principal, ya yi ta bata hakuri kan rashin zuwana makaranta na lokaci mai tsawo bana jin dadi
ne, da kyar ta hakura.Ya ce dani, Daddy zai zo da kanshi ya daukeni in an tashi, daga gobe
kuma akwai direba John da zai dinga kawoni yana dauko ni kullum”.
Ya kara jaddada min in kama kaina ba ruwana da kawaye, kuma kada in dinga fada musu an yi
min aure, kowa ya ce me ya sa bana zuwa in ce bana jin dadi ne. Shi zai wuce Lagos sai ya
dawo.
Ina yi mishi bye-bye har ya qule na daina ganin shi bai daina daga min hannu ba.

Da aka fito break muka hadu da Nadiya muka yi ta tsalle muna labarin bayan rabo. Daga
bayanmu Safinah ta daka mana tsawa.Ta ce,
“Ke Sakinah yanzu fa ba daya kike da Nadiya ba da za ki biye mata kuna tsalle-tsalle. Girma ya
hau ki, kada in kara ganinki kina wannan tsallen”.
Karfe biyu Daddy da kanshi ya zo ya dauke ni. Na tarar da Sabuwa mai aikin da Abba ya dauko
min daga ‘Yan Leman har ta rigani isowa, muka gaisa na wuce daki don in cire kayan
makaranta.
Zaman mu ni da Sabuwa gwanin sha’awa, Sabuwa mace ce mai tsafta da zafin nama, kafin in
tashi barci ta rigani ta tsaftace gidan, kafin in gama wanka in yi shirin makaranta ta kammala
kalaci ta zuba min wanda zan tafi da shi cikin flask, sai in ci in fito in tadda John mu wuce
makaranta. Yau da aka fito break muka hadu ni da Nadiya muka nufi gindin bishiyar goba muna cin abinci,
na Nadiya muke fara ci sannan mu ci nawa.
Muna ci ta ce, “Sakinah ya ya sunan mijinki?’ Na ce, “Sunan shi Mijin-Sakinah”. Ta ce,
“Mijin-Sakinah?’ Na ce, “Eh, shi ya ce min sunanshi haka”.
Ta jinjina kai ta ce, “Uhm! Ban taba jin wannan sunan ba”. Na ce, “To haka ya ce sunansa”. Ta

ce, “Kin san kuwa Abba ya auro Yaya Suwaiba ta ‘Yan Leman?”
Cikin mamaki na ce, “Yaushe?”
“Yau satinta daya, kuma Mami da Adama sun yi fada ta kore ta, don ta gane cutarta take, in ta
aike ta wajen malamansu ba ta zuwa sai ta zuba kudin a aljihunta ta kawo mata magungunan
karya.
Yanzu gaba daya Abba ya watsar da Mami sai Yaya Suwaiba, kuma ya hanata zuwa ko ina.
Mami har tausayi take bani”.
Na ce, “Allah sarki Mami, gara ta rabu da Adama, don ba mutuniyar kirki ba ce, amma inda za
ta gane ta zauna lafiya da Yaya Suwaiba don tana da kirki sosai”.
Ta ce, “Abin da Yaya Safinah ta gaya mata ke nan”.
Aka kada kararrawa muka koma aji. Har aka tashi yau ina tunanin hirar da mu kai da Nadiya.
Gaskiya ne addu’a ba ta faduwa kasa banza, addu’ar da nake kwana da wuni ina yiwa Abbana
a kan Mami, ba ta fadi a banza ba. Tunda gashi alqadarinta ya soma karyewa, Abba ya fara
zama namijin duniya.
Tunda Mijin-Sakinah ya tafi, bamu gaisa ba, don bani da waya. Ga shi ya ce in zai dawo zai
sanar dani in yi mishi girki.
Don haka na bi na damu, don ban san ranar da zai dawo ba. Sai na kintata tunda ya ce wannan
satin ba zai zo ba sai sati na sama, don haka ranar juma’a ta sama na shiga kicin don ganin
abin da ya dace in girka masa.
Sakwara na fi kwarewa da yi, saboda yadda Mami ke son ta, take kuma yawan samu mu yi ni
da Adama. Don haka da kaina na kirba doyar a turmi.
Sabuwa na yankan alayyahun miya muna hira, sannan na fiddo kayan ciki a firji na wanke na
dora sanwar farfesu. Ina gamawa na yi wanka na sanya daya daga cikin riga da siket da
Mijin-Sakinah ya sayo min na fesa turare na dawo falo na zauna kallon mutanen nawa
(larabawa) a tauraron dan adam. Shiru-shiru tun ina duban kofa har na soma mikewa ina leka waje, babu Mijin-Sakinah babu
alamun shi. Har magariba babu shi babu Abdallah.
Na dawo cikin kujera na yi zugum dani, damuwa karara ta bayyana a fuskata. Kamin ka ce
meye wannan? Sai hawaye, wasu na korar wasu.

