Author : Sumayya Abdulkadir Category : Taskar Novels
sunkuyar da kai na ce,
“Daddy ina so in koma makaranta”.
Ya ce, “Wacce kike zuwa?” Na ce, “Al-Amin International”. Ya ce, “Bari zan yi waya da
Abdulhakim in ba zai samu zuwa ba wannan satin sai Abdallah ya mai da ke”. Na ce, “Daddy na
gode”.
Ya yi murmushi,
“Babu godiya tsakaninmu Sakina, ni Babanki ne kin ji?” Na gyada kai.
Daddy yana isa ofis ya kira Abdulhakim a waya, ya yi qasa da murya yana gayar da Daddyn. Ya
amsa, ya ce,
“Ya ya Abdulhakim za ka samu zuwa gida this week?”
Don kada Daddyn ya dago shi a kan kin zuwa gida da yake yi ya ce,
“Zan zo insha Allahu”.
Ya ce, “To shi ke nan Allah ya yi maka albarka”.
Karshen satin ya tattaro ya nufo gida Abuja. Wannan satin ya riga Abdallah sauka, wanda bai
iso ba sai yamma lis. Tunda ya zo yana tare da Hajiya suna zancen tsarin filinta da za a soma
gini, ta bar zancen gini ta dube shi sosai ta ce.
“Abdulhakim”.
Ya dago ido ya dube ta ba tare da ya amsa ba. Ta ce, “Fisabilillahi me kake nufi da auren ka?
Ina lura da kai har yau baka je inda matarka take ba. Ba fa kare aka ajiye maka ba dan mutum
ne mai kima da daraja. Idan har kana so mu shirya, to a yau nake so ka tattara komi naka ka
koma gidanka, kada ka bari Daddy ya san halin da kake ciki ranshi ba zai yi dadi ba”. Haka ya taso ya fito duk jikinshi babu kwari. Ba ranshi ne ya baci ba, yarinyar ce kawai ba ya
so. A ganinsa he is old enough da ya yi ma kanshi zabin abokiyar rayuwa tunda Daddy bai fi shi
idon ganin mata ba. Ba kowacce mace ce ke da abubuwan da yake so a diya mace ba sai
FARIDA. Ya soma tattare duk wani abu da ya san mallakinshi ne daga dakinsu da Abdallah yana
sanyawa a katuwar jaka, ya kammala ya kira Sadi mai wankin Hajiya ya soma diba yana kaiwa
gidanshi. Bayan ya ba shi mukullin dakin da zai sanya su.
Ladiyo tana dakin da ya zama nata tana barci, ni kadai ce a falo kishingide a three seater, cikin
doguwar riga kirar Bahrain baqa wuluk. Da ‘remote’ a hannuna ina kallon yadda sojojin Amurka
ke ragargaza ‘yan’uwa musulmin Palastine da tankokin yaki. Hawaye shabe-shabe a idanuna
don tausayi.
Wata sassanyar murya mara amo, wadda ke dauke da rashin kuzari ta yi sallama a falon,
mamallakin gidan ya bayyana zahiri yau a gabana.
Ba sai an gaya min ba, kallo daya na yi mishi na gane shi ne dan Alkali Khalil Ribadu, kuma
mijina, saboda tsabar kamannin su.
Abdulhakim ya dade a tsaye hannunshi zube cikin aljihun sassalkar farar shaddar ‘getzner’da
yake sanye da ita dinkin Mohammed, yana nazarin yarinyar da aka kira, SAKINAH, kuma
MATARSHI. Kallo na rahama da salama, wanda bai san yaushe kwayar idanunshi ta rikide ta ke
yi ba. A zahiri kuka take, tana kallon talabijin, amma bai taba ganin wadda hawaye ya yiwa kyau
irin wannan yarinya ba.
Duk wani kulli, fushi, bacin rai da ke cikin zuciyarshi sai ya ji yana bacewa. Ya ci gaba da kallon
ta, kallon rahama, cikin dakikan da basu gaza biyar ba. Kafin ya yiwa kanshi mazauni a daya
daga cikin kujerun da suka yiwa kayataccen falon qawanya.
