Zuciyar Mutum Book Complete By Sumayya Abdulkadir Takori .pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Taskar Novels

Chapter   5 / 7

12K to 15K   out of 19.8K words

ina ta kuka cikin yadin laffaya, kuka nake haikan kamar raina zai fita. Abba bai
yi magana ba har sai da shesshekar kukan ta tsaya mini na yi shiru. Ya sauko daga kujerar shi
ya dawo gabana ya zauna a kan gwiwoyinsa ya ce.
“…..Sakinah ‘yar Sakina-ta, jikar Liman Tukur!”

Na yi saurin dagowa na dubi Abba domin ji na yi yana magana da wata murya mai wani irin
amo tamkar ba tashi ba. Sai na ga hawaye suna gudu a kundukukin shi, yana kuma murmushi
duka a lokaci daya.
Ya ce, “Yau ce rana ta biyu da zan kara dandanar wani bakin ciki da farin ciki duka a lokaci
daya. Bakin cikina shi ne, zan rabu da Sakinah…. mai tuna min da Sakinah ta. A kan dole ba
don na so ba, ba don ta kai munzali ba sai don hankalina da nata ya kwanta.

Farin cikina shi ne, ban kai Sakinah mugun hannu ba ko hannun da za ta tozarta ba, na kaita
hannun da nake da yakinin cewa da nawa da shi duk daya ne. Ko bayan rai na.
Sakinah ki yi hakuri na yi gaggawar yi miki aure a lokacin da baki isa ba. Ban yi hakan don cutar
dake ba, sai don hankalina da naki ya kwanta. Don kullum zan fita daga gidan nan cikin
fargabar halin da kike ciki nake, wanda har hakan ya shafi lafiyata.
Sakina na yi duk iya kokarin da zan iya in mai da ke ga Mamanki in ba ta amanarki, amma
hakan ya ci tura, don haka ne a karshe likitana ya bani shawarar in yi miki aure don hankalina
ya kwanta naki ya kwanta, wanda nake fatan ni da ke mu ci ribarsa a duniya da lahira.

Na aurar da ke ga dan aminina Alkali Khaleel Ribadu. Ga nan sadakin ki”.
Ya debo kudin da Tasi’u ya tattaro a falon Mami ya danqa min cikin hannuna, ya kara da cewa.
“Ki yi abin da kike so dasu don hakkinki ne, ki zamo mace ta gari kamar mahaifiyarki Sakina.
Halayenki na kwarai da na sanki dasu su zamo jagoranki a gidan aure.
Allah ya yi miki albarka Sakinah, Sakinah Allah ya yi miki albarka. Na yafe miki duniya da lahira,
nima ki yafe mini rayuwar kuncin da kika rayu cikinta a gidana na kasa daukar wani mataki a
kai.
Allah kadai ya san cikin halin da nake rayuwa, ina neman waraka daga gareshi, ki dinga sanya
ni cikin addu’arki a duk lokacin da kika yi sallah, kin ji Sakinah?”
Na gyada kai, na fyace majina da gefen laffayar. Ya ce,
“To tashi ku je, ina kara cewa ALLAH YA YI MIKI ALBARKA!”

Yasa murya ya ce, “Zainaba!” Ta shigo da sauri. Ya ce, “To ku je sai kun dawo. A bar Inna
Ladiyo ta yi sati tare da ita don ta saba ni da kaina zan maidota ‘Yan Leman insha Allahu”.

Cike da mamaki suka ce, “To”. Suka amince lallai ba abin da ya fi karfin addu’a. Addu’ar da
suke kwana da yini yi a kan dan’uwansu, yau Allah ya karba ya fara juyo musu da hankalin
dan’uwansu.
Zainaba ta yi mishi murmushi, shi ma ya yi mata. Sai ta ji hawaye sun ciko idanunta. Don haka
ta yi saurin kama hannuna muka fita inda motocin daukar amarya suke jira a harabar gidanmu.
[9/14, 9:59 PM] Asmau: Na ce, “Shi ba a yi masa aure ba?” Ya yi dariya, ga dukkan alamu
Abdulhakim gwanin dariya ne, abin dariya bai da wuya a wajensa, ko kuma yarintar amaryar
tashi ce ke ba shi dariya da sanya shi nishadi?Allah A’alam.