Aka murda kofar falon a hankali aka shigo, na daga kaina a hankali don ganin mai shigowa.
MIJIN-SAKINAH ne, rataye da falmaran din baqaqen ‘Italian Suit’ da yake sanye dasu.
Ya yi tsaye a kofar yana kallona yana murmushi, hannayenshi duka biyu zube cikin aljihu, kafin
ya bude min dukkan hannuwanshi da nufin in zo gare shi, na maida hannuwa na baya na
sarqesu ina murmushin da ni kaina bansan irinshi ba.
Murmushin farin-ciki indeed! Amma hawayen basu bar ambaliya ba.
Da sassarfa ya karaso gareni, ya rage tsaho ya rankwafa ya kamani ya rungume, muka saki
ajiyar zuciya mai nauyi a tare. Ya dago fuskata da hannun daman shi ya soma share min
hawayen.
Ya ce, “is O.K matas, na yi laifi da na dade ban iso ba, ba zan kuma ba, ban taso da wuri bane
sakamakon dimbin ayyuka da suka tare ni. Ki yafe ni........ I’m terribly sorry….!”.
Ya kai gwiwoyinshi kasa ya kama fatar kunnenshi, ya sake cewa, “I’m-sorry!”

Na tuntsire da dariya duk da maqalallun hawayen da ke idona.

Ya mike yana cewa, ‘Lemme take a shower, I’ll be back to you soon.... (bari inyi wanka ina zuwa
gareki yanzu)”
Ya wuce dakinshi yana cewa, “Biyoni da brief case din nan”.
Na dauka na bishi a baya.

Ban taba shigowa dakin Abdulhakim ba sai yau, makeken family bed ne dan kasar Italy, sai
wardrove ta jikin bango, sittirun shi ne a jere reras saqale jikin ‘hanger’ wanda duk rabi suit ne
kala-kala, baqaqe da rowan toka samfurin Tommy Hilfiger, Armani, Louis Vuitton, Dolce and
Gabbana, Versace, DKNY gasunan dai barkatai wanda kallonsu kadai ya isheka kimanta
tsadarsu, sun kuma isa su nuna maka cewa mamallakinsu dan gaye ne na karshe.
Dakin shimfide yake da marbles farare sol har a jikin bango. Sai split mai kwararar da
ni’imtaccen sanyi wanda ya gauraye da qamshin room-freshna respberry ya ba da wani nau’in
sanyi da sassanyan qamshi mai ratsa zuciya.
Sai dai dakin a hargitse yake ko ina takardu da taswirar zane-zane. Don haka yana shiga
shower na soma kintsa dakin.
Na hada takardun wuri daya na adana komai a muhallinsa, na sa mopper ina goge marbles,
nan da nan dakin ya hau sheki.
Ya fito daure da tawul ya tsaya yana mamaki. Na dago ido na kalle shi na yi saurin dauke ido a
kanshi, don ban taba ganin babba babu riga ba.
Ya yi murmushi ya ce, “Haka kike da aiki Sakinah?” Ban amsa mishi ba, na soma kokarin fita ya
riko hannuna na kuwa tamke idona tam!
Ya langabar da kai abin tausayi ya ce, “Ni mijinki ne Sakinah, ki rage jin kunyata”. Na ce, “Ai fita
zan yi kasa riga”. Ya ce, “To ai ni wai da tausa nake so ki yi min”. Na zaro ido. Babu bata lokaci
na ce, “Ban iya ba”. Ya ce, “To zo in koya miki”. Ai kuwa na ce kafa……. me na ci ban baki
ba…..na falfala da gudu na koma kichin. Ban kara dawowa ba. Ina jera abinci a dining ya fito cikin caftan na wata jiqaqkiyar wagambari deep green, sai sheki
take saboda maiqo.
Ya tsaya jikin tebir din yana kallona, na dukufa wajen shirya table, ya ce, “Dama kin daina
wahalar da kanki, wajen budurwata dana gaya miki labarinta zan je in ci, kuma ta yi min tausa”.
Da sauri na dago na dube shi, na kuma yi saurin sunkuyarwa don fuskarshi babu alamun wasa.
Na ji wani haushi ya zo ya tokare ni a zuciya.
Zai wuce na yi saurin shan gabansa, idanuna rau-rau suna niyyar zub da hawaye, “Don Allah
kar ka je”.
Ya dube ni sosai kamar yayi dariya amma ya dake, ya ce, “In ban je ba za ki yi min ne?” Da
sauri na daga kai. “To amma kar ka cire riga”.
Ya murmusa ya ce, “Ba zan cire ba, amma mu fara cin abincin”.
[9/14, 9:59 PM] Asmau: Na ji dadi, na dau filet na soma zuba mishi. Ya soma ci ya ce, “Amma
dai da inji kika daka sakwarar nan”.
“A’a, da hannu ne, me ka gani?”
“Ta yi kyau ne sosai, ga dadin taunawa, you are a good cook, na gode Sakina”.