Da bayan hannu nake share hawayen kamin in sauko da gwiwoyina kasa ina gaishe shi, alama
ya yi min da in koma in zana bisa kujera. Allah mai juya al’amura, a take Abdulhakim ya ji nan
duniya ba abin da yake so irin Sakinah.
“Ke kadai ce a gidan?”
Ya tambaya cikin kallo na. Girgiza mishi kai na yi alamar “A’a, ba ni kadai ba ce”.
“Kukan me kike yi?” Ya sake tambaya.
Da dan yatsana na nuna mishi talabijin,
“Suna ta harbin musulmi ne”.
Ya kai ganin shi ga tashar CNN ya yi murmushi, “Ni a ganina addu’a ya kamata ki tayasu ba
kuka ba”.
Na sake share hawayen ba tare da na yi magana ba.
“Kin sanni?”
Ya tambayeni yana nuna kanshi da dan alinshi.
Gyada mishi kai na yi alamar, “Eh, na sanshi”.
Ya yi murmushi ya ce,
“Kin sanni ke nan Sakinah?”
Na ce, “Eh”.
“Ya ya sunana?”
Wannan karon girgiza kai na yi, wato ban sani ba.
“Ashe mace tana manta sunan mijinta?”
Ya tambaya with a low tune.
“Ba mantawa na yi ba, ban sani bane”.
Ya yi murmushi, “To daga yau in kin ganni na zo gidanki, sunana MIJIN SAKINAH”.
Da sauri na dago na dube shi, “Mijin Sakinah?” Na tambaye shi cikin sigar tambaya.
“Eh, mijin Sakinah”. Ya maimaita cikin tabbatarwa, dauke da siririn murmushi bisa siraran
lebbansa.
Nima sai na yi murmushi na ce, “Wannan ba suna bane”.
“In ba suna bane mene ne?”
“Inkiya ce”.
“Ashe kina da wayo? Su Hajiya suke cewa Sakinah yarinya ce?’
Murmushi na yi, “Ni ba yarinya ba ce, ina da kannena ma Nadiya, Ilyas, Nazir da Abba, duk na
girme su”.
Ya yi dariya wadda ta fiddo wasu fararen jerarrun hakora kamar kankara, ya ce, “Ina ma nine ke
Sakinah, ni bani da kanne”.
Na ce, “Kai kadai ne a gidanku?”
“Ni kadai ne Sakinah”.
Na ce, “To ba gani ba an kawoni gidanku sai in zame maka kanwa”.
Ya dara sosai, kafin ya ce, “I like you girl…., zo mu kulla abota”.
Na rufe fuskata da tafukana ganin ya miko min hannunshi. Wanda ke daure da wani irin
sassalqan agogo samfurin ‘swatch-blustery’. Ganin na rufe ido naki mika mishi hannun. Sai ya
taso ya iso har gabana, ya kai hannunshi ya bude tafukan da na rufe fuska dasu. Na kuwa
kyalkyale da dariya. “Kin ce fa ni Yayanki ne don me za ki ji kunyata?”
Dariya ta kamani, na cigaba da kyalkyalawa sosai, bai katseni ba sai da na gama. Yana
murmushi ya ce,
“Wani ya taba gaya miki kina da kyau Sakinah?’
Kamin ince komi ya miko min dan yatsanshi na mika nawa, muka sarqe su, ya ce, “Friends…?”
Na gyada kai cikin murmushi.
Daidai lokacin da Inna Ladiyo ta fito daga daki ta ga mutum durqushe gaban Sakinarta ya kama
hannuwanta ya cukuikuiye, ta saki salati mai razanarwa ta ce,
“Wane ne kai?”
Mikewa ya yi yana dariya ya russuna yana gaishe ta, amma ba ta amsa ba tambayar shi ta
sake yi,
“Wane ne na ce?” Ya sunkuyar da kai kafin a hankali ya ce,
“Abdulhakim”.
Ta ce, “Ba sunanka na tambaya ba, cewa na yi wane ne kai? Ko kuma don kana Abdulhakim
sai ka shigo gidan matar aure ka cacumi hannayenta?”
Dariya ya sake yi sosai kafin ya yi magana nayi hanzarin cewa.
“Inna shi ne MIJIN-SAKINAH”.
Ya kama baki yana mamaki, ya ce da Inna,
“To kin ji Sakinah ta hutassheni”.