A yadda ya fahimta ba ta san mene ne mijin ba, baya ga abokin hira, kuma yana jin dadin
hakan. Gaskiyar Hajiyarshi ne Sakinah yarinya ce danya sharaf, ba ta san komi ba sai abin da

zai koyar da ita.
Ya ce, “Shi ba a yi mishi aure ba Sakinah, saboda yarinyar da yake so ya aura ba ta son shi”.
Na ce,
“Ba sai ya rabu da ita ya nemo wata ba?”
Ya murmusa ya ce, “Gane min hanya dai matas, nima akwai wata wadda nake so mai kyau
sunanta Farida, amma iyayenta basa sona saboda ni ba millonnaire bane. Da na hakura ba
gashi Allah ya bani Sakinah ba? Wadda ta fi Farida kyau da komai?”
Na dube shi sosai na ce, “Ba wanda ya taba gaya mini haka cewa ina da kyau, sai na dauka ni
bani da kyau irin na Safina”.
Ya yi murmushi ya ce, “Wace ce Safinah?’
“Safinah Yayata ce”.
Ya ce, “Kin fi Safina kyau Sakinah, duk da ban ganta ba, don dai ita babba ce, ta san yadda
zata gyara kyanta, kema in kika girma za ki kara kyau fiye da wannan da kike da shi”.
Ya debo fried-rice a cokali ya ce, “Bude bakin matar Abdulhakim”. Na bude cikin murmushi ya
saka min na tauna, ya lumshe ido yana kallon taunar matar shi very gently. Yana kallon
wadannan kissable lips da ‘beauty point’ din da ke lotsawa ciki sosai ayayin taunarta. Ga uban
gashi cunkus dunkule cikin tafkeken ribbon na larabawan usli. Wani al’amari ya soma zarya
cikin wasu sassa na jikinsa da bai taba ji a rayuwarshi ba.
To amma ya yi alqawarin rainon Sakinah ne, har sai ta zama mutum kamin ya mai da ita
cikakkiyar matar aure.
Ya ce, “Kin iya girki Sakinah?” Na daga kai, “Amma Mami ta ce jagwalgwalo nake yi”.
“Ke kika yi wannan girkin?”
“A’a, bani ba ce wancan kabilan da Hajiya ta kawo ne”.
Ya ce, “To daga yau in zan zo zan yi miki waya in gaya miki ki yi min duk irin jagwalgwalon da
kika iya shi nake so. Bana son na Uche, kina jina?’
Na daga kai.
“Kin ga da kamin ki zo Hajiya ce take yi min da kanta, sai dai ki dinga yi a hankali kada ki kone.
Ki daina kallon fadan Larabawa tunda kuke suke sa ki”.
Na girgiza kai, “Ai Abba ya gaya min Mamana tana can, shi yasa nake son su”. Ya dube ni sosai
ya ce, “Wace kasa ya ce miki?”
Na ce, “A Libya”. Ya ce, “Na yi ta tunani tun dazu kan jinsin da matar Abdulhakim ta fito, ashe
Sakina-ta babban tsatso ne. Na kara GIRMAMAKI, na kuma kara GIRMAMA zaben Babana.
Haka na kara son sa, sannan na yi nadamar wautar da na so na yi a baya, na kuma yi alqawari
Sakinah watarana zan kai ki Libya idan mun samu adires a wurin Abba...... Manzon Allah (S.A.W) yace “ku so larabawa sabida abu uku; na daya ni balarabe ne, na biyu
Alqur’ani balarabe ne, na ukku harshen ‘yan Aljannah shine larabci”.
Ban san sanda na kamo hannunshi ba ina murmushi, kamin hawaye su ballo su mirgino. Ba
wanda ya taba gayamin kalaman da suka farantamin a duniya irin wadannan bayan Abbana,
ya kai hannu yana share min ya ce,
“Kada ki yi kuka, bana son hawayenki, tukuicin da nake so ki yi min idan na kaiki Libya shine, ki
tsaya ki yi karatu, ki bani sakamakon da zan yi alfahari da ke.
Dazu Daddy ya yi min zancen makarantarki, don haka zan kai Monday don in kai ki. Sai dai ina
so ki kula da kanki Sakinah, ki sani da da yanzu ba daya bane, yanzu ke babba ce tunda kina