A kwana biyun da Abdulhakim ya yi wannan satin, na qware da yi mishi tausa, mun kara
shaquwa, kauna ta musamman ta kara habaka a tsakaninmu. Har tsoro nake lahadi ta zo ta
rabani da mijin Sakinah (kamar yadda ya kirayi kanshi) ya kuma ce min da hakan yake so in
dinga kiran shi don yana jin dadi a ce shine mijin Sakinah. Ya koma ranar lahadi nima na koma makaranta ranar litinin. Jarabawar karshen zango na uku
ta matso, wadda daga ita zan shiga aji uku na karamar sakandire.
Mun samu hutu bayan kammala jarrabawa, Abdulhakim yana Lagos, sai karshen satin nan
muke sanya ranshi.
Na duba kicin na tarar duk naman da ke cikin freezer ya kare. Na kira Sabuwa na ba ta kudin
cefane har da naman.
Bayan ta kawo muna killace kowanne a inda ya dace, kararrawar kofar shigowa ta yi kara.
Sabuwa ce ta je ta bude, sannan ta gaya min cewa ina da baki.
Na wanke hannuna da sabulu cikin sink na fito, nan na yi arba da Abbana, Safinah da Nadiya
da autanmu Nazir.
Na yi tsalle na rungume su daya bayan daya, na rasa inda zan sa kaina don murna. Nan muka
shiga hidimarsu ni da Sabuwa.
Safinah da Nadiya suka ce, “Mami na gaishe ki”. Na yi murmushi na ce, “Ni kuwa?” Abba ya ce,
“Mamin ku na gaishe ki da gaske, da tare ma zamu zo to sai ta yi baki”.
Nadiya ta ce, “Baki san Mami bane ta sauya yanzu. Yaya Suwaiba ma tana gaishe ki, za su zo
tare da Mami”.
Na ce, “Duk ina amsawa Allah ya kawo su”.
Mun kebe ni da Abba a karamin falon Abdulhakim, mun baro su Safinah suna ta ciye-ciye. Abba
ya ce, “Babu matsala dai ko Sakinah?’
Ina murmushi na ce, “Babu Abba”. Ya gaya min cewa ya je Libya yana kara bincike har ya samu
mutumin da ya gaya mishi sunan garin da su mahaifiyata suka koma a Egypt wato Qatar, yana
nan yana fafutukar neman adireshin, da ya samu zamu je insha Allah.
Da wannan daddadan labari suka tafi suka barni. Ko da Abdulhakim ya zo a wannan satin da
labarin da na tare shi da shi ke nan, shi ma ya tayani murna.
Ya sunkuce ni muka yi dakinsa yana cewa, “Ki yi min tausa..... I missed your tausa Sakinah….!”.
Sai da nayi mishi tausar ya tausu, ya kama hannuwana ya rike cikin nasa, ya soma murza ‘yan
yatsuna a hankali yanayinshi yana sauyawa a yau. Yana kallona da wani irin murmushi mai
sanyi da sanyaya zuciya.
Na kwace hannuna na ce, “Barci kake ji ne Mijin-Sakinah?”
Daga can karkashin maqoshinsa ya ce, “Uh!”
Na ce, “To bari in tafi ka kwanta”.
Ya girgiza kai ya kara damke hannuna, damka sosai kamar zai ballani, nayi ‘yar kara nace “zaka
karya ni” yace “bazan karyaki ba, amma Sakinah Mata da mijinta basa raba makwanci Sakinah,
yau dai daya da zan yi miki sallama, ki tayani kwana!”.
Cikin firgici na ce,
“Ina za ka je?”
Ya yi matashi da kafafuna yana ja min yatsu a hankali ya ce,
“Wajen aikinmu sun zabe ni zan tafi wani course a Beirut (Lebanon) tsayin shekaru biyu...... ba
don makarantarki ba da tare zamu tafi, amma zan ke zuwa akai-akai ina ganin ki...”.