Kunya ta kama Inna ta juya tana cewa, “Au maigidan ne? Ai ni fushi nake da kai tunda na zo
gidan nan yau sati hudu baka kawo min kudin cefane ba”.
Ya ce, “Ki yi min uzuri Inna, bana nan ne ina wajen aiki, amma tunda gani na dawo cefane sai
kin ce ya ishe ki”.
Ta koma daki ba ta kara magana ba. Aka danna kararrawa, ya isa ga kofar ya bude. Hajiya
Laila da Abdallah suka bayyana a falon.
Ta kalli kowannenmu, sannan ta yi murmushi cikin jin dadin ganin fuskar Abdulhakim da
walwala. Ta ce,
“Sakinah yau ga maigida ya zo, babu sauran damuwa ko?”
Na yi murmushi ban yi magana ba. Shi kuma Abdallah sai ya tintsire da dariya ganin ‘yar
kwailar matar Abdulhakim.
Don haka Hajiya tana ba da baya Abdulhakim ya harare shi, “Uban me kake yiwa dariya?”
Bai ba shi amsa ba ya ce,
“Sakinah baki sanni ba ko?”
Na yi murmushi. Ya ce, “Laifin angon ki ne da bai yi introducing dina (gabatar dani) ba. I’m
Abdallah Ribadu”.
Na ce, “Sannu da zuwa Abdallah”. Ya ce, “Kema sannunki da zuwa cikin family dinmu. Ga nan
Abdulhakim shi ne angonki, yana ba da hakurin rashin ganinshi tun lokacin da aka kawo ki,
wannan ya faru ne a dalilin ayyuka da suka sha gabansa.
Abdulhakim mai kirki ne Sakinah, ki saki jikinki cikin gidan auren ki kike. Ai kina son shi ko?” Ya
fadi cikin daga gira.
Na rufe fuska da hular da ke jikin rigata, kafin in falfala da gudu in yi daki. Ina jiyo dariyar su da
hirarrakin su, har aka yi kiran sallar magariba suka fita.
Karfe tara na dare na fito falo saboda in ci gaba da kallon yakin Larabawa da nake son gani.
Mijin-Sakinah ne a kan dining yana cin abinci.
Ya ce, “Kawo min ruwa Sakinah”. Na nufi kicin inda firij yake, Uche (kukun gidan) ne yake
wanke kwanukan da ya yi amfani dasu a sink, ya russuna yana gaisheni kamar kullum muka
hadu a kicin din.
Na dauko robar ruwan FARO da lemun Squashda kofi na dora a karamin faranti, na kawowa
Mijin-Sakinah.
Murmushi ya yi ya nuna min kujerar kusa da shi ya ce in zauna. Na zauna ina cewa, “Ina
Abdallah?” Ya yi murmushi ya ce,
“Shi gwauro ne, yana can dakin gwauraye yana cin nasa abincin”
[9/14, 9:59 PM] Asmau: Abin ya baiwa Kawu Tasi’u dariya, har sai da ya murmusa a
mamakance da abin da M.T ya yi mata a yau, ta figi waya ta yi kiran aminiyarta Hajiya Laila.
A tare dukkansu suka hada baki suka ce,
“Kin ji abin da M.T ya yi min ko?” Amma ita Lailar cewa ta yi,
“Kin ji abin da Ribadu ya yi min ko?”
Mami ta ce,
“Wai ya aurar da Sakinah”.
Hajiya Laila ta ce,
“To ai nima haka yake gaya min yanzu, wai ya karbawa Abdulhakim aure, yaron da ke cikin
halin jinyar zuciyarshi a kan rasa yarinyar da yake so?”
Mami cikin tangardar harshe da matsanancin faduwar gaba ta ce,
“To ko dai Sakinah ce ya aura mishi?”
Hajiya Laila ta yi wata sassanyar ajiyar zuciya a ranta ta ce,
“Allah ya sa!”.
Amma a fili sai ta ce,
“To wa ya sani ne? Ni aikin Na-dutse ban ga yana ci kamar na dan Ikko ba. Kwata-kwata na
kasa gane kan Ribadu a kwanakinnan. Idan ya yi kamar ya zo hannu sai kuma ya baude ya
dinga yi min abubuwa na gadara.