da aure.
Ba ruwanki da kawaye barkatai, ki mai da hankali kawai kan abin da ya kai ki, ki kawo min
kyakkyawan sakamakon da zan ji dadi. Kina jina matar Abdul?”
Na ce, “Ina ji Mijin-Sakinah, kuma na yi alqawarin zan yi abin da ka ce”. Ya shafa gashin kaina
ya ce,
“Na gode”.
Har dakina ya rakani, Ladiyo tuni ta yi barci a dakinta. Sai da ya ga kwanciyata ya ja lallausan
bargo ya rufe ni, ya kashe lantarki ya bar min na gefen gado mai raunin haske.
Ya yi kamar zai sumbaci goshina, ko me ya tuna? Kuma ya fasa. Ya yi min murmushi ya ce,
“Good night”. Nima murmushin na mayar masa, mai nuna jin dadi da kulawar shi.
Da baya da baya ya fita daga dakin, ya maido kofar ya rufe. Na lumshe ido barci mai dadi ya
fizge ni, cike da mafarkai masu dadi, duk rabi a kan Abdulhakim din da ya kirayi kanshi da mijin
Sakinah.

****







Agogon alarm da na saita shi ya tashe ni, na gabatar da sallar asubahi. Ina lazimi bisa darduma
barci na dibana kadan-kadan, na ji an murda kofar an shigo.
Mijin Sakinah ya bayyana a dakin cikin farar jallabiya da carbi a hannunsa. Wani lallausan
qamshi ya bakunci hancina.
Ya zo ya tsugunna a gabana, tuni barcin ya wartsake, na yi murmushi na ce, “barka da asubah
an tashi lafiya?” Ya ce, “Ai ni ban yi barci ba matas sai tunaninki”.
Na rufe fuska da hijabina, ya rike gefen hijabin ya ce, “Na roke ki, ki daina yi min wannan rufe
fuskar, kinga ni da ke yanzu we are one. Tashi muje kicin mu yi abin karyawa kafin Baba Ladiyo
ta tashi”.
Na ce, “To, jeka waje in cire rigar baccin”. Ya ce, “To, na yi waje”. Ya fita.
Na mike na canza rigar barci na da pakistan ruwan madara, na je toilet dina da ke manne a
dakin na yi brush yadda na saba na kuskure bakina da ‘listerine’, sannan na cimmashi a kicin
har ya soma firar dankali.
Na ce, “Ai akwai na’urar fere dankali”. Ya ce, “To kawo”. Nan da nan ya kammala na zuba mai a
‘fryer’ na kunna. Nan da nan muka gama sassauqan karin kumallo.
Soyayyen Dankali ne chips da plantain, sai soyayyen kwai da ruwan lipton, na kwaso na kai
dining yana biye dani da flask din ruwan zafi. Daga nan muka yi daki kowanne ya nufi toilet
dinsa don ya yi wanka.
Cikin kayan da Hajiya ta bani matsayin lefe na zaro wata lallausar super ruwan kwaiduwar kwai
da ratsin blue, na fesa turare ‘Azzaro Visit’, na taje sumata na hadeta waje daya a tsakiyar
kaina. Sai ban daura dankwalin ba na kawo dan karamin gyale na nade kaina na matse da fil.