Kuka nasa sosai, “Ni ba zan zauna ba, wallahi sai dai mu tafi tare ko ka mai dani gidan
Abbana”.
Ya ce, “Gidan Abba kuma? Kina so Mami ta ci gaba da lakadarki ko?”
Na ce, “To zan bika”.
Ya ce, “Makarantar fa? Na gaya miki zan dinga zuwa ba zan yi watanni uku ban zo ba”.
“To ka mai dani gidanku wajen Hajiya”.
Ya ce, “A gidanki za ki zauna, ita ma Hajiyar a gidan mijinta take”.
Na ci gaba da sharar hawaye yana lallashina.

Washegari tunda muka yi sallar asubahi bamu koma barci ba. Nasihohi yake yi min a kan in
kula da kaina, in kula da amanar aurenshi, in mai da hankali a kan karatu.
Ya ce yana so kafin ya zo in dauko 1st position zai yi min babbar kyauta. Ya fada toilet ya yi
wanka ya shirya cikin riga da wandon versace, yana kumbing kanshi, ya juyo ya dube ni na yi
tagumi a gefen gadon shi, idona cike taf da kwallah.
Ya aje matajin ya karaso ya tsuguna a gabana, ya kama hannuwana sannan a nutse ya ja ni
cikin jikinshi, ya soma kissing bakina zuwa dogon wuyana bayan ya rike tufkar gashina da
hannun hagunshi, cikin wani irin ‘passionate kissing’ mai tsirgawa har cikin kwakwalwa…..
Da karfi na yi baya, na ce, “Wannan ai iskanci ne Mijin-Sakinah, meye haka? Sai kace wasu
tantabaru?……”.
Ya rufe baki yana dariya ya gyada kai ya danne dariyar ya ce,
“To na daina iskanci, sallama ce nake miki matar Abdulhakim irin ta turawa, ko ba kya gani suna
yi a talabijin”.
Na ce, “Ina gani, amma kai ai ba bature bane, don me za ka kwaikwaye su bayan su ‘yan iska
ne daman?”
Ya kama baki ya girgiza kai yana so ya kara yin dariya amma ya dake, ya kama hannuna muka
zauna a gefen gado. Ya jawo loka ya debo kudi masu kauri ya zube min a cinya.
Ya ce, “Ku dinga yin cefane kafin in zo”.
Sannan ya miko min kwalin waya yana nuna min yadda zan ke amfani da ita, na rike wayar nan
ina murna. Ya kama hannuna ya lumshe ido ya ce,
“Sakinah me za ki bani? Wanda zan ke tunawa da ke kullum?’
Na ce, “Me kake so in baka?” Ya rufe ido ya nuna min kuncinsa na dama, “Kiss me here........”
Na zaro ido na ce, “Allah ba zan iya ba”.
Sai ya kamoni ya rungume a kirjinsa yana saukar da numfashi da sauri da sauri. Ya ce, “I will
miss you so much...... plz Sakinah kiss me....”
Jin roqon ya yi yawa, ga shi yana ta bata lokaci, sai na runtse ido na yi yadda yake so. Nayi
mishi sumba, mai tsayi, da zurfi. Ya kara kankame ni qam-qam tamkar ya tsaga kirjinsa ya
sanya ni.
Al’amarin ya soma kokarin sauya alkibla daga Abdulhakim a yau, gabadaya ya rikice mani, da
wasu sabbin al’amura da ban sani ba, ban kuma taba tsintar kaina a ciki ba,ban sansu ba, cikin
kananan shekaru na, wanda hakan ya haifar da matsanancin tsoro a gare ni.
Sallamar Abdallah a falo ita ta katse duk wani hanzarinsa, ta qwaceni daga hannun mijin
Sakina, wanda nake tunanin babballani yake so ya yi, na rufe ido saboda kunya, duk ya
cukuikuiye min shaddata da ta sha guga.

Ya ja babbar jakar na ja karamar muka fito falo. Abdallah ya ce, “Kana duba agogo kuwa? Ka
san nisan airport din nan amma ka yi zamanka. Sakinah dauko mayafinki mu tafi su Daddy
suna mota suna jira”.
Ya ce, “Ba za ta je ba, don kuka za ta yi”. Yasa murya yai kiran Sabuwa, ta fito suka gaisa. Ya
ce, “Ni zan tafi, don Allah ki kula da gida da Sakinah”. Ta ce, “Insha Allah Alhaji”. Ya fita yana
waiwaye na ni kuma ina sharar hawaye.

Tun tafiyar Mijin-Sakinah sai na zama wata irin sukuku ba kuzari, na saba da

6 / 7