Yanzu saboda Allah ya dace ya yiwa dana aure ba tare da sanina da yardata ba? Idan ke bake
kika haifi Sakinah ba ai Abdul ni na haife shi”.
Mami ta ce,
“Na shiga uku ni Lami! Idan Abdulhakim ne mijin Sakinah na fadi ba nauyi, na tabbata daga
Safinah har Nadiya babu wadda za ta yi sa’ar da ta yi.
Wato Sai da ya daddage ya zabo miji na nunawa sa’a, ya tsallake ‘ya’yana ya ba ta.....”. Ta
rushe da kuka.
Hajiya Laila wadda ke ta hamdala a zuciyarta ta ce,
“A’a, Lami kar ki kuka, babu abin kuka a nan”.
“Ya ya ba zan yi kuka ba? Abdulhakim mijin Sakina........duk mugun burin da naci a kan yarinyar
nan ya ruguza min shi, ya shammaceni, ya yi min bazata.
Ni ina tutiyar na mallake shi, ashe har yanzu gangar jikinsa na mallaka zuciyarsa na kan
Sakieenah da ‘yarta. Ki taimake ni Hajiya Laila kada ki bari auren nan ya je ko ina”.
Hajiya Laila ta ce a ranta, me zai kaini yin surukuta da ke Da na ya zama M.T Liman? A fili
kuma tace.
“A wane dalili? Kina tunanin idan na raba auren zai yiwu ya auri Safinah ne?”
Ta ce, “Na san ba zai yiwu ba, amma akalla duk sun rasa”.
Hajiya Laila ta yi murmushi ta ce, “In gaya miki gaskiya? Irin auren da nake so Abdulhakim ya yi
ke nan, ba wannan auren da ya je nema aka hana shi ba.
Bana son Abdul da auren macen da yake so, don ni hoto zan zama, in zama kura da shan bugu
gardi da amshe kudi.
Don haka na karbi Sakinah a surukata, ba ya sonta kuma ita ma ba ta san komi ba, sai abinda
muka koyar da ita, don haka ki sanya ranki a inuwa.
Idan har Sakina ce surukata na karbe ta da hannu bibbiyu, ga kyau ga kyan hali.
Ga shi ta fito tsatson mutumin kwarai irin M.T Liman. Ni kuwa Laila me zan nema a suruka
tagari banda wannan?”
Mami ta saki kunnuwa tana sauraron aminiyarta cike da mamaki, ta ce,
“Haka za ki min Hajiya Lailah?”
Ta ce,
“To ya kike so ayi? Don Sakinah tana ‘yar kishiyarki cewa nake ita ma ‘yar M.T Liman ce?”
Mami ta kara rikicewa da mamakin Hajiya Laila, ta kashe wayarta tana jujjuyata cike da zargin
ko karya ta gaya mata? Ko kuwa mafarki take? Laila ta fi kowa sanin yadda ba ta kaunar
Sakinah, amma yau ta zabi su bata a kan Sakinah.
Karfe biyar na yamma Kubra, Dije da Zainaba kannen Abba da Suwaiba ‘yar Baffa Sule, da
Innarta Ladiyo suka iso Abuja a 506 din Abba da ya tura a debosu daga ‘Yan Leman. Abba ya
ce ba ya son wani bidi’a, su gyara ni washegari su rakani dakin aurena, kada su damu da Mami
da duk abin da zatayi bata da cikakken hankali.
Ban san abin da ke faruwa ba, ina bayan gida ina wankin kayan Mami. Nadiya ta lallabo ta rufe
min idanu da hannunta ta baya, na soma kici-kicin ture hannunta ta rankwafa dai-dai kunnena
ta rada min;
“Albishirinki, wai Abba ya yi miki aure, wai yau za a kai ki gidanki, ga ‘yan ‘Yan Leman can ma
sun zo tafiya dake”.
Na dube ta galala! Ban damu da abin da ta ce ba na ci gaba da wankina. Ta ce, “Wallahi
Sakinah da gaske nake, har goro da alawa mun ci”.
Ta waiwaya ta tabbatar ba mai kallonmu, ta kara kaskantar da murya ta ce, “Har da kudin
sadakin mun gani, Mami ta watsar dasu a falo”.