Na fito dining na zauna ke nan sai ga Mijin-Sakinah ya fito, wannan karon cikin kananan kaya,
bakin wandon jeans da shirt din Armani, sai qamshi yake.
Ban taba jin wanda ke qamshin Abdulhakim ba, turarenshi na daban ne, haka komi nashi is
special kamar yadda shi din ma yake na daban, da sauran al’umma dana saba gani.
Ya ja kujera kusa dani ya zauna, kafadunmu na gugar na juna. Har yanzu ban daina kallon shi
ba. Ya murmusa ya ce,
“Wannan kallo haka matas?’
Na yi murmushi tareda saurin dauke ido a kanshi na ce, “Ka yi kyau ne”. Ya ce, “Allah ko
matas?’ Na ce, “Allah da gaske”. Ya ce, “To ai ban kai ki ba”. Na ce, “Allah ka fini”. Ya ce, “A’a,
ban da washi Sakina-ta”.
Aka danna kararrawa ya je ya bude, suka shigo tare da Abdallah. Ya ce, “Wane irin sammako
ne haka Abdallah?” Ya ce, “Don ka samu abokiyar hira ni sai ka manta dani bayan ka san ni
bani da kowa”.
Ya yi murmushi ya ce, “To ka yi zuciya mana? Kai ma ka samu mai tayaka hirar”. Bai ba shi
amsa ba ya ce, “Amaryarmu wane delicious aka shirya mana?” Ya fadi yana bude filet din.
Mijin Sakinah ya ce, “Ci ne fa da shi uwa rumbu, yanzu in kika yi wasa sai ya tashi da dukkan
abincin nan”.
Na yi murmushi na ce, “Ba zai iya cinyewa ba”. Ya ce, “To sa ido ki yi kallo”. Abdallah ya ce, “Ki
dinga yin girki dani Sakinah in ina nan, gwauro sai da taimako. Don Hajiya ta hanani ta ce nima
in yi zuciya in yi aure”.
Na ce, “Ai gaskiya ta fada, in wadda kake son ba ta sonka, ni ina da kanwa mai kyau zan baka”.
Ya hangame baki yana mamakin inda naji wannan zancen ya dubi Abdulhakim yana girgiza kai
ya ce, “A’a, Sakina bana son ‘yar kwaila, ke kanki nawa kike balle kanwarki?
Barni da Safiyyata in nan ina lallaba ta a hankali za ta so ni”. Na ce, “To Allah ya sa”. Mijin
Sakina dai cin abincinshi yake bai sa mana baki ba.
Uche ya zo ya kwashe kayan ya yi kicin dasu. Inna ta fito suka gaisa suka fita tare da Abdallah.
Na kaiwa Inna abincinta har dakinta na zauna muna hira.
Ta ce, “Tunda maigidan ya dawo ni ya kamata in koma ‘Yan Leman gobe insha Allahu”. Nasa
mata kuka na ce, “Nima wallahi ba zan zauna ba sai dai mu tafi tare”.
Kuka nake kashirban. Ta ce, “An taba haka Sakinah? Nima nawa tsohon angon jirana yake yi,
muje mu lallaba tsufanmu. Ga mijinki yaron kirki mai son mutane da girmama su, auren ke nan
Sakinah, kowacce mace haka ta gada”.
Na sake tsananta kukana, “Ai ba zama zai yi ba, ya ce ran Monday in ya kaini makaranta zai
koma”.
Ta ce, “To bari ya dawo sai mu yi maganar ko wata ce ba sai a samo miki ba, amma ni zamana
har yaushe?”

Suna tafe cikin motar Abdulhakim, sanyin raba na ratsa su. Wani nishadi ne na musamman
tattare da Abdulhakim Khalil Ribadu. Wanda dan uwansa Abdallah bai taba ganin sa cikin
kwatankwacinsa ba. Abdallah ya dube shi yana murmushi ya ce,
“Yar yarinya ta ci gari ga dukkan alamu”.
Shima ya yi murmushin ya ce, “Kasar ta ci gaba daya ba garin ba. Abdallah, sai yanzu na gane
son da nake yiwa Farida ba natural bane, burgewa ce da sha’awa. Ga son da nake ji har cikin

kashi da bargo ba kuma don wani dalili ba, sai Allah da ya sanya mini.
Abdallah na kamu da love at first sight na yarinyar da ba ta gama sanin kanta ba balle ta san
ina yi”.
Abdallah ya ce, “Nima na lura da hakan, shi yasa ake so mu zamanto masu biyayya ga
iyayenmu, don ba za su taba yi mana abin da ba alheri bane a garemu. Na gode Allah da ya
ganar da kai da wuri da ka zo kana dana sani wadda ba ta da amfani”.
Daidai sanda suka iso ofishin Daddy cikin federal high court, kan wasu takardu da ya ce ya
debo masa don ranar ta kasance lahadi babu aiki.
Ya yi parking a inda aka tanada don adana motoci, shi kadai ya shiga ya dakko ya fito suka
juya. Ya tsaya a wani kasaitaccen shago cikin wata Plaza suka shiga tare.
Sayi banza sayi wofi duk bai san dalilinsu ba, duk saboda Matar Abdulhakim. Ya yi mata
shopping mai yawa da tsada, sannan suka juyo gida.
Ya tarar da ni na ci kuka na qoshi duk a kan sai Inna ta zauna da mu. Ya zauna dab da ni ya
kama hannuna ya ce, “Ni ba kya son zama dani Sakinah?”
Na yi shiru ina share ido. Ya ce,
“Ki bi Inna tunda ni ba kya so na”. Ya fadi cikin alamun hushi, don lallashin karamin yaro.
Inna ta ce, “Rabu da rigimar Sakinah, tafiya ba makawa gobe zan yi ta”. Ya ce, “A samo wata su
zauna tare mana”. Inna ta ce, “Sai dai uwarta Suwaiba, tunda ita maigidanta ya rasu, idan na
tafi gobe ita za ta zo jibi”.

Abbana da kanshi ya zo daukar Inna, murna a wajena kamar-kamar me. Na kama shi na
rungume abin da ban taba yi ba a rayuwata, saboda ban isa ba, ban kai wannan matsayin ba.
Sai yau da ya zo da kafafunshi gidan aurena, inda nake da ‘yanci. Mijin Sakinah ya cika da
mamakin ganin kukan da nake saboda ganin Abbana, maimakon in yi farin ciki. Abba Ya kawo
kudi masu yawa ya bani, ya kuma godewa Abdulhakim makaranta da zai mai dani.
Ya ce, “Suwaibar ma ba za ta zo ba rana ita yau daurin auren shi da ita, amma za a samo min
mai aiki a can ‘Yan Leman su taho tare”. Da wannan suka lallaba ni suka tafi.
Shi ma Abdulhakim fita ya yi tare da su. Bai shigo gidan ba sai karfe tara na dare. Ina falo ina
sana’ar tawa (kallon Larabawa). Ya sa ‘remote’ ya kashe, na daga ido a hankali ina kallon shi.
Ya karaso ya zauna gefena bayan ya ajiye ledojin da ke hannun shi. Ya juya min baya ya ce,
“Fushi nake dake Sakinah”.
Na ce, “Ai ina son Inna ne”. Ya ce, “Ni ba kya sona?’ Na girgiza kai, “A’a, ina sonka”. Dariya ta
kama shi amma ya gintse, saboda yadda na fadi, “Ina sonka”, din kadai zaka karanta tsabar
kuruciyata karara. Sannan ban san wane irin so ma yake nufi ba.
Ya janyo ledodin dake gefe ya bude ya soma zaro tsala-tsalan kayan dake ciki riga da wando,
siket da riga, dogayen riguna da abaya kala-kala.
Ya ce, “Duba ki gani za su yi miki daidai?” Cikin murna nake karasu a jikina ina cewa, “Sosai ma
kuwa, na wane ne?”
“Na Sakinah ne, mijinta yana so ta dinga sanyasu a gida tana yi mishi kwalliya”.
Na kyalkyale da dariya na ce, “Na gode, Allah ya kara budi”.

Ya ji dadin addu’ar da na yi mishi. Ya kama tafukana ya rike cikin nasa ya ce,
“Gobe zan koma Sakinah, I will miss you so much…., ko za ki bini?’

Na ce, “Makaranta fa?’
Ya ce, “Hup! Na manta ne, in ina tare dake sai in manta komai”.
“Za ka dawo wani satin?’
Ya ce, “A’a, sai sati na sama saboda zan je Ibadan kan Shimfida wani titin jirgin kasa da zamu
yi”.
Na ce, “Titi kake ginawa?”
Ya yi murmushi ya ce, “Ni magini ne Sakinah, ba abin da bana ginawa. Tun daga makarantu,
jami’o’i, gidaje, ma’aikatoci da asibitoci kin gane?”
Na daga kai. Ya ce, “Nima in tambaye ki, me yasa dazu

5 / 7