Ba ta rufe baki ba Ladiyo da Zainaba suka shigo daga kofar cikin gida, ta kwasa da gudu ta yi
ciki. Na cika da mamakin ganin ‘yan ‘Yan Leman yau a gidanmu, kada dai zancen Nadiya
gaskiya ne???
Ba su ce min komi ba, Ladiyo ta kama jikakken hannuna suka nufi sashen baki dani, ta hada
ruwan dumi cikin kwami ta yi min wanka irin wanda ba a taba yi min ba.
Ta tsefe birkitaccen kitson da ke kaina ta wanke min da ruwan kumfar wanke gashi na (Fa).
Ladiyo na cewa,
“Mu a wurin mu ai har haihuwa Sakinah za ta iya yi tunda mai manyan barage ce, a haka wani
sai ya ce ta yi shekaru sha biyar”.
Zainaba ta ce,
“Ni ba ina kamarta aka yi min auren ba? Me ya cini? In banda zamani da bature da ya lalata
duniya ai haka ya kamata al’ummar musulmi su dinga yi don koyi da Manzo (S.A.W); $$# da
zinace-zinace sun ragu, alfasha ta ragu, Allah ya yiwa Yaya Muntari arzikin duniya da lahira, ya
dubi niyyarshi ta alheri ya shirya mishi zuri’arsa ya zaunar da Sakinah a dakin mijinta har
abadan-abadan”.
Sai na fashe da kuka da dai na tabbatar zancen Nadiya ya tabbata gaskiya. Gidanmu za a bari
dani a kaini wani gida da ban sani ba.
Duk da izayar da Mami take min daidai da rana daya ban taba tunanin in bar gidanmu ba, wai
saboda wahala. Ni ina son ‘yan’uwana kamar yadda suke sona, bana fatan abin da zai rabamu.
Ladiyo ta ce, “Daina Kuka Sakinah, aure dole ne a kan duk wata diya mace. Sai in lokacin bai
zo ba, idan ya zo kamar habo yake, dole sai ya zubo, wato dole sai anyi ana so ko ba’a so.
Don haka ki daina kuka, ki yi addu’ar Allah ya baki aljannar da ake samu a dalilin aure”.
Kubra na tsane min dimbin gashin kaina da tawul ta ce,
“Wannan ango ya more, gashi kamar a India, kyau kamar a birnin Omani. Allah ya sa ki yi hali
irin na mahaifiyarki ba halin marikiyarki ba”.
Suka sanyani a tsakiya, Yaya Dije ta sa kakkaifar kibiya tana yarfa min kananan kitso suna ta yi
min fada, duk a kan zaman aure, wanda ban taba ji ba, ban taba kawowa wai nan kusa za a yi
min ba. Kallon komai da jin komai nake kamar almara.
Karfe shida daidai motocin daukar amarya suka iso. Wata daga cikin kawayen mahaifiyar ango
ta kawo wasu kaya cikin (kit), ta ce su za a sanyawa amarya, lefe sai daga baya don ba lokaci
basu kintsa da wuri ba”.
Zainaba ta ce, “Babu komai”. Ta karba ta bude, wani lallausar farin cotton lace ne da yarfin
ruwan kasar furanni da kananan (stones), a qalla kudin shi ya kai naira dubu saba’in, a dinke,
dinki na alfarma da haiba.
Sai wata laffaya ita ma ruwan kasa mai laushi da mannewa a fatar jiki. Yaya Zainaba ta sanya
min da saitin Dubai da warawarai masu nauyi mahadin set din guda hudu a hannuna na dama.
Tuni na fito a Sakinah ta, na yi kyan da ban taba yi ba. Ni kaina ban san ina da kyau ba sai yau.
Duk abin nan da ake Mami ba ta fito ba tana daki tana fama da kuncin rai, ta nunawa duniya
adawarta dani da bakin cikinta a fili, sannan ga bakin cikin ‘yan uwan Abba sun zo sun cika
mata gida.
Safinah ko ta yi nan ta yi can tana kara kawo kayan da za a yi min kwalliya. Bayan an gama
shirya ni an fesheni da turaren (Avon) aka kaini falon Abbana, ya ce da su Zainaba su jira a
waje yana son yin magana dani ni kadai.
Abba ya dube